page 9

36 4 0
                                    

WAYE SILA. ©®2019
AN HEART BREAK STORY
SHORT AND IT'S MIND BLOWING
STORY WRITER
ABDUL ALHAJI MUSA (10K).
PHONE NUNBER 09077974042.
KARKASHIN
MIRINGA YOUNG WRITERS ASSO.

Page 09
Not edit
Pls amin ahuwa da typing error.

Lisa murmushi tayi tace"waye wannan Wanda ya sace miki zuciya"
Juyawa laila tayi alamar kunya tace"yah kasance yana yawan murmushi".
Lisa tace'okay".
"Sannan ya iya bada kulawa,baya kuma banbata mutane dan kyaunsu kokuma arzikin su,sannan baya iya barina cikin kadaici"
Lisa tace"meye sunan sa?".
Tace"sultan..... sultan .. . ..sultan,shine alawar zuciyata bazan iya rayuwa babu shiba Lisa.....shiya sa zan sanar dashi ina sonsa yau".
Rigume lisa tayi tana cike da farin ciki.

Sultan tafiya yake jikinsa sanyaye, ya kasa cewa komai,kwallace ke kwararowa fuskar sultan,yayyaga wasikar yayi ya kuma yarda fulawar ya tattaka.
Sauka kasa yayi kan gwiwowin sa ya soma zabga kuka.

12:32
Laila hallau tsaye take taki tafiya tana jiran sultan ya Kai ta,fitowa Lisa tayi daga ciki tace"aunty laila har yanzu kike tsaye anan,karfe sha'biyu da rabine fa yanzun"
Budar bakin laila tace"sultan"
Lisa tace"baki kirashi a waya bane?"
Tace"yafi so dari amma yaki ya daga,nakuma tura mishi sako yafi a irga amma shiru"
Lisa shawo kan laila tayi suka tafi tare,amma laila sai hankalinta ya kasa zama wuri daya,tana ta waigewaigen naiman sultan amma kash ta kasa samun sa.

Laila tazo na daya cikin tarun dubbannin dalibai wajen hazaka da kuma nuna kokari wajen tirenin,an bata awot ta butun butumin mutun,Wanda akayi ta da zinari dakuma gilashi mai fadi sosai.
Rikewa tayi hannun ta taje da gudu ta ringume Lisa.
Laila tayi farin ciki matuka amma kuma dai sai tunanin sultan ya lullube ta.
Tace"taya zan karbi wannan kyautar ba tare da sultan gefe naba."

Sultan komawa gida yayi ya tara da komishina da mahaifiyar sa na zaune cikin falo,ummartasa tsayawa kallon sa tayi saiga kamal da Anna sun shigo.
Sultan yace"Mom na amince da bukatanki,naje na duba rihana".
Cike da mamaki ummar sa ta tashi tace"yaron albarka,nan da sati daya za'a daura muku aure".

Wuce wa yayi ciki kamal da Anna suka biyo shi.
Rike kafadar sultan Anna tayi tace"meya sa....ka hanke wannan mummunar shawaran"
Kamal yace"yah ka gabatar da soyayyar takan"
Bai ceda su komai ba ya wuce ciki.
Anna da kamal suka kalli juna suka bishi ciki.

Umman sultan shewa tayi tace"komai yazo daidai,inason ka soma shiryeshiyen biki nanda ranar asabar"
Komishina yace"okay zamu yi katin gayyata gobe"
Tace"yayi kyau,jeka ka soma"
Tafiya yayi ya kiyale mahaifiyar sultan cikin dakin ita kadai.
Tashi tayi ta gofe hannaye ta sannan tayi murmushi tace"_komai zai tafi a yanda aka tsara".
Sannan ta fashe da dariya.

Laila kimanin kwana shida tayi tana kiran wayan sultan amma yaki dauka,kwana ta shida sai ta yake shawarar zuwa gidan su taga lafiyar sa takuma nuna masa lambar yabo data samu.

Shiga adaidaita tayi aka sauke ta kofar gidan,mamaki tayi yanda taga an kawata gidan da furanni da kuma dogayen kiyalle mai sheki,taso ta kasa gane gidan amma daga baya sai taga mai gadin gidan Wanda ta taba gani.tace"sannu yanaga tarun jama'a".
Mai gadin yace"laila ko"
Tace"eh "
Yace"bikin kawarki akeyi"
Tace"wace kawar tawa kenan"
Yace"nidai a iya Kotancen ki da akamin kece"
Tace"okay tace da Kai meye wai?"
Mai ganin yace"na baki wannan turaran kwalbar ki Kai Mata".
Tace"okay bani"
Laila karban tiraran tayi ta shige ciki,shigarta keda wiya saiga asalin lailar da akaiwa maigadin kotance tazo tace" bani turaren"
Mai gadin yanuna yabawa wata daban. tace"okay barina duba ciki in tambaya kozan sami me shi"

.laila takawa tayi cikin farfajiyar gidan Inda kowa harkar gabanshi yake.
Laila tafiya take tana ta surutun cewa"taya za'ayi bikin kanwar sultan ba tare da ya sanar dani ba"
Tana cikin wannan maganan bayan ta Kai tsakiyar gidan,sai taga wani gabjejen hoton bango Wanda hoton sultanne ke marne jiki tare da rihana.
Ganin haka yasa laila taji wani abu ya sauke ta a ranta.
Kwalbar dake rike hannun ta ya fadi kasa ya fashe,karar fashewar wannan kwalbar ne yaja hankular kowa dake gurin suka juya.
Anna tsaye take tare da kamal suka juya cikin mamaki Anna tace"laila!!!!!!"
Da sauri laila ta tsunkuya ta soma shesshekar kuka tana kuma dibe kwalaben.
Umman sultan dake nesa da Inda take tace" wacece wancen?"😨


😢😓

WAYE SILA?Where stories live. Discover now