page 47

94 5 0
                                    

🅰 *S🅰N🅰DIN GROUP*🙊🙊

*Written by*
 
💅💅 *SADNAF*💞

  *PURE MOMENT OF  LIFE WRITERS*

    _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_  *P.M.L*

*A short story based on true life story*

*Wanan shafin naki ne ke kadai Auntyna ( AUNTY SIS💞) thanks for your love and support*

*Ban manta dake ba Meenahtraj Fck novels ina mik'a sakon gaisuwata gareki*

*kuna raina*

*Aseeya Nasser*
*Saudat idrees muhd*
*Shamsiyya shamsudeen*
*Momyn sultan kd*
*Mrs marafa*
*Ayush*
*Bilkisu*

*IN FACT  INA  YINKU 'YAN  ZAUREN  BIEBIE ISAH KUNA BURGENI IRIN TOTALLY*

*WISH YOU SPEED RECOVERY MY FATY AZLAND GET WELL SOON DEAR*

*Page:-* 47

Yusuf kuwa yana barin hotel d'in bai zame ko ina ba sai gida, yana zuwa sallah yayi ya had'a kayansa dan ayau yake so ya koma Abuja, yana dab da ficewa daga d'akin idonsa ya sauka akan wayarsu bad boy da ya k'arba koma wa yayi ya zauna a gefen gado,ya d'auki wayarsu ya shiga gallery aikuwa hotuna da videon manal da yake kyautata zaton duk abokanan Ton g suna dashi awayarsu su yagani kaca kaca,gogewa ya fara yi hawaye na zubo mishi dan Manal ta cuceshi matuk'a da ta tura sirrinsa mutane wajen shidda suka gani ganin goge hotunan duk b'ata lokacine,yasa ya sun gume wayoyin ya fita waje,ya bud'e rijiyar dake kai ruwa saman tank ya jefa wayoyin a ciki,ya koma d'aki ya d'auki jakar kayansa ya fita waje ya hau mota ya d'au hanyar Abuja.


Manal kuwa aranar k'arfe Tara aka sallamesu daga asibitin likita ya bata shawarwari da ta rage tunani jininta yana hawa sosai,tunda suka je gida,Manal ta kule a d'aki in banda kuka babu abinda ta keyi,Mallama Rabi ko kallon inda d'akin yake bata yi ba ballantana akai ga ta rarrashi Manal dan gani take duk abinda ya faru ita ta janyowa kanta,daddare su Mustapha suka hallara a gidan dan su tatauna yanda za 'ayi a samu Yusuf a tambayeshi sakin Manal yayi ko kuwa, Abduljabbar da Babangida suka yanke shawara suje ranar Asabar su sameshi da haka suka ringa maida zance inda suka ringa cewa matsawar Auren Manal mutuwa yayi,lailai Manal zata ci ubanta a hanunsu,da haka suka yiwa Mallama Rabi sallama suka nufi gidajensu.

Wata biyu kenan da tafiyar Yusuf abuja bai k'ara waiwayar Kano ba,waya kawai yake bugowa Hajiyarsa ta had'a shi da yaransa ,Hajiya Munawwara tayi mishi fad'an har ta gaji, Yusuf kuwa yana sane yak'i zuwa duk wanan lokacin,so yake zuciyarsa ta k'ara sanyi kafin ya dawo,Dan har lokacin ya kasa manta abinda Manal tayi mishi,duk da kewarta da Santa dake addabarsa haka ya d'aure,yana San ganinsu Hanif amma haka ya d'aure yak'i zuwa Dan gani yake In yazo ya gansu zasu iya karya mishi zuciya ya maida Manal,shi kuwa ba yanzu yake so ya mayar da Manal ba yafiso sai Manal ta shiga hankalinta tasan mai take yi tukuna zai maidata,Dan ya Dad'e da yafe mata bayan dogon tunanin da yayi yagane shaid'an ma ya bada tashi gudunmawar wajen dulmiyar da Manal,amma Idan ba haka ba babu abinda zai sa ya maidata.

B'angaren Manal kuwa tunda ga lokacin da yayanta Babangida yaje gidan Yusuf ya dawo yace gidan a kulle yake, Mustapha ya kirashi awaya Yusuf ya basu hak'uri da zai zo da kansa amma ba yanzu ba,Manal ta shiga cikin tashin  hankali  da damuwa ,bata da aikin da ya wuce kuka bata barcin dare Sam,kullum tana kan sallaya tana kuka tana Neman yafiyar Allah,tabi ta rame tayi baki,ga kewan yaranta dake damunta,haka kawai in tana zaune sai ta ringa  jiyo muryar Su Hanif,tasha yunk'urin taje  gidansu Yusuf taga su Hanif dan tasan babu inda Yusuf zai kai yaran da ya wuce nan,amma kunya kan hanata zuwa Dan gani take kamar Yusuf ya gaya wa Hajiyarsa abinda ta aikata,Mallama Rabi tun tana share ta tana nuna mata halin ko in kula har ta dawo ita ce ke mata naseeha,tana rarashinta akan ta kwantar da Hankalinta watak'ila ita kuma tata jarrabtar kenan...........................



*HAUSA NOVELS* 📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚
*HAUSA NOVELS* 📚📚📚

A SANADIN GROUPNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ