yanda tina da agalher sukayi sanadiyyar rasa 'ya'yayenmu inaso su dinga d'and'anar mutuwar 'ya'ya har 'karshen rayuwarsu. Inaso 'yarsu taishu tayi 'bakin jinin da ba'a ta'ba halittar wata halitta dashi ba, banaso ta haifi 'ya'ya maza ko da zata haifa na sadaukar dasu gareka daga nan har 'karshen rayuwarta" ________________________________________ Ta taso cikin tsana da tsangwamar mutanen 'kauyensu, suna kiran mahaifiyarta mayya sanadiyyar mutuwar duk wani d'a namiji da ta haifa, suna kiran karime karfa sanadiyyar mutuwar dukka wani namiji da ya ra'beta, meyasa? Menene 'kullalen sirrin dake bibiyar karime da mahaifiyarta? A Ina zasu sami mafitar halin da suke ciki? Har wani lokaci zasu d'auka kafin duhun da suke ciki ya yaye?