PART 2

24 3 0
                                    

💓💓 *_RAYUWAR INDO AISHA_* 💓💓

      *_CIGABAN LITTAFIN INDO AISHA_*

                          *_LITTAFIN_*
           *_NAFISAT ALIYU FUNTUA_*
                    ((Ummuhfadima))

*_{MAGA YAƘIN KAINUWA⚔️⚔️}_*

*_Bissimillahirrahanirrahim ina miƙa dubun godiyata ga Allah ubangijin talikai da yabani damar cigaba da wannan littafin na INDO AISHA bayan dogon lokaci, ina roƙon Allah da yabani ikon rubuta abindazai amfani al'umma baki ɗaya ya Allah ina roƙon gafarar ka akan abinda zan rubuta na kuskure acikin wannan lbr Allah kayafe mana kura kurammu alfarmar annabi muhammadu s,a,w._*

BABI NA 3~4

Wani irin ihu Indo tasaka wanda saida Haidar ya rufe kunnuwanshi da dukkan hannuwanshi, hakan be isheta ba ta miƙe tana ta tsalle a falon tana kuka "wayyo Baffah na wayyo Baffana" abinda kawai take ta mai mai tawa kenan, shide Haidar yama rasa tacewa ganin da yayi batada nufin bari gashi har tana neman tayiwa kanta da ɗan cikinta illa yasa shi miƙewa da hanzari ya taro ta, fisgewa tayi daga jikinnashi tana cigaba da dire direnta.

         Ƙarfi yasa mata yajawota jikinshi sannan ta natsu tana jan ajiyar zuciya saida yaga ta natsu sannan yace mata "haba my Aysha meye haka kikeyi ne? Kinason kijamin asarar abinda na ƙwallafa rai akanshi ne?" Baki ta turo gaba tace " to bakai bane kace bazakaje dani ba" murmushi yayi yana da ɗa jawota ajikinshi yace "haba my hipness kinsan bazan iya tafiya ba ainabarki ke kaɗai ba kawai fa tsokanarki nakeyi".

        Harar shi tayi sannan tace "Allah tunda kayi min haka saina rama" dariya yayi yace " to aikin riga kingama ramawa wannan faɗuwar gaban dakika sani aita isa" baki ta murgu ɗa mishi tace "yo aikoma meye kai kaja" "tonaji kuma natuba shikenan ko?" Da "eh" ta amsa mishi.

      Ranar Assabar suka shirya tsab abinsu domin tafiya Indo baki har kunne za aje arewa shekara biyar aiba wasa ba, Bashir ne da wasu sojoji sukayi musu rakkiya zuwa ear pot kasancewar shi sai ana gobe ɗaurin aure sannan zasu shigo shida Anty Billy, basu bar ear pot ɗin ba saida suka ga tashin su.

         Misalin ƙarfe 01:30pm jirginsu ya sauka birnin tarayya Abuja, sakkowa sukayi daga jirgin hannuwansu haɗe, duk wanda yakkalesu sai ya ƙara kallonsu saboda dacewar su ga wani irin fittinane kyau dasukayi kasancewar babu wanda yasan da zuwan nasu shiyasa babu wanda yazo tararsu drop ɗin texe ya ɗaukar musu har zuwa gida, a dai dai kata faren get ɗin gidan direban ya tsaya yana horn kamar yadda oga Haidar yabashi dama.

       Me gadin gidanne ya leƙo ganin besan motar ba sai ya fito gaba ɗaya daga get ɗin gidan ya taho leƙa motar yayi, yana cewa "malam wakake nema ne agidannan?" gyaran muryar da Haidar yayi ne yasa me gadin kallon set ɗin baya ai da sauri jiki na ɓari yace "oga ashe kaine tafe don Allah kayi haƙuri wallahi bansani ba shiyasa."Ya idasa maganar yana juya da gudu ya wangale musu get ɗin gidan.

      A parkin space ɗin gidan direban yayi parking sannan Haidar ya buɗe murfin motar yana zuro kyakykyawar ƙafarshi wadda tasha takalmi sau ciki, cikin izza irinta ga wurtattun maza ya fito daga motar, yaza gaya wajen ɗayar ƙofar da Indo take ya buɗe mata hannu ya miƙa mata ta takama hannunshi sanna itama ta zuro ƙafafunta waje, fitowarta daga cikin motar yayi dai dai da fitowa Anty Hafsat daga cikin gidan.

       Da gudu ta juya tayi cikin gidan tana ihun kiran "Mommy! Aisha! dukku fito ga su Yaya Haidar nan shida Indo" Aisha dake kitching tana dafa indomie ai batasan sanda tayo waje aguje ba kota kan kowa bata biba tayo hanyar waje wanda yayi dai dai da sukuma sunkawo zasu shigo cikin falon saura kaɗan suyi gware, da sauri Haidar yajenye Indo wadda tayi baya kamar zata faɗi "keeeeeeeeeeee!!!" yadaka mata tsawa wadda ba ita da akayiwa tsawar ba har ita kanta Indo saida ta tsorata.

          Da sauri tayi baya tana ƙunƙunai jawo Indo yayi domin su shiga cikin falon ƙwace hannunta tayi tayi wurin sister ɗinta tana oyoyo my blood sis rungume juna sukayi, sunata murnan ganin junansu Haidar dayaga alamar ma Indo ta manta dashi kawai sai yashige cikin falon  yabarsu awajen.

       "Assalamu alaikum" yashiga falon bakinshi ɗauke da sallama "Wa'alaikassalamu" Mommy ta amsa mishi fuskarta cike da farin cikin ganin ɗannata wanda Allah ya ɗora mata soyayyarshi fiye da sauran ƴaƴanta tana ɓoyewa ne kawai dan azauna lafiya, murmushi yasakar mata me kwantar da zuciya yace "Mommynah sannu da gida dafatan mun sameku lafya?"

       "Lafiya qlau Gadanga ta howa ba sanarwa?" be ansa mata ba saide dariya kawai dayayi itama bata saurari ansawar tashi ba saboda tasan ba lallai ya amsa ɗin ba saboda ita tafi kowa sanin halin ɗannata na miskilanci.

     Hannushi taja ta zaunar da shi kan kujerar falon ta ɗagashi daga tsugunnon da yayi, Anty Hafsat ce ta fito daga kitching hannunta ɗauke da jus da ruwa ta ajiyewa yayansu tana cewa "yaya sannuku da zuwa ya hanya?" "Lafiya" kawai yace mata Mommy ce ta zuba mishi ruwan a cof ta miƙa mishi, amsa yayi yana murmushi yace "nagode Mommynah" murmushi ta saki tana kallon ɗannata saboda misalta irin murnar da take ciki maba zai yiwuba.

     Hannun su riƙe da najuna suka shigo cikin falon kowansu fuskarshi cike da annurin ganin ɗan'uwanshi, sam hankalin Mommy bekai kansu Indo ba dasuka shigo yanzu ba hankalinta nakan ɗannata wanda ke tambayar ta "Mommy Daddy fa ko baya garine?" Ta amsa mishi da "eh bayanan amma yace min zuwa jibi zai dawo insha Allahu" "huuumm" kawai yace mata.

    "Mommy sannuku da gida dafatan mun sameku lafiya" da sauri ta juyo saboda jin muryar Indo da tayi aiko itaɗince lokaci guda dukkan wata fara'arta ta ɗauke ta haɗe fuska kamar an aiko mata da saƙon mutuwa, kowa a falon da kallo ya bita "Mommy ana gaisheki" Aisha take gaya mata mitsssssssssssssss! wani dogon tsaki taja ta miƙe tabar falon hartaje ƙofar shiga bedroom ɗinta ta juyo tace ina son ganinka aciki ta idasa shigewa abinta ta banko ƙofar ɗakin gwarammmmm................ tofa gwarama ana wata saiga wata fa nide banida tacewa fan's.

*PLEASE READ & SHARE*

ummuhfadima111@gmail.com

RAYUWAR INDO AISHA CIGABAN LITTAFIN INDO AISHAWhere stories live. Discover now