YASMEEN.

Od JannatMN

1.2K 63 13

Labari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin... Více

Page 1 ✍🏻
Page 2✍️
Page 3✍️
Page 4&5✍🏻
Page 6&7✍🏻
Page 8&9✍🏻
Page 10&11✍🏻
Page 12&13✍🏻
Page 14&15✍🏻
Page 16&17✍🏻
Page 18&19✍🏻
Page 20&21✍🏻
Page 22&23✍🏻
Page 24&25✍🏻
Page 26&27✍🏻
Page 29-30✍🏼
Page 31-32✍🏼

Page 27&28✍🏻

26 1 2
Od JannatMN

*༺•⚘🌺YᎪᏚᎷᎬᎬN🌺⚘•༻*
             *1442H/2020M.*

   
 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN*

*SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

   
           *😭KUKAN KURCIYA.....🕊(8)* 

        _*Ƴan uwa ni'ima tana buƙatar godiya. Musiba tana buƙatar haƙuri. Zunubi yana buƙatar Tuba (Istigfari). Duk wanda ya yi godiya, ya yi haƙuri ya kuma tuba haƙiƙa ya samu jin daɗi....Allah ya jiyar damu daɗi duniya da lahira...Allahumma Amin. Allah yasa mu dace. Ameen Ya Allah 👏🏻*_

      _Wannan shafi tukwici ne a gareki Ummu Haidar fan's ɗin ƙwarai. Ina godiya da kulawarki ga novel ɗin Yasmeen. Ki yi komai ba komai bane a wajena, wannan shafin naki ne halak malak gaba ɗaya shi._

*SHAFI NA 27-28📑*

    
*__________📖* Da biyu Fadwa ta yiwa Safrat haka tunda ta hanata bin Safnat ta tsokaneta, shiyasa ta yi mata haka dan ta tada mata da hankali. Tana shiga gidanta ta kulle ƙofar da mukulli ta hayewarta sama tayi kwanciyarta.
  
    
        Da saurinta ta ƙara so gidan Fadwa ta kama kofa zata buɗe ta shiga ta ji ƙofa a garƙame, hankalin Safrat in yayi dubu ya tashi da kulle ƙofar da Fadwa ta yi, dafe kanta tayi a ranta ta rinƙa cewa, _Na tabbata Fadwa fushi tayi, yau naga ta kaina, ta ya zan fahimtar da ita ba haka nake nufi ba._ Safnat ce ta faɗo mata a rai aiko da sauri ta kuma juyawa inda ta fito.

        Ɗakinta ta nufa ta tura ƙofar bakinta ɗauke da sallama ta shiga, bata ɗaugo ta kalleta ba ta amsa mata sallama, ƙarasowa tayi har inda take kwance ta zaune gefen gadon tace,

        "Sister ki taimaka min Fadwa tayi min bahuguwar fahimta, ranta ya ɓaci ta fita tana fushi na bi bayanta na fahimtar da ita, sai na tarar da ta kulle gidanta."

        Tashi tayi daga kwancen da tayi ta kalli Safrat fuskarta ɗauke da murmushi ta ce,

       "Haba! Safrat kamar baki san wacece Fadwa ba, amma gaskiya kin ban mamaki da kika manta wacece Fadwa, sanin kanki ne ba'a ɓatawa Fadwa rai, ballantana ma tayi fushi, sai dai ta ɓata ran wasu tasa wasu yin fushi, yanzu me kika yi mata har ranta ya ɓaci tayi fushi?"

    
     Nan ta kwashe duk abinda ya faru a tsakaninsu ta gaya mata, dariya sosai Safnat tayi har sai da taga Safrat ta fara ƙulewa sannan ta daina dariyar tace,   
  

       "Wallahi Safrat har yanzu baki gama sanin wacece Fadwa ba duk shirin da kuke yi da ita, ba fushi take ba kuma ranta bai ɓaci ba sam, ta gaya miki haka ne dan ta ɗaga miki hankali, tunda kin hanata yin abinda tayi niyya da biyu ta gaya miki haka, inda har ranta ya ɓaci da gaske ba zata kulle ƙofar gidanta ba, ta san dole zaki biyo bayanta ki bata haƙuri, shiyasa ta ƙulle ƙofa dan ta ƙara tayar miki da hankali, yanzu haka tana can tayi kwanciyarta ko tana karance-karancenta ke kuma ta barki cikin damuwa, ki rabu da ita kawai, da kanta zaki ga ta fito tazo har nan, kuma ta tsokaneki."  
   
     
      Ran Safrat ne ya ɓaci da ta tuna ko wacece Fadwa tace, "Amma gaskiya Sister Fadwa ta cini wannan wasa kuma wallahi ba zan haƙura ba sai na rama."   
   

     "Hhhh! Wannan kuma kun fi kusa, Ni dai shawarar da zan baki kada ki kuskure kice zaki rama, dan wallahi kika ce zaki rama kanki abin zai dawo, kin ma ji na gaya miki gaskiya ban taɓa ganin abinda ya taɓa ɓatawa Fadwa rai ba, ita wata irin mutun ce daban, kiyi haƙuri kawai ki rabu da ita, sai ki ɗauki matakin daina damuwa da duk abinda zata gaya miki, sai ku zauna lafiya, amma in ba haka ba kullum kece cikin damuwa."

   
    "Yanzu Sister haka zan barta, ba zan rama ba?"

      "Yes! Ki rabu da ita kawai, ki bari a ɗan kwana biyu sai ki rama."

   
      "Taya zan rama bayan kin ce ranta bazai ɓaci ba?"
   
  
     "Hhh! Kina ban mamaki Safrat sosai, kamar kin matan menene lagwan Fadwa."
   
 
       "Menene lagwanta Sister? Tuna min na manta?"
 

       "Kishinta shi ne lagwanta, indai kina so ki rama abinda tayi miki yanzu to kiyi amfani da abinda ta tsana, shine kawai zaki yi nasara a kanta, amma in bashi ba baza zaki taɓa iya rama abinda tayi miki ba."
   
 
      "Okay! Sister gode sosai, amma taya zan iya amfanin da kishinnta na rama abinda tayi min?"
   
  
       "Ke kin kuma fa isheni na gaji, ki je idan na tashi daga barci zan gaya miki komai, da yadda zaki ki yanzu ina buƙatar hutawa."
  

     "Hmm! Ba zaki taɓa canzawa ba Sister ba komai ki huta lafiya, ba dalili ba kin aikata haka mun miki uzuri, ballantana ma yanzu da komai ya sauya kike da dalilin, ai dole mu yi miki uzuri."
   
   
      Dalla mata harara tayi tace, "Me kike nufi da haka?"
   
   
      "A'a! Babu abinda nake nufi, kawai ina so nace wai wata nawa ne."
 

      Banza tayi mata ta koma kwanciyar da take ta juyawa mata baya, dariya Safrat tayi tace,
   

       "Haba Sisterna ko kin ɓoyewa kowa bai kamata ace ki ɓoye min ba, Ni bana iya ɓoye miki duk abinda nake ciki Sister, ko har kin manta yanda muke da ke ne? Ke fa ƴar uwar haihuwa ce kuma mahaifarmu ɗaya, komai  kike ciki nima ina ji a jikina, dan haka ni a ganina bana ɗaya daga cikin wanda zaki rinƙa ɓoyewa lamuranki, don ko kin yi hakan ni ba zan kasa gane hakan ba, domin dole na ji a cikin jikina, ki huta lafiya sai anjima in kin fito."

  
      Tana gama faɗin haka ta juya zata bar ɗakin, har ta kama kofa zata bude ta kira sunanta, juyowa tayi ta kalle itama kallanta take tace,
 
 
      "Kiyi haƙuri Safrat ba na ɓoye miki bane, nima ban san ko wata nawa bane, abinda kawai na sani ina da juna biyu amma ban je asibiti ba har yanzu an tabbatar min, sanin kanki ne komai Safnat zata yi ko take ciki kafin kowa ya ji ko ya gani Safrat ce farko, kuma kome zan yi sai na nemin izininki ƴar uwata, naji yayi miki kuma ya dace na yi, in kuma bai miki ba nima bai min ba, saboda abinda Safrat ta ke so shi Safnat ke so, in kuma Safrat bata son abu Safnat ma bazata taɓa sansa ba, kiyi haƙuri kin ji ƴar uwa rabin jikina."
  

       "Lah! Kada ki damu Safnat, Ni babu abinda kikai min wallahi, wai na ɗan yi miki tuni ne dan kada wata rana ki manta da hakan, kuma ya kamata gobe insha Allah ki je asibiti a dubaki kinji, yanzu kwanta ki huta abinki, zan je na ɗaura abincin rana, bana san yau mu kai yammah bamu ci abincin rana ba."

      "Ba zan taɓa mantawa da ke ba ƴan uwata a kullum kina cikin raina, abincin rana kuma kin manta ni nake yi? Ai ke na dare kike yi ba na rana ba."
   
 
     "Ki huta kawai Sister ni zan yi gaba ɗaya, daga yanzu har ki haihu ba zan ƙara barin kiyi aiki mai wuya ba."
   
 
      "Hhhh!" Dariya tayi ta tashi daga kwance da take ta sauko daga kan gad,o ta ƙaraso har inda take ta dafa kafaɗar ta tace, "Kin ban dariya Safrat, muje muyi abincin tare barcin ma ya tafi."

   
        Kallanta kawai tayi bata ce komai ta buɗe ƙofa suka fita, dan tasan ko tace ta koma tunda har ta taso ba zata koma ba.

   
       Saukowa suka yi ƙasa turus suka tsaya suna kallanta, itama kallansu tayi ta kauda kai ta cigaba da karanta littafin da ke hannuta, itama  Safrat ɗauke kanta tayi ta nufi kitchen ita kuma Safnat ta nufe ta, zama tayi a kusa da ita tace, "Har kin wuce kenan?"

        "Meye damuwarki da hakan?"

   
       "Babu kawai na tambaya ne, kin san ance matambayi bashi ɓata, kuma ai na ga tambaya mabuɗin ilimi ce, ko ba haka bane?."

   
        "Haka dan naga alama kam."

   
      "Hmm! Allah ya shiryeki Fadwa ni kin ga tafiyata kitchen, sai kin taho ina kina ra'ayin haka."
   

       "Allah ya shirya mu gaba ɗayan mu, yanzu dai ba zaki bani amsata ba ko?"

   
         "Tame fa?"

       "Ta ɗazu da nayi miki mana."

      "Ohh! Sorry na manta yanzu dai taso muje, anjima zan baki amsar duk tambayar da zaki min."

        Kallanta ta ɗanyi na ɗan wasu saƙani sannan tace, "Lallai ma Safnat Ni zaki yiwa wayo, da ace ban san halinki ba ne sai ki gaya min haka na yarda, malama indai kina so a zauna lafiya ki gaya min abinda nake buƙatar ji yanzu."

       "Kai Fadwa kina da matsala, tunda nace miki zan gaya miki anjima wallahi da gaske nake zan gaya miki."

         "Kin yi alƙawari?"

   
       "Eh! Na yi insha Allah zan gaya miki komai kike buƙatar ji daga gare ni."

   
      Murmushi tayi ta miƙe tsaye tace, "Okay! Muje."

   
         "Yauwa ƴar ƙanwata muje."

  
      Harara ta dalla mata tace, "Kada ki ƙara ce min kanwarki."

      Miƙewa tayi tace, "To! Mama na ji muje." Tana gama faɗin haka tayi tafiyarta, bayanta ta biyo suna shiga kitchen suka tarar da Safrat har ta fara yanyanka abinda zasu buƙata, tayata suka shiga suna yi suna hira kamar basu ba.
   

      Bakinta ɗauke da sallama ta shigo kitchen ɗin, amsa mata suka yi ta gaishe da su, suka amsa cikin sakin fuska da kulawa, murmushi tayi musu ta tsaya tana kallan abinda suke yi.

   
                "Zan taya ku."

       "Mun gode Yasmeen je ki huta."

  
      "Ni na gaji da zama wajen ɗaya bana komai, a gida ni nake komai dan Allah ku bari na taya ku."

   
       Maggi Fadwa ta ɗauko ta miƙawa mata tace, "To! Gashi ki tayamu"

   
      Murmushi tayi ta karɓar ta nemi waje ta zauna ta fara ɓare maggin.
   
   
   
                      _*(•)(•)(•)(•)(•)*_
   
   
   
         "Alhamdulillah! Ɗan uwa munyi nasara mun gamsar da partners ɗin kasuwancin, sun saka hannun karinsu a kamfanin mu yanzu sai fara aiki gadan gadan."

       "Haka ne Nabil amma ni fa hankalina bai kwanta da Alhaji Muktar Akram da ya saka hannu jarinsa a kamfanina ba, ka duba fa ka ga tun kan nayi masa bayanin yadda abin yake ba, amma kawai ya amince da yin aiki tare da ni."

          "Gaskiya ne Yassar dan ni kai na na fara kokwanto akan yadda yake maka wani irin kallo, kamar da wata manufa yake san ya kusance ka."

         "Nima abinda nake gani kenan ka duba ba ka gani kwanaki da yazo wajen Dadday, lokacin muna gida ya rakoshi wajen motarsa da zai tafi, mu kuma a dai-dai lokacin muka fito daga sashen mu zamu shiga ciki mu gaida Momy mu fita, tun daga nesa yayi ta kallona har muka ƙaraso wajensu muka gaishe da su bai daina kallona ba, dama suka cigaba da tafiya banda waiwayena da yake yana kallona babu abinda yake, har tuntuɓe yayi saboda waiwayena da yake, sai da Daddy yayi masa maganar yana lafiya kuwa sannan ya daina kallona ya shiga motarsa ya tafi."

      "Hmm!" Ajiyar zuciya Kabir ya sauke sannan yace, "Haba ƴan uwa bai kamata ku rinƙa zargin Alhaji Muktar Akram ba, saboda in kuka yi duba da Daddy ne ya haɗamu da shi, kuma kunsa Daddy na zai taɓa haɗamu da abinda zai cutar damu ba, kun ga kuwa mutumin kirki ne shi, ta yiwa kana masa kama wani wani ne da ya sani shiyasa yake ta kallanku, kuma kun san zargi ba shi da kyau ko kaɗan, to! dan Allah ku daina zarginsa, insha Allah babu abinda ke tsakanimu da shi face ɗunbin alheri, Ni ina kyautata zatona akan sa kuma Please ku ƙyautata zatonku akansa kun ji."
   
  
     "Hakane Kabir mun gode da wannan tunatarwar taka, Allah ya saka maka da alheri."

   
     "Bakomai kada ku damu, ai iya wuya muna tare ƴan uwana." Ya kalli Yassar yace, "Amm nace ya maganar kai Yasmeen makaranta ɗan uwa?"
   

      Murmushi yayi yace, "Tana nan gobe insha Allah zan kaita."

   
         "Yawwa! Allah ya kaimu."

   
     Gaba ɗayansu suka amsa da, "Ameen Ya Allah.
   
      Nabil ne yace, "Amma wace makaranta zaka kaita ne ƴan uwa?"

   
      Bai ɗago ya kallesa ba a ɗan takaice yace masa, "Makarantar su Raudat zan kaita, domin ina so suyi kwance tare da Raudat, kamar yadda mu ɗin nan muke."

   
      Cikin farin ciki Nabil yace, "Masha Allah! Haka ake nima dama ita nake ta tunani tun farko mu kaita, amma kuma ina shaƙar yi maka maganar a saninka da nayi zaka iya gwalishe ni ! Tunda gashi da kanka kayi wannan tunani hakan."

   
      Ɗagowa yayi ya kallesa yace, "Ban taɓa yin tunanin haka daga gareka ba Nabil, ni a ganina duk abinda yake mallakina kaima mallakinka ne, amma sai gashi yanzu kana nuna min baka da ikon kan Yasmeen, gaskiya ban ji daɗin haka na har cikin raina wallahi."

   
       Hakuri Nabil ya shiga bawa Yassar, amma ya yi masa banza kamar bai san yanayi ba ma, ƙarshe ma ɗauke kansa yayi.

   
      Kabir ne ya dafa Yassar yace, "Ba haka yake nufi ba kai kanka kasan babu mai iya maka sai Allah, yanzu sai mutum ya zage jiki yayi maka wata magana ko wani abu amma in bai maka ba sai ka gwalishe shi, Ni banga laifin Nabil ba da yace haka ba, dan ko Ni kaina ina san yi maka maganar amma ina  tsoron kada ka gwalishe ni."

   
      Tabbas ya san shi ne bashi da gaskiya a wannan fegin, duk abinda suka faɗa ya san gaskiya ne, "Hmm!" Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya kallarsu yace, "Kuyi haƙuri kun ji na san nine bani da gaskiya, amma dan Allah ku gafarce insah Allah zan yi ƙoƙari canja kaina kun ji."

   
      Murmushi suka yi suka a tare suka ce, "Karka damu ɗan uwa in ka canza kuma ai bazaka yi kyan ganin ba, ɗabi'unka sune suffarka kuma sun matuƙar dace da kai, in kace zaka canza suffaka ba zaka taɓa yin ƙyau ba."

   
      Dariya yayi a wannan kaɗan yace, "To! Ai shikenan duk yadda kuka ce haka za a yi ƴan uwa rabin jina." Suma ganin yayi dariya ya sa suka dara, tare da tamƙe hanayena junansu alamun ana tare iya wuya.

   
        Nabil ne yace, "Ɗan uwa ni zan siyawa Yasmeen duk kan materials ɗin da ake buƙata na..."

       Kabir ne yayi saurin tarar numfashinsa yace, "Haba malam ai ka dai raba biyu ka ɗauki ɗaya ka bar min ɗaya ba ka haɗe duka ba."

       "Afuwa ashe masu neman sunan suna da yawa hhhh!"

      Harara Kabir da ya watsa masa yace, "Kai dai kake neman suna amma bani ba."

         Cikin tsokana Nabil yace, "To! In ba neman suna ba menene kake yi?"

        Cikin yanayi na fusata Kabir yace, "Ban sani ba, sai naji shaƙa sannan sai na gaya maka."

   
         Dariya sosai Nabil yakewa Kabir, Shi kuma Yassar ban da kallansu yana murmushi babu abinda yake yi, sai da yaga abin nasu na kusan zame musu rikicin wasan nan ya dagatar dasu yace, "Yanzu ku sulhunta kanku tun kan kusa kaina ya ɗau caji, na hana dukanku yin wani abu akan Yasmeen."

        Nan suka shiga sulhunta kansu ɗaya ya ɗauki siya mata kayan da zata yi amfani da su, ɗaya kuma yace zai siya mata uniform da takallimi da filas ɗin abinci da dai sauransu.

       Yassar ya ji matuƙar daɗi ganin yadda suke masa kara akan masoyiyar ƙanwansa, godiya ya shiga yi musu suka nuna mishi su sam basa san yana musu irin haka akan Yasmeen, tunda duk ɗaya suke ba amfanin yayi haka. Kai kawai ya girgiza alamun ba zai ƙara ba, daɗi suka ji zukatansu suka kamu da murna ganin ɗan uwan nasu ya fara gyaruwa.

   
         Hira suka shiga yi na ɗan wani lokacin a game da yadda zasu bunƙasa kamfanuwansu, tashi suka yi kowa ya nufi kamfaninsa dan ganin yadda al'amura suke tafiya a ciki, sannan su tafi gidan dan kasancewa da iyalansu.

                   _*(•)(•)(•)(•)(•)*_
   

       
           Da fara'ar akan fuskarsa yayi sallama ya shiga cikin farko da gudu suka yo kansa suna cewa, "Oyoyo! Daddy sannu da zuwa." Duƙawa yayi ya rungume yaran nasa cikin farin cikin da jin daɗin tarbar da sukai masa.

        Sumbatar goshinsu yayi su biyu sannan ya miƙe, ya kama hannusu suka ƙarasa shigowa cikin ɗakin yana kallanta, sai zuba masa ni'imtaccen murmushin da yake ƙara tsuma zuciyarsa take.

        Kusa da ita ya zauna yace, "Hajiyata lafiya kuwa kike na ga duk kin yi sanyi?"

       "Hmm!" Murmushin yaƙe ta ƙaƙalo Wanda bai kai har zuci ba tayi masa tace, "Me ka gani? Ni lafiya ƙalau nake, sannu da zuwa, an dawo lafiya? Ya meeting ɗin naku Allah yasa an yi nasara?"

       "Alhamdulillah! A yi nasara, ai na gaya miki kamfanin da nake san yin haɗaka da su na Alhaji Muhammad Bashir ne, amma yanzu ya mallakawa wani ɗansa Yassar halak malak nayi sa'ar yaron ya amince da ni a matsayi wanda zamu yi kasuwanci tare."

        "A da ina tunani ba bazan samu haɗin kansa ba sai kuma naga akasin haka, dan Yassar yaro ne mai hankali da nutsuwa da sanin darajar ɗan Adam, a gaskiya Alhaji Muhammad Bashir ba ƙaramin dace yayi ba da samun wannan yaron a matsayi ɗa, sai naji ina ma ace shi ɗin yarona ne, da na kasance me matuƙar alfahari dashi. Duk da alhamdulillah! Nima Allah ya bani yaro mai nutsuwa da tarbiyya, amma bai kama ƙafar Yassar ba, dan ba za a iya haɗa su ba."

     Umma da tunda ya furta sunan Yassar  a zancensa ƙwaƙwalwarta da zuciyarta suka birkice mata, ban da sunan Yassar babu abinda suke ta nanatawa, suka rinƙa saƙa mata abubuwa da dama, lokacin guda ganinta ya ɗauke, kunnuwanta suka toshe ta gaina gani kuma ta daina ji, duk abinda yake faɗa mata bata jinsa amma a duk lokacin da ya ambaci Yassar sai ta ji sunan, kuma duhun da take gani a idanuwanta da toshewar kunnuwanta sun ƙara yallawa.

 
       Zabura tayi ta miƙe tare da tafe kanta taku ɗaya biyu uku tayi ta sulale a ƙasa sumamayi. A matuƙar tashin hankali Daddy yayi kanta yana girgizar tare da kiran sunanta,

             "Khadijah! Khadijah!! Khadijah!!!"

   

   

_*See me next page✍🏻*_
_*Vote*_
_*Like*_
_*Share*_
_*Comment*_
_*#JannatMN*_   

      
   
*©JANNAT M. NASIR•*

Pokračovat ve čtení

Mohlo by se ti líbit

42.1K 2.5K 22
𝐁𝐨𝐨𝐤 # 𝟏 𝐨𝐟 𝐓𝐡𝐞 𝐑𝐚𝐚𝐳 𝐬𝐞𝐫𝐢𝐞𝐬. Love or betrayal? Consumption of betrayals. Internal betrayal? Yes! Will they be overcome? Or W...
1.7M 111K 26
#Book-2 in Lost Royalty series ( CAN BE READ STANDALONE ) Ekaksh Singh Ranawat The callous heartless , sole heir of Ranawat empire, which is spread...
45.2K 702 16
DELULU & GUILT PLEASURE
2M 100K 37
Presenting the story of ISHIKA MEHRA Whose innocence made the king bow down to her AND ABHIRAJ SINGH RATHORE Whose presence is enough to make the per...