Chp(27)wannan din menene?

51 7 0
                                    

(The legendary novelist),🌄🌄

(The legendary story)
📒💎↗↗🎿👿👽
written by💟 SADY-SAKHNA💟
     
💎💐  ..... WATA RAYUWA....💎💐

phone number:09035784150

telegram :https://t.me/joinchat/-_Qs5O8XH6cwYjQ0

whatpad :@SAKHNA03

  ......Dedicated to proficient writer association........

Chp(27)
Saida sukayi tafiya mai dan nisa kafin suka tsaya suka huta sannan suka cigaba da tafiya.
Kwanci tashi har su fahreeyah suka isa masarautar sardaham,saidai kowa kagani acikin bayin bazaka ce zai rayu ba saboda tsabar wahalar dasu ka sha a hanya.
Wajen bangaren bayi aka nufah dasu tareda sauke kayan da kuma basu dama su huta kafin lokaci yayi,kowa idan zai wuce sai ya kalle su saboda ko a cikin bayin ma su Kaskantattune wanda kowa zai iya musu abinda yaga dama,saida suka gama hutawa aka debesu zuwa sashen gimbiya nasreemah wato sirikar sarki huruddeen
***mai karatu inbaku manta ba munfara tabo labari daga cikin masarautar sardaham kuma da ikon allah zamu cigaba da shi a gaba kadan****
Zuba su akayi a farfajiyar wajen domin tsimayin zuwanta.
Bayan wani lokacine wata baiwa tafito tareda sanar dasu cewar gimbiya nasreemah bazata samu damar fitowa ba saboda tana hutun gajiyar hanya akaisu cikin bayi dasuke kulada hidimomin sashenta.
Dakine mai girman gaske wanda aka cikashi da yayin ciyawa saboda kwanciya,suna shiga daki dayar da suka zo tare ta kwanta rilif kaman kayan wanki,samun waje fahreeyah tayi ta zauna tana nazarin yanda rayuwarta ta kuma kasancewa ,maganin da inna kainana ta bata ta tuna,inda tafito dashi tana kallonsa acikin wata yar kwalba har takai baki zata sha saikuma ta tuna yanzu babu abinda take bukata sama da hutu sannan idan ta sha kuma fah aka samu matsala,gwanda ta bari idan tasan muhallinta saita sha.
Washa gari da wuri aka zo aka iza keyarsu itada sauran bayin zuwa wajen uwar bayi,a tsaye take sai kuma gimbiya nasreemah a cikin rumfa akan kujera bayi sunayi mata fiffita,kara zuba su akayi kaman jiya a kasan wajen,inda gimbiya nasreemah ta umarci uwar bayi da ta ware wanda za'a kaiwa surukarta ,hakan kuwa akayi ,sannan tasake nuna wasu guda biyu daga cikin maza wanda zasu na kula da dawakan da'aka bata daga gidannasu,uwar bayin ce ta nuna wasu kuma tace akai bangaren babbar sarauniya,wasu kuma akai bangaren mahaifiyar mijinta,wanda ciki harda fahreeyah.
Wata mata ce ta musu umarni su biyota inda suka farayin wata hanya daban,sun danyi tafiya mai nisa kafin suka zo sashen daza a kaisun,alama ta musu su dakata bari tashi ga ta dawo,basu wani dade ba tace musu su shigo,a kasan falon suka zauna ita da wasu maza guda biyu suna ware idanuwa,wata yar dattijuwar matace tafito wanda take daukevda kamala akan fuskarta,samun waje tayi ta Zauna akan kujerar inda suka fara gaisheta tana amsawa,
"Ahh nasreemah ce ta aiko a kawomin?"
Ta tambaya tana kallon Wanda ta shigo dasudin,
"Eh rank I yadade"
"Allah sarki toh kice mata nagode sosai,ansha biki kenan,su nameemah an tafi daki,toh wannan mazan ki kaisu wajen yan barga mana dama aikin yayiwa wanda suke yi din wahala,ita kuma Wannan"
Tafada tana nuna fahreeyah
"Ya sunanki yarinya?"
"Sunana fahreeyah tul Sharmeelah,"
"Ayyah,ki kaita wajen su jaliyyah ko goge goge saita tayasu na wajen abinci"
"Iyah goge kuma ranki ya dade,acikin kaskantattun bayi fah take sai a bata wannan karamin aikin"
"Banason kina irin wannan maganar da kanku,toh kuma kuna kokarin musgunawa junan ku a matsayinkku na bayi to saiku ga laifin iyayen gidanku idan sun muku?koh wanne mutum yanada baiwa kuma yana da daraja sannan baki san mai dan adam yake dashi ba ,watakila allah ya kaita matsayin daya fi naki watarana,kuje ki kaita inda nacemiki kuma vanason naji wata magana ta fito"
Ta shi tayi sum sum taja fahreeyah sukayi sashen inda bayin sarauniya safeenah suke,tana shiga suka dago suka kalleta,tareda maida kallonsu zuwa kan fahreeyah.
"Wannan itace baiwar da aka kawomuku dan ta tayaku aiki,saidai karku ragamata saboda akanku take ,a cikin kaskantattun bayi take,duk wani aiki ku bata tayi dan hakanne aikinta"
"Angama shugaba"
Suka fada a tare, kallon fahreeyahn tayi tana Murmushin mugunta sannan tace,
"Harda sarauniya zata hadani dake,toh karki taba mafarkin kamoni a matsayi vare kuma kifini,ke kaskantacciya ce kuma haka zaki Zauna"
Tana gama fada ta wuce ta bar wajan.Jaliyyah ceh ta tashi daga kwancen datake tace,
"Shikenan ma ,dama yanzu nakejin kyiwar tashi zuwa yin wanke wankennan,dan haka maza ki sanja kayan jikinki na karamar masarautar nan kije ki wanke su,babu wanda yayi magana a wajen saboda Jaliyyah itace shugabar bayin da suke karkashin sarauniya safeenah,wanda ta karbi shigabancin da karfin gaske,saidai suma suna ganin zasu huta tunda aka kawo wanda suma suka fita.
Tsugunnawa fahreeyah tayivta dauki kayan da Jaliyyah ta wurgo mata kafin ta tambayesu bandaki cikin sanyin murya,kaman bazasucamsa mata ba saikuma wata acikinsu tayi mata nuni da bandakin da hannunta,bin hanyar tayi har ta isa bandakin.
Shiru tayi kaman mai nazari tana tsaye a bandakin ,sai kuma tafara cire kayan dake jikinta,maganin da inna kainana ta bata ne ya fado daga cikin kayan jikinnnata,inda ta dauka tana juyashi sai kuma tace,
"Ohh allah na manta da maganinnan,kuma tacemin inna zo nasha,wayasani ma ko maganin gajiya ne inaga,saboda tasan zan gaji idan nazo,allah sarki innah,allah yasakamiki da taimakon da kika min"
Dan goge hawayen daya zubo daga fuskarta tayi kafin ta daga maganin ta shanye dukka saboda ya mata maganin gajiyar da take jikinta,karar bugun kofah taji wanda hakan ya ankarar da ita ashe a bandaki take,sauri tayi ta gama saka kayan da aka bata ta fito tana sunkiyar da kai,mtswwww,matar data buga kofar taja tsuka kafin ta buge fahreeyah ta shiga bandakin,ajiyar zuciya ta saki da abin yatsaya iya haka ma kafin ta wuce inda akace wanke wanken yake.
Zaro ido tayi da taga yawan wanke wanken da zatayi kuma ita kadai,saidai ganin ba sarki sai allah,sannan kuma inta zaya wankin babban bargo zai kaita dare ,sai kawai tafara wankewa.
Ta dau wasu Dan lokaci tana wanke wanken can kuwa sai taji cikinta yah murda kaman wanda aka saka abu aka daure shi,wata kara ta saka mai huda kunnen mai sauraro,tareda zubewa a wajen tana rike cikin,alamar motsin mutum ta ji daga nan kuma bata sake jin komai ba sai duhun daya lullube ganinta.
Bude idonta tayi sukayi arba da daya daga cikin yar dakinnasu,saidai wajen da suke zaune ba dakinnasu bane,kallon ta take itama tana kallonta,murmushi tayi mata tareda tambayar ta yajikinta.
Fahreeyah batayi mata magana ba sai gyda kai da tamata alamar taji sauki,
"Sunana khairiyyah nazo wucewa ne naji karar da kikayi lokacin danazo kuma har kin fadi,kwanan ki uku kenan kina sume na karbo maganine a wajen wata uwar dakina na shafa miki,ga kuma abinci kici"
Tafada tana mikawa fahreeyahn wani
abinci acikin akushi,ganin taki karbane kuma tana kallon wajen sai tace mata,
"Karki damu babu abinda zanmiki,abinda yasa nakawoki nan kuma saboda karva gane bakida lafiya,dan idan akasan daga zuwanki kin fara rashin lafiya za'ayi zaton kina dauke da wata cutar ne,yanzu kici abincin saimu tafi,bazan cutar dake ba"..........................
Hannun ta fahreeyah ta riko da karfi jin yadda cikin ta yake juyawa ,itama khairiyyah riketa tayi tareda tambayar ta,
"Wannan din menene??"

Ohhhhh!!!!!!!!!!😊😊😊😊

SADY-SAKHNAceh❤❤❤

Wata RayuwaWhere stories live. Discover now