"Mahir!"
D'ago shanyayyun idanun shi yayi akan Hajiya kaka.
"Ince baka da hannu a cikin wannan lamari!"
Wani karamin murmushi yayi, sannan ya cigaba da abinda yake yi.
"Baka ce kome ba?"
"Hajiya babu hannuna a cikin, yarinyar nan na."
"Kame? Nasan baka iya karya ba, karka fara akan wannan al'amarin."
"Hajiya na sami Parent ɗinta, suka ce ba yarsu bace, a gidan marayu na jos suka daukota, shi yasa na turata can."

"Son Yaushe ka fara?"
"Ummi zan miki karya ne?"
"Kawai yadda kake maganar kamar akwai wata a kasa."
"Mh"
Yace mata,.yana gama cin abincin ya mike tare da nufar cikin Mansion din su, bin shi suka yi da ido, faruwan Al'amarin ya sanya su kara fahimtar wani abu, domin bai cika tashin hankali ba, amma haduwar shi da yarinyar da ta gallabe shi, ta saka shi iya jan dogon magana.

         **
Yana isa gidan shi,.ya kira Likitan. Nan take gaya mishi ai badan ya kawo ta akan lokaci ba, toh ba makawa mutuwa zata yi domin yanzun haka ana bukatar jini ne.
Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya shiga dakin shi ya dauki key din ranger  da sauri ya fita,.kai tsaye asibitin da yake agege ya nufa, aka gwada jinin shi.

          Lumshe idanun shi yayi lokacin da ake diban jinin, ana gamawa ya mike tare da jingina da bangon dakin, yana sauke ajiyar zuciya, sai da yakai minti ashirin da biyar, kafin ya sauka ya kira Abokin shi Brrst Usman Kamfut, ya kai shi gida. Kota kan Noorh bai bi ba.

         --- kwana biyu kacal yayi bai leko ko falon shi ba, Haroon yake mishi kome, tare da kai mishi abincin shi, da duk wani abinda yake bukata, yana kuma bibiyar lafiyar Noorh, daga gidan shi, shiryawa yayi yau cikin kananun kaya sannan ya nufi gidan su. Da kafa yake takawa, hango motar Nazzir yayi. Ya dauke kanshi kamar bai ga gidan su ba.

      Har yazo zai wuce, Nazzir yace mishi.
"Lion!"
Kallo daya yayi mishi tare da murmushin ina jinka.
"Baka ji labarin an rufe Kamfanin bane?"
"Ni na tura musu da a rufe Kamfanin bayan na saka an biya mutanen da suke aiki da kamfanin Hakkokin su."

     "Amma kaji labarin mutuwar yarinyar nan? Da fatan babu hannunka a cikin?"
Wani irin jan iska yayi tare da fesarwa, sannan ya wuce abinshi yana faɗin.
"Haka nima naji!"
"Wai meye nayi maka ne?"
"Me yasa kake zargin kanka?"
"Ni kuma? Akan me zan zargi kaina bayan kai ne kake nuna min halin ko in kula!"
"Toh shikenan daga yau zan na kulaka."
Daga haka ya wuce abun shi, cikin bakin ciki da damuwa yabi bayan Mahir da harara, kome nashi sai ya nuna iko akai,nan gaba ma sai ya nunawa duniya shine yake juya mutane.

     Da wannan ya kad'a kai yayi tare da shigewa gidan shi yayi dan ya dauko wata kodaddiyar yarinya ce, zai rage dare da Ita.
  •••Sosai ya tsakuri abincin da aka dafa mishi, yana ci abincin Zoolfa da Kanwar shi suka shigo gidan, hango shi a saman table yasa suka nutsu, yana gamawa ya mike tare da ɗaukar wayar shi da Key din Motar Ummi, ya juya zai fita, ya juyo muryan Zoolfa tana faɗin.
"Allah kasa Ya Mahir ya aure ni!"
Wani karamin murmushi yayi, sannan ya juya tare da kallonta, a tsorace ta sunkuyar da kanta.

     Sanan ya saka kai ya fita, a ranshi yace. "Faduwa tazo dai dai da zama"
Sannan ya fice daga gidan baki daya, yana kara nazarin yadda zai duba masu bin bayan shi.

    .. lokacin da ya isa asibitin ya same ta, ta farka, kanta sunkuye sumar kanta ya basu a fuskarta da kafad'arta, yadda yake ɗaukar idanu ya sashi nazarin yanayin jinsin mutanen da tafito, kallon kafad'ar ta yayi wanda yake waje, sai rigar da wandon da aka saka mata, a kai kaice yake hango tudun kirjinta, da yadda dukiyar fulaninta ya taso cur, har wani kara tsini suka yi, ga bakin yayi wani daukar ido a cikin rigar, dukar goshinsa yayi cikin nutsuwa, sannan ya isa gabanta yaja kujeran dakin ya zauna tare da Crossing leg din shi.
"Zombia!"
D'ago kai tayi kamar tasan sunan nata ne,
Tashi yayi tare da tattara mata gashin kanta, ya kai bayanta ya kalli yadda idanunta suka yi jajjur.
Rike hannun ta yayi ya kwace tare da yin baya, kallonta yayi yadda take murza yatsun hannunta, rike hannun yayi ta nemi kwacewa, ya kuma rikewa, ihu ta fasa mishi tare da niman faduwa, nurse suka shigo da Dr.
"Ku bani Alluran!"
Ihun take tana kokarin kwacewa, tare da kai musu duka. Idan yakai alluran zai mata sai ta kai musu dukkan tare da fasa ihu, a hankali ya taso, sannan ya isa gurin su, ture hannunsu yayi sannan ya rungume ta, tana ihu, tana kome, haka ya daura kanta a kirjinshi, kuka tasaka tare da shasheka.
"Ayna Ammyn! Waina Abbi! Muhabub! Nimrah!"

"Tab'jam! Dr mike faruwa kuma?"
"Kamar ta manta wasu abinda ya faru ne ko nace kamar akwai wani boyayyen matsalar da ta sami brain ɗinta, domin tinda ta farka bata magana kuma bata cewa kowa kome, sai dai Kamar larabci ne kawai take."

          Komawa tayi ta kwanta,.tuni barci ya dauketa,.kallon kafar da aka daure yayi, tare da bin zararran yatsun kafarta da ido, ajiyar zuciya ya sauke, sannan yace.
"Ko zaku bincika brain ɗinta, bana son wani abu ya same ta?"

     Yadda yayi maganar zaka Fahimci daga kasar zuciyar shi yayi, gyada kai Dr yayi take ya bada umarnin a kaita dakin bincike, tare da mahir ɗin hada hannun shi yayi yana zirga zirga, ya kasa tsayuwa guri guda, zunzurutun tashin hankali, tsoron shi karta sami matsalar da zai iya shafar rayuwarta da tayi abaya, yana bukatar wani abu daga gareta, matukar haka ya faru, Tabbas ya kwala kai kuma yayi biyu babu, domin bai da yadda zai dawo da kamfanin shi.
             A hankali ake dauko hoton ƙwaƙwalwar ta, suna exam dinshi. Sun kai awa daya da rabi ana abu daya, haka zasu duba dubawa, can Allah ya taimaka suka fara samun abinda suke bukata, kallon juna Dr suka yi da wasu abokan aikin shi, sannan suka kalli Mahir, dayan su yace.
"Sake duba mana ciwon ya kai tsawon wani lokaci ne?"
Sake zooming suka yi suka ci-gaba da aikin su. Jikin mahir yayi mugun sanyi, yana kallon yadda suke tattaunawa akan matsalar ta.
"Amma abin da tashin hankali, tsawon wannan lokacin babu wani treatment? Baka ganin zai iya zama cancer?"
"Wannan wani irin shirme ne?!"
"Sir Mahir! Ka nutsu akwai matsala"
Sake dubawa suka dayan yace.
"Gaskiya ya jima! Kuma bai wani samun kulawar Asibiti ba, da ace an sami haka ba mamaki ba zai zauna haka ba, kuma yanzun babban tashin hankalin matukar ta farka tana bukatar wani na jikinta. Domin haka ne kawai zai rage mata tasirin ciwon, domin ya tab'a wancan gefen ƙwaƙwalwar ta, cizon karen nan ne ya dawo da shi sabo."

   "Wai me kuke nufi dani ne? Meye ya same ta? Ba zaku gaya min ba?" Ya faɗa a tsawace.
Dafa shi Dr yayi tare da bude baki zai mishi magana, ya ture hannun shi.
"Meye ya sami Noorhhhhh!"
"Sir, yarinyar ta sami Matsala ne muke hasashen tun da jimawa, abin bayi tasiri ba, sai cizon da kare yayi mata tare da buga kanta, shine karfin tasirin abun.

    Amma ka bincika mana wani abu ko zamu sami masalaha ga yadda zamu sha kan matsalarta, but am sorry, sabida any more zata iya samun da sai..."
"But me yasa kuke magana akan Cancer?"....🤨 A hankali dai makiya na kuma samun Approched. Indai dan Noorh ne kake tsawar ba zai hana idan ta tashi ta falla maka Iskancin ba..

MAH~NOOR🌹Where stories live. Discover now