page 39

111 5 0
                                    

🅰 *S🅰N🅰DIN GROUP*🙊🙊

*Written by*
 
💅💅 *SADNAF*💞

  *PURE MOMENT OF  LIFE WRITERS*

    _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

*A short story based on true life story*

*WANAN SHAFIN NAKU NE MASOYANA ABUN ALFAHARINA INA MUTUK'AR JI DAKU,FHAREEDAT SWREERY,HAUWA SARAUTA, MAIMUNA NIGER,ALLAH YA D'AUKA KA KU YA BIYA MUKU BUKATUNKU NA ALHERI*🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

*BAN MANTA DAKU BA*

*AISHA ALI *GARKUWA*
*MEELA ADEEL*
*SHOLINGAYE*
*MINASH*
*MAMAN FADEEL*
*MASHKURATA*
*AUNTY MAMY*
  *AMNOOR*
*MARYAM I GITAL*

*KUNA RAINA SOSAI ALLAH YA BARMU TARE*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Page:-* 39

Ton G sabida tsabar wahala ido kawai ya gwallo yana gyad'a kai wayar Yusuf ya mik'a mishi cikin rawar jiki yafara kiransu bad boy,yanda Yusuf ya tsare shi da ido ne yasa ya daidaita muryashi,sai da ya tsara abakonan nasa ya zuga su akan au taho da sassafe zasu ji dadi ga kud'i mai tsoka su kuwa abokanan nasa dayake suna da Rabon shan bulala murna suka ringa yi suna da asuba zasu taho,fisge wayar Yusuf yayi daga hanunsa bayan da ya gama wayar yace Dan iska kawai zakuci ubanku yayi hanyar waje ya rufo k'ofar,yana fita Ton G ya fashe da kuka yana tab'a wawulon bakinsa da hak'ora biyu suka zube.

Yusuf kuwa aranar matsuwa yayi gari ya waye yaci ubansu Hajja Kaltume,

Inda b'angaren Hajja Kaltume taga kamar lokaci baya tafiya Dan ta matsu ta duro kano ta ji dadi.

B'angaren su Manal kuwa ba ita ta farka ba sai wajen sha d'aya na dare a lokacin su mustapha na zagaye da ita har da Mallama Rabi ta buga uban tagumi tana kallon Manal,Manal sai da tabisu da kallo d'aya bayan d'aya ta juya musu baya ta fashe da kuka,kuka take sosai kamar ranta zai fita Dan kunya take ji,ji take kamar ta mutu,duk kallon tsana taga 'yayenta na mata,babu Wanda yayi yunkurin rarrashinta,ahaka ta cigaba da kuka wajen sha biyu su Mustapha suka mik'e suka fara yiwa mallama Rabi sallama,Mallama Rabi ita kadai suka bari da affan a asibitin,Manal kuwa sai da taga sun fita ta juyo da kanta,Had'a ido suka yi da Mallama Rabi tayi sauri ta sunkuyar da kanta.

Sunkuyar dakai tayi
Hawaye na zubo mata,Mallama Rabi ido dai ta zuba mata bata ce komai ba,har yanzu gani take kamar mafarki take yi, Manal bazata tab'a iya aikata haka ba, Manal d'aurewa tayi tafara magana "Umma kuyi hakuri Kuyi yafemin sharrin shaidan ne babu yanda banso na k'aucewa Hajja Kaltume amma sai da tayi nassara akaina nayi dana sanin biyewa San zuciyata Umma,nayi nadamar abinda na aikata ni kadai nasan mai nake ji a zuciyata Umma,kuyi Hakuri Ku yafemin,ban tab'a aikata zina ba,waya kawai na keyi da wani,Daddyn Hanif ya kamani, Umma nasan nayi laifi na cancanci kuyi min kowane irin hukunci amma Umma kuyimin adalci karku manta kunsan halina Allah ya Riga ya kaddara sai hakan ta faru," Tunda ta fara  magana Mallama Rabi ke kuka tana kallonta jin abinda tace ne yasa ta katse ta tace" babu wata Kaddara Manal San zuciyarki dai ta kai ta Baro ko,idan bera da sata ai daddawa ma nada wari,ina mamakin mutane da zasu yi Abu Dan San zuciyarsu daga baya suzo suna cewa kaddara ce Allah ya Riga ya hukunta hakan zai faru Sam ban yarda da wanan zancen ba dan babu yanda Allah zai jarrabceku ku aikata mumunan Abu da aurenku,domin Allah ma d'aukakin sarki ba azzalumun bawa bane,Kune dai kuka d'orawa kanku masifa  da San zuciya,shaidan kuwa yana daga gefe yana kad'a muku ganga, idan ba haka ba Manal ina ke ina huld'a dawani awaya fisbillahi,da  iliminki da tunaninki,mai Mijinki ya rage ki dashi,wlh ko a mafarki akace min zakiyi haka karyatawa zanyi,aganina yau ko fad'uwa nayi na mutu,ke xaki zamto tamkar uwa awajensu Aneesa duk wani Abu da kike ganin sunyi ba daidai ba ke zaki musu fad'a ki d'ora su ahanya sai gashi ke da kanki kinyi abinda ko ameera bana jin zata yi abinda kika yi "Sai da suka kai Ukun dare Mallama Rabi na mata fad'a da Naseeha,Manal jikinta ne ya k'ara sanyi nadama da da nasani na kuma rufeta,ji take Dama hanun agogo ya koma baya da ta gyara kuskurenta amma ina aikin gama ya Riga da ya gama,kuka taci ta gode Allah,a k'arshe ta mik'e ta nufi band'aki ta d'aura alwala tazo ta tada sallah,addu'a ta rin ga yi sosai tana Neman yafiyar Allah akan abinda ta aikata,ta ringa rok'on Allah yasa kar Yusuf ya saketa,Allah ya huci zuciyarsa ya yafe mata ko Dan 'yayanta aranar ko sau d'aya barci bai yi gingin d'aukarta ba har aka kira sallahr asuba tayi sallah tana zaune akan sallaya tana Jan carbi,Mallama Rabi kuwa tsantsar tausayin Manal ne yasa ta ringa  share hawaye akai akai.


B'angaren Yusuf ma kuwa ranar  barci bai ga idonsa ba Dan idonsa na kan agogo ya kagu garin Allah ya waye, su Hajja Kaltume su iso yaci ubansu,Allah yasan da ace Hajja Kaltume ba matar aure bace baisan wane irin mataki zai d'auka akanta ba Dan itace silar komai,amma duk da haka baya d'aukarta a matar aure Dan a karuwa ya d'auketa sai ya ci ubanta fiye da tunaninta kuma a k'arshe ya had'a ta da 'yan hisba,kiraye kirayen Sallar asuba da yafara jiyo wane yasa ya mik'e ya nufi band'aki ya d'aura alwala yazo ya tada sallah,sai da ya dade yana addua kafin ya shafa,Dan massalaci yaso zuwa amma sabida yara yafasa zuwa massalacin,bayan ya idar da sallah,Kitchen ya nufa ya d'orawa su Hanif breakfast, daga nan ya wuce d'akinsa,tashinsu yayi da su tashi suyi sallah,suka mik'e gabad'ayansu da adduar tashi daga barci,d'aya bayan d'aya suka ringa shiga band'akin suna d'aura alwala yana zaune a gefen gado yana kallonsu, Haneef ne yaja su sallar,sallah sukeyi cike da nutsuwa kamar wasu manya taufiqa ma tafi bashi mamaki Dan yanda take sallar kamar wata babba bazaka tab'a yarda 'yar shekara hud'u bace,mamaki bai gama rufeshi ba sai bayan da sukayi sallama yaga dukansu sun koma sun yi sujjadar shukur,lumshe idonsa yayi Hawaye na zubo mishi Dan yasan wanan duk koyarwar Manal ce,Manal tayiwa yaransa tarbiyya sosai da ba ya shak'ar shiga dasu ko ina yaransa suna da ilimi addini sosai da duk wani taro ko gasa idan za'ayi 'yayansa ne akan gaba,su hukumar makaranta kan zab'a Dan bai zai iya fad'ar sau nawa yaransa kan ciyo gasa ba ta fanin addini,kuma duk Manal ce take jajircewa wajen ganin sunyi karatu sun kuma iya,amma abun mamaki Manal d'ince ta tak'e duk  iliminta da saninta ta keta alfarmar da martabar aure,tasan duk abinda take yi haramune ta biye wa San zuciyarta,muryar Hanif ce ta katse matsa tunanin da yake yi,Suratul duha yake karantawa cikin zazzakar muryarsa Su Saleem nabinsa,ahaka ya shagala da kallonsu sai da ya tuna da ya d'ora abinci ya mik'e da sauri ya nufi kitchen, atakaice shi ya shirya Taufiqa da kansa su Hanif kuma suka shirya dakansu,suna cikin breakfast Hindatu ta shigo gidan ta gaishe shi ta fara aikace aikacenta,ganin suna breakfast ne yasa shima ya nufi d'akinsa shima yayi wanka ya shirya dan ya mik'a su makaranta,yana fitowa ya tarar da sun gama breakfast duk sun dau lunch box d'insu suna jiransa,umarni ya musu da su wuce su tafi,bayan sun gama ficewa daga palon ya kalli k'araso..........................



*HAUSA NOVELS* 📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

A SANADIN GROUPWhere stories live. Discover now