03

134 2 0
                                    

            ♡
                  ♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
          _(The Elephant's Foot)_

  _★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

 

       *FInd out💥*
     

       *WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*
          
_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_
__________________________________

                *BABI NA UKU♡*
___________________________________

     ↗0⃣3️⃣

"Tabbas Ta shigo dubani dazun ammh bata Wani jima ba ta wuce, Shine ta turo yar’uwarta Ummi hadda kayan dubiya ma wallahi, Ka ganta nan ma Zaune bata wuce ba...’’
Hajiya ta fada tana duban Ummi wacce wawan ajiyar Zuciya ya kufce mata ganin Hajiya ta rufe gaskiyar Zance.
Tayi kokarin kare yar’uwar tata.
Abul yace"Hajiya kin tabbata tazo...?’’
Rage fara’ar fuskarta tayi Tana fadin"Ai! Ni zan maka karya ne Bawan Allah...?kodai ka dena yarda dani ne in sani Tun wuri.....’’
Ajiyar zuciya ya Sauke ba don ya yarda da Zancenta ba dai yace"A’ah wallahi ko daya, Na yarda da Zancenki Hajiyata, agaida ita Ummin Muna godiya....’’
Kayatacciyar Murmushi Hajiyar ta saki tana fadin"Ai wallahi baka ga yadda Ummin take nan da nan dani ba, Ko gud'a fa batason ya rabi inda nake, Yau har ciyar dani tayi sai dana kat sa’annan ta rabu dani, Yanzu haka ma magungunana nake shirin Sha shine ka kira.....’’
Farin ciki mara misaltuwa ne Ya mamaye ilahirin Zuciyarsa, arayuwarsa Yana tsananin kauna da kuma begen mahaifiyarsa, Duk kuma mutumin da zaya gwada mata k'auna koda kuwa na minti daya ne tou fa wannan d'in ya zama masoyinsa.
Ummi kuwa sai murmushi take ta zubawa tana jin yadda k'aunar wannan 'yar talikar matar ke sake hud'a duk wata gaba da jini ke gudana acikin jikinta.

"Hajiya naji dadi sosai wallahi, Ki sani duk wani wanda zai nuna miki k'auna da kulawa koda na second guda ne toufa wannan d'in Sunansa masoyi agareni, Don girman Allah bani ita Ummin mu gaisa sa’annan na mik'a godiyata agareta da irin kulawar da take gwadawa Uwar data kawoni duniya.......’’
Hajiya jiki na Rawa ta mik'a mata wayar.
Afarko tsuru tsuru da idanuwa tayi kan daga bisani ta karba gabanta na harbawa da sauri dasauri.
Hajiya da Nana suka kura mata na mujiya kowanne da bikin da zuciyarsa ke raya masa agame da halittun biyu.

"Salam alayk Yah Abul kana lfy?Ya Ibadah?Ina kuma Alhaji Abbi?’’
Ta jero masa wa’ennan Tambayoyin alokaci gud'a.
Yace yana fadada fara’arsa"Duk muna lfy, Ummi Zainab idan na fadi daidai ko?’’
Kwarai taji mamaki dayasan ainihin Sunanta, kodayake kuma ba abun mamakin bane Tunda ayanzu mutum ake kiwo ba dabba ba.

Tace"Haka yake *UMMI ZAINAB* ....fadi ka kara yayanah...’’
Lumshe idanu yayi don sosai dama yake yabawa hankalin da ake ikrarin tana dashi, Sai dai ba fiya shiga sabgarta yake ba in ba yau ba, Ya tsokaneta sosai har yake ce mata ta kusa Zamowa tashi Nan da Sati uku masu Zuwa.Wato dai wasa yake mata amatsayinta na k'anwar Najlat.
Hajiya da Nana sai dariya suke ta saki kasa kasa domin kuwa sosai abun yayi musu dadi, Ji suke inama ace da gasken itace zata zamo matar tasa ba ita Najlat d'in ba.        
Ita Kuwa Ummi sai taji gabaki daya wasar bata mata dadi ba ko kadan, yake kawai take ta masa ammh kam gabanta sai dukan uku uku yake tayi, Gani take kamar hakan na iya kasancewa gaskiya......
Katse Mata tunani yayi"Kodai har kin soma fargaban Shigowa gidan nawa ne da wuri haka naga kinyi Shiru..?’’

"Kai Yah Abul tadai soma.....’’
Gaba daya aka saka dariya don yadda tayi maganar dole zaisa ka dara, Abul akwai son barkwanci, Kuma bai taba mata wasa ba kamar yau don har mamaki ita kanta takeyi ganin yadda ya zage yana tsokanarta, hakan baya rasa dalili da kasancewarsa Cikin farin cikin abunda mahaifiyarsa ta fadi masa agame da Ummin, Wato yad da take nuna damuwa akanta.
Can Yakoma wata zancen bayan yaci Serious"Ahmm..! Zainab Sannu da kokari Hajiya ta fad'a mun yadda kike kular mun da ita, bazan iya misalta miki irin farin cikin da kika jefani ciki ba, domin kuwa duk wanda zai kaunace mahaifiyata tamk'ar nine ya kaunata, Nagode sosai Zainab kuma ki sani daga yau ke ba marainiya bace, idan ma kina yiwa kanki kallon hakane tou maza ki daina domin kuwa kina da Hajiyarmu, Inaso ki dauketa amatsayin Mahaifiya kinji ko...?’’

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now