page11

36 4 0
                                    

WAYE SILA. ©®2019
AN HEART BREAK STORY
SHORT AND IT'S MIND BLOWING
STORY WRITER
ABDUL ALHAJI MUSA (10K).
PHONE NUNBER 09077974042.
KARKASHIN
MIRINGA YOUNG WRITERS ASSO.

Page 11
Friday/July/2019
Not edit

Laila Zara idanu tayi ta kuma anbaci sunnan rihana,cikin mamaki.
Sultan da sauri yace"rihana bari na miki bayani"
Daga tafin hannun  tayi alamar ya'isa,tace"Mai kuma zan sake ji daga gare ka sultan,babu abinda zaka sake gayamin ta shige kokwalwa ta".
Laila da sauri ta karasa wajen rihana tace"dan Allah rihana ki tsaya ki saurare ni".
Kwallace ta Zibo idanun rihana tace"toh meye kuma zaki Kara fadamin,ya wuce kice dani kuskure aKa Samu... Toh indai wannan ne naji komai sannan kuma naga komai da idanuna".
shesshekar kuka take sannan ta sake cewa"sultan ba mafarki nake ba,sannan kuma ba labari ake bani ba.
Yau idanuna ne suka tabbatar min,sultan ban damu ba wai dan baka sona domin son danake maka ya isheni nayi alfahari".
Laila Kiran sunnan rihana  tayi.
Rihana ta daga mata tafin hanu tace"A'a laila karkiyi kokarin tsayar dani,ki barni kurun na furta abinda ke raina".
Laila tace"but..kin....".
"Please laila kiyi hakuri"inji rihana.
Shiru laila tayi ta zubawa rihana ido.
Rihana ko ta soma amar da abinda ke ranta.
Kamar haka
"Ban damu ba, ko babu soyayya cikin ranka,nidai nasan cewa Ina sonka..kuma soyayyar kace ta cenjamin rayuwa ta sultan, dan haka na yanke shawarar.......

Ji tayi an wankawa laila Mari da sauri tayi shiru ta juya dan taga waye wannan.
Gani kawai tayi mahaifiyar sultan ne ke tsaye gefenta.
Cikin mamaki rihana tace"umma......"

Cakumo gashin kan laila tayi ta jata har tsakiyar farfajiyar, inda ake wannan taron.
Rihana da sultan biye suke da momyn su, sun kasance kuma suna bata hakuri amma Ina taki sauraransu.
Bayan ta Kai laila tsakiyar farfajiyar Inda suke fiskantar kofan fita,sai ta zunguri kan laila ta baya.
Laila fadiwa kasa tayi yanda kasan  wacce bata da dangi haka laila ta koma cikin jama'ar dake wurin.
Sai faman zubar da kwalla take,wannan matan kuma tsaye take kanta.
Sai tace"atetion everyone"
dukkan mutanen dake gurin suka juyo.
Sannan tace"nasan kunason kuji meye dalilin dana kirawo hankulan ku,sannan kuma meya sa nayiwa wannan baiwar Allah haka"...

Murmushi tayi sannan ta soma kewaye laila tana kuma cewa"toh Ku kasa kunnuwan Ku danjin wannan labarin mai matukar ta kaici."
Sai ta soma da cewa"budur wace taga saurayi tace tana son sa,sai ta sanar dashi,shikuma sai yace da ita I'm sorry babe inada Wanda nake so,ita kuma tunda daman dukiyar sa take so bashi ba sai ta yanke shawaran cewa tazo ran auran sa ta dakatar da auren kota halin kaka........ajiyar zuci tayi ta sake cewa"nasan zaku ce surutan banza nake amma nikuma nasan Inda na dusa".
Da sauri mahaifin sultan yace"meye kike haka?".
Sai tace"I'm sorry but I can't listen to you my dear,so stay out of this matter".
Yace"heyyyyyy!!!!, you are crossing the limit".
Tace"yeah nasan haka zaka fada domin kwatakwata baka tsarawa y'ay'an ka rayuwar da zasuyi nan gaba,dan haka ka kiyalenin nayi abinda ya dace".
Juyawa tayi ta Cigaba da tozartar laila cikin jama'anan.
Anan saiga mahaifiyar laila tare da auntyn ta sun shigo.
Tarar da cin mutuncin da akeyiwa laila sukayi.
Da sauri suka daga laila.
laila tace"umma ki fitar dani daga wannan gidan don Allah".
Mahaifiyar laila tace"mai ya sameki laila?".
mahaifiyar sultan amsawa mahaifiyar laila tayi kamar haka"maiyasa kike wani abu kamar baki San komai ba malama,....da fari na dauka talakawane kawai amma kuma dana ganki sai Kika tabbatar min da cewa ku karuwai ne,so yanzu cikin d'an na kuka kawo kokuwa".
Sultan cikin fushi ya ambaci sunan mahaifiyar sa.
Sai tace"laila can you belief this,Yaron dana haifa shine yau zai kirani da sunan da ubansa yake kirana dashi".
Mahaifiyar laila tsaye take tayi shiru taki cewa komi,kuma sai faman komawa take da baya.
Umman sultan sake cewa tayi"tunda nake a rayuwa ta bai taba kirana da haka ba sai da Kika shigo rayuwar sa,...laila you are bad lack to this family".
Babu irin takaicin da laila bata yiba,sai ta juyawa cikinta a sanyaye tace"aunt muje KO".
Sultan kirawo sunan laila yayi sai Mahaifiyar sa tace"karka kuskura".
Tsayawa yayi cek domin dama haryayi niyar binta.
Laila juyawa tayi cikin mamaki tace"aunt Ina umma?".
Auntyn nata tace"nanfa take tsaye,mituna biyu da suka wuce".
Rugawa laila tayi da gudu ta fita waje,tarar da Mahaifiyar ta na tsallake titi,sannan kuma fuskar ta cike take da alamar damuwa,kunnuwanta kuma basu jiyo komai ta kuma tsunkuyar da dai tana taku a hankali,kamar kazar da ruwa yayiwa duka.

Ihu laila tayi sannan ta Kiraye Mahaifiyar tata.
Juyawa tayi tana fuskantar laila,ta danyi murmushi ta mika hanu alamar tazo.
Tsaye take tsakiyar titin,Lisa dajin muryar laila yasa ta juya, dan ita bata bisu sun shiga tare ba,ita ta tsaya wajen motor.
Laila rugawa  tayi da gudu dan takuma nufi wajen Mahaifiyar tata,da shike tsakanin nasu nada dan tazara,laila karasawa tayi dan bai wuci taku uku ba tsakanin su sai wata makekiyar bakar mota tazo tayi sama Mahaifiyar laila.

WAYE SILA?Where stories live. Discover now