ALMAJIRA Babi na shida

539 4 0
                                    

9:15 PM] Writer: 🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
       *AL-MAJIRA*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
              *NA*

*JEEDDAH TIJJANI*

          *ADAM*

*(Jeeddahtulkhair)*

*EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

5⃣1⃣

Shiru Nauwar tayi tana sauraren abinda Alhaji Talle da aunty Amarya ke fada, sai da suka kammala tsaf sannan tayi musu magana.

"duk naji abinda ku ka fada Aunty, amma ni ban amince da wannan hadin ba, dama nayi xaton Alhaji ya taimaka min ne saboda Allah, dan ni a matsayin uba na dauke shi, don haka baxan iya auren shi a matsayin abokin rayuwata ba"

rike baki aunty amarya tayi tana mamakin kalaman Nauwar.
"lallai yarinyar nan kin cika butulu, dama bahaushe yayi gaskiya da yace tsintacciyar mage bata mage, yanxu duk mutuncin da Alhaji yayi miki, kin mance har xaki watsa masa kasa a ido kice bakya son shi, to idan baki yi auren ba uban me xaki yi"
ganin aunty Amarya nata faman fada,  shi yasa Alhaji dakatar da ita.

"haba Amarya abin ai bana tashin hankali bane, don tace bata sona ai bata yi laifi ba, saboda ba a soyayya dole amma abinda xa a yi duk abinda tasan nawa ne, ni na bata ko na kashe mata, xan rubuta list yanxu ta tattaro min kayana ta bani, idan ba haka ba kuma xan shigar da kara wajen hukuma"

gumi ne ya rika yankowa Nauwar ta ko'ina, ina xata samu kudin da xata biya shi abinda yayi mata, alhalin duk kudin da yake bata aunty Amarya ke karbewa ta kashe abinda yake xuwa hannunta ba mai yawa bane.

katse shirun da suka yi Aunty amarya tayi.
"wace shawara kika yanke game da al'amarin nan, Alhaji yana da abin yi ke kawai yake jira"

hawaye ne ya rika yankowa daga idanun Nauwar, bakinta na rawa ta amsa musu da
"na amince"

farin ciki ne ya bayyana a fuskar Alhaji Talle ya shiga washe baki.

"yauwa ko kefa ai haka ya fi miki, Allah ya min arxiki na samu tsuntsu daga sama gasashshe, ke kuma Amarya Allah ya saka miki da alkhairi da wannan hadi da kika yi"

"ba komai Alhaji ai yiwa kai ne"

duban Nauwar tayi,  tashi ki tafi tunda an gama maganar da xa a yi da ke, mikewa Nauwar tayi ta bar dakin.

tana fita Aunty Amarya ta dubi Alhaji.
"yanxu abinda ya rage sai a fara shirye-shiryen biki, kudi xaka rika bayarwa ana siyo mata kayan da xa a jera a daki, kasan ba tada kowa sai ni sai kuma kai,don haka duk wani gata da uba xai yiwa yarsa kaine xaka yi mata"

duk wannan ba matsala Hajiya hannu yasa a aljihu ya xaro kudade masu yawa ya mika mata,  ki fara siyo mata kayan aikin gida, saboda nan da sati biyu nake son a yi komai a gama.

Tun daga ranar da Alhaji talle yaxo gidan Aunty Amarya aka yi maganar auren su da Nauwar,  ya kara dagewa wajen yi mata hidima, ita kuwa tun daga lokacin ta fada cikin damuwa ta daina walwala, saboda tana cikin tsaka mai yawa, gaba daya rayuwa tayi mata xafi.

Ana saura kwana uku daurin aure, Aunty Amarya ta gama shirya mata komai na gida inda aka fara shirye-shiryen tafiya jere, samun Nauwar tayi a daki ta hada kai da gwiwa.

"har yanxu baxa ki hakura da damuwar nan ba, aure fa ba fashi saboda Alhaji baxai yafe miki kudin da ya kashe miki ba, dama shi ba a cin kudinsa a kwana lafiya don haka ki kwantar da kai, ki samu rabonki, yanxu xan kira mai kunshi da gyaran jiki tayi miki"

"kinga Aunty kada ki fara a kirawo min kowa, ba wani kunshi da xan yi,  wlh da ina da kudin da xan biya wannan mutumin abinda ya kashe da tuni na biya shi, na huta da masifa, dan gaba daya bana son auren nan ni ba aure ne a gaba na, idan na aure shi ya xan yi da mahaifiyata"
ta karasa maganar tana kuka.

AL-MAJIRA CompleteWhere stories live. Discover now