Dan haka ya mai da hankali sosai, inda ya kuma saka wani wasan Chased din, wannan karon yana jin da kwarin gwiwa ke da ra'ayin buga wasan, dan haka koda ya gayyyace su, dariya suka saka. Tare da tabbatar wa zasu yi nasara akan shi.

       •••
Algers.
A hankali tafiya kafaffunta a kumbure, gashin kanta yayi buzu buzu. Duk inda ta tsaya sai an koreta, dan ganin mahaukaciya suke mata,.ita kuwa tsakaninta da Allah take niman danginta.

                  Idan taji yunwa, ta koma gefe ta zubawa titi idanu tana kuka, a yanzun take kuma yarda da cewa. Mahir shine yafi dacewa da rayuwarta, dasuka mata haka da ta zauna ta gaya mishi Tabbas zai kawo ta, gashi bata haddace Number shi ba, balle tayi kokarin kiran shi. Haka tayi kuka har ta godewa Allah.

  Dayawan mutane idan suka ganta jefa mata kudi suke, tare da yan guntun abinci, haka zata dauka tana ci.

      ---
Dr Hisham Abdullahi keluarga
Zaune suke sun saka mahaifiyar su a gaba, tayi shiru tare da juya cokalin dake hannunta.
"Jiya nayi mafarkin Omar da Salha, tare da wata yarinya. Zuciyata tana raya min yar su tana raye,kuma tana bukatar mu a tare da ita"

          "Dadah Insha Allah, zamu nime ta, amma kuma ai zuwan Hussain ya tabbatar ta rasu." Wani hararar shi tayi sannan tace mishi.
"Abubakar! Baka da kirki bata mutu ba, tana raye amma ban san inda take ba."

      "Assalamu alaikum! Tsohuwa me ran karfe!" Inji Dr Naaz.
"Likita bokan Turai, Barka da zuwa ina Saudat da Mahaifinki?"
A hankali ta isa kusa da ita, ta zauna tare da kallon wani katon hotun kakansu.
"Dada mutumin nan yana kama da wata mara lafiya da ta gudu a cikin asibitin mu."

Ta nuna Alhaji Abdullahi keluarga.
"Haba?"
Ta tambaye ta,
"Wallahi yarinyar daga Nigeria take kuma bata san kowa nata ba, tazo niman su. Gashi an mata cunen kayan maye a cikin jakarta karki.."
Mikewa Me girma Minista yayi da Abubakar tare da sauran yan uwan shi.
"Naaz! Ina take Yanzun."
Wayarta ta ciro tare da nuna musu hoton Noorh, aikuwa Dadah tana gani ta fashe da kuka, tana gaya musu jikarta ce.

Kar wani ya shigo mata shashunta sai da Noorh, maza su bazama niman Noorh, Ita kuwa Dr Naaz tasha addu'o'in,.

Ana aka bazama nimanta, sannan Dr Hisham Abdullahi keluarga ya kira Barraq Yayan Maman Noorh ya gaya mishi, Noorh tana kasar amma basu san inda take ba, don Allah ya taimaka musu da sojojin ƙasa a bazama nimanta.

           Haka shima yaje ya gayawa Yan uwan shi, aka fara niman ta.
....
Ni kam tafiya tayi bakin kogi wai tayi wanka, anan ruwa ya kusa. Tafiya da ita, aka samu wasu mutane suka fito da ita, kafarta da ta ji ciwon yana nan sai kara ruruwa yaƙe. Dan jan shi take zunzurutun yana niman lalacewa.
      Haka ta dauki kayanta ta saka tare da barin gurin.
•••
Lagos.
Ganin Mahir ya tarfo su, yasa suka san yadda suka haɗa kai aka sace Dan gidan Hidaya wacce suka tafi mall, aka sa lallai sai Mahir ya janye wasan ko kuma su kashe Yaron. Babu yadda ya iya dole ya hakura da wasan ya janye. Sannan suka bakuci yaje.

Tunda suka maido da yaron, shi kuma suka rike shi. Tare da bashi wahala. Kamar ba zasu barshi ba.
Bayan wata biyu.

       Karshe Baban Nazzir ya fitowa Ummi a mutum sak ya ce ta saka hannu akan takardun su. Babu musu ta saka hannun, sanan ya tafi da Adeemah, yace mata.
"Kamar yadda Mahir yayi min sanadin bakin cikin Y'ata haka kema zan miki sanadin bakin cikin Yarki. Kamar yadda ya gaya min zai bi yar cikina ta baya, haka shima zan saka abu bayan Yarki. Kamar yadda ya cusa min bakin ciki haka ke ma zan cusa miki. Zan bawa Nazzir damar yayi ta kwanciya da ita har sai ta daina motsi."

                 Dariya Ummi tayi sannan tace mishi.
"Da ace Mata zallah na haifa da zan fashe da kuka, amma dana samu Allah ya bani garkuwa,sai bana jin kome jeka da ita,iya cikin gidan nan zaka iya fita da ita,ba sai ka sami damar fita waje da ita ba."

    Haka ya fita da ita, daga gidan. Cikin isa da gadara, sai dai me yan sanda da a suka kewaye shi yasa shi sake yarinyar, murmushi Mahir yayi lokacin da ya fito daga motar yan sanda. Maida glass din shi yayi yana murmushi ya isa inda Yarinyar take ya miqa mata hannun da gudu ya isa jikin shi tana kuka, tare da gaya mishi abinda Baban Nazzir yace.
"Ya isa ina Shbah? Bar kuka karshen su yazo."

Juyawa yayi tare da kallon yan sanda yace musu.
"Karku mishi kome kusaka idanu akan shi, amma Insha Allah jibi za ayi baikona da Tasleem."

Babu musu suna barshi ya tafi sannan suka zagaye gidan su, Tasleem kam tana can Nazzir yana kwakule ta, kuma iyayenta suna makale da su, zunzurutun kwaɗayi.

   Koda aka ce an sace Mahir basu damu ba, kawai abinda suke bukata ayi kome a gama. Dan haka suka mai da hankali akan yar su.

       ... A lissafin Mahir cikin Noorh wata biyar, dan haka yake kokarin ya gama abinda zai yi ya bazama nimanta, sabida rabon shi da ita wata biyu da wasu kwanaki kenan.

Dan haka ya sake kudi aka fara shirin baiko babu b'ata lokaci. Ana gobe baikon ma sai da aka zabga rikici da Nazzir da ita kanta Tasleem din domin ya d'ago tana dauke da cikin shi, dan haka ya fara mata maganar karta kuskura ta zubda mishi ita kuma tayi mishi maganar banza, ya kamata yayi mata dukar kawo wuka.

    Amma iyayen ta dake Mayun kudi ne tura masu kuɗi Baban Nazzir yayi suka yi shiru, amma duk da haka ransu ya b'aci dan tunda suke basu tab'a tunanin zasu daki yar Gwala ba. Sai gashi Nazzir ya mata dukar da sai da aka kwantar da ita asibiti, domin  aman jini tayi ta yi. Tun suna b'oyewa har suka gayawa Mahir abinda ya faru. Cikin ko in kula ta gayawa Ummi.

         Da kanta taje asibitin, ta sami yarinyar cikin mugun yanayi, bincinke aka yi aka gaya musu dukar da aka mata a cikin ta ya tab'a mata hantar ta, shi yasa take anan jini. Sanadin da ya sa Ummi bawa Mahir Umarnin a kama Nazzir da Mahaifin shi. Babu b'ata lokaci aka kama su,

      Iyayen Tasleem kamar zasu yi hauka,.sakamakon jin yar su zata iya rasa rayuwarta. Gashi nan dai basu sami yadda suke su ba, ga yar su a kwance. Dan haka suka tattara da ita suka nufa Algeria.

    Bayan an kama Nazzir da Mahaifin shi, aka garkame su. Inda ake tuhumar sun laifin shirya hatsarin jirgin kasa, sannan aka kuma fitar da sakamakon lalata sunan kamfanin Hamoud Boualem, sannan da kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba. Suka yi ta bankado munanan aiyukan da suka aikata, tare da hana su bill din su. Sannan aka shigar dasu kara akan lokaci.

     Abin da mugun tab'a zuciya, Zoolfa da Mamar ta, guduwa suka yi bayan sun kwashe dukan dukiyar da yake nasu wanda zai taimaka musu yin karamin rayuwar da zasu fara nan gaba.
   •••
A can algeria kuwa, har saukar Alqur'ani ake dan Allah ya bayyana musu Noorh, kullum Dadah sai tayi kuka, Sabida damuwar halin da jikarta ke ciki.
*Sorry Guys! Wallahi zazzaɓi yake damuna Insha Allah zaku ganni gobe idan muna da nisan kwana*

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now