Bakwai.

1.3K 201 69
                                    

~~~~~~

"Mark my words, idan har wani abu ya same ta, babu wanda zan saurara Ishaq, babu wanda zan saurara."

Muryar Ma'aruf, ta faɗa a cikin ɗakin asibitin da misalin ƙarfe takwas na wannan daren, yana zaune daga gefen gadon ɗakin da waya kare a kunnensa yayin da daga tsakiyar gadon, wata ƙaramar yarinya ce kwance tana bacci.

Da hannunsa ɗaya ya shafo kansa sannan ya sake cewa.

"Saboda me? Shekaru biyu ta hana ni ganinta amma yau sai na tsince ta a tsakiyar wannan gidan arnan? Idan kana yiwa Allah ka gaya min cewa zan iya maka ta a kotu a hukunta ta."

Daga cikin wayar Ishaq ya sake cewa.

"Ka taimaka ka fara kwantar da hankalinka yanzu B, ba dai yarinyar tana hannunka ba? ai anci rabin matsalar abinda zai biyo ba mai yawa bane. Sannan na tabbata shi kansa Baffan yanzu idan yaji komai, ba zai sake goyon bayanta ba, mu godewa Allah ma da ba'a dauki shekarun da suka fi haka ba."

Baice komai ba ya cigaba da motsa yatsunsa a cikin gashin kansa kawai yana sauraren duk bayanin da yake yi kafin wayar tasu ta kai ƙarshe, suka yi sallama bayan Ishaq ɗin ya gaya masa cewa sai jibi zai dawo don aiki ya kaishi wani gari a can hanyar Abuja.

Ma'aruf ya sauke wayar a lokacin da idanunsa suka sake komawa kan yarinyar, Hamida ce... ƴarsa, har yanzu tunaninsa ya kasa gasgatawa, ya kasa yarda cewa ita ɗin ya gani bayan tsawon shekaru rabonsa da ita kuma a wani waje da bai taɓa zato ba.

Tsawon sati uku kenan da ya sadaukar da duk lokacinsa da komai wajen ƙoƙarin daidaita al'amarin da yake faruwa a kamfanin nasu. Wata irin asara suka yi da bata da tushe, bata da reshe kuma babu wani abu da yaja zuwanta. Dawowarsa kawai aka wayi gari da report din ɓatan maƙudan kuɗaɗen da babu ma wanda ya kula dasu sai a lokacin da aka zo fitar da wani kaso na harajin ƙarshen shekara da ake cirewa a duk ƙarshen kowanne wata.

Anyi duk wani bincike amma babu abinda aka tarar daga ƙarshe, don haka Baffa yace a rufe zancen kawai su karɓi hakan a matsayin ƙaddara,. kasuwancinsu ya cigaba da gudana, amma haka kurum sai zuciyarsa taƙi bashi cewa hakan daidai ne, wannan aiki ne da ya riga ya saka ransa akai... Ba yana yinsa don yana sonsa bane yana yinsa ne don ya zame masa dole, dolen da a cikinta ba zai taɓa bari a lissafa da wata tangarɗa ba, don haka ya bi maganar Baffan ya cigaba da gudanar da aikinsa a gefe guda kuma shi da Faruk suna cigaba da bincike akan lamarin.

A cikin binciken nasu Faruk ya samo wani mutum ne a cikin ƙananun ma'aikatan wajen da yace yana yana da wani bayani da zai iya basu, amma bayan Faruk ɗin yaje ya same shi har gida, sai ya ƙi bashi haɗin kai game da hakan duk kuwa yadda yayi dashi. Sun fahimci tsoro ne ya kama shi don haka shi yace zai je ya same shi duk kuwa da magiyar da Faruk ɗin yayi masa akan cewar kar yaje, magiyar da ya riga ya san ta mecece don dukkansu du niyun sun san cewar idan lamarin ya ɓaci babu wanda zai iya kallon Baffan a cikinsu da wani bayani.

Amma shi kansa Faruk ɗin ya san cewa tunda har ya saka ransa babu abinda zai tsaida shi don ba tun yau ya sani cewar idan har ya furta abu zai yi to tabbas zai yi ɗin, bai taɓa ganin ya sa kansa yin abu ya fasa ba.

Don haka kai tsaye bayan ya tashi daga aikin ya nufi unguwar sabongari da address ɗin da Faruk din ya turo masa don ba yadda zai yi. Ya isa da kyar bayan ya haɗa da tambaya sannan kwatancen ya tsayar dashi a daidai kofar gidan mutumin da yake nema.

Sunansa Okafor, wani dattijo ne arne daya dade yana aikin shara a kamfanin, ya san shi tun lokacin da idan sun dawo hutu daga makaranta yake zuwa kamfanin, kuma har sai bayan ya fara aiki ne sannan aka ƙara masa matsayi zuwa aikin hada takardu saboda tsufan da ya kama shi, ya kalli takurarren gidan dake gabansa, mutane ne ke ta fitowa daga ciki kamar gidan tururuwa, a ransa ya ayyana cewa idan har Okafor yana da sa'a watakila zaman gidan ya kusa kare masa shi da iyalansa.

Farar Wuta.Where stories live. Discover now