PART 3

31 3 2
                                    

💓💓 *_RAYUWAR INDO AISHA_* 💓💓

      *_CIGABAN LITTAFIN INDO AISHA_*

                          *_LITTAFIN_*
           *_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
                    ((Ummuhfadima))

*_{MAGA YAƘIN KAINUWA⚔️⚔️}_*

*_Bissimillahirrahanirrahim ina miƙa dubun godiyata ga Allah ubangijin talikai da yabani damar cigaba da wannan littafin na INDO AISHA bayan dogon lokaci, ina roƙon Allah da yabani ikon rubuta abindazai amfani al'umma baki ɗaya ya Allah ina roƙon gafarar ka akan abinda zan rubuta na kuskure acikin wannan lbr Allah kayafe mana kura kurammu alfarmar annabi muhammadu s,a,w._*

*_Naga addu'o'inku ƴan uwana ngd sosai wlh bataɓa sanin inada masoya a media kamar haka ba saida wannan abun yafaru dani naga saƙonninku da wa inda suka kirani ngd Allah yabarmu tare sukuma wa'inda suka damfarenin kansu sukayiwa ni guzurin chen sukayi min bakomi ƴan uwana insha Allahu yanzu zakuci gaba da jina insha Allahu._*

*_WANNAN SHINE LAST PREE PEGE ƊIN INDO AISHA DAGANAN DUK MESON TAJI CIGABAN LABARIN HAR ƘARSHE SAITA BIYA WALLAHI HARGA ALLAH BANYI NIYAR MAIDA SHI NA KUƊI BA AMMA DON DOLE YASA NI MAIDASHI NA KUƊI YANZU ZANGA MASOYAN LITTAFIN INDO AISHA NA GASKIYA DUK WADDA ZATA SIYA ZATA IYA YIMUN MAGANA TA NUMBER TA NAGODE._* 09033587886

SHAFI NA 5~6

Tsit falon yayi babu wanda ya iya motsawa bayan wucewar Mommy, Indo ce ta ɗago iadanunta ahankali ta sauke su akan Haidar wanda yake zaune kamar andasa shi agurin, haɗa idanu sukayi saboda shima idanun shi akanta suke, shanye komi tayi ta sakar mishi da kyakykywan murmushi sannan tayi mishi alama da idanu alamar yatashi yabi Mommyn, murmushi yasakar mata tare da kashe mata ido ɗaya murguɗa mishi baki tayi tare da jujjuya idanunta, sannan ta miƙe tsaye daga durƙuson da tayi.

        Hannun Sister ɗinta takama tana cewa. "Ke wai haka ake tarar baƙone? ko ɗan ruwa baki bani ba muje kiji wani abu akwai labari fa" dariya suka saka gaba ɗayansu suka tafa sannan suka nufi hanyar ɗakin su, da kallo ya bisu har saida suka shige sannan yaja ajiyar zuciya yana ƙarajin wani irin ƙaunar yarinyar aranshi, ƙwafa yaja sannan ya miƙe yabi bayan Mommyn.

       Atsaye yasame ta acikin ɗakin tana ta kai kawo acikin ɗakin, da sallama yashi ga cikin ɗakin, bata juyoba kuma bata amsa shi ba, shine yace. "Mommy gani" shiru kamar bazata amsa mishi ba sai chen tace. "Ainaganka Aliyu ya mukayi da kai akan wannan ƴar ƙauyen yarinyar kuchakar?" duum kanshi yayi amma de bece mata komi ba sanin ba cewar zaiyi ba yasa taci gaba da maganarta. "Yanzu abinda kayiwa matarka ka kyauta kenan kaje har gaban mahaifanta ka sakar musu ƴa duk akan wannan baƙauyar yarinyar to wallahi tallahi kaji na rantse maka dole cikin biyu kazaɓi ɗaya kode ka rabu da wannan shegiyar baƙauyar kokuma ka mayarda matarka Hauwa ɗakinta kokuma wallahi intsine maka".

      Gaban Haidar ne yayi wani irin munnunan bugawa! damm! damm! daramm! daƙyar ya buɗe baki yace. "Haba Mommy kinkosan wacece Hauwa da kike cewa ummaidata gidana yarinyar da batasan darajata ba batasan darajar aure ba kwata kwata yarinyar da akwai igiyar aurena akanta amma takoma tanabi maz....... ya isheni hakan Mommy ta katseshi koma me ta aikata abaya yanzu tayi nadama sosai saboda zuwanta garinnan yafi aƙirga, tana kuka da hawayenta don haka ina baka umarnin sanarwa mahaifinka idan ya dawo cewa zaka maida matarka idan ba haka wallahi saide kanemi wata uwar ammade bani ba".

      Da ƙyar ya buɗe bakinshi yace. "Don girman Allah mommy ki fahim..... katse shi takumayi da cewa. Aliyu wannan Umarnine na baka ba shawara ba" tana idasa faɗar haka ta juya tashige tolet ɗin dake ɗakin tarufe batare da ta kuma saurar komi daga bakin Haidar ba, shima da ƙyar yaja jiki yabar ɗakin hankalin shi yayi ƙololuwar tashi.

        Ɓan garen su Indo kuwa suna chen sun ƙule acikin ɗaki shewarsu kawai kakeji Anty Hafsat ce tashigo ɗakin hannunta ɗauke da faranti wanda tajerowa Indo kayan abinci akai, da da dariya afuskarta tace. "lallai Aysha naga radda zakiyi hankali ace ko ruwa kikasa ɗakkowa Indo tasha koda ba baƙuwa bace amma ai akwai gajiyar hanya atare da ita" Indo
tayi karaf tace. "Barta Anty kinsan yarinta na damunta haryanzu wannan Angon nata de zai sha hauka meybe ma ta dinga barin shi da yunwa" dariya sukasa dukansu Aysha tace "wallahi Indo zammiki rashin mutuncin fa ammade aikinsan nagirmeki ko?.

       Indo tace "oho de kekisan wannan amma yanzu dole kice dani Anty umba haka ingayawa sojana ya saitawa mutum zama" "aikam dama zaki faɗa mishi yaɗan saita mana ita" Anty Hafsat ce ta amsa tana dariya, firarsu sukeyi hankalinsu kwance sunata raha abunsu har akayi kiran sallah sannan Anty Hafsat ta miƙe zata fita tajuyo ta kalli Indo tace. "please Sister kiyi haƙuri akan abinda Mommy tay..... Indo tayi maza ta rufewa Anty Hafsat baki sanan tace "Haba Anty karfa ki manta Mommy mahaifiyace agareni kuma kowacce uwace dole taji ba daɗi nasan hadda laifina da bankiranta ina gaisheta".

        Murmushi kawai duk sukayi saboda dukkansu sun san Indo nayawan kiran Mommyn saide Mommynce bata ɗauka kwata kwata kota kira ƙarshema tayi blocking ɗinta yadda kota kira bazata same ta ba.

               *_ƘAUYEN GWARAM_*
Wayyo! Allah na wayyoni kaina! malam ka taimake ni ƙafata zata cire malam wannan azabar tayi min yawa yazanyi da rayuwata malam yimin addu'a konaji salama. Gwagwgo ce keta sambatu saboda azabar ciwon da ƙafarta keyi mata ƙafar ta kumbura tayi sintum har wani ƙyalli takeyi saboda azabar kumburi gashi tayi suntum don talinka ɗayar biyar agirma, haka kullum take rayuwa cikin wannan azabar kuma aduk sanda ƙafar ta isheta da azaba haka zatai ta tsinewa Abuwa.

        Baffah bawan Allah duk da irin azabtarwar da gwagwgo tayi mishi arayuwa be hana shi tsayawa ya taimaketa ba da zuciya ɗaya shine komi nata ayanzu saboda kowa ya gujeta babu ƙawaye babu ƴan'uwa kowa ya barta dama ba'a maganar maƙwafta wa'inda duk ta ɓata dasu babu komi tsakaninta dasu sai kayan tijara, yanzu aiga ranarsu ta gani.

      Wani sabon tashin hankalin da Gwagwgo tashiga ciki shine, jin motsi da takeyi acikinta musamman idan tanajin yinwa haka abu zaita faman motsi acikinta, ita ba yarinya bace tasan motsin ɗa aciki tasan na cuta, to tabbas inde har hasa shenta gaskiya ne to tabbas tana ɗauke da ciki ajikinta, tashin hankali kenan to ita yanzu tambayar da takeyiwa kanta akoda yaushe shine shin cikin waye ajikinta tasande bana mijinta bane saboda ita kanta bazata iya tuna shekarun da tabashi haƙƙinshi na aure ba, tabbas dole ɗayan biyu kode na Boka kokuma na masu tsaron Abuwa............. tab wata sabuwa kenan inji masu cha cha ana wata ga wata toni kaina Ummuhfaɗima banida amsar da zambawa Gwagwgo amma bansani ba ko fan's kunada amsar bata?...

*_HUUUUMMMMHHH GADE MOMMY TACE HAIDAR SAIYA DAWO DA HAUWA TSOHUWAR MATARSHI SHIN ZAI DAWO DA ITANNE? TO INYA DAWO DA ITA YA RAYUWAR INDO AISHA ZATA KOMA AGIDAN? GAKUMA GWAGWGO DA CIKI AJIKINTA SHIN CIKIN WAYE ? BOKA KO MASU TSARON ABUWA? SHIN WAI YA LABARIN HAJIYA ABUWA NE? HARUNA BAWAN ALLAH MIJIN DOLE GA ABUWA KO WANNE HALI YAKE CIKI YANZU KOYA DAWO HAYYACIN SHI KO HARYANZU YANAN YANA MA ABUWA BAUTA? DOMIN JI WA INNAN AMSOSHIN NAKU KU BIYO ƳAR MUTAN FUNTUA ACIKIN WANNAN ƘAYATACCEN LABARIN AKAN FARASHI ME SAUƘI, SAINA JIKU._*

           *_CHAKWAKIYA IYA CHAKWAKIYA RIKICI IYA RIKICI KAI ABUMFA BABU SAUƘI DOMIN ACIKIN LABARINNAN BAMUYI KOMI BA KEDE MASOYIYAR GASKIYA MAZA GARZAYO KI MALLAKI NAKI DOMIN KI MORE KARATUNKI HANKALI KWANCE AKAN FARASHI ME SAUƘI _*
          *_TABBAS YANZU ZANGA MASOYANA NA GASKIYA SHIN DA GASKE KUNA SON LABARINNAN HAR ZUCIYARKU? TO GANI GANI, WATA SHEGIYA TA KIRANI TA ZAGANE KAN KWANA BIYU BANYI TYPING BA TUNDA A ABUN BABU UZIRI SHIKENAN GA DUK MESO TAYI MIN MGN 09033587886_*

*_PLEASE READ AND SHARE_*

09033587886

RAYUWAR INDO AISHA CIGABAN LITTAFIN INDO AISHAWhere stories live. Discover now