13

98 3 0
                                    

      ♡
                  ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

  _★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

 
  *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

                *BABI NA SHA UKU♡*
___________________________________

                     1️⃣3️⃣

Har tayi shirin kwanciya kenan sai taji wayar da Abba ya bata na ruri, sai bada sautin booomm!booomm! yake kasancewar ah vibration ta saka wayar.Sunan data gani na yawo ajikin screen ne ya kad'a hantar cikinta wato *ZAID...* Nanata sunan ta shiga yi aranta don ah iya saninta bata da wani Zaid acikin saved contacts d'inta, dadin dad'awar ma bata da wani mai suna Zaid da take huld'a dashi.Can ta tuna Abba yayi saving wani lamba awayar har yake fad'a mata cewa za'a k'irata, Kai tsaye ta bawa kanta tabbacin lallai babu tantama shi d'in ne yake k'ira.Gabanta ne ya shiga bugawa da sauri da sauri, idanunta akan wayar harta katse bata daga ba.Akaro na Uku da aka sake doko k'ira, sai daya kusan tsinkewa sa'annan ta daga, Shiru tayi mishi taki magana, ab'angarensa kuma wawan ajiyar zuciya ya sauke, daqyar ya lalubo muryarsa dake can k'asa yace"Haba Gimbiya Zeey wani laifin ne nayi haka da har aka horani kafin adaga k'irana.?"Kamar bazata yi magana ba sai kuma tace cike da mamaki"Ban gane ba, ya za'ai ka k'irani akaron farko sannan kace ko Laifi ne kamun da har yasa nake horaka.?azatona ni dakai bamu ma tab'a ganawa ba, yau ne karon Farko."saurin taran numfashinta yayi"Haba masoyiya ban sanki da tsiwa bafa, ah iya sanin da nayi wa masoyiyata k'yakk'yawace mai yawan fara'a a fuska, akalamai kuma tana da dad'in zance, wlh Zainab kina matuk'ar burgeni, sam baki da girman kai, mu'amalarki da mutane kuma abun sha'awa ne, Zainab gaki da hak'uri kuma inason ki cigaba da wannan hak'urin watarana zaki ci ribarsa."Wani irin juyi ne tayi akan gado, da alamun sosai hirar ke mata dadi tsakaninta da wannan bak'on da bata san ko waye shi d'in ba, Cikin sassanyar murya tace"Bawan Allah haka kayi wa Zainab sanin gaske.?kusan zan iya cewa kama fini sanin kaina." Kasaitaccen dariya ya d'an saki mai burgewa, shi karan kansa dadi ne ya lullub'eshi ganin kamar bazai wani sha wahalar samo kanta ba.Yace"Sanin da nayi miki Zainab ai ya wuce yadda ma kike zato, kamun kanki da kuma nagartattun halayenki  su suke kara kwadaitamun son naga na mallakeki amatsayin matar aurena! Ina fatar ya'yana zasu samu irin wannan tarbiya.?" Jin zancensa tayi tamk'ar saukan aradu, cike da rashin fahimta tace"Ya kake mun zancen aure bayan ban sanka ba.?meyasa baka fito fili ka nuna mun kanka ba sai kawai ka biyo ta hanyar mahaifina.?Ko kuwa azatonka bazan karbi tayinka bane shiyasa kaji tsoro kabi ta kafar mahaifina.?"

Girgiza kai yayi tamk'ar yana gabanta yace"No No No ba tsoro naji ba Zainab illa nabi hanyar da addini yace ayi ne, ance idan kaga wata yarinya wacce kakeso, To farkon abunda ya dace kayi shine kayi kokarin neman izinin manyanta kafin ka fara tsayuwa da ita.Zaka iya sanar da ita cewa kana sonta ta hanyar wani abokinka ko Qawarta ammh ba zaka fara karban lambarta ko kuma zance da ita kai tsaye ba har sai da amincewar magabatanta, Wanda hakan shine nayi, na bi tsarin komi amusulunce, Don haka abunda nakeson ki sani shine tare da izinin magabantanmu duka nake wannan zancen dake." Ko da wasa bai yi gangancin goranta mata ba, don kuwa inda ace wani ne yana iya mata gori yace ai Abbanta da kansa ya sameshi ya rok'eshi akan ya aureta.Ammh tunanin hakan bai yi gigin fad'o ran Zaid ba.Shi k'ok'ari ma yake ya koyawa zuciyarsa sonta don ko kadan bata da wani makusa atattare da ita, sai ma ababen So data tara.

"Shi Abban bai fad'a maka cewar ina da wanda nakeso bane.?" Tayi kokarin kawar da dogon silent d'insu.Cike da mamaki yace"Ni bai sanar dani zancen wani ma neminki ba, watakila bai san dashi ba don kin sani sarai ba kowa ne yake bin irin tsarin dani nabi ba, ko kuma yana sane dashi ammh dai gamsuwa da halayensa ne bai yi ba sai nawa, ko kuma a'ah ya bawa kowa damarsa ne ya gwada sa'arsa, kenan kowa ya iya allonsa sai ya wanke fakat! Kuma ina rok'on Allah ya bawa mai rabo sa'a, in nine na sameki Alhamdulillah! In kuma shine to haka Allah yaso, Fatana ayanzu dai Allah ya had'aki da wanda zai soki ya kuma ji tausayinki aduk halin da kika tsinci kanki, Zainab bana son kije inda za'a wulakanta mun ke, Ki zauna kiyi nazari dak'yau akanmu dukah, Nasan baki sanni ba ammh idan kin ganni azahiri zaki Tuna dani, sai dai kuma ina rok'onki alfarma, muddin ki ga ganni banason ki raya wani abu aranki don bani da mugun nufi akanki, hasalima ma in har akan lamuran da suka shafeki ne to fa zuciyata wankakkiya ce, Tun ba yau ba i always want the best for u, Kuma bani son ki ritsa Abbanki da tambayoyi akaina, i dnt want that why? and how? Questions don yin hakan zai sa ki rud'ashi sosai, Tashin hankalinki zai sakashi shiga cikin cakwak'iya, Ki sani Abbanki bazai tab'a zab'a miki abunda zai cutar da rayuwarki ba, Mutumin nan ba shine ya haifeki ba ammh i can swear that yafi son farin cikinki akan nashi, Dan girman Allah do him a favour by accepting me, Ki rungumi kaddararki ayadda tazo miki don tabbas ni *ZAID* ni nike shirin zamowa kaddararki *ZAINAB* , Karbana amatsayin mijin aurenki shine kadai zaisa ki dawwamar da Abbanki cikin Farin ciki, sab'anin hakan kuma Astagfirullah ba fata ake ba yana iya janyo masa wani matsalar sabida sosai ya yadda dake, kai tsaye yace mun bazaki tab'a bashi kunya ba, So pls Zainab kar in cikaki da surutu zan k'yaleki ki shawarta da zuciyarki, zan baki kwanaki uku kacal asannan kin gama yanke duk wani hukunci kafin in k'iraki, in kin amince dani sai in bayyana agareki sa'annan na turo magabatana, in kuma kinki to shikenan ba sai kin wahalar da kanki wajen sanina ba." izuwa yanzu shesshek'a take, ga jikinta daya dauki rawa sosai, kanta ya cunkushe yayi duhu, daga shi har Abban sun jefata cikin cakwak'iya, cike da rawar murya tace"Zaid dan girman Allah na rokek'a ka bayyana mun kanka, nayi maka alk'awari zan sharewa Abbana hawaye, bazan tab'a bashi kunya ba kamar yadda dai ya fad'a maka don na sani sarai shi d'in mai sona ne, bani da kamarsa acikin duniyata, Abbana bazai tab'a zab'amun abunda ba daidai ba, Komi ya sameni in har daga Abbana ne to tabbas alheri ne, Ka sani Zaid koda baka kwanta mun arai ba tunda har shi Abbana ka kwanta mishi arai to fa ka sanya ranka a inuwa don ka gama samun *ZAINABU*." Tana gama fadin hakan tayi saurin yanke call d'in tana cizgar kuka.Shikenan yanzu zuciyarta ba zata tab'a samun abunda takeso ba sai Wani Zaid.?kodayake ita kadai ce ke haukarta ammh shi wanda take neman kashe kanta akansa bai ma san da zamanta doron kasa ba.Can taji k'arar sak'o ya shigo wayarta, Tana dubawa taga ai sak'on daga Zaid ne.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now