Kogin tunanin da ya fada da mabambantan yanayin dake bayyana a fuskarsa kowace dakika sun sanyaya ran Salihi. Alamu ne na cewa tarkonsa ya kama kada. Da shirinsa ya shigo dakin Mubashir domin yana fata yau ta zama rana ta farko kuma ta karshe da irin wannan fadan zai shiga tsakaninsa da dansa. Wayarsa ya kunna har yanzu suna tsaye a bakin kofar ya kunno abin da yake so ya nuna masa. Bidiyo ne wanda ke nuni da jama'a suna jam'in sallah. Bayan kamar sakan goma anyi kabbarar dagowa daga sujjada amma wani matashi a sahun gaba bai tashi ba. Koda aka sallame aka duba ashe rai yayi halinsa. Mutane suka yi ta kabbara da ambaton Innalillahi.

Mubashir bai san lokacin da ya soma kuka wiwi ba yana cewa,

"Baba kaga fa ya rasu"

"Kamar haka ne ajali ke riskar kowane bawa a lokacin da bai yi zato ba. Da ace naka lokacin yayi a jiya karshenta da sai dai yanzu a kirani inda kaje party ace inzo in karbi gawa" tsigar jikin Mubashir ta tashi da tunanin hakan kawai.

Salihi kuwa  dafa kafadarsa ya yi suna fuskantar juna.
"Abin tunani shi ne da ace kaine na cikin bidiyon nan da kila har nima na koma ga Allah ina bada labarin mutuwarka. Kai nayi imani 'yan bakinciki sai sun mutu saboda sun san cewa nayi babban rabo. Ranar lahira mune 'yan hura hanci saboda nayi dacen samun dan da Allah Yake so har ya karbe shi a sujjada. Haka zaka karbi cetonmu ka kaimu aljanna idan ayyukan alkhairinmu sunyi karanci" Sai da ya ja numfashi sannan ya dora da "da kuma ace ka mutu a wurin patin haka zanyi ta boye fuska kada idon sani su ganni. Kuma ina mai imani da cewa zan dawo gida nayi ta gillawa mutane karya. Ba zan taba yarda a san a inda ajali ya riskeka ba. Kaga anyi biyu babu. Ka tafi a banza ka bar ubanka zai tafi a hofi tunda ya zama makaryaci"

Jikinsa Mubashir ya fada yana kuka duka jiki na bari. Salihi ya dinga bubbuga masa baya da rarrashi. Sai da ya kula nutsuwa ta zo masa sannan ya yi masa tambayar da ta zo masa a ba zata.

"A ina ka sami kudin da kayi waccan soyayyar? "

***

Bacci mara dadi Uwani tayi sakamakon abubuwan da suka faru a gidan Munzali jiya. Da suka dawo gida tare da Asabe tayi mamaki sosai da Innayo bata tambayeta daga ina suke ko dalilin fitarsu tare ba. Kalmar 'kema 'yarki ce' da Munzali ya yi amfani da ita lokacin da yake cewa ba zai roketa rufin asirin Qibdiyya ba tayi mata karan tsaye a wuya. Makomar rayuwar yarinyar a gaba ya sanyata cikin damuwa. Shikenan rayuwarta ta baci tun yanzu? Sai kuma nata 'ya'yan da basu wani dameta ba suka fado mata. Anya ta ma san wani abu cikin rayuwarsu sama da dan abin da ba a rasawa? Irin abin da kowa ma zai sani muddin ya zauna dasu. Ita dai a matsayinta na uwa ba za ta dorar da komai ba. Babbar 'yarta Amira ta tuna. Yarinyar da har almajiri take sawa yi mata tsarki lokacin da take karama saboda bata son tashi daga kemis dinta. Sai ta bawa almajirinta mukullin gidanta ya tafi ya gyaro mata jiki su dawo. Kudi ne kawai a gabanta sannan bata son mai aiki mace don kada ta dauke hankalin mijinta. Ta biyun kuma Anisa a lokacin tata kuruciyar wani kanin Salihi da yake karatu ta sakarwa ragamarta. Sai da Salihin ya yi mata tatas lokacin da ya farga. Idan ma da mugun nufi kila har anyi an gama. Yaran basa kaiwa shekara biyar take barinsu su fara wanka. Saboda ita ce Uwani ina kika fito neman kudi, ina zaki neman kudi. Mubashir ne ma ya dan samu kulawa a matsayinsa na dan fari kafin ta gaji ta watsar. Duk wannan tunanin sai ya kare a inda take ganin cewa ai kudi take nema musu.

'Kudin da baki iya kashe musu' zuciyarta ta tuna mata.
'Kudin da suke neman salwanta a banza?'

Kamar an tsikareta haka ta tashi firgigit ta janyo wayarta. Nambar Habibu ta dannawa kira ta kara a kunne. Ta shiga har ta katse bai dauka ba. Ta cigaba da gwadawa missed calls sun kai goma zai gani amma  duka shiru. Lokaci ta kalla sai taji bari tayi masa uzuri kila bai tashi ba. Nan kuma ta canja akalar kiran ga Salihi. Kiran yaje gareshi lokacin da Mubashir cikin kuka ya fada masa da kudin wa yayi sayayya. Sam bata yi la'akari da cewa yanzu ake sallar asuba ba. Kudadenta kadai take tunani.

UWA UWACE...Where stories live. Discover now