ALMAJIRA Babi na goma

417 11 0
                                    

  *AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆
            *NA*
*JEEDDAH TIJJANI*
         *ADAM*
*(jeeddahtulkhair)*

🍆🍆🍆🍆🍆🍆

*Wannan shafin gaba daya naki ne halak kiyi yadda kike so da shi, SISTER FURERA MUHAMMAD (Maman Hauwa) ina yinki ina kaunar ki, Allah ya bar xumunci da kaunar juna*

9⃣1⃣

Yau tun safe nauwar bata fito ba a daki ta wuni saboda tana jin kunyar  fitowa tsakar gida don kada ta hadu da yaya sadeeq ya rika sakar mata wannan asirtaccen murmushin nasa mai sanya mata kasala, don ko gaida mama da Abba bata fita tayi ba, shirun da mama taji ne babu motsin ta a waje shi yasa ta shigo dakin dan jin dalilin da yasa bata ganta ba.

Kwance ta tarar da nauwar kanta na kallon sama da sallama ta shigo dakin, tsayawa tayi ta karewa nauwar kallo sannan ta karaso inda take.

A hankali ta dago kai ta Kalli mama, tare da tashi xaune.
"sannu da gida mama"

Cikin sakin fuska mama ta amsa.

"yauwa nauwar, lafiyanki yau gaba daya ban ji motsinki ba, ko dai tunanin Amminki kike yi baki fada mana ba"

Murmushi nauwar tayi.
"A'a mama yau bana jin dadi ne kawai "

Cikin kulawa ta dubi nauwar.

"Ayya Allah ya baki lafia amma ai bai kamata kiyi shiru baki fada min ba,  shikenan da ban shigo ba haka xaki xauna da ciwo a jikinki baki yi magana ba"

Kiran saimah mama tayi cikin xafin nama ta karaso dakin Tsugunnawa tayi.

"Gani mama"

"yanxu dan sakarci Kin san nauwar ba lafiya amma baki fada min ba, sai da na shigo yanxu naga yanayinta nasan ba tada lafiya da ban shigo ba  sai dai ciwo yayi ta cin jikinta kenan Allah ya shirye Ku yaran nan"

Dariya saimah take yi
"Lallai mama Kina cikin gidan nan amma ana binne Ki, duk abinda yake faruwa baki sani ba, to nauwar lafiyarta kalau "

Cike da mamaki mama take duban saimah, ita kuwa nauwar kara danna kanta tayi cikin bargo saboda ruwan da saimah ta ballo mata "

Magana mama ta cigaba da yiwa saimah
"kin fara magana kuma kin yi shiru, ni fa wannan sakarcin ne bana so"

Duban nauwar saimah tayi tana dariya.
"na fada ko nayi shiru? "

Shiru nauwar tayi mata ba tare da ta bata amsa ba, sai hararta da take yi kawai.

Cikin kakkausar murya mama ta sake maimatawa saimah tambayar da tayi mata.

"xaki fada min ko sai na Saba miki"

Murmushi saimah tayi tana kallon mama.
"mama ya naga duk kin tashi hankalin Ki abin farin ciki ne fa xai faru ke dai kiyi addu'a kawai "

"to
naji ko na Farin cikin ne ki fada min yanxu ina saurarenki"

Rufe fuska saimah tayi.
"da ke da Ammi kun xama surukai mama"

Cikin mamaki mama ta jawo saimah ta xaunar da ita tana kallon fuskarta.

"da gaske kike ko kuma xancen Ku ne na yara"

"Wlh da gaske nake mama yaya Sadeeq yana son nauwar "

Farin ciki ne ya bayyana a fuskar ta.
"kai amma naji dadin wannan al'amari ashe xumunci baxai yanke tsakanin mu da Ku ba nauwar, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ai kuwa xan samu sadeeq yanxu yasan da wannan abin alkhairin bai fada min mun yi magana da ammi ba har ta tafi"

Saimah ce ta bata amsa.
"to ai kunyar ki yake ji ne mama shi yasa bai fada miki ba, kuma baya son a fada miki saboda kada nauwar ta rika jin kunyar ki ta kasa sakewa a gidan nan"

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 04, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AL-MAJIRA CompleteWhere stories live. Discover now