Part 01

15 1 1
                                    

بسم الله الرحمن الرحيم

Dᴀ sᴜɴᴀɴ Aʟʟᴀʜ ᴍᴀɪ ʀᴀʜᴀᴍᴀ ᴍᴀɪ ᴊɪɴᴋᴀɪ
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

💕ᴡᴀɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴅᴀᴢᴀᴋᴜ ᴋᴀʀᴀɴᴛᴀ,...ᴋᴜɴɢɪʏᴀʀ
Sᴋʏʟɪɴᴇ♥Wʀɪᴛᴇʀs♥Sϙᴜᴀᴅ
sᴜᴋᴀ ᴅᴀᴜᴋɪ...ɴᴀᴜʏɪɴ ᴋᴀᴡᴏ ᴍᴜᴋᴜ.❤

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

*♪Cɪʏᴏɴ Yᴀʀ Mᴀᴄᴇ♪*
_{ɳα ყαɾ ɱαcε ɳε}_

*Pᴀʀᴛ 0⃣1⃣*

_Bʏ Aʙɪ Sᴜғʏᴀɴ Uᴍᴀʀ_

_ᎬᎡᎡϴᎡՏ ᎪᎻᎬᎪᎠ_
♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪
Wasu hadadun...indian wears ne sanye ajikinta...doguwar riga mai dogayen hannu...da'akayima ado agabanta da beads masu sheki hade da wandonta kalar maroon,...sai wani madaidaicin mayafi data yafa akirjinta, shima kalar maroon....Wani style din daurin dan'kwali ne akanta wanda yaba dogon gashinta...zubowa bisa gadon bayanta yayi kwance wul-wul. Jakarta mai sarka, kalar chocolate dake rataye akafadarta, hadi da takalmin datake sanye, bakake wul, sunyi matukar dacewa da kayan dake jikinta.
Kasancewarta fara, doguwa.... sai kayan sukayi masifar yimata kyau....kamar dan ita aka kerosu. kalo daya zakayi mata, ka tabatar da hakan.

Ta jima tsaye gindin wata bishiya, tana jiran kawarta Meenat ta karaso, ama babu Meenat, babu alamunta....gashi sai kiranta take kuma bata dagawa. Saida ta bata wasu mintunan ahaka, kana can, ta hangota tana zuwa da sasarfarta, takalminta ahannu, kamar wace keneman kubuta.

Koda tasamu karasowa, da ido kawai take kalonta alamar tanbaya karar akan fuskarta. "Miye kike wani tsureni da ido, muje tinkafin yafahimci bana gida" cewar Meenat, da sai alokacin tasamu damar saka takalminta. Mai adaidaitan dayazo zai wuce ne, suka tsayar tareda shigewa suna masa bayanin inda zai kaisu, babu bata lokaci kuwa yaja suka tafi.

Film House Cinema
Cikin tafiyar da bata wuce ta mintuna bakwai ba sai gasu a film house cinema kano, tare suka shiga cikin cinemar bayan sun salami mai adaidaitan daya kawosu. Saida suka saye duk wani abun kwalama da zasu bukata kana suka tinkari dakin kalon kai tsaye. Ana saura mintuna biyar afara haska film din dasuka zo kalo, sumayya tanemi wayarta ta rasa, ta mata neman duniyarnan ama wayar tamata sama koh kasa, dibarar komawa wurin mai siyarda Pop-corn  ne tafadomata, cikin sauri kuwa tabar dakin kalon bayan ta sanarma meenat, a'inda meenat ta bukaci data biyomata da gorar ruwa.

Isowarta wajen mai Pop-corn keda wuya, ta hango wayarta ajiye inda ta barta. Alama tama mai Pop-corn din, gami da kai hannu ta dauka. Har zata wuce saikuma tadawo....tareda cema mai Pop-corn din yabata sunwater.
Tinawa tayi bata rike da jakarta, kuma gashi har ya dauko yana sakawa aleda, tabude baki zatace ya mayar kenan, yayi daidai da lokacin dawata sanyayar murya tace
“Baiwar Allah, ga kudinki” juyowa sumayya tayi domin ganama idonta mai maganar, a'inda sukayi ido hudu da wani kyakyawan samari dake cikin shigarsa ta kamala.

Kin amasar kudin tayi, hakan yasa dan samarin fakewa da cewa “Kawarkice tace na kawo miki” dan karamin murmushin daya tsaya iya laba sumayya tasaki, tareda kai hannu ta karbi 1k  dayake bata tana yimasa godiya. Dakin kalon takoma, bayan tabiya mai Pop-corn kudinsa. Ta taki sa'a kuwa dan tana shiga ana fara haska kayatacen film din dasukazo kalo mai taken So Gamon Jini, zamatayi awurin zamanta tana mikawa meenat gorar ruwa dake hade da canjin da mai Pop-corn yabata, kana tadauki Pop-corn dinta, tanaci tana kalo.

Duka duka 1hour yadaukesu, film ya kare, nan mutane suka fara watsewa daga cikin dakin kalon. Meenat da tintini taso yima sumayya tanbaya akan kudin data bata ne tasamu damar cewa “Sumayya wanan kudin name?” “canjinki mana” sumayya wace kefaman danar wayarta tafada atakaice. Tsayawa meenat tayi, gami da cewa “Ni?” tana nuna kanta, mamaki kwance karara akan fuskarta. Dakatawa sumayya tayi daga dane-danen datakeyi, hanayenta duka biyu akan waist dinta tashiga tanbayar meenat “tsaya..., wai dama bake kika aikomin da dubu daya ba?”
Girgiza kai meenat tashigayi kafin tace “A'a walahi....kawajo, toh dama bada kudi kika fitaba?” Nanauyar ajiyar zuciya Sumayya ta sauke kafin tace “Alokacin.......na zata ina tare da jakata, sai danaje biyan kudin sunwater ne, na lura tana wajenki, toh alokacin ne fa wani ya bani 1k da cewar ke kikace yabani.”

Jijiga kai meenat tashigayi ahankali kafin tace “Uhm....kinji wani Sabon salo, nida tin shigowata ba wanda magana ta hadamu, toh yanzu yaza'ayi da sauran canjin?” fadar meenat, tana tsure kawarta da manyan idonta. Dan jim sumayya tayi kafin tace  “Mayar masa da abinsa zamiyi” waro manyan idonta meenat tayi, cikin mamakin kawarta takecewa “Ina zamu gansa cikin dan-dazon jama'ar nan sumayya, mutumin da yau kika fara ganinsa”
“Hakane...kuma fah,... kinga muje kawai” cewar sumayya tana gyara zaman jakarta. Mai napep suka shiga tsayarwa bayan sun samu damar isowa bakin titi, saidai amadadin mai napep, wata sabuwar mota tayi parking ta gabansu. Da ido duk suka shiga bin motar da kallo, motar na tsayawa aka shiga rage glass din murfin motar, wanda hakan yabasu damar ganin na cikin motar. Azaune yake, ya hakimce cikin motarsa sai kamshi yake zubawa, cikin cool voice dinsa ya fara yimusu salama, yana sakar musu tatausan murmushi.
“Ameen wa'alaika salam” suka amsa akusan tare. Sumayya data ganeshi ne, ta ida karasawa dab da motar tana ciro 1k acikin jakarta, cikin sakin fuska ta soma cewa “Nagode fah, da taimakona dakayi d’azu” ta ida maganar tana mika masa kudin. Kin amsar kudin yayi, cikin cool voice dinsa yake cewa “A'a ni dan Allah nabaki, saidai idan bakya so” Dan jim sumayya tayi, badan taso ba, tashiga yimasa godiya, jiki asanyaye. Har ta juya zatabar wajen ne, ta tsinci muryarsa yana cewa “Ji mana” dakatawa tayi, tareda juyawa garesa, cigaba yayi dacewa “Idan bazaku damu ba, kushigo na rage muku hanya mana” Har sumayya tabude baki zatayi magana, kawarta meenat ta kwatseta ta hanyar cewa
“Da koh ka kyauta, bawan Allah”
Har ga Allah yaji dadin yada meenat ta nuna amincewarta, sabanin sumayya da yake ganin, da kamar wuya tanuna amincewarta.
Murmushin daya bayana fararen hakoransa yasaki kafin ya bude musu kofar baya. Meenat ce tafara shiga....sai sumayya wace sam bataso ba, suna gama shiga, ya murza ma motar key suka bar film house cinema. Bisa hanya kuwa....suna tafiya, yana dan jansu da fira, har suka kawo areansu sumayya.

*.A.L.H.A.M.D.U.L.I.L.A.H.*

‘Mᴜ ʜᴀᴅᴜ ᴀ ᴋᴀsʜɪ ɴᴀ ɢᴀʙᴀ’

_Kᴜʏɪ ʟɪᴋᴇ ᴋᴜᴍᴀ ᴋᴜʏɪ ᴄᴏᴍᴍᴇɴᴛ, ᴅᴏᴍɪɴ ɪɴsᴀɴ ᴋᴏʜ ᴄɪɢᴀʙᴀ ᴢᴀɴʏɪ ᴋᴏʜ ᴋᴜᴍᴀ ᴅᴀᴋᴀᴛᴀᴡᴀ ᴢᴀɴʏɪ_

♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♥♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪♪

_⚛Kᴀʀᴀɴᴛᴀ Lᴀʙᴀʀᴀɴᴍᴜ Gᴀᴍɪ Dᴀ Tᴏғᴀ Aʟʙᴀʀᴋᴀᴄɪɴ Bᴀᴋɪɴᴋᴜ, Sʜɪɴᴇ Kᴀʀғɪɴ Gᴜɪᴡᴀʀᴍᴜ Kᴜᴍᴀ Fᴀʀɪɴ Cɪᴋɪɴᴍᴜ⚛_

*τακєи мαяυϐυϲι*

♪Cɪʏᴏɴ Ƴᴀ Mᴀᴄᴇ♪Where stories live. Discover now