Ranar kamar yadda Abba ya umurce shi, bayan sallar la'asar ya dawo gida yayi shirin sa tsaf ya futo fesfes da shi. Motar da Abba ya bar masa ya dinga amfani ya wuce ya hau ya kama hanya zuwa gidan abokin Mahaifin nasa dan ganin diyarsa kamar yadda iyayensa suka umurta. Hamidu ne zaune gefen sa yana nuna masa hanya dan kasancewar Ibrahim ya dade baya qasar kuma ya dade rabonshi da gidan Haji Modu, bazai iya kai kansa gidan ba.

Ranar tun safe Yaburra ta kasa tsaye ta kasa zaune sai shirya Shatu takeyi. Tun asubah aka ba Hadiza kayan ta ta goge tayi musu turare, aka kawo wasu hade haden magunguna wadda wata qawar Yaburra ta kawo mata cewar na farin jini ne aka ba Shatu ta shanye su tas. The previous day dama yini guda Yaburra da qawarta suka kashe suna koyawa Shatu yadda ake rangwada da kashe murya da duk wata dabara da zata yi dan janyo hankalin sa. Rana na yi aka sa Hadiza yin girkin abinci me dadi sosai ta yanka ganye kan tazo ta murza flour ta yi dan chinchin sabida zuwan baqi. Fusam kam tana dawowa makaranta aka aika ta siyo drinks a shago aka saka su a fridge din dakin Baba dan suyi sanyi. Ranar har wankan lalli da turare aka yiwa Shatu, aka mata su halawa duk dan zuwan Ibrahim Bukar Baba-Ganah. Hannayen ta jazur da lallin da aka sa Hadiza ta kwaba ta yanka tape tayi mata daren ranar alhamis. Su dai Hadiza da Fusam sai kallon ikon Allah suka yi ta yi suna mamakin wani baqo ne zai zo gun Shatu ake ta shirya ta haka. Gab da zuwan baqin Yaburra ta dauko turaren wutan ta da ya fi kowanne tsada da kamshi ta bawa Hadiza ta je ta saka a babban falon gidan koh ina ya dau kamshi. Tana cikin turaren bata gama ba Ibrahim suka shigo tare Hamidu da Hamza wanda ya futo welcoming dinsu. Hadiza na jin shigowar su falon ta ije kaskon turaren a can wani gefe ta durqusa qasa a ladabce ta gaishe su, Ibrahim ya ansata fuskar shi ba yabo ba fallasa dan gaba daya hankalin sa be kan ta, koh kallon gefen da take be yi ba ya ansa gaisuwar ta.

"Shiga ki ma su Yaburra magana, kice musu baqin mu sun iso". Hamza ya ce dan dama duk yaran gidan su ma Yaburra suke kiranta kamar yadda mutane ke ce mata. Toh kawai tace kan ta a qasa dan Hadiza Allah yayi ta da tsananin kunya especially ma kuma maza. Wucewa tayi ta isar da saqon Hamza. Yaburra ce ta fara shiga suka gaisa kan ta futo Shatu ta cika Hadiza da tambayoyi.

"Kyakyawa ne shi?".

"Fari ne koh baqi?".

"Dogo ne?". Ita dai Hadiza tace a gaskia ba wai kallon shi tayi ba dan haka ba sani zata yi ba. Suna haka Yaburra ta shigo ta cewa Shatu taje su gaisa. Wani irin harara ta gallawa Hadiza kan ta daka mata tsawa "Dalla banza wuce kitchen ki hado kayan abinci ki kai musu, kin tsaya nan kina gulma. Wawuya yar jaka". In zagi ne ba sabon abu bane wurin Hadiza dan ta saba shan shi wurin Yaburra. Kitchen ta wuce kamar yadda aka umurce ta ta fara hada tray din kayan abinci da snacks. Parlorn ta wuce ta jera musu kayan abincin a qasa ta miqe zata wuce Shatu ta tsayar da ita.

"Ki tsaya ki zuba musu mana". Komawa tayi ba gardama ta zuquna ta fara serving abincin.

Ibrahim be niyyar cin abinci ba amma ya rasa meyasa tunda yaji ance yarinyar da ta kawo abinci, wadda suka shigo suka sama tana turare tayi serving abinci yaji yana so ya ci. Kallonta yayi ta yi as she served the food, addu'a yike ta yi a zuciyar shi ta daga kai su hada ido amma ta qi, tunda ta sunkuyar da kai tayi ta aikin ta cikin nutsuwa bata dago ba sai da tayi serving abinci a plate biyu ta fara ije plate daya a gaban Hamidu kan ta qaraso gaban shi ta ije dayan plate din. Godia ya mata kan ya anshi plate din abincin daga hannunta.

Hadiza kam tana gama serving din su abincin ta fice daga dakin da saurin ta ta koma dakinsu ta sama Fusam kwance. Wucewa tayi inda ta boye yan chinchin inda ta deba sanda Yaburra bata kusa ta dauko ta miqawa Fusam. "I got them for you, dan na san kina so sosai". Murna sosai Fusam tayi ta matso tayi hugging Yar uwar nata tana fadin ta gode kan ta fara ci a sace dan gudun kar Yaburra koh wani cikin yaranta su fado dakin su gani a qala musu sharrin sata.

"Kin tuna chinchin dinnan da ake mana lokacin in mun je Yola da Mama?". Fusam ta tambayi yar uwar ta wadda ta ansa ta da ehh. Shuru dukansu suka yi suna tuno mahaifiyar ta su wadda ta rasu shekaru goma da suka wuce.

Haji Modu ya hadu da matarshi ta farko me suna Maryama ne wani tafia da yayi zuwa garin Yola. A wurin bikin wani abokinsa suka hadu da Maryama wadda ta kasance babbar qawa ga amaryar abokin nasa. Nan da nan suka qulla soyayya dan koh bayan da Haji Modu ya koma Borno be bar tunanin Maryama ba itama haka bata bar tunanin sa ba. Shi dai Haji Modu wanda asalin sunan shi Muhammadu ya kasance dan garin Borno, cikakken kanuri kuma shine d'a na fari a wurin mahaifinsa. A lokacin da ya taso ya kammala karatun secondary dinsa Allah yayiwa mahaifin nasa rasuwa dan haka responsibilities din mahaifin nasa suka fado kan young shoulders dinsa. Sana'ar ubansa yayi gado wato kasuwanci har Allah ya albarkace shi sana'ar yayi ta bunqasa, daga runfa biyu ta mahaifin su ya mutu ya bar musu suka koma suna da runfuna fin ashirin a kasuwa. A haka ya cigaba da kula da iyayenshi mata da kuma yan uwanshi har yayi auransa na fari, ya aura sahibar sa Maryama ya dauko ta daga garinsu can Yola ya kawo ta Borno. Allah ya albarkaci auransu dan wata tara daidai da aure Allah ya basu qaruwan diya mace wadda suka sa mata sunan mahaifiyar Maryama wato Hadiza. Hadiza nada shekara daya dai dai a duniya Allah ya bawa Maryama wani cikin ta haifo diyar ta ta biyu wadda aka bata suna Fusam. Bayan nan ta dan jima kan Allah ya qara azurta ta da samun wani cikin wanda tun daga samun shi tayi ta ciwo har zuwa sanda ta haifi abunda ke cikin wanda sanadin haka ta rasa ranta. Abunda kuma ta haifa aka rada masa suna Ali, yayar Maryama ta anshe sa ta koma can Yola da shi dan ta shayar da shi. Rasuwan Maryama da wata shidda cur wani abokin Haji Modu ya basa kanwar shi Zaynaba wadda kowa ke kira da Yaburra ya aura wadda ita kuma a lokacin auran ta ya mutu. Haji Modu ya auro ta ta tare gidanshi tare da yaranta biyu Hamza da Shatu wanda ta haife su a gidan auranta na fari. Shekara daya da auran su Allah ya basu qaruwan diya mace wadda aka ba suna Mairam, Mairam tana da shekaru biyu a duniya aka haifo Abdi. A lokacin su Hadiza da Fusam sun fara gasuwa da wahala dan tun lokacin aka fara azabtar da su ta hanyoyi iri iri, Hadiza tana shekaru goma a lokacin amma ita ke dorawa Yaburra ruwan wankan jego itace zuwa aike itace rainon yaro itace wanke kayan kashin yaro. Abdi na jinjiri aka maido da Ali gidan ubansa dan ya taso da sauran yan uwansa, hakan yayiwa su Hadiza matukar dadi dan uwansa ya dawo zama da su.

Yaburra bata dubi kankantar Ali ba wanda a lokacin kwata kwata shekaru hudu gare shi a duniya kuma yaro ne me lalurar sickle cell ta dinga gana masa azaba iri iri. Komi zafi, komi sanyi Ali akan siminti yike kwanciya barci wai dan yana futsarin kwance ta hanasa kwanciya kan gado ga kuma horo da yunwa da take musu. Ba ta basu abinci isasshe su ci su koshi. Watarana Haji Modu ya dawo yana cin abincin dare yana zaune tare da yaran Ali ya matso kusa ya cewa mahaifin nasa yunwa yike ji.

"Ba a baka abinci bane?" Haji Modu ya tambaya yana kallon yaron nasa da duk ya bushe yayi baqi dan azaba, koh kyaun kallo a ido babu sai kai kawai rankwalele.

Su Hadiza suna ta mintsilin qanin nasu cewar yayi shuru amma ya qi shuru ya fadawa mahaifin su cewar abincin da ake basu baya isan su. Nan Baba ya lura da duk yadda yaran nasa su uku suke a rame kamar basa samun isasshen kula. Da Baba ya fara mata fada ranar, sai da Yaburra ta kwana kuka sannan ta dau alwashin sai ta rama cin fuskar da Ali ya sa aka mata kuma ta san dole ta dau mataki akan Haji Modu, dole ta kadar da hankalin sa daga kan yaran ta sa ya daina sauraron qorafin su. Hanyar da kawai zata bi kenan ta sama shan iska, ta sheqa ayar ta yadda ta so a gidan. Ita da yaran ta.

End Of Chapter 3.

How's the story so far? Loving it?

Lawh-Al-MahfouzWhere stories live. Discover now