37

4.4K 489 129
                                    

UWA UWACE...37

Batul Mamman💖

{Fatan alkhairi ga masu bibiya tare da hakurin jiran post. Ba zan gaji da bayar da hakuri ba. Ciwon hannu ya sakoni a gaba. Wadanda muke group tare da masu turo sako private duk sun daina ji na sai jifa-jifa. Sakonninku birjik a whatsapp da wattpad harma da instagram amma dubawa ta gagareni. Masu kira Allah Ya saka muku da alkhairi. Babu dama na daga waya sai nayi jinyar hannu. Ina kan magani yanzu kuma Alhamdulillah sauki yana samuwa. Shi yasa nake ta lallaba hannun. Na so kwarai sai na kammala tas kafin na kara post. To amma na sami kiran wasu da sako wadanda suka ce na turo abin da ya samu ko babu yawa. Bana son zama mai karya alkawari tunda na kan ce na kusa a yayinda nake jin saukin hannun. Da zarar ciwo ya dawo sai na bar rubutun. Ku kara hakuri mu lallaba har mu kai karshen Uwa Uwace.}

For THE QUEENS, because they deserve it. Na gode


***

Abbati ya zagaye gidansa yafi a kirga. Babu wani lungu da sako da bai leka ba bayan fitowarsa daga wurin Baaba Mari. Akwai wuraren da rabonsa da taka kafarsa tun ana ginin. Wasu irin tunane tunane suka dinga zarya a cikin kansa. Son muhallin nasa ya darsu a zuciyarsa irin wanda bai taba ji ba. Sai idanu sun zaga sosai a cikin garin nasu ma za a sami gida makamancin nasa. Lallai shi yasa ake cewa idan an ga matashi da kudi bayan bashi da kwakkwarar sana'a ya kamata a bincike shi. To wai ma ya aka yi bai taba jin korafi ko da wasa game da tarin arzikinsa da wadak'ar da yake da kudi ba a garin? Ko ana tsegungumi a bayan idonsa ne bai sani ba? Yau daya da ya yiwa gidan kallon tsanaki sai ya fahimci yawan titsiyen da Baaba Mari take yi masa akan wurin aiki. Wajibi ne uwa ta matsu da son jin silar rayuwa irin tasa. Ga gida ga motoci ga kudi kamar bai san ciwonsu ba. Samarin garin da dama idan sun kawo kawunansu ko iyayensu sun musu jagora akan ya saka su a hanyar sana'arsa sai da ya cikasu da kudi. Ana karbe kudin zaka ga mutum ya ja gefe an koma kasuwanci ko a cinyesu a banza. Ya gode Allah da ya kasance ba shi da alhakin sanya d'an kowa a layinsu. Da yanzu bai san yadda zai yi da lodin zunubai ba. Ga nasa da yake fatan samun gafara ga na wasu da babu lallai su so tuba.

Kan kasaitacciyar kujerar kushin din dakin da aka yi domin kwanciya ya tafi ya kwanta rigingine. Tunani bai barshi ba har ya luluka yana tuna masa yadda aka yi suka kawo zuwa yanzu. Yayinda Munzali ya zama mukullin bude masa wannan duniyar, shi Abbati, shi ne ya fara mayar musu da ita sana'a a lokacin da Munzali ya kwanta ciwo. Shi ne ya nemi Shazali wanda ya kaishi wurin wani babban mutum.

Tunanin komai da kowa ya yakice ya sanya kansa a faifan zuciyarsa yana tuhuma. Shin yana wannan dabiar ne a matsayin sana'a ko matsayin namijin da yake jindadi mu'amala da jinsinsa? Amsarsa ita ce zabi na biyu. Hakika ya yi mugun sabo da wannan dabi'a wadda ta sanya har yanzu sha'awar mu'amalar ta kan taso masa. A kalla kusan bayan kwana bibbiyu ko uku ya kan sami kansa a mugun yanayin son wannan abu. Yana jin wahala har ma ya kai ga siyan magani don wani zubin ko bacci kasawa yake. Haka kuma take a wurin Munzali shi ne ma dalilinsa na biya musu makudan kudade domin samun lafiya. Matsalar irin wannsn zinar ya wuce mutum ya tashi watarana kawai yace ya tuba. Ita jiki take bi tana yi masa illah. Idan bukatarta ta taso mutum dole ya nemi hanyar biyanta ko ya wahala. Allah ne shaidarsu amma rabonsu da neman juna tun gabanin ciwon Munzalin. Shamaki ne Allah Ya saka musu sannan Ya maye musu zukata da tsaftatacciyar kaunar juna domin lokaci irin wannan.

Duk wannan abu zuciyarsa bata fasa fada masa cewa shi din har yanzu namiji bane. Soyayya dai ta zuciya da zuciya Farha yake yiwa. Tunaninta kadai sai da yasa tsigar jikinsa ta tashi. Yana sonta da dukkan abin da zuciya za ta iya bawa wanda take kauna. Burinsa na duniya akan mace ahi ne ya mallaketa a matsayin matar aure. A wayi gari wasu yara suna kiransa Baba suna kiranta Mama.  Duk mazan da yake mu'amala dasu kallon maza yake yi musu. Mata kuma suna nan a mata. Bai taba sanya kansa a ajin 'yan daudu ko wadanda suke karyar cewa da son jinsinsu aka haifesu ba. Shi lafiyayyen namiji ne wanda ya mayar da kusantar maza 'yan uwansa sana'a. Idan babu namiji zai rayu sarai da mace sai dai kawai illar wancan abu zai dinga damunsa kafin Allah Ya yaye masa jarabar. Infact yana daga cikin dalilansa na cigaba da zama da Hanne duk irin rashin dadin zamansu kuwa. Tuntuni auren ya wuce na umarnin Mal. Sa'idu, domin kuwa a irin kudinsa da ya saketa idan har da mai ce masa don me ba zai wuce Baaba Mari da Gwaggo Jummai mahaifiyarta ba. Sauran kowa so yake ya zo ya auri tasa 'yar. Abin da ya hada auren nasu ma tuni an manta dashi. Shi da ita suna zaune ne kawai saboda auren rai gareshi. Babu soyayya, babu shakuwa sannan babu damuwa. Gara ma shi yana bata kulawa domin sauke nauyin hakki. Ita kuwa tsakaninta dashi bai wuce kudi idan har ta neme shi. Ga misali yanzu rabonsa da gida tun asabar daga zuwa daurin aure. Amma har yau ko flashing bata yi masa ba.

UWA UWACE...On viuen les histories. Descobreix ara