ALMAJIRA Babi na biyu

473 7 0
                                    


*AL-MAJIRAH*
🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
          *NA*

*JEEDDAH TIJJANI*
                 
          *ADAM*
             *(Jeeddahtulkhair)*
*♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*

🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆🍆
*Alhamdulillah, Allahu mun gode maka bisa da ni'imar da kayi mana👏🏻A Yau Allahu madaukakin sarki ya nufemu da kammala karatun mu na degree, Allah ya bamu abinda muke nema na sakamako kyakkyawa*👏🏻

*congratulation MARIAM TIJJANI ADAM on your POP (NYSC) I Wishes all d best, in all your indeavors may mighty Allah, guide help and give you all d best*

1⃣1⃣                                 

                       
*C*ikin xafin nama Ammi ta sheqa da gudu, take samarin suka bita, amma ina tuni ta yi musu nisa sosai, don haka suka yanke shawarar su samu machine su bi ta, gudu take yi ba kak'kautawa,  don haka suka nemi taimakon mutane akan su riqe ta, cikin taimakon Allah suka samu nasarar kamata.  dawo da ita suka yi kangon sannan suka bawa Almajira shawara ta daina fita ko'ina gudun kada ta sake guduwa, godiya ta yi wa samarin sannan  suka yi sallama da saimah ta wuce gida.

"zaunar da Amminta tayi tana xubar da kwallah, ita kuma Ammin sai xare idanu take yi tana naushinta da hannu".

"Ammi ina xaki je alhalin baki san kowa a garin nan ba, kina son na shiga garari ne Ammina? kece farin cikin rayuwata, ke kadai nake gani naji dadi,  idan kika tafi kika barni ina xan sa kaina, muxuranta ta cigaba da yi, tana 'kara kai mata duka,  sai dai tana kawo hannunta Allah yake bata sa'a sai ta kauce.

********************************

saimah ce a gaban mahaifinta ta sunkuyar da kai tana wasa da 'yan yatsunta. kanta na kasa ta kasa fad'awa mahaifinta abinda take son isarwa gareshi, ganin shirun yayi yawa, yasa ya fara magana.

"yar lelen Abbanta da magana kenan tunda naga kin yi wannan gurfanan." Shiru tayi da d'an lokaci sannan tace, eh!! Abbah dama......dama cewa nayi da xamu taimakawa su AL-MAJIRA mu basu d'akin soro su xauna,  saboda a can kangon da suke ba su da daki,  ga shi damina ta kusa sauka"

shiru yayi na d'an lokaci " haka ne Autar Abbah, kin yi tunani mai kyau,  saboda Allah yana taimakon bawansa,  matukar bawan yana taimakon d'an uwansa. yanxu kije xan yi waya kasuwa a taho musu, da ledar tsakar daki da labule xuwa yamma sai mu je mu taho da su".

hawayen farin ciki  ta fara yi "Abbah na gode Allah ya saka da alheri Allah ya 'kara arziki" Amsawa yayi da ameen yar Abbanta Allah yayi miki albarka.

"kai tsaye waje ta fito,  ta nufi wajen su AL-MAJIRA, tararwa tayi ana kokawar mayar da Ammi cikin kangon saboda ta sake yunqurin fita, da kyar aka samu aka shigar da ita. shiga cikin kangon tayi fuskarta cike da annashuwa, take sanar da ita yadda suka yi da Abbanta, farin ciki ne ya lallu6e AL-MAJIRA har ta rasa bakin godiya sai kuka da take yi, har kasa ta tsagunnah tana yi wa saimah godiya, tashinta tsaye tayi ta dafa kafadarta, kada ki damu kawata da sannu xa kiyi rayuwa ta jin dadi ki koma kamar kowace diya mace.

"godiya ta 'kara yi mata, ban ta6a tunanin xan yi rayuwa mai dadi ba ko da a mafarki, saboda tunda muka bar gida, bamu sake had'uwa da wanda ya tausaya mana ba, koda da ruwan sha ne ballantana musa rai da wajen kwana, sai gashi Allah ya yanke mana wahala, tunda na hadu da ke na bar fargabar abinda xa mu kai bakinmu, shi yasa a kullum nake muku addu'a, yadda ku ka sakamu farin ciki, ku ma Allahu ya yaye muku bakin cikin duniya da lahira.

"amsawa tayi da ameen, haka suka xauna suka rika hira har xuwa yamma sannan 'yan uwanta suka xo tafiya da su AL-MAJIRA. d'aki a ka basu a soran gidan, an gyara musu shi, an sa musu labule da ledar tsakar daki, shigar da su dakin aka yi, suna xama aka kawo musu abinci da kaya,  nan da nan su AL-MAJIRA suka canja kaya suka ci abinci sannan tayi sallah.

AL-MAJIRA CompleteWhere stories live. Discover now