page10

48 2 0
                                    

WAYE SILA. ©®2019
AN HEART BREAK STORY
SHORT AND IT'S MIND BLOWING
STORY WRITER
ABDUL ALHAJI MUSA (10K).
PHONE NUNBER 09077974042.
KARKASHIN
MIRINGA YOUNG WRITERS ASSO.

Page 10

Lisa tsaye take tsakiyar falon su,tana kuma rike da akwatin ta a hanu alamar tafiya ce tatashi.
Bashiri sai ga ummarta ta fito tace"Lisa kinsan halin daddyn ku da zaran yace ayi to dole ayi"
Murmushi lisa tayi,sai auntyn su tace"tsarin banza,yanzu mafa ko irin tow weeks dinnan bamu yiba amma kawai Ana rana tsaka yace yana son ganin yau."
Ummar tace"sister karki damu insha Allah,zamu zo wani lokaci muyi irin one month haka".
Murmushi Lisa ta sake tace"ai ya kamata mu sake koda one week ne".
Ummar tace"gaskiya kam amma to ya muka iya,dolene yasa zamu tafi.......Ina laila ta shigane ban ganta ba?"
Dafa goshi Lisa tayi tace"Ooops na manta ban fada muku ba tace zata gida su sultan,ta duba ko bashi da lafiya".
Auntyn tasu tace"dole na kaiku gidan kuyi sallama da juna".
Ummar tace"karki damu zamuyi waya kawai"
Lisa tace"haba mom muje mana"
Lisa tayi tawa ummar tasu magiya har ta amince.

Laila durkushe take tsakiyar jama'an tana tsintar kwalban daya fashen.
Anna da kamal suka yi sauri suka Karasa wajen laila,ganin laila na diban kwalaban ba tare da wani Abu ba,diba take tana rikewa a hannu.
Anna ta tsunkuya tace"laila kina zibar da jini"cikin siririyar murya Anna ta furta haka,biris laila tayi ta cigaba da abinda take takuma tsunkuyar da kanta.
Anna ganin laila taki cewa komi,sai tace"laila ki saurareni!!!!"tafurta hakanne cikin bacin rai.

Sultan zaune yake gaban madubi, shiru yayi kurun yana ta kallon hotan kansa.
Nan sai ga babban abokin sa mai suna Harris ya shigo..
Shigar sa yace"Alhamdulillah,sai faman sauri nake nufina Karna zo naga ka shirya....don kuwa nayi alkawarin Nizan kinsa ka."
Sultan baice dashi komai ba,amma shi kuma sai faman surutu yake..
Budar bakin sultan yace"zuciyata nagawa da sauri Harris".
Juyawa Harris yayi ya kalleahi yace"haba karka dami kanka, Ina ganin zanyiwa likitan ka waya"
Sultan yace"A'a.....bahaka bane,wannan alamace ta laila tashigo gidannan,
Domin lailace kadai kesa zuciyata bugawa".
Harris ajiyar zuci yayi yace"wacece wannan"?
Bayan ya tambayi sultan haka batare da yajiyo amsar  sa ba ya sake cewa"kuma meye alakarku"
Duk way'annan tambayoyin dayake ya bawa sultan baya,ji yayi sultan yayi shiru sai ya juya da niyar ya tabashi.
Tarar da kujeran da sultan yake zaune a Kai  babu kowa ,sai ya duba gabar da yanman cikin dakin baiga sultan ba.

Anna kamo hannun laila tayi ta Kai ta store tace"me yasa kike azabtar da kanki ta wannan hanyan,eyye laila".
Laila dago kai tayi kalli Anna,idanuwan ta cike take da kwalla tace"gaskiya....."
Anna katse ta tayi tace"nasan komai ai,kobaki sake min bayani ba"
Laila lumshe idanu tayi sai kwalla ta soma zubowa fuskar ta.
Anna tace"kiyi hakuri nasan baiyimiki daidai ba,amma bai Kama ta kiyi haka"
Laila tace"toh Mai yakamata nayi Anna,kukanne kawai zai ciremin kunar danake ji cikin rai na"
Anna tace"nasan yadda kike ji aranki laila amma first bari na dauko akwatin wanke ciwo,a dakin umma na wanke miki raunin naki."
Tafiya Anna tayi ta kiyale laila cikin dakin.

Nan laila take tana sheasshekar kuka cikin wannan store din,sai ga sultan yazo wucewa ta bakin kofar,jin sautin kukan laila yayi da sauri ya juya ya kalli kofar store din.

Anna dauko akwatin tayi tajuya zata fito sai ga mahaifiyar ta, tace"Anna me zakiyi da wannan"
Anna hada fuska tayi ta kalleta cikin salo na bacin rai tace"umma wanke wa wani rauni zanyi"
Ummr tasu tace"waye wannan"
Anna takawa tayi ta karasa wajen mahaifiya tata tace"bai zama dole ki iya gane meshi ba,koda namiki kotance".
Anna hada fuska tayi ta tsaya kallon ta.

sultan jikinsa a sanyaye ya karasa wajen laila yace"Mai yake saki kuka laila?".
Jin haka yasa laila ta tsayar da kukan da take.
Sultan sake cewa yayi "kodai wani abune ya same Ki?."
Laila da fari ta dauka gizo ne take ganni amma daga misani ta gane cewa sultan din ne ke tsaye bayan ta.
Tashi tayi cikin yanayi ta kasala tace"babu komai sultan".
Ajiyar zuci tayi, sannan  tayi yunkirin tafiya sai sultan ya riko hannun ta ta baya.
Yace"kina boye wani abu laila".
Laila tace"babu abinda nake boyewa".
Juyata yayi yasoma kallon cikin idanta yace"dana kalli cikin idanun ki,sai ya sake tabbatarmin da cewa kina boye min wani abu"
Laila tayi shiru amma sultan sai yaki sake mata hannu yanata mata wasu iriyan tambayoyi.
Laila tun tana boye fushin ta ga sultan amma sai yakai har ta baiyana fushin a fili.
Jan hannunta tayi sai ta soma yiwa sultan bayanin yarda take son sa.
Kamar haka"ban tsanmaci yaudara daga gare kaba sultan,a koda yaushe tunanina ni takace kai kuma tawane....amma meye na samu in return yaudara".
ajiyar zuci laila tayi ta sake  cewa"nazo gidannan daniyar na nuna maka kyautar dana samu a wajen aikin da nake,nakuma duba lafiyar ka domin naji shiru kona kiraka baka dauka,amma kuma Mai na tarar bacin Raine tsantsa".
Laila ta karashe batun nata da cewa"sultan bana fatan naji komai daga bakin ka,domin abinda idona ya gane min ya isheni".
Sultan Shiru yayi saida ta gama bayanan nata sai yace"Dan Allah kibani miti biyu don ki saurari hujjojina"
Laila tace"a'a sultan ka konamin raina shine kawai,bazanso na Kara ganin ka ba".
Durkusawa yayi gaban ta yace"kiyi danni laila please,kodan yadda kike sona laila".
Ya laila ta iya yazama dole yasa ta saurare shi.

shima Kuma sultan din ya bata labarin lokacin dayaje da niyar baiyana soyayyar sa gare ta,yajiyo cewa ba sonsa take ba.
Laila tace"sultan Ina son ka,gaskiya bazan iya rayuwa babu Kai ba,amma gashi sai ka juya da niyar auran wata......nasan ciwon zuciyace kawai zatayi ajalina a duniyar nan".
Sultan rungume laila yayi kafin yace"Ina sonki laila bazan taba rabuwa da keba"
Murmushi laila tayi lokacin dasuke a sangamen.
Sai ya riko hannun laila bayan sun sake juna daniyar zasu fita daga dakin.
Juyawarsu keda wuya sai suka Tarar da Rihana na tsaye bayan su.
Takuma cika idanuwan ta da kwalla.
😥😨

WAYE SILA?Where stories live. Discover now