06

121 3 1
                                    

      ♡
                  ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

  _★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

 

       *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

                *BABI NA SHIDDA♡*
___________________________________

     ↗0⃣6️⃣

............Tunda Suka fito har suka tsaya siyen magunguna kwata kwata Ummi bata sake gane kan Abba ba, da alamun yana cikin damuwa Kuma ta lura kamar bayason su had'a ido, Sai kau da kai yake tayi har Suka kamo hanya.

Sun d'anyi tafiya mai nisa don har sunyi rabin hanya, Tafiya kadan ne yayi saura su isa gida, Sai kawai taga ya gangara gefen titi ya paka motar.
Bai ce da ita kala ba ya kifa kansa asaman sitiyari, ya dauki tsawon mintina 2 ahakan, Can taji ya hau shesshek'a yana magana kasa kasa, Muryarsa bata fita sosai balle kaji abunda yake fadi.Abunda kawai ta iya tsinta acikin zancen nasa shine Sunanta daya ambata.

Gabanta ya tsananta bugawa, Hankalinta ya tashi ainun, Ji tayi itama ta rushe da kukan, Jikinta ya dauki rawa sosai don bata tab'a b'atawa Abbanta rai har haka ba.Shikenan anyi nasarar shiga tsakaninsu.

Kukanta ne ya maido dashi Cikin hayyacinsa, arud'e ya dago yana dubanta yace"Ummina meya faru?kodai jikin ne?"

"Abbana Sun shiga tsakaninmu! Ammh dan girman Allah Abbana ka yarda dani ni wallahi ban ma da Saurayi balle nayi Tunanin Zuwa wajensa akodayaushe.Sharri kawai suka kullamun don adasa kiyayya atsakanina dakai, Abba na rokeka kabar Zubar da hawayenka akaina, Allah ne shaidana bana aikata abunda suke Tuhumata akai..."

Ta ida magana tare da sakin Wani sabon kukan Tana girgiza kai Wanda zai tabbatar maka da cewa iya gaskiyarta ne ta fad'a.

Ah rud'e Abba yasa hannu yana tab'a fuskarsa don har ga Allah Shi bai san cewa Kuka yake har taji shi ba.

"Ummina waya fad'a miki kuka nake?Sa'annan waya ce ban yadda dake ba?Wallahi Zainab nafi Kowa Sanin irin tarbiyar da dan'uwana Dauda ya baki Tun kafin ki Komo hannuna, Koda kika komo hannun nawa, Rashin kulawar da Karima take Nunawa akanki hakan bai sa ko kadan kiyi Tunanin watsar da tarbiyar da aka baki ba, Zainab ina matukar alfahari dake, Zainab ah iya tsawon rayuwarki kin min biyayyar dako wanda yake amsa Sunan mahaifinki baki masa shi ba, Zainab ki sani ko kasheni za'ai bazan tab'a yadda da abunda Suka fadi akanki ba, sunyi ne don su aibantaki sannan kuma su b'ataki awurina, Sai dai kuma sunyi babban kuskure, Zainab su Karima Sun dad'e suna cutar mun dake ammh ban dauki Wani kwakkwarar mataki akai ba, Na biyewa Zurfin Cikinki na nannad'e hannu ina kallo banyi komi akai ba, Sai kurin banza Wanda ayanzu nake nadamar hakan, Ashe abunda ban sani ba Shine inata nakasa rayuwarki ne, Na bari Su Karima Suna ta k'unsa miki damuwa har takai ga shafar lafiyarki, Yanzu kina ganin Dauda Zai tab'a yafemin?"

Karki ji kunya ki gayamun kina ganin Mutum kamarni Zai samu rahamar Ubangiji bayan ya wulakanta rayuwar Marainiyar Allah?"

Cike da rud'ani ta katseshi Tana sharar hawaye"Abbana ban tari numfashinka ba, dan Allah me kake nufi da maganganunka don kwata kwata ban fahimci inda ka dosa ba..."

"Zainab Likita ya shaidamun cewa ciwon hawan jini ke dab da kamaki Muddin bamu kiyaye ba, tou wake da alhakin Wannan ciwo naki in banda ni? Ban tab'a matsa miki akan ki fadan damuwarki ba, haka Zalika ban tab'a takuraki ki gayan Abunda kikeso ba, Kullum hak'uri nake baki Wanda tun zuciyarki tana k'arba har tazo ta gaza, ban Sani ba ashe babbar illa nake ta tanadar mata, Yanzu irin Sakayyar dazan wa dan'uwana kenan? Na bari har 'yarsa mai k'ankantar Shekaru ta Kamu da Hawan jini akan Rashin kulawana?"

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now