ALMAJIRA Babi na takwas

355 3 0
                                    

PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
         *AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
                *NA*
    *JEEDDAH TIJJANI*
             *ADAM*
    *(jeeddahtulkhair)*

🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆


7⃣1⃣

Haka suka kasance a wannan hali a kullum akwai kalar abubuwan ban tsoro da xata ci karo da shi, ga ciwon Ammi ya dada dawowa sabo saboda rashin kulawar da take samu, sannan ga kwana a kusa da bola, a lokuta da dama har ji take ana kiran sunan ammi ana cewa ta taso su tafi sai ta tsananta addu,a sannan take daina jin muryar da take kiranta, ba karamar wuya take sha ba a halin yanxu ita kanta aljanun na mata baraxana da rayuwarta, dagewa tayi da fadawa Allah matsalarta Sannan taji saukin abubuwan.

Yau ma kamar kullum dankwali ta yafa ta fita yin bara, kallo daya xaka yi mata ka gane tana cikin matsala kuma tana matukar bukatar taimako, duk kayan jikinta sun yage, takalmin kafarta ya tsinke sai kullewa tayi da Leda, ga dauda ko ta ina saboda ta dade bata ga ruwan wanka ba, duk tayi baki ta fita daga hayyacinta, kafin ta fita sai da ta daurewa ammi kafa da tsumma don gudun kada ta haura katanga ta gudu, kulle kofar kangon tayi sannan ta fita, yau dai a sa'a ta fita domin kuwa ta samo alkhairi masu yawa, mutane da dama sun tausayawa halin da suka ganta a ciki, wannan dalilin yasa suka rika bata sadaka, sai dai ta samu abincin da xai riketa kwana uku ba tare da ta fita bara ba.

Haka rayuwar su ta cigaba da kasancewa har tsawon sati bakwai yau da dadi gobe ba dadi, wata rana su samu abincin kaiwa bakin salati, wata rana kuwa sai su yi kwana biyu basu samu abinda zasu ci ba, haka suka xauna cikin wannan hali har xuwa lokacin da Allah yasa saimah ta kai su gidan su inda ta roki mahaifanta alfarma ya ba su daki.

Lallai baxa ta manta da karamcin da iyayen saimah suka yi mata ba, su suka fitar da su daga halin kunci da takaicin da suka kasance a ciki na shekara da shekaru.

Tana kammala tunanin da take yi ne, taji anyi sallama cikin dakin da suke, saimah ce da Abbanta da mamansu tare da yayyenta guda biyu suka shigo dakin, sallama suka yi, cikin nutsuwa nauwar ta amsa musu sallamar samun guri suka yi suka zauna.

Cikin nutsuwa ta tsugunnah har kasa ta gaida su, tare da sakin fuska suka amsa mata da lafiya lau.

Duban Ammi suka yi suka yi mata sannu, kwance take tana ta faman sharar bacci cikin kulawa Abban saima ke mata magana.

"Tunda kun samu watanni a gidan nan kun huta kun dawo cikin nutsuwar ku, ya kamata musan tarihin rayuwarki da abubuwan da suka faru da ku domin mu san irin taimakon da ya kamata mu baku."

Share hawaye nauwar tayi ta fara basu labarin abubuwan da ya faru da su da irin gwagwarmayar da suka yi da makiya, kuka sosai suka rika yi saboda labarin su cike yake da abubuwan takaici da bakin ciki.

Cikin karfin hali Abban saima yake magana.

"lallai yarinya kina cikin yanayin da ya kamata duk mai imani ya tausaya muku, kuma insha Allah muna da taimako na musamman da xamu baki, abinda xamu fara yi yanxu shi ne mu nemo nahaifinki mu sanar da shi halin da ake ciki yanxu"

Mayar da kallon shi yayi gareta.

"kina da number wayarsa ne mu kira mu sanar da shi inda zai same mu?

Share hawayen da ya cika idonta tayi.

"ba nida ita Abba, ammi ce kawai ta haddace "

Cike da tausaya ya dubeta.

"bana so naga kina kuka, kiyi hakuri mu bi komai a sannu insha Allah xamu same shi ba tare da mun sha wahala ba"

Godiya ta yiwa Abba.
"ba komai nauwar insha Allah kinxo inda xa a tausaya miki daga nan kuma Xaki hadu da abbanki"

AL-MAJIRA CompleteWhere stories live. Discover now