YASMEEN.

By JannatMN

1.2K 63 13

Labari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin... More

Page 1 ✍🏻
Page 2✍️
Page 3✍️
Page 4&5✍🏻
Page 6&7✍🏻
Page 8&9✍🏻
Page 10&11✍🏻
Page 12&13✍🏻
Page 14&15✍🏻
Page 16&17✍🏻
Page 18&19✍🏻
Page 22&23✍🏻
Page 24&25✍🏻
Page 26&27✍🏻
Page 27&28✍🏻
Page 29-30✍🏼
Page 31-32✍🏼

Page 20&21✍🏻

15 1 0
By JannatMN

*°🔘°YASMEEN°🔘°* 
     *1442H/2020M.*
   
   



®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼


*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN*

*SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

   
           *😭KUKAN KURCIYA.....🕊 (4)* 

        _*Ƴan uwa Rinjayar mai ƙarfi ba shi ne gwaninta ba, gwani shi ne wanda ya iya bakinsa, ya rinjayi zuciyarsa, ya iya haɗiye fushinsa.*_
         _*Komai ka rasa za ka iya samun wanda ya fi shi, amma ban da kwanakin rayuwarka, idan sun tafi sun tafi kenan, don haka ka da ka ɓata rayuwar ka wajen abinda ba zai amfaneka ba, yi ƙoƙari wajen yin abinda zai amfaneka duniya da lahira...Allah yasa mu dace*_
           _*Barkan mu da Juma'a. Da fatan mun wuni lafiya? Allah ya bamu lafiya da ƙarfin arziki, Allah ya sada mu da alkhairan wannan rana. Ameen ya Allah👏🏻*_   



*SHAFI NA 20-21📑*

  
   
*__________📖* "Umma dan Allah yaushe Yaya zai dawo? Gaba ɗaya gidan ya yi mana wani irin."

        "Ayman nima ina kewar Abdallah, amma ba yadda zamu yi dole mu yi haƙuri har ranar da Allah zai sa muje masa ziya, dan ba zan iya jira har sai ya gama karatunsa ba sannan zamu ga juna."

         "To..! Umma yaushe zamu je masa ziyara?"

        "Ka bari Daddy ku ya dawo sai ka tambayesa, amma na san ba yanzu zamu je masa ba sai an ɗan jima."

   
        "Saboda me yasa ba zamu je masa ba yanzu Umma?"

   
         "Saboda in dai muka ce zamu ta ƙura masa, ba zai maida hankali a karatunsa ba, kana san mu zama silar rashin cikar burin Yayanku?"

   
         "A'a! Umma bana so, mu barshi ya yi karatunsa a nutse karda mu takura masa, ni na haƙura da zuwa masa ziyar zamu rinƙa video call da shi har ya gama karatunsa gaba ɗaya ya dawo."

   
         Hamdala ta yi a cikin ranta da samun damar shawo kan yaran cikin sauƙi, ba tare da sun sha wuya ba. Murmushi ta yi tace, "Aiko da Yayanku ya yi matuƙar alfahari da ku."

   
        Sai a lokacin Aymana ta buɗe baki tace, "Indai Yaya zai yi alfahari da mu, na yarda da abinda Ayman yace ba zamu ta ƙura masa ba."

   
         "Wow! Yarana masu tunanin manya, Allah ya albarkanci rayuwarku, ya kuma raya mana ku twin's ɗin Abdallah."

        
      Juyawa suka yi in da sautin maganar ke fitowa, da gudu suka yi kansa suna faɗi, "Oyoyo Daddy!" Rungume juna suka yi muna murna.

   
      "Sannu da zuwa Daddy, an dawo lafiya?"

   
      "Lafiya kawai twin's ɗina, fatan na same ku lafiya."

   
       "Eh! Daddy lafiya ƙalau muke."

   
         "Kun ci abinci kuwa."

   
         "A'a! Kai muke jira ka dawo muci."

   
       "Ayyah! Abin alfaharina, ku zo muje na baku a baki ku ci ku ƙoshi."

         Da murna su suka ƙarasa falon, ya zauna a kurera yace a kawo masa abinci yau anan zasu ci abinci, dariya ta yi sannan ta tashi ta haɗo kulolin abinci ta kawo masa, ledar cin abinci ta je ta ɗauko ta shimfiɗata a tsakiyar falon, kowa ya sauko ya zauna itama zama ta yi ta zuba musu abincin ta miƙawa kowa nashi, "Hajiyata a plate ɗaya zaki zuba mana kuma babba."

         Murmushi ta yi tace, "An gama ranka ya daɗe." Ta tashi ta je kitchen ta ɗauko babban plate zato ta haɗe abincin a plate ɗaya, ta tura musu zata tashi yace, "Haba Madam ina zaki ne kike ta wannan hanzarin." Jiyowa ta yi fuskarta cike da annurin tace, "Ranka ya daɗe babu inda zani, gefe zan koma na zauna naita kallanku." Ƴar dariya ya yi marar sauti yace, "Wato ki ta kallan mu, gidan zoo kika mai damu."

 
        Wannan karan dariya ta yi tace, "Haba alhajina ni na isa, yanzu dai me kake san na yi?" Kallanta ya ɗan yi yace, "Zama zaki yi mu ci abinci tare yau." Dawowa ta yi ta zauna suka saka hannu suna ciyar  da junansu cikin farin ciki.

   
   
                     _*<<<<<~•~>>>>>*_

   
   
           Shigowa suka yi har bakin gadon da Yasmeen take su ka je, baki suka buɗe ganin tsananin kyauwun da Yasmeen take da shi a ransu suna cewa, _Ayan yarinyar nan bahaushiya ce?._ Ita kuwa Safnat da ta ga yarinyar, sai ta ga duk ƙyan da take ganin Yassar yana da shi ashe ko rabin yarinyar nan bayyi ba a fagen kyau ba. A takiyanke suka ji ƙaunar yarinyar ya shiga zuciyoyinsu.

    
             Ya jiki suka yi mata, kai kawai ta gyaɗa musu bata tankawa kowa ba, sun ɗan yi mamaki suka jiyo suka kalli Yassar, wanda yabi ya haɗe girar sama da ta ƙasa, saboda kar su kawo masa raini. Safrat ce tace, "Ya Yassar ya bata yi mana magana ba?"

   
           "Bata magana, amma tana jin abinda kuke cewa." Tausayin yarinyar da ƙaunar ta ne suka ƙara shiga zuciyoyinsu musamman Kabir da tunda ya shigo ya kasa cire ido akanta, shi ko Nabil tunda ya shigo ɗakin ya ɗaura ido kan yarinyar ya dan firgita, sai mai nuna ba amma jefi-jefi in ya kalli yarinyar sai ya ɗago ya kalli Yassar, shiru ya yi bai gayawa kowa abinda ya gani ba, amma kuma ya kasa sakewa a cikin ransa.

   
           Safnat ce ta zuba abinci zata bata a baki ta kauda kanta alamun ba zata ci ba, mamaki ne ya kama Safnat ta jiyo ta kalli Yassar da ke bayanta tace, "Taƙi cin abincin Habibyna." Takowa yayi ya ƙaraso har inda take yace, "Baci ne ba zata yi ba, kece bata yarda da je bane, amma bani ki ga." Tashi ta yi ta bashi wajen tare da miƙa masa plate ɗin, ya karɓa ya zauna.

   
          Murmushi ya sakarwa Yasmeen itama ta yi masa, abin ya matuƙar basu mamaki dan tun da suka shigo ɗakin babu wanda ta yiwa fara'a, sai dai kawai kallan da take binsu da shi.

   
          "Ƙanwata zaki ci abinci?" Kai ta gyaɗa alamun eh zata ci, murmusawa ya ɗan yi ya riƙa bata abinci tana ci, sai da taci ta ƙoshi sannan ta kaɗa masa akai alamun ta ƙoshi, aje kwanan ya yi ya yago tishu ya goge mata bakinta sannan ya bata ruwa ta sha.

    
         Hannuta ta ɗaura kan nasa ta ƙara yalwata murmushi ta kaɗan kanta, ya gane me take nufi yace, "Bakomai Ƙanƙara ba godiya tsakanin mu, ni ai Yayanki ko?" Kaɗa kai tayi alamu eh yace, "Yauwa! Ƙanwata kada ki ƙara yin min godiya a duk abinda na yi miki." Kaɗa kai ta ƙara yi alamun to. Sakin dai baki suka yi suna kallan ikon Allah.

   
         Nuna mata su Safnat ya yi ya ce, "Ƙanwata kin san waɗannan?" Kai ta gyaɗa alamun a'a bata sansu ba, "Ai ba zaki sansu ba ƙanwata bari na yi miki bayanin su, duk ƴan uwanane su."

          Ya nuna Safnat yace, "Wannan ƴar uwata ce Safnat kuma matata ce ita." Ya nuna Nabil da Fadwa yace, "Suma ƴan uwanane Nabil da Fadwa kenan suma mata da miji da mata ne." Ya ƙara nuna Kabir da Safrat yace, "Ƴan uwanane suma Kabir da Safrat miji da mata ne suma."

           "Kin gane su yanzu ko." Ta kaɗan kai alamun eh ta gane su yace, "Yauwa! Yasmeen Ƙanwata." A razane Kabir ya ɗago yace, "Ɗan uwa Yasmeen fa ka anbata?"

         "Eh! Kabir ban san samanta ba, kuma gashi bata magana, shiyasa nace mata na rinƙa kiranta da Yasmeen ta kaɗa min kai alamun ta na son sunan."

   
         A jiyar zuciya ya yi alamun gamsuwa da abinda ya Yassar ya gaya masa, shi dai Nabil bai ce cikanka ba kawai kallan su yake. Ranar Yasmeen ta ga gata wajen su Kabir musamman ma Safnat da ta zage damtse wajen ganin Yasmeen ta saki Jiki da ita, amma kuma taƙi sakin jiki da ita da sun ɗan matso kusa da ita sai ta fara ja da baya.

          Dr. Ne ya shigo ɗakin suka gaisa da jama'ar ɗakin, sannan ya tambayi Yasmeen bata jin komai jikinta, ta kaɗa kai alamun eh bata jin komai, murmushi yayi mata yace, "Masha Allah!" Sannan ya juya ya kalli Yassar yace, "Jikin Yasmeen ya yi kyau sosai zamu iya sallamarta nan bada jimawa ba."

        Hamdala Yassar ya ringa yi a fili da zuci sannan yayiwa Dr. Godiya suka yi sallama ya fita.

   
        Har bayan magariba suna asibitin, abincin rana da na dare duk daga gidan Daddy ake kawo musu, sai bayan sallar isha Daddy da Momy suka zo asibitin, tunda Momy ta shiga ɗakin take ta kallan Yasmeen ko kyafta ido bata yi akan Yasmeen, sai da aka dtan taɓa ta sannan ta dawo daga dogon tunanin da ta tafi.
    
   
         Ya jiki suka yi mata sannan Yassar ya gabatar mata dasu a wajensu, suma kaɗa musu kai kawai ta yi wajen suka nema suka zauna akan ɗan taɓa hira, Daddy ya tashi yace zasu tafi Allah ya bata lafiya. Godiya Yassar ya shiga yi musu har sai da Daddy ya takatar da shi sannan ya daina.
   
   
          Ita dai Momy har suka bar asbiti bata daina kallan Yasmeen da Yassar ba, Nabil ya lura irin kallan da Momy ke yiwa Yassar da Yasmeen, irin wanda yake musu ne shima, a ransa yace, _Ko dai itama Momy ta ga abinda na gani?_ A fili kuma yace, "Bro muma bari mu tafi kada dare ya yi mana." Ya kalli Yasmeen yace, Ƙanwar mu mun tafi, gobe insha Allah zamu dawo." Kai ta gyaɗa masa kawai yayi murmushi.
   
   
        Sallama suka yi mata da Yassar suka tafi, sun ce Safnat ta zo su tafi ta ce su yi tafiyarsu kawai, dariya suka yi mata sannan suka yi tafiyarsu, ɗaki ya rage daga Yassar sai Safnat da Yasmeen.
   
   
   
        Sai da suka ɗan jima da tafiya sannan, ya kallenta ya ce, "Saboda me yasa baki bisu ba?"
   
   
         "Nima so nake yau na yi jiyar ƙanwarmu ne."
   
   
          "Hmm! Ke dai ki faɗi gaskiya kawai a wuce wajen."
   
   
          "To..! Me kake so nace maka? Ni yau anan zan zauna."
   
   
         Kallanta ya ɗan yi na wasu lokuta ya yi murmushi yace, "Shikenan ki tsaya da ita ni bari na tafi, amma ai naga baki taho da abinda kike buƙata ba."
   
   
        "Eh! Amma ai ba matsala zan yi amfani da naka kawai, amma me yasa ba zaka tsaya mu zauna tare da ita ba?"
   
   
         Ɗagowa ya yi ya dalla mata hararar wasa yace, "Waye zai tsaya anan ɗin? Ke me yasa baki da kunya Safnat asibiti ne fa nan."
   
   
          Hamma tayi tare da miƙa tace, "To..! Meye a ciki?  Dan ka tsaya a nan ai ba wani ɗaki nace a bamu muyi jinyar juna ba, a nan zamu tsaya kusa da ƙanwar mu, kawai bana so ka ƙara yi min nisa ina so idan na buɗe idanuwana na sauke su akan...." Da sauri ya rufe mata baki bata ƙarasa abinda take san faɗa ba, ya raɗa mata a kunne ya ce, "Haba Safnat a fa gaban yarinya kike, ya kamata ki ɗan rinƙa sakayawa."
   
   
         Hannusa ta cire daga bakinta ta kalle sa ta kashe masa ido ɗaya tare da ɗaga masa jira tace, "Zaka tsaya ne ko tafiya zaka yi?"
   
   
         Shiru ya yi ya maida fuskarsa kalar tausayi yace, "Haba ranki ya daɗe, ki dai ƙara duba lamarin nan kada a samu matsala, kin ga ba mu kaɗai bane a ɗakin."
   
   
         Haɗa girar ƙasa da ta sama tayi alamun ita sam bazata yarda ba tace, "Eh! ko A'a!?"
   
   
         Kallanta ya ƙara yi ya kauda kai yace, "Shikenan na yarda, amma da sharaɗi ɗaya in kin yarda."
   
   
        Cikin sakin fuska tace, "Me ye sharaɗin naka?"
   
   
         "Ke zaki kwanta a wancen ɗayan gadon ni kuma a ƙasa, kuma kada ki sake ki sauko ƙasa in da nake, indai kin yarda zan tsaya, in kuma baki yarda ba sai nayi tafiyata."
   
   
         Dariya sosai ta yi a cikin ranta tace, _Ai dama ko baka ce haka ba, ba a kusa da kai zan kwanta ba, kawai ina maka haka ne dan kada ka tafi ka yi nisa da ni ne._ A fili kuma ta kamar zata yi kuka tace, "Haba Habibyna yanzu..." dakatar da ita yayi ta hanyar cewa,
   
   
          "Bana san jin komai daga bakinki yanzu, amsar sharaɗina nake jiran ji kawai."
   
   
          "Shikenan na yarda, ai duk yadda kace haka za'a ranka ya daɗe."
   
   
         Jiyowa yayi ya kalli inda Yasmeen take yaga barcinta kawai take yi, a ransa yace _Haba! Shiyasa Safnat ta saki baki sai sakin zance take yi, ashe ta san yarinyar nan ta yi barci shiyasa take min haka._
   
   
         Kallanta ya yi yaga sai dariya take masa har da duƙawa yace, "Yi dariya san ranki zaki shigo hannu ne."
   
   
         "Hhhh! Ashe haka kake da kunya kamar wata bafullatanar budurwa?" Cafka ya kawo mata ta goce tace "Ai gaskiya na faɗa, wato indai daga ni sai kai ne sai ka ta sakin baki har tsoro kake ɗan ban, amma indai da wani a gurin har guduna kake yi saboda tsabar kunya, ai kuma tun da ka bari naga yadda kake takunka ka kaɗe."
   
   
         Hararar wasa ya rinƙa zubo mata ita kuwa sai dariya take masa, da dai yaga zata mai da shi mahaukaci kawai sai ya fice ya bar mata ɗakin.
   
   
         Zama ta yi tana maida numfashi dan dariyar da tasha ta yi yawa, zama tayi a gefen gadon da Yasmeen ke kwance, idanta ne ya sauka akan damtsen hannun Yasmeen ta ga wani baƙin abu a jiki, matsawa tayi ta shafa abun a ruɗe.
   
   
         Ba komai ne ya faɗo mata arai ba sai tambayar da ta yiwa Yassar kwanaki akan wani baƙin abinda ke damtsensa, _Habibyna baƙin abun da ke damtsen hannuka na menene? Da shi aka haife ni Habibtyna, akwai mutum biyu da suke da shi a dai-dai inda kika ga nawa yake. Su waye? Bar zancen kawai Habibtyna dan Allah taimako min da ruwa mai sanyi._
   
   
         Janye hannuta tayi cikin sauri a fili ta ce, "A'a! Haba ta ya ma zai zama gaske?" Ƙurawa Yasmeen idon ta yi yadda take barci haka shima Yassar yake nasa, irin barcin nan na rabin ido a buɗe rabi a rufe, kuma ga tsatan kamanin da suke sun bayyana kansu ƙuru-ƙuru. A ranta tace, _Anya! Ba wannan ce ƙanwar Yassar da yake ta nema ba? Amma bai san idan take ba._
   
   
         Lokacin guda duk tabi ta fita a hayyacinta, shigowa ya yi yaga yadda ta canza lokacin guda ya shiga tambayarka lafiya take kuwa, shiru tayi masa sai dai ta kallesa ta kalli Yasmeen kawai. Rugumeta ya yi yana bubuga bayanta na ɗan wasu lokuta sannan ya janyeta a jinsa, har gadon da zata kwanta ya kaita ya kwantar da ita, sannan ya dawo ya gyarawa Yasmeen kwanciyata shima yayi tashi shimfiɗa ya kwanta. Ranar Safnat raba tare tayi tana ta saƙe-saƙe akan Yasmeen da Yassar.
   
   
        Kwanana su uku a asibiti aka sallameta a lokacin Yasmeen ta saki jiki da Safnat, itama ta zage sai kulata take da ita, gidan Daddy suka taho dan yace in aka sallamesu su zo gida su yi magana, kowa ya hallara a falon Daddy Yasmeen na tsakiyar Yassar da Safnat, Daddy ne yasa fara magana.
   
   
        "Alhamdulillah! Allah ya ba Yasmeen lafiya, abinda yasa nace kuzo nan shi ne, ina san na ɗauki Yasmeen na haɗata da Raudat mu cigaba da rainansu."
   
   
        Dum-dum yaji gabansa ya faɗi zuciyarsa ta shiga bugawa da ƙarfi jin ance za'a rabasa da yarinyar da ya ke ganin kamar ƙanwarsa, itama Yasmeen tana cin furucin Daddy ta ƙanƙame Yassar tana kaɗan masa kai shima riƙeta yayi sosai yace, "Daddy dan Allah kayi haƙuri ka bar min ita na raineta wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba."
   
   
        Kallansa Daddy ya yi yace, "Haba Yassar ta ya za'a bar maka yarinya ƙarama kamar wannan ka rena, bacin baka san ya ake raino ko haihuwa ba ku yi ba, auranku ko wata biyar bai cika da yi ba, ta ya kake zaton zan yarda na baka yarinya ƙarama ka raina?"
   
   
       Wannan maganar ta Daddy ta fusata Yassar har ya manta matsayin Daddy a wajensa ya kama hannu  Yasmeen ya miƙa yace, "Ni bazan bada yarinyar nan ba ni na ɗauko kuma ni zan raini abata." Abinda Yassar yayi ya matuƙar girgiza su, a karo na farko da Yassar ya yi ma Daddy musu a tsawon shekarun da suka kwashe da shi, Hanya ya kama zai fita Momy ta taka masa tsawa tace, "Kai Yassar a cikin hankalinka kuwa kake? Ta ya kake tunani za'a bar baka wannan yarinyar? To kama sake tunani, dan mu ba zamu bar maka wannan yarinyar ba, dole ka barta a nan in yaso sai ka rinƙa zuwa kullum kana ganinta."
   
   
       Gurkushewa yayi a wajen ya fashe da kuka yace, "Dan Allah taimake ni kada ku raba ni da ita, wallahi ba raba ni da ita tamkar raba ni da farin cikina ne." Kuka yake sosai kamar wani ƙaramin yaro, girgiza suka yi gaba ɗayansu ganin Yassar na kuka abinda basu taɓa gani ba.
   
   
       Cikin tsawa da faɗa ta buɗe baki tace, "Rabu da su Yayana daina kuka babu wanda ya isa ya ƙara rabamu......"
   
   
   
   

   
_*See me next page✍🏻*_
_*Vote*_
_*Like*_
_*Share*_
_*Comment*_
_*#JannatMN*_   

      
   
*©JANNAT M. NASIR•*

Continue Reading

You'll Also Like

123K 3.5K 25
Warning: 18+ ABO worldကို အခြေခံရေးသားထားပါသည်။ စိတ်ကူးယဉ် ficလေးမို့ အပြင်လောကနှင့် များစွာ ကွာခြားနိုင်ပါသည်။
85.7K 252 25
Smut 18+ ONLY! ⚠️WARNING⚠️ ⚠️CONTAINS MUTURE CONTENT⚠️ ⚠️VERY SEXUAL 18+⚠️ 22 year old Raven Johnson is just going to her yearly doctors appointment...
59.7K 5.9K 117
A story following a young hunter named Jay. He has grown up in a world where dungeons, monsters, and humans with leveling systems are a cultural norm...
61.1K 1.6K 62
"mom, dad, Im married!" lahat ng relatives namin ay nagulat sa announcment ko. Sino ba naman kasi ang mag aakala na ang unica ija ng pamilyang Letpr...