10

94 1 0
                                    

          ♡
                  ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

 
_★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

        *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

  *°DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_

__________________________________

                 *BABI NA GOMA♡*
___________________________________

               
                       1️⃣0️⃣

........ *Juma'a* Rana ce da hausawa ke yin k'irari da Hajji, babbar Rana.Sai dai bana farin ciki biyu ne ya riski musulmai, Sallar Juma'a da kuma hawa idin babbar Sallah.In ji wani Sheikh Ibrahim Khalil yace"Babban makasudin idi shi ne sanya wa mutane farin ciki, don kuwa rai dangin goro ne, ban iska yake so. Dan'adam yana bukatar samun farin ciki lokaci zuwa lokaci.atak'aice dai sallar idi ma'anarsa farin ciki wanda yake maimaituwa.Kowa ka gani awannan ranar Fuskarsa dauke yake da tsantsar Farin ciki, Zuciyar nan kuma fal nishad'i domin kuwa ayau d'in ranar Fed'e Fed'e ce da kuma yanke yanke.Su Najlat an bada himma ana girkin Surukai, Ummi na tayata don izuwa yanzu ta soma sakar mata fuska ammh d'ar-d'ar Ummin take da ita don kwata kwata bata yadda da wannan sabon sauyin da aka samu ba.Najlat Sai raye-rayen wak'an Farin ciki Take, Ludayin miya ta tumbula acikin miyan taushen dake tururi akan wuta Tana d'and'ana taste d'insa, Ummanta nacan gefe Tana suyan Sinasir, kasancewar sosai Hajiyar Abul ke k'aunarsa shiyasa suka ci alwashin Faranta mata rai ayau kadai.Kodayake ko dama can sun saba kai mata girkin Sallah ammh bana na musamman ne Wanda su kadai suka san dalilinsu na hakan.A b'angare d'aya kuma Ummi ce ke had'a Lemon karas sanin da Tayi na cewar Hajiya na sonsa sosai, shiyasa aka bar mata Wannan d'awainiyar.Najlat da Ummah ka barsu kawai d'uwawunsu d'aya.Basu b'oyewa juna komi, domin kuwa ita kanta Umman nan da nan take tayi da Ummi kasancewar Najlat ta feshe mata labarin yadda sukai da K'awarta Surayya, Shiyasa take k'okarin Tayata Jan Ummin ajiki, ammh sarai ita Ummin ke ankare dasu. "Charkwai! Lallai Ummah agaisheki Wannan miyan Taushen yasin d'and'anonta har k'wak'walwa yake kai wa, Duk wanda yaci sai ya sara mana, Ummana you are the best cook, babu wacce zata Nuna miki iya girki."
K'yalk'yacewa da dariya Umman tayi tana Fadin"Najlat an gaya miki Ni d'in ta wasa ce.?idan suka ci Wannan girkin dole ne su raina kansu, Ga Sinasir d'in Tayi k'yau sosai bata k'one ba." Najlat tace"Eh! Wlh Ummah Tayi k'yau sosai, dan Allah ki koyamin yadda ake yinta don kwata kwata Ni ban iya girke-girken gargajiyan nan ba." Harara Umma ta watsa mata Tace"Ina fa zaki iya Tunda baki zama kusa ki ga yadda akeyi, ke dai abarki kawai da k'ak'alen abinciccikan zamani wanda basa Wani k'osar da cikin Mutum, Kuma ina rayuwa zata tafi ahakan ace ba'a had'a wa dana gargajiyan.?" Cuno baki gaba tayi tana Fadin"Kai ni Ummah wlh ban cika son abinciccikan gargajiyan bane, wlh ko agidan Mijina bazan dunga tuk'a Tuwo ba, babu Ruwanmu dashi, kai infact girkin ma ba kullum zan tayi ba, Tunda dai Allah ya had'a ni da Miji mai abun hannu, kin ga basai na dunga Takura kaina ina shiga kitchen ba, Kawai gidan abinci zamu dunga Zuwa." Dariya ne yaso kufcewa Ummi ammh sai ta nok'e Tana sauraronsu, Umma tace cike da Tsokana"Lallai kuwa kuna da aiki agabanku, Najlat Allah ne dai kawai ya taimakeki daya had'aki da Mai kudi in ba haka ba da talaka ne zai yi wuf dake ai da kinji jiki.." saurin Taran numfashinta tayi Tana yarfe hannu"I reject it Ummah, ai ni idan kinga na had'a iri da Talaka to ma'aikaci ne agidana wlh."

"Uhmmm!.." shine abunda Ummi Tace.
"Ke! Miye na wani Uhmm.?" Najlat ta watsa mata tambaya, bata tankata ba ta cigaba da juya Lemonta da wani cup don tabbatar da cewa sugar yayi daidai.Ummah ma cigaba Tayi da tuyanta, Tana yi tana koyawa ita Najlat d'in yadda ake had'a Sinasir.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now