05

144 1 0
                                    


♡ ♡
_*🐘SAWUN GIWA...!*_
_(The Elephant's Foot)_

_★For How Long Will The Elephant's Foot Be Radioactive?_

*FInd out💥*

*WATTPAD*➖ _HAFNANCY01_

*DEDICATED TO:-Mamina (Sis Nerja'art & Yayata (Ummudilshad)*

_*•SPECIAL GIFT TO:-Tawar (Maman Kausy)*_

__________________________________

*BABI NA BIYAR♡*
___________________________________

↗0⃣5️⃣

................ _ASIBITIN DUTSE_ dake _POLY ROAD_ Abba yakai Ummi, Wanda asibiti ne da suka saba zuwa idan basu da lfy, hatta haihuwar Idrisu da Najlat anan ne aka karba, Sosai Abba ke yabawa aikinsu, shiyasa da zarar Wani yace yana jin koda ciwon kai ne sai kaji yace maza shirya muje Asibitin Dutse.

Malaria Fever ke damun Ummi don haka akai mata allurai biyu atake, sannan aka rubuta mata magungunan da zata siya ah pharmacy dake can wajen asibitin.

Likitansu Abba Dr.Hashim Wanda shine ya saba duba iyalen shi Abban, yace ya biyoshi office dakwai maganar da yakeson su tattaunawa akai.

Abba bai ci musu ba yabi bayansa da sauri sauri, yabar Ummi awajen wata Nurse.

Abba na shiga ya tarar already Wani na jiran shigowar shi Likitan ne, Sai daya jira suka gama tattaunawa ya sallameshi sa'annan ya dubi Abba, Zare farin gilashin daya mak'ala ah idonsa yayi yana mai sauke ajiyar zuciya ajere.

"Alhaji nasan zakai mamakin jawoka da nayi Zuwa ofis bayan na sallameku ko?"

Abba yace"Eh! agaskiya nayi mamaki, meke faruwa ne halan? Ko dakwai wata matsalarce daban?"

Dr.Hashim yace"Kwarai kuwa, dalilin dayasa na bukaci kebancewa dakai kenan don mu tattauna..." Gaban Abba ya buga, cike da fargaba yace"Me....me...menene ke damun 'yata kuma bayan Zazzab'i?"

"Hawan jini ne yake gab da kamata......."

Ah kid'ime Abba ya mik'e jiki na rawa yake fadin"Whattttt???"

"Dr.Hashim ko kasan abunda yafito daga bakinka kuwa? Taya za'ai yarinya kank'anuwa kamar Ummi ace tana da hawan jini?She is just 22 fa?"

Abba ya furta cike da damuwa, Tuni Hawaye ya tarun masa acikin kwarmin ido, Dr.Hashim ne ya shiga kwantar masa da hankali kana yacigaba da jawabinsa bayan ya tabbatar Abba ya d'an natsu.

"Wato Ni kaina abun ya shayar dani madarar mamaki, Sai dai kuma ah bincikena sakamakon dana samu kenan, Alhaji dani dakai mun san juna Tun da jimawa, hasalima kun daukeni family doctor d'inku, sabida me? Sabida kun yarda dani, hakan yasa bana iya b'oye muku komi, gaskiyar gud'a daya ce Wannan yarinya Ummi gab take da kamuwa da ciwon hawan jini, Ba abun mamaki bane ace ah 'yan shekarunta ta kamu da wannan lalurar don azamanin yanzu ciwo bai san babba ba haka zalika bai san karami ba, kowa yana iya kamawa, Sai kaga jinjirin da aka haifa ayau ace maka yana da hawan jini ko kuma ciwon siga, Tou ita agode Allah bawai yayi Wani high bane ammh ana iya magancewa tun wuri idan aka kiyaye kafin abun yayi nisa, Kuyi kokari ku zaunar da ita ta fadi muku damuwarta, in abune Wanda bai fi karfinku ba sai ku biya mata bukatarta da wuri, in kuma yafi karfinku Sai ku lallasheta da tayi hakuri tabarwa Allah komi, Sa'annan ku gargadeta data cire wannan abun aranta don yana kokarin cutar da lafiyarta, Allah dai ya kiyaye..."

Cikin Rauni Abba ya amsa da Ameen don tuni ya soma Zirarar da Ruwan hawaye, Wai Zainab ce hawan jini ke shirin kamawa? Yasan ba kowa ne ya jefata Cikin wannan hali ba illa iyalinsa, Yanzu Amanar da dan'uwansa ya damk'a mishi ya kasa kular masa dashi Tunda har ya bari babbar cuta kamar Wannan yake kokarin kama 'yarsa.Yasan duk inda Dauda yake ayanzu yana can yana kuka dashi.Bai kular masa da Ummi ba, bai tab'a jawota ajiki ya matsa mata ta gaya mishi damuwarta ba, bai tab'a tambayarta abunda takeso ba, idan ya bukaci ta gaya mishi abunda ke gudana arayuwarta agidanshi, cewa take babu komi suna zaune lfy dasu Ummah.

SAWUN GIWA...!🐘Where stories live. Discover now