Yana jin haka , ya sake murmushi, yana jin dadin yadda take kokarin kame kanta, da wata yarinyar ce tuni ta sake jiki dashi amma ita ta kasa sakin jiki dashi. A hankali ya cigaba da barci.
....itama a d'akinta kasa barci tayi sakamakon kamshin turaren shi da ya rike mata kaya, haka tayi ta juyi, har kusan karfe uku,kafin barci me nauyi ya dauke ta.

                     Da asubar farko, ta tashi ta gyara jikinta, sannan ta dauko kitchen ɗin ta haɗa abin karyawa tsaf, ta kai falon sama, ta jera mishi sannan ta koma d'akinta ta kwanta, bata kuma farkawa ba, sai karfe goma..tana jin kamar ana sa'in'sa, a hankali ta tashi zata fito. Taji Muryan Mahir yana faɗin.
"Ina ruwanka da rayuwata? Na tab'a bin rayuwar ka? Har kai ka isa ka nima min abokiyar rayuwa? Dat's my Opinions ba wani ne ya isa ya nima min mace da karfin cin tuwo ba. Ko ce aka akayi Ni Womeniser ne?"

"Mahir kana boye wani abu a cikin gidan nan naka?koma meye We shall see, aure kuma kasaka a ranka zaka yi shi domin kuwa Zoolfa itace mafarkin Hajiya."

    Wani wawan shak'a ya kai mishi tare da wullo shi waje, aikuwa take mara mutunci, ya cigaba da gaya mishi magana har da kiran shi dan luwadi, wannan kalmar ta dame shi ainun domin ko bayan tafiyar Nazzir, tsakanin shi da Allah yaji ciwon abun dan haka yaga Noorh sanye da wata doguwar rigar English wear, kawai yana tashi ya nufe ta.

      A hankali take ja da baya, yana kuma Binta har suka isa bangon falon, kafin ya zuba mata idanu, dauke kanta tayi daga kallon shi.
"Wai ni d'an luwadi ne?"
"Wallahi ban san kome ba a wannan rayuwar don Allah ka barni na tafi gurin dangina!"
"Idan na barki zaki dawo gare Ni?'
"Cab'ijam, me zanyi maka me zan karu da kai Ni dai ka barni na tafi gurin dangina."
"Ba zaki tafi ba, sai kin gaya min zaki dawo gare Ni!"
"Wallahi gwara na mutu da a dawo gare ka, akan me?"

   "Me nayi miki? Meye laifinta? Meye laifi" yana tambayar a haukace, wani irin aazabebben tsoron shi ya kamata,  dan haka a takure ta kalle shi.
"Don Allah ka rabu dani, meye nayi maka da ba zaka hakura ka yafe min ba."
Fisgota yayi tare da jefata kirjin shi yana me saka kanta a kafad'arshi, zaro idanu waje tayi. Kwalla na cika mata su, kokari take ta kwace daga jikin shi, ya matsa ta sosai.
         Kukan da take ne ƙasa ƙasa, yayi masifar tasiri a kan shi, kasa saketa yayi yana niman yaga fuskarta, d'ago kanta yayi tare da zuba mata ido,

                  "Baki jin kome a kaina Noorh?" Yayi mata tambayar cikin damuwa.
"Ni bana jin kome?"
"Da gaske?"
"Kana tamtama ne?"
"Me yasa baki jin kome a kaina?"
"Kawai bana son damuwa ne, kuma Ni zuciyata tana inda ya dace"

     "Ok!" Ya janye daga jikin ta, yana sauke ajiyar zuciya, ya wuce dakin shi baki daya.
Bai kula ta ba ma, itama bata damu ba, ta juya zata wuce taga shigowar Haroon, suka shiga kitchen, a tare suka yi abincin ranar, sam Mahir baya cikin nutsuwar shi, dakyar ya shirya tare da barin d'akin, yana fitowa falon yaji muryan Haroon da Noorh ana ta hira.

    Abin ya kona mishi, wato shine D'an iska ba zata mu'amalance shi da mutunci ba, sai wasu mutane na daban, kwafa yayi tare da barin gidan baki daya. Tunda ya isa gidan Ummi ya sameta tana shirin fita, zuba mishi ido tayi kafin tace mishi.
"Da na tura Nazzir ya kira ka shine ka ki zuwa, sannan ka buge da cin mutuncin shi."
        Shafa kanshi yayi tare da kallonta, sannan ya  dashi.
"Kiyi hakuri!"

Duk sai taji babu dad'i, ta kuma shi cikin kulawa tace mishi.
"Me yasa baka son ana zuba gidanka ko akwai abinda kake b'oyewa ne?"
A firgice ya kalle ta, can kuma ya wani boye razanar shi..
"Ni kuma? A'a kawai."
"Idan na kuma jin kana hana mutane shiga gidanka zan je naga abinda kake b'oyewa."
"Toh Ummi, babu kome ma a gidan."
Yadda yayi maganar sai da jikinta yayi sanyi, bata son fara zargin shi, domin kamar ta bashi kofar aikata abinda bai yi a baya ba.

   Shiga gurin Hajiya yayi itama ta kare mishi zagi, sannan ta kuma gaya mishi cewa an tsayar da maganar shi da Zoolfah, cikin b'acin rai yace mata..
"Wallahi kika Kuskura kika makala min ita, sai na saketa ana daura auren."

MAH~NOOR🌹Kde žijí příběhy. Začni objevovat