YASMEEN.

Від JannatMN

1.2K 63 13

Labari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin... Більше

Page 1 ✍🏻
Page 2✍️
Page 3✍️
Page 4&5✍🏻
Page 6&7✍🏻
Page 8&9✍🏻
Page 10&11✍🏻
Page 12&13✍🏻
Page 14&15✍🏻
Page 16&17✍🏻
Page 18&19✍🏻
Page 20&21✍🏻
Page 22&23✍🏻
Page 26&27✍🏻
Page 27&28✍🏻
Page 29-30✍🏼
Page 31-32✍🏼

Page 24&25✍🏻

16 1 0
Від JannatMN

*°🔘°YASMEEN°🔘°* 
     *1442H/2020M.*
   
   





®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼




*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN*



*SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*



Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*



   
               *😭KUKAN KURCIYA.....🕊 (6)* 

        _*Ƴan uwa jomai ka rasa za ka iya samun wanda ya fi shi, amma ban da kwanakin rayuwarka, idan sun tafi sun tafi kenan, don haka kada ka bata rayuwar ka wajen abinda ba zai amfane ka ba, yi ƙoƙari wajan yin abinda zai amfaneka duniya da lahira...Allah yasa mu dace. Ameen Ya Allah 👏🏻*_





*SHAFI NA 24-25📑*

  
   
*__________📖* Juyi kawai yake ya kasa rintsawa, abinda ya faru ɗazu da rana ke tayi masa yawo a ƙwaƙwalwa, ita kuwa Safnat tuni barci yayi gaba da ita bama ta san meke faruwa ba, da dai ya ga juyin da yake tayi ba zai masa maganin abinda yake ji ba ya tashi daga kwancen da yake ya nufi bathroom ya ɗauro alwala ya fara gabatar da nafilfilu da addu'o'i tare da roƙon Allah ya bashi ikon kula da ƴar uwarsa har ƙarshen rayuwarsa.

          Bayan ya gama addu'o'insa ne ya miƙe ya fita a ɗakin, ɗakin Yasmeen ya nufa ya tura ya shiga ciki, turus ya tsaya yana kallan abinda yayi tozali da shi, kwance take saman tayal sai barcinta take cikin kwanciyar hankali, yadda kasan ta samu lallausar katifa ƙarasawa yayi inda take kwance ya tsuguna ya ɗauke ta cak, ya kwantar da ita akan gadonta ya ja bargon da yake saman gadon a gefe ya luluɓe mata ƙafafuwanta zuwa cikinta.

        Addu'o'i yayi ya shafe mata jiki da su sumbatar goshinta yayi, ya miƙe da nufi barin ɗaƙin ya ji an riƙon hannusa, juyawa yayi ya ganta tana masa murmushi kuma ta riƙe hannusa gam, ɗagowa yayi ya zauna shima murmushin yayi mata yace, "Dama ba barci kike ba?"

   
   
          "Barci nake, farkawa na yi tun lokacin da ka shigo ɗakin ai ina jinka, ai ni bani da nauyi barci duk barcin da nake ko ya aka ɗan yi motsi sai naji na farka."

   
   
         Mamakine ya kamasa aransa yace, _Wannan wace irin yarinya ce, a hankali fa na buɗe kofar na shigo amma har ta farkar caɓ! To yanzu da banko ƙofar nayi na shigo sai na iya firgitar da ita fa._
   

   
          Yaƙe yayi yace, "Lallai ƙanwata Allah ya baki kinji daɗinki, yanzu dai kwanta ki koma barcinki dare yayi sosai."

   
         "To! Yayana amma sai nayi nafila sannan zan koma, Yaya Ahmad ya gaya min ana so mutum ya rinƙa yin nafila idan dare ya raba, yace ba ƙaramin lada da alheri mutum yake samu ba idan yana yin nafilar dare, kuma yace duk abinda ka roƙi Ubangiji a wannan lokacin yana amsa maka roƙonka, ya kuma biya maka dukkannin buƙatun da ka roƙesa, ka ga ni lokacin ina gida ina yawan farkawa cikin dare, kuma bana jin tsoro nake fita na yo alwala nazo nayi nafilata na roƙi Allah ya bayyana min ku, nayi addu'o'i da Yaya Ahmad ya koyan na rinƙa yi indai ina gabatar da nafilfilu na, Allah sarki Yaya Ahmad ko yana a cikin wane hali yanzu ina kewarsa Yayana ka kaini wajensa dan Allah ko gaisawa ne mu yi."

   

   
        Tsabar mamakin da ya shiga da jin kalaman Yasmeen yasa shi kasa buɗe baki yace mata ƙala sai dai kawai ido da yake binta da shi, abinda ke basa mamaki bai wuce yadda yarinya ƙarama kamar ta har tasan wandanɗan abubuwan wai har ma tayi yisu..

   
   
          Jin yayi mata shiru baice komai ba yasa ta girgiza hannusa tace, "Dan Allah Yayana ka kai ni wajen Yaya Ahmad mu gaisa ina kewarsa."

   
   

          Yaƙe ya kuma yi a karo na biyu yace, "Kwantar da hankalinki ƙanwata zan kai ki wajen Yaya Ahmad ɗinkin, amma kafin nan wane ne Ahmad kuma ni ban sansa ba?
   
  

          Jin yace zai kaita yasa ta ƙara faɗaɗa murmushinta, ta yaye bargon da take cikinsa ta miƙe ta nufi bathroom zata shiga yace, "Ƙanwata baki ban amsata ba."
 

   
         "Ina nace zan baka bayyana maka wane ne Yaya Ahmad zai ɗan ja wasu ƴan mitina, shiyasa zan fara yin nafilata kada lokacin ya ƙure min sannan sai na baka amsarka."
   

  
          Baki ya buɗe yace, "Ikon Allah!" Ta yi caraf tana dariya ta ƙarasa masa maganarsa da, "Sai kallo." Sannan tayi addu'ar shiga banɗaki ta shiga.
   

 
          Shima dariya yayi har haƙoransa suka bayyana sannan yace, "Allah shiryaki ƙanwata." Ɗagowar da kansa da zai yi ya ga Safnat tsaye ta saki baki tana kallan abinda bata taɓa gani ba.
   
  

          Ganinta da yayi bai sa ya daina dariyar da yake ba har sai da ya mai isarsa sannan yace, "Kinga wata irin yarinya, wallahi ko a labari ban taɓa ji labarin yarinya mai irin wannan ɗabi'un ba, wai ita nan nafila zata yi...." Ya ƙarashe maganar yana dariya ita dai bata ce komai ba ban da kallansa da take, ya futota yayi da hannusa, alamun tazo ƙarasowa tayi inda yayi mata nuni ta zauna, gefen sa ta zauna har a lokacin kallansa take shi kuma bai daina dariyar ba.
   

   
       "Wannan irin kallan da kike min na mene ne fassara?" Ya ƙarshe maganar yana ɗage mata gira tare da kanne mata ido ɗaya. Kai da girgiza masa alamun bakomai yace, "Oho! Na ma gane matsalar bakin ne ya samu matsala."

  
   
       Janyo ta yayi ta faɗo jikinsa har suna jin numfashi juna yayi mata wani shu'umin murmushi yace, "Faɗuwa tazo dai-dai da zama, tun da gaki ga likitanki baki da wata damu, bari yanzu na duba miki bakin naga wane loko ne ya samu cika." Ya daɗa matse ta a jikinsa, ta gane nufinsa ta zato idanuwa waje tayi saurin fizge jikinta ta mike tace, "Wallahi bakomai, na tafi sai da safe barci nake ji ma." 
   
  

        "Hhhhh! Matsoraciya kawai ga tsoro ga jan faɗa da kada ki buɗe baki kiyi magana ki ga abinda zan yi miki." Dariya sosai yake mata yana nunata da yatsa har da riƙe ciki yake tsabar dariyar da yake yi, ita kuwa ban da hararar wasa da murguɗa masa baki babu abinda take yi.
   
   

        "Ni kike murguɗawa baki?" Yin ƙurawa yayi zai kamota bude kofar da Yasmeen tayi ne yasa shi tsayawa cak ya fasa abinda yayi niyya, amma kuma yana aika mata da sakon zai kamata ne ta ido ita kuma gwalo tayi masa ta ɗauke kanta.
   

   
        Ko kallansu bata yi ma ta shimfiɗa sallaya ta saka hijjab har zata tada sallah jiyo tace, "Yayana akwai Alƙur'ani a ɗakin nan?"
   

   
      "Eh! Akwai me zaki yi da Alƙurani yanzu ƙanwata?"
   

   
       "Tilawa zan yi in na idar da nafifilolina."
   
   

         "To! Yi nafilarki zan ɗauko miki na aje miki a gefen sallaya" Bata ce komai ba ta tada kabbara, lokar dake gefen gadonta ya jawo, Alƙur'ani da abin da ake ɗaurawa akai ayi karatu ya aje mata a jefen sallaya kamar yadda yace mata.
   

   
           Tun suna ƙirga sallamarta har suka gaji suka daina kuma kowace raka'arta sai ta jima a cikinta, Safnat tsabar mamaki yasa ta riƙe baki da neman waje ta zauna ba shiri, shi kansa Yassar ranar mamaki sai da yasa shi riƙe baki yana jiran ya ga tayi dungure-dungure ta gama ashe ba haka za tayi ba.
   

   
        Raka'o'in ƙarshe ne suka ji tana ta zuba addu'o'i ba ko ƙaƙƙautawa, kasa ɗaurewa Yassar yayi sai da ya leƙata ya ga itace take yi ko ba ita bace, bakinta ya ga yana motsawa dawowa yayi ya zauna ya doka uban tagumin yana ganin ikon Allah!

         Bayan ta idar da nafilfilunta tayi azkar ɗin da ake gabatarwa in aka idar da sallah, ta buɗe alƙur'ani mai girma ta fara rera ƙira'ar ta ciki tajiwid, tana baiwa ko wane harafi haƙƙinsa, Suratul Zumar ta ke karantawa.....

         Sadaƙalhul'azim ta ja a lokacin da ta gama karatunta....tashi ta yi taje ta maida Alƙur'ani a in da Yassar ya ɗauko mata, sai bayan ta aje maida Alƙur'anin ne, ta kula da duk sunyi barci Yassar a saman gadonta Safnat kuma a saman kujerar ɗakin, kai kawai ta girgiza, ta yi murmushi ta ja bargon da ke gefensa ta luluɓesa, sannan ta ɗauko wani bargon da ke gefe a ajje ta luluɓe Safnat, sannan ta dawo saman sallayar da tayi sallah tayi kwanciyarta abinta.

          Kiran sallah asuba ya farkar da shi daga barci yaye bargon da ta lulluɓesa yayi ya miƙe, mamaki ne ya kamasa da ganin duk sun yi barcin da basu san lokacin da ya ɗauke su ba, bargon ya ɗauka ya je ya luluɓeta bai yi gangancin taɓata ba, dan yana tsoron kar ta kuma farkawa kamar ɗazu, sannan ya ƙasara kujerar da Safnat ke barci akai ya yaye bargon da ta yafa mata ya ɗauketa cak suka bar ɗakin.

           Yana zuwa ɗakin su ya kwantar da ita a saman gado ya lulluɓeta da bargo, ya nufi bathroom ya ɗauro alwala ya tafi masallacin.

  

           Bashi ya dawo ba sai da gari ya fara sha sannan ya dawo daga mallacin, ba in da ya zame sai ɗakinsa yayi kwanciyarsa domin barcin dake cinsa a idonsa.
   
   
   
   
                          _*((•))((•))((•))((•))((•))*_

  
   

            Ba shi ya farka ba sai wajen 8:30am tashi yayi a gaggauce ya gama shirinsa ya fito hannusa ɗauke da jakar zuwa office, ɗakin Safnat ya fara zuwa ya ga bata ciki, hakan ya tabbatar masa da tana ƙasa, fitowa yayi ya shiga ɗakin Yasmeen itama ya ga wayam ba kowa a ciki juya yayi ya sauko ƙasan.

          Zaune ya samesu suna hira hakan ya tabbatar masa da har sunyi karya shi kawai suke jira, yana ƙarasowa ya ce musu su tashi su tafi office ana jiransu tashi suka yi suka nufi hanyar fita.

   
   
          "Habibyna baka fa ci komai ba, Please ka tsaya kasa wani abu cikinka."

   
   
         "Kiyi haƙuri Safnat wallahi mun makara sosai 10:00am muke da wai meeting mai muhimmanci da wanda zasu saka hannun jari a Companys ɗinmu kuma kin ga yanzu 9:15am, zan nema naci a wajen karki damu kin ji."

   
   
          "To..! Allah ya bada nasara a dawo lafiya, amma Please kada ka zauna da yunwa kaji."

   
   
         "Ameen Ya Allah matar aljannah, Insha Allah ina fito daga meeting ɗin zan nemi abinda zan sawa cikina."

   
   
          Yana gama faɗin haka ya ce gaba da tafiyarsa har yasa ƙafa a ƙofar fita yaji ta kira sunansa da ƙarfi, juyowa yayi yaga ta nufinsa da gudu hannuta ɗauke da plate da robar ruwa da tishu, tana zuwa inda yake ya jawo hannusa alamu ya rage tsawansa, ganewa yayi ya har sai da gwiwoyinsa suka taɓa ƙasa.

     
          Ta fara bashi soyayyan dankalin da ta ɗebo buɗe baki ya rinƙa yi tana basa a baki har ya cinye dankalin tas, sannan ta goge masa baki da tishun da ta ɗauko ta buɗe robar ruwa ta bashi ruwa a baki yasha sannan ta ce, "Alhamdulillah! In ganta lafiya yafi komai Yayana, ka ga yanzu sai kafi jin daɗin yin komai da ka cika cikinka, Allah ya bada sa'a a dawo lafiya."

   
   
        Mamaki da al'ajabi yarinyar ne ya kama su Nabil da su Safnat suka buɗe baki suna kallan ikon Allah, yarinya ƙarama ta san ta shawo kan babba ina ga in ta girma, a ransu kowa fatan Allah ya rayata suke yi.

   
   
       Sumbatar goshinta yayi yace, "Ameen Ya allah, Na gode My Princess Allah ya bar mu tare."

   
   
       "Ameen Ya Allah Yayana tashi kaje kada ka makara kaji."

   
   
      Tashi yayi da fara'a suka bar gidan, ita kuma ta je ta aje plate, robar ruwa da tishu ta dawo inda su Safnat suke ta ce, "Aunty ki zo ki haɗan kayan da kaku ɓata na wanke su tun kan su bushe suyi wuyar wankewa."

   
   
       Su Safnat da har lokacin basu daina mamakin abinda tayi ma yanzu gashi kuma tana son ƙara basu wani Safrat ce tace, "Haba little princess wannan aikin ba baki bane yafi ƙarfinki, zo ki zauna kin ji akwai me yi yanzu zaki gata wanke su."

   
   
        "Bai fi ƙarfina ba Aunty kumatu ki haɗan ki ga tas zan wanke su."

   
   
         Dariya suka Fadwa suke yi da ƙara nanta sunan da Yasmeen ta baya wai Aunty kumatu, ita kanta Safrat dariya sunan ya bata sosai tace, "Yanzu dan Allah little princess ki rasa wane suna zaki samun sai Aunty kumatu?"

   
   
       "Ai Aunty kumatu bana iya gane ki da Aunty matar Yayana sai da kumatun da kika fita da kaɗan, shiyasa naga ya dace na rinƙa kiranki da Aunty kumatu dan kada na manta wannan gaba."

   
   
       Dariya su Safnat kawai suke wa Safrat Fadwa har da ƙwalla dan dariya ita kuma Safrat murmushi kawai ta yi, ta yi shiru bata ƙara cewa komai ba dan taga faɗan yafi ƙarfinta, kallansu Yasmeen tayi ta cewa Fadwa, "Aunty goshi dariyar ƙeta fa babu kyau ki dai."

   
   
        Ba shiri Fadwa ta gimtse dariyar da take yiwa Safrat jin sunnan da aka bata itama, kamar tayi kuka tace, "Littel princess kin gama da ni wallahi, Aunty goshi fa kika ce min."

   
   
         Safnat bata san lokacin da ta faɗin daga kujerar da suke zaune tsabar dariya muguntar da take musu, itama Safrat dariya take wa Fadwa sosai jin sunan da ka ba Fadwa yafi nata muni, ita kuma ta sha kunu ta mike tace, "An cini wasan nan na tafi gidana sai kuma wani lokacin."

   
   
         Safnat ce ta maƙale murya tace, "Aunty goshi inzo muje?" A futace ta jiyo zata fara masifa taji Yasmeen na cewa, "Kai Aunty doguwa ba kyau ba tsokana fa ki dai kinji."

   
   
        Ai ba shiri ta dawo ta zauna tanawa Safnat dariya da hamdala da aka bata itama nata sunan, Safrat kuwa tsabar dariya ta hanata cewa komai sai dariya.
   

        Safnat ce ta marairaice murya tace, "Yanzu dan Allah kin kyauta min da kika kira gni da Aunty doguwa? doguwa sunan wani gari ne a Kano fa."

   
   

_*See me next page✍🏻*_
_*Vote*_
_*Like*_
_*Share*_
_*Comment*_
_*#JannatMN*_   


      

   
*©JANNAT M. NASIR•*

Продовжити читання

Вам також сподобається

308K 15.4K 47
Ruby King is your average young woman who is starting to attend college full time. Everything is going great until she notices that there seems to be...
36.6K 3.3K 19
A Royal family renowned for their illustrious name and fame, A family full of pride and rage, A Family for which everyone bows their head - The Agnih...
135K 3.7K 25
Warning: 18+ ABO worldကို အခြေခံရေးသားထားပါသည်။ စိတ်ကူးယဉ် ficလေးမို့ အပြင်လောကနှင့် များစွာ ကွာခြားနိုင်ပါသည်။
37.4K 623 11
This story is based on village story with lots of smut...