YASMEEN.

By JannatMN

1.2K 63 13

Labari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin... More

Page 1 ✍🏻
Page 2✍️
Page 3✍️
Page 4&5✍🏻
Page 6&7✍🏻
Page 8&9✍🏻
Page 10&11✍🏻
Page 14&15✍🏻
Page 16&17✍🏻
Page 18&19✍🏻
Page 20&21✍🏻
Page 22&23✍🏻
Page 24&25✍🏻
Page 26&27✍🏻
Page 27&28✍🏻
Page 29-30✍🏼
Page 31-32✍🏼

Page 12&13✍🏻

36 1 0
By JannatMN

*°🔘°YASMEEN°🔘°* 
    *1442H/2020M.*
   
   


®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

         '''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*🏇🏼



*NA MARUBUCIYA:-*
*JANNAT M. NASIR✍🏼*
*Wattpad_@JannatMN*

*SADAUKARWA GA:-*
*MY BLOOD SISTER*
*MARYAM M. NASIR (MANAB ƳAR BABA)*

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*
Gmail:-gakiyawritersassociation@gmail.com
Youtube Channel:- *GASKIYA 24TV.*
Facebook page:- https://www.facebook.com/Dokinkarfe2019/
Bakandamiya:-
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION.*

*RIBACI RAYUWARKA DA AYYUKAN ALKHAIRI.*

      _*•Ka k'ara zage damtse wajen ganin ka ninninka ayyukan alkhairi a wannan rayuwa ta duniya, domin ita ce kad'ai mafita ga rayuwar tabbas ta gobe alk'iyama.*_
      _*•Kasancewa cikin ayyukan alkhairi da wuraren da ake aikata alkhairi, tare kuma da aikata alkhairin gami da yi don Allah shi ne ke datar da bawa duniya da lahira.*_
      _*•Don haka kada ka rai na aikin alkhairi komi k'ank'antarsa, ribace shi ka ga ka fa'idantu da shi, sai ka samu guzuri mai tsoka da zai taimake ka ranar da zinari da azurfa ba sa amfani, sai wannan ƙyawawan ayyukan ne kad'ai za su yi amfani.*_
       _*•Allah ya ba mu ikon aikata alkhairi a dukkan tsawon rayuwar mu ta wannan duniya, ya ba mu ikon tuba daga zunubanmu, ya kuma sanya mu daga cikin bayin sa nagari.*_

_*ALLAH YA SA MU DACE. AMEEN YA ALLAH👏🏻*_


*SHAFI NA 12-13📑*

*__________📖* Zaune suke suna wasan da suka saba, ita kuma ta kura masa ido ta rasa me yasa a duk lokacin da ta kalli Abdallah take ji a ranta kamar itama tana da yaro namiji kamar sa, amma ita a iya saninta bata da wani yaro da ta haifa sama da Ayaman da Ayamana.
    
    “Hmm!” Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce, “Na fuskanci Abdallah kana so yaran nan dai su rainaka, ace kullum kana tare da su in kana gida kuma wai kana wasa da su, ya kamata fa ace ka rage wasa da su dan kasan yaro bai san wasa ba, kuma hausawa na cewa da wasa da yaro gwara kwana da yinwa.”

    Dagowa yayi ya kalleta yana murmushi yace, ”Umma da wa zan wasa in ba da ƙannena ba? Ba ni da wani ɗan uwa ko yar uwa sama da Ayaman da Aymana suma haka, kuma kin ga idan ban jasu a jikina ba wa zan ja Umma?”

  ‘’Babu, a cigaba da wasa, wai Abdallah yaushe za ku je gidan hajiya? in zaku je dan Allah ka yi min magana zan baka saƙo ka kai mata, ka ji yaron kirki?’’

    "To..! Insha Allah zan miki magana, ina jin ma muje yau tun da ba islamiya, kin ga gobe insha Allah juma’a sai na kai Aymana pack ɗin da suka ce suna son zuwa.’’

     ‘’Hmm! Ku dai bakwa taɓa gajiya da zuwaye-zuwaye wajen wasanni.’’

      ‘’Umma ai da Yaya zamu je ba….’’ Bai ƙarasa maganar da ya ke san yi ba Umma ta bige masa baki har sai da ya dan fashe ta kallesa tace, ‘’Daga yau in ana magana ba da kai ba ka ƙarasa baki, kuma na ƙara jin kana abin da ya shafi rashin kunya a bakinka.” Juyowa ta yi ta kalli Abdallah tace, “Ka da ka sake ka tafi yau da gobe da Ayman ka tafi da Aymana kawai, kuma bana buƙatar kace zaka ban haƙuri dan ba in da zai je tun da bashi da kunya.’’ Abin ka da yaro kuka sosai Ayman yake ganin jini a bakinsa, jin Umma tace ka da a tafi da shi ko ina yau da gobe yasa ya kara fashewa da kuka yana cewa, ‘’Umma dan Allah ki yi haƙuri na dai na ba zan ƙara yin rashin kunya ba wallahi.’’

       ‘’Rufe min baki! Ko na zubar da haƙoranka babu ida zaka yau kama ji na faɗa maka, maza ka tashi ka tafi ɗakinku kada ka sake na ƙara ganinka anan ƙasa, in kuma ka bari na ganka sai na faffasa maka jiki.’’ Tashi yayi yana kuka ya tafi ɗakinsu, itama tashi ta yi ta kalli Abdallah tace, "Ka biyo ni ka karbi saƙon da za ka kaiwa Hajiya.’’ Tana gama faɗin haka ta haye sama, jikinsa a sanyaye ya bi bayanta dan har cikin ransa bai ji daɗin hukuncin da Umma ta yake akan Ayman, saboda duk fitar shi yace masa yana zuwa pack da gidan Hajiya, amma ba yadda ya iya Umma ta yanke hukunci kuma tace kada ya yi magana akan haka. Karɓo saƙon ya yi ya sauko ya cewa, Aymana da ke zaune tayi shiru itama da alama bata ji daɗin hukuncin da Umma ta yanke akan ɗan uwanta, ‘’Tashi ki sako hijabinki da takalminki mu tafi ki yi sauri kin ji Aymana.’’

      ‘’To..! Yaya.’’ Tashi ta yi ta nufi ɗakinsu dan dauƙo hijibinta da takalminta, tana shiga ɗakin ta tarar da shi sai kuka yake yi.

  ‘’Ayman ka yi haƙuri ka dai na kuka ka ji.’’

    ‘’Umma tace ba zan je gidan Hajiya da pack ba, kuma ina san zuwa Aymana dan Allah ki bawa Umma haƙuri na dai na  wallahi.’’

      ‘’Duk laifinka ne Ayman kullum sai an ja maka kunne akan wannan rashin kunyar ta ka, amma baka ji ga shi nan yau kana ji kana gani Umma ta hanaka fita.’’

     ‘’Dan Allah Yaya ka ba Umma haƙuri.’’

    ‘’To..! Ayman zan ba ta hakuri, amma kasan yau dai ba zata barka ka fita ba, saboda ka ɓata mata rai da yawa tana fushi da kai, ka yi hakuri insha Allah gobe zata bari a tafi da kai.’’

    ‘’To..! Yaya Allah ya kaimu na hakura.’’

      ‘’Mun tafi sai mun dawo.’’

      ‘’A dawo lafiya.’’

      ‘’Ameen Ya Allah.’’

      Fita suka yi su bar gidan, shi kuma ai Ayman ya cigaba da zaman ɗaki, kamar yadda Umma ta umarcesa da yayi.

            _*••••••••••*_
  

    Shirye-shirye dai ya kan kama a gidan Daddy, dan Safra, Safna da Fadwa su kamala jarawarsu, haka ma angwaye suma sun zage sai shirye-shirye su ke, haka ma amaren sun sha gyara na gaban kwatance, domin bikin sati biyu ya rage a sha shagali, a gidan Daddy  kam ba a managa, invitation babu inda bai zaga a ciki dangi da abokan arziki ba. Daddy da kansa ya haɗowa yaran nasa lefe saboda yace baya so kowa ya yayi wani abu da kansa, in dai ya shafi bikin, komai ake bukata ayi masa managa komai ƙanƙantarsa bai yarjewa kowa yayi ba.

      Soyayya kam takankama a tsakanin masoyan, su Nabil sun kasa gano ainahin abin da ke tafiya a tsakani Yassar da Safna, saboda har yanzu ba su ga suna keɓewa su yi magana ba, kuma ko waya basa yi ballantana su ce sun shan soyayyar su a waya ne ko da basa haɗuwa, har sun fara tunanin anya suna san junan su kuwa, ko dai sun amince da wannan haɗin ne saboda farantawa Daddy rai, ganin sun kasa gane komai ne yasa suka fita a shirginsu suka daina bi ta kansu, dan sun lura muddun suka cigaba da bi ta kansu zasu iya haifar musu da ciwon kai. Su kuwa ba su san me ma yake wakana ba, harkokinsu kawai su ke yi kamar yadda suka saba, amma a cikin rayukansu dariya suke musu kawai tsabar miskilanci ne yasa ba su nuna musu sun san me suke ciki ba.

         Abinda basu sani ba shine soyayya mai karfi ce a tsakanin Yassar da Safna, kuma suna zantawa sai dai duk lokacin da zasu yi magana babu wanda ake sani, duk lokacin da zai riƙe wayasa suna tare suna shan soyayyarsu.

                  _*(•)(•)(•)(•)(•)*_
 
                                                            
       Allah ya yayi, dama bahushe na cewa ranar wanka ba a ɓoyen cibi, yau take Juma’at babbar rana, kuma a ayu take ranar daurin auren yaran Daddy, bayan saukowar sallar juma’ah jama’a suka shaida ɗaurin auren Yasar Abubakar Ishaq da Safnat Muhammad Bashir, Kabir Abubukar Ishaq da Safrat Muhammad Bashir, Nabil Muhammad Bashir da Fadwa Aliyu Bashir. Da yake Daddy ya shaida musu baya san waɗannan bidi’o’in, kawai ya yarje a yi iya mata kawai ban da maza, itama walima cewa za'a yi sai an kai amare ɗakunansu sannan za’a yi ta, haka kuwa aka yi sai da aka kai amare ɗakinsu sannan aka yi walima, da yake gidajensu uku a jere suke da juna, get ɗaya ne gida ne kowa da nasa amma a cikin juna su ke, shiyasa ma da aka zo gudanar da walimar ta yi armashi kowa ya ji daɗin haka.

     Bayan sati biyu da bikin su Yassar Daddy ya kira su yace yana nemansu, suka amsa masa da ga su nan zuwa, ko awa ɗaya bai yi da kiransu ba sai gasu sun hallara a falon gidan Daddy, gaisawa suka yi sannan ya ɗan yi gyaran murya yace, ‘’Kuyi hakuri da kiran da nayo muku, ina fatan ban takura muku ba?’’

     ‘’Eh! Daddy baka ta kura mana ba, muna fatan kiran na lafiya ne? Allah yasa ba wani abu mu ka yi ba Daddy?’’

     ‘’Hmm! Babu abinda kuka yi Yassar, kun tuna kwanakin baya da na kira ku nace ku zo ina san magana da ku? Har na shaida muku abu biyu yasa na kira ku, na gaya muku ɗaya, nace ɗaya sai nan gaba zan gaya muku shi ko?"

     Nabil ne yayi caraf da cewa, "Eh! Daddy an yi haka."

     "Yauwa! Alhamdulillah! Da baku manta ba, Abu na biyun da ban fada muku ba a lokacin nan shine, magana akan karatunku da kuka kammala yanzu, kuma nasan ko wane daga cikinku yana tsaye da k'afafunsa,  kuna da abin yi wato kuna da jari da sana'a mai k'arfi. Kuma dukanninku business kuka karanta kuma shi kuke yi yanzu, kuna da wayewar kai akan kasuwanci 100%, kunsan yadda zaku tada 50 ta koma 200 ba tare da kun sa alkush a cikin kasuwancinku ba. Haka ne yasa na yanke hukuncin baiwa kowanenku ɗaya daga cikin Companys d'in da nake da su, kuma kada ku yi zaton ɗauraku Manager zanyi, a Company da nace zan ba kowane ku a'a! Ƙyautar Allan zan baku, yanzu haka wannan takardun da kuke gani a gabana, ba kowane takaddu bane face na Company da zan ba kowanne ku, yanzu nan kowa zai saka hannu nima zansa. Sannan ga lawyer na nan  Barrister Aliyu na san kun san shi farin sani ma kuwa, shi zai zama shaida duk da komai a rubuce yake. Kowa yazo ya d'auki takarda ɗaya a cikin takardun nan...."

       Matsawa suka yi kowa yasa hannu bakinsu ɗauke da bisimillah, kowa ya ɗauki takarda ɗaya a cikin tarun takardun da suke baje a saman canter table din dake gaban Daddy.

      "Masha Allah kowa ya ɗauka kenan, abinda ya rage kusa hannu."

       "Toh..! Daddy"

      Ɗaya bayan ɗaya suka riga saka hannu a kowacce takardar da aka miƙo musu, duk wannan abin da ake babu wanda yasan wane irin Company ya samu ba da inda yake.

     Sai da suka gama gaba ɗaya saka hannun da ake buƙata su yi sannan Daddy ya ce,

       "Alhamdulillah! Yanzu kowannenku yana da Company kuma mallakinsa, zaku yi mamaki da har yanzu ba ku san wane irin Company kowa ya samu da kuma a ina yake ba, ka da ku damu na san tashin hakalinku ka da ace zaku yi nisa da junan kuna. Toh..! Ku kwantar da hankalinku kuna tare ba zaku yi nisa da junanku ba, kowanenku Company'nsa a wannan garin yake, amma bazan sanar muku da a ina yake ba kuma wane irine sai ranar da komai ya kammala sannan zaku sani, a lokacin zan haɗa muku ƴar walima ta taya ku murna..."

          Bud'a baki sukayi da niyar za su yi magana amma ya dakatar da su ya haɗe fuska ya ce, "Kada kuce zaku yi min godiya in ba haka yanzun nan rayukanku zasu b'aci..."

         "To..! A yi mana afuwa Daddy insha Allah baza muyi maka godiya ba."

     "Yauwa Allah yayi muku albarka."

             "Ameen ya Allah."

    "Za ku iya tafiya, sai kun ƙara jina in komai ya kammala."

      "To..! Daddy sai anjima, mun barka lafiya."

      Tashi suka yi zasu fita yace, "Ku gaishe min da ƴaƴan nawa."

         "Za su ji inasha Allah."
   
       Suna gama faɗin haka suka fice a farkon suka nufi cikin gida, gaida Momy sannan suka koma gidajensu.
   
   
   
                     _*<<<<<~•~>>>>>*_

        Sanɗa take a hankali dan kada a ji motsinta a hanata fita, har taje ƙofar fita ta ji an daka mata tsawa, "Keee! Ina zaki haka tun da sassafe nan?"

     Inda-inda ta shiga yi abinka da yarinya gaba ɗaya ta birkice, hakan da tayi ya ƙara fusatashi ya taho da niyar rufeta da duka, sai tayi caraf ta ce, "Yaya Adam ledoji zan samo, domin haɗawa Mama wutar ɗaura sanwar safe."
   
     "Shine kuma kina ji ina tambayar ki kika yi min banza, Allah ya taimakeki aiki zaki wa Mama da yau naci ubanki, kan shirun da kika yi min da na tambayeki."
   
     "Ka yi haƙuri Yaya Adam bazan ƙara ba."
   
       "Kima ƙara jikinki ne zai gaya miki, ke wallahi ma bazan haƙura ba jeki dawo yau babu mai raba ni da ke a gidan nan, tunda na lura kin rainani ko? dan kin ga ina ɗan ɗaga miki ƙafa ba kamar Mama da Jafar ba, shiyasa kika rainani ko? To wallahi daga yau kin shiga uku, in dai kika bari na yi ido biyu da ke ko kin min laifi, ko baki min ba saina ci uwarki na tattakaki, wannan alƙawari na ɗauka ni Adamu mai hannun ɓera."
   
     Ya ƙarashe maganar yana mata dariyar mugunta, sannan ya ƙara daka mata tsawa da cewa, "Keee! Uban me kika tsaya jira ne? Ba zaki sauri ki je ki dawo ba na kwashi ladana ba."
   
     Jikinta na rawa ta fito a gidan bata ce masa komai ba, saboda ta san ko tace da shi wani abu ba ƙarawa kanta wahala za tayi.
   
     Inda ya gaya mata yace ta zo ta same shi, a nan zai riƙa koya mata yadda zata zana jarabawa, nan ta je kuma ta samesa zaune a saman tabarma yana jiranta, da sallama ta ƙasa wajensa, fuskarta ɗauke da murmushi tace, "Yaya Ahmad ina kwana?" Shima murmushi ya yi mata yace, "Lafiya ƙalau ƙanwata, fatan kin tashi cikin ƙoshin lafiya?"
   
      "Alhamdulillah! Yaya Ahmad lafiya ƙalau na tashi kamar yadda kai ma kake." Ta ƙarashe maganar tana dariya, shi ma dariyar yayi sannan yace, "Ƙanwata mun hanzarta yin abin da za mu yi, dan kada ki daɗe sosai Mama ta dakeki."

        "To..! Yaya Ahmad mu fara ni dai a shirye nake."

        "Hmm!" Murmusawa ya ɗanyi sannan ya zaro littafi ɗaya a cikin jerin littattafan da ke gefansa ya miƙa mata ta karɓa, nan ya shiga nuna mata yadda zata yi da cike wajen suna da yadda ake zaɓar amsa duk ya nuna mata, duk abinda ya nuna mata kamar na'ura mai ƙwaƙwalwa haka take dire shi cikin kanta. Agogon dake maƙale a hannusa ya duba ya ce,
      "Ƙanwata tashi ki tafi takwas saura minti sha biyar yanzu, kuma kin ga takwas Mama take fitowa ɗaura sanwa, kada ta fito ta ga baki haɗa mata wuta ta dake ki."

         "To..! Yaya Ahmad na tafi sai anjima, idan na zo ƙarin Alkur'ani."

          "To..! Ƙanwata Allah ya kaimu anjimar da rai da lafiya sai kin zo."

        "Ameen Ya Allah Yaya Ahmad ɗina."

        Fara'arsa ce ta  faɗaɗa ya kumshe ido, dan har cikin ransa ya ji wannan sunan da ta kirasa da shi, bai san lokacin da ta tafi ba sai dai ya ɗago ya buɗe ido ya ga ta wajen har ta ɗan yi nisa. Cikin sauri-sauri da gudu-gudu ya biyo bayanta yana ƙwalla mata kira, hannusa ɗauke da wata leda baƙa, jiyuwa tayi ta ga mai kiranta tsayawa tayi tana mamaki me yasa ya biyota. Ƙarasowa yayi wajenta yace, "Ƙanwata kin manta da wani abu mai mahimmanci."
  
      "Ni kuma Yaya Ahmad me na manta?"
   
      Murmushi ya yi ya miƙo mata ledar da ke hannusa ya ce, "Gashi."
   
         "Yaya Ahmad menene wannan?"
   
              "Buɗe ki gani."
   
         Buɗewa tayi taga tarin ledoji ne a ciki, cikin mamaki ta ɗago zata yi magana ya ce, "Ba sai kin ce komai ba ƙanwata je ki."
   
        Juyawa tayi ta cigaba da tafiyar ta har ta ƙulle masa da gani bai bar kallan hanyar da tafi ba. "Hmm!" Wata sanyayiyar ajiyar zuciya ya sauke, sannan shima ya juya ya koma ida suka zauna suka yi karatu.
   
   
   
             _*(•)(•)(•)(•)(•)*_

   
           Allah ya taimake ta tayi sa'a Mama bata tashi daga barci ba, Adam ma ya koma ɗakinsu ci gaba da sana'ar da suka saba (wato barci).
    
   
          Haɗa wutar ta shiga yi, ba ta ɗau wani lokaci ba wutar ta haɗu, ta ɗauko ƙatuwar tukunyar nan da take rinjayarta ta daura kan murhun, ta shiga zuba mata ruwan dama ƙoƙon. Tana gamawa ta haɗo kayan wanke-wanke ta shiga wake su har ta gama ta kai kwanukan madafa Mama bata fito ba, sai da ta kusan gama sharara tsakar gidan sannan ta fito, gaishe ta ta shiga yi ko bi ta kanta bata yi ba ta nufi madafa, ta ɗan yi mamaki ganin Yasmeen ta gama haɗa komai kawai ita take jira ta fito ta dama dan har ruwan ya tafasa, damawa ta shiga yi sannan ta mai da ɗumamem tuwa.
   
          Ta gama komai ta kasa ta kira Yasmeen ta kaiwa yayyanta kamar yadda ta saba, haka ta ɗauka jikin ta na rawa ta nufi ɗakin su Jafar, Allah ya taimake ta basu farka ba, har ta fito a ɗakin tazo ta dauki nata kason ta nufi ɗakinta ta faraci abinta hankalin kwance.

           Bayan ta gaba ci ta fitar da kwanukan da aka yi amfani da su ta dawo ta zauna, barci ne ya yi gaba da ita sakamonkon gajiyar da ta yi nayin aikin da ya fi ƙarfinta.
    
          Shigowa yayi dakin hannunsa riƙe da wani katon reshe mai kauri, yana ƙasowa ida take ya ɗauki hannu ya ɗauke ta da wani gigitaccen mari, farkawa ta yi a gigice ta rasa inda zata sa kanta dan marin ta ji shi sosai, kafin ta dawo hayyacinta daga marin da yayi mata wanda yafi ƙarfinta, ya ɗauka wannan reshen bulala mai kauri ya ringa lafta masa shi a jiki, ihu ta ke da neman ɗauki, amma babu wanda ya zo dan cetonta tun tana iya buɗe baki ta yi ihun har ta kasa, shi kuma bai fasa dukanta ba sai dan kasa sannan ya ƙyaleta, shima ba dan Allah ba sai ɗan reshen da yake dukanta da shi ya karkarye shiyasa ya rabu da ita, yashe kamar matacciyaya duk ya fasa mata jiki, abinka da farar fata tuni dukan ilahirin jikinta ya yi jajir ya kunkunbura, ya fita yana faɗin, "Dan ubanki daga yau kya ƙara raina ni, kuma wallahi ko anjima na ganki in dai kika bari muka haɗa ido da ke saina ƙara cin ubanki, shekiya ƴar iska kawai."

         Yana fita yaci karo da su Mama, Jafar da kuma Jummai tsaye a bakin kofa sai dariya suke, Jummai ce tace, "Sannun yaron kirki kasha aiki zauna ka ɗan huta kaji." Kujerar da Mama ta kawo mata ta zaune da ta zo ta miƙa masa, karɓar yayi ya zauna ita kuma Mama fifita ta rinƙa masa Jafar kuma ruwa mai sanyi ya ɗebo masa a randa duk wai dan ya sauke gajiyar da ya kwaso a wajen dukan Yasmeen a cewarsu.

          Ita kuwa baiwar Allah tana kwance in da ya barta ko yatsa bata iya motsawa, tsabar ta daku ƙwalla ce kawai ke fita a idonta da ya yi jajir, tana motsa bakinta da kyar tana kiran, "Yayana! Yayana! Yayana!"

      Su kuwa suna ta hirar su hankali kwance, sai da su Jafar suka bar gidan sannan Jummai take cewa, "Ƙawata albishirin ki." Tace, "Goro." Ta kuma ce mata, "Ja ko baki?"
   
      "Hhhh! Kai Jummai baki da kirki, ana fari ko ja ke kina cewa, wai ja ko baki."
   
      "To..! Maimunah abinda zan gaya miki ai ba na alkhairi bane, kin ga kuwa babu abinda zai sa mu alkantashi da fari."
   
       "Haka ne kam Ƙawalli, to ni wane ma zan zaɓa?"
   
       "Hhhh! Kawai kice baƙiƙirin dan shi yafi dacewa da abinda nake tafe da shi."
   
      "To..! Jummaita baƙiƙirin."
   
      "Yauwa! Ko kefa to kawo kunnanki ki ji."
   
       Miƙa mata kunne ta yi ta raɗa mata abinda ke tafe da shi, ta ɗan razana kaɗan da jin abinda Jummai ke tafe da shi daga baya kuma suka kwashe da dariya har da tafawa. Gaɓar zaninta ta kama ta kwace ta fito da wani baƙin ƙullin abu ta kama hannunta ta saka mata tace, "To..! Ki kula sosai kada a samu matsala fa, dan wallahi aka samu wata matsala ni da ke mun shiga uku ɗan kanmu abin zai juya ko kan zuri'armu."
   
       Dariya ta dan yi sannan tace, "Ke Jummai wallahi kamar baki san wacece Maimunah bala'i ba."
   
       "Ni kuwa nasan ko wacece Maimunah  bala'i, na san wannan ƙaramin aiki ne a wajenki, amma duk da haka ki kula kin san masu iya magana na cewa riga-kafi yafi maganin."
   
      "Hakane kama to zan kiyaye karki damu akan haka."
    
       Haka suka cigaba da firarsu wanda ba komai bane a ciki sai tsabar haɗa hatsabibinci ne da mugunta. Sai da aka kira azahar sannan suka yi sallama ta tafi gidanta, da ƙara jaddada mata da ta kula kuma ta aikata duk abinda ta ce mata.
   
       Cikin ɗakin tayi ta shiga tace, "Ayyah! Sannu Yasmeen, ke kuwa me kika yiwa Adamu yayi miki haka? Gaskiya bai kyauta ba irin wannan duka haka kamar ya samu wata dabba, ki yi haƙuri kin ji.
   
       Ita dai Yasmeen kallanta take, tana nan a inda Adam ya tafi ya barta, dan har a lokacin bata iya motsa ko yatsanta, amma kuma a cikin ranta tana mamakin canjawar Mama lokacin ɗaya, dan tana jin firarsu ita da Baba Jummai ko da bata ji komai suke ƙullawa ba, amma ta san da walakin goro a miya duk da yarintar dake tattare da ita ta gane da akwai abinda ake shirin ƙullamata.
   
   
        Kamata tayi ta miƙar da ita tana mata sannu da kanta ta dafa ruwan zafi ta gasa mata jiki, sannan ta samo mintileta ta shafa mata a duk inda ya kunbura. Ta je ɗakinta ta ɗauko mata filo da ƙaramar katifarta ta kwantar da ita a ƙasa har wannan lokacin sannu take mata, tun Mama na bata mamaki har ta fara bata tsoro. Lura da tayi kallan da Yasmeen ke mata ne yasa ta ɗan yi murmushi tabce, "Ki daina mamaki ƴata na yi nadama da dana sani abubuwan da nayi miki, ki yi haƙuri ki yafe min in Allah ya yarda ba zan ƙara cutar da ke ba, kuma ba zan ƙara barin wani ya taɓaki ba."
   
        Abinka da yarinya ƙarama, har cikin ranta ta yarda da abinda Mama tace mata, ta saki jikinta da Mama.

       Sai da Yasmeen ta yi sati guda a kwance tana jinya, kuma Mama bata bar Yasmeen ta yi wani abu ba ta hanata fita, kullum tana kwance tana kula da ita a cewarta, tun su Jafar na masifa akan abinda take yi wa Yasmeen, har suka daina da kanta ta sake su ta shaida musu shirinta akan Yasmeen shiyasa duk take yi mata wannan abubuwa, sun ji daɗi da jin abinda Mama tace, sannan suka taya ta kyautatawa Yasmeen, ita kuwa ta yarda da su akan canzawar da ta yi shiyasa ta saki jikinta da su.
   
       Kullum Ahmad yana hanyar gidansu dan ya ji lafiya ya ji Yasmeen ɗinsa kusan sati ba ita ba labarinta, amma in yazo sai ace masa tana lafiya ƙalau kai tana ɗan fama da zazzaɓi ne shiyasa baya ganin, haka zai juya ba dan ya yarda ba ya koma inda ya fito jiki a sanyaye.

   
   
                 _*(•)(•)(•)(•)(•)*_

   
           Wannan karan yasha alwashin sai ya ganta, haka ya shirya tsafa ya nufi gidan su ƙanwarsa, tun akan hanyar zuwa gidan su yaji gabansa na faɗu, ambata Allah ya ringa yi har ya shawo kwanar gidan, dai-dai waje zuciyarsa ta shiga bugawa da ƙarfi gabansa ya cigaba da faɗuwa, zuciyarsa ce ta shiga raya masa, _Anya zuwanka gidanan alheri ne kuwa Ahmad? ka koma kawai kazo wani lokacin._ wani bari na zuciyarsa kuma ya shiga raya masa, _Insha Allah babu abinda zai faru, ka tafi kawai ka ga ya lafiyar amanar da aka bar maka take._ Da shawatar zuciyarsa ta biyu ya ɗauka ya cigaba da tafiya, yana ta ambatan Allah a cikin ransa har ya ƙarasa kofar gidan yayi sallah.
   
            "Assalamu Alaykum."
   
             Kamar jiransa suke yi, suka yi caraf suka amsa masa suna masa murmushin da ya kasa fassara shi, ya ɗan yi mamakin ganin haka, amma sai ya basar ya gaishe da ita, amasa masa ta yi cikin sakin fuska har da tambayarsa ya mutan gidan kamar gaske.
   
              A nan yake tambayar Ƙanwarsa suka ce masa tana ciki kwance ya shiga ya dubata, dan ba ta jin daɗi, tashi yayi ya nufin ɗakin ta da yake gidan ba baƙo bane a wajensa, yana kama labulen zai shiga, ya ji gabansa da zuciyarsa sun buga da karfi, ba shiri ya saki labulan yana ambatan Allah a cikin ransa.
   
              "Lafiya dai Ahmadu naga ka tsaya?"
   
                "A'a! Bakomai Mama."

           Da sallama ya shiga cikin ɗakin, kwance take ta ba ƙofar baya, tana jin muryarsa ta juyo da sauri ta tashi tayi kansa tana, "Oyoyo! Yaya Ahmad ɗina, nayi kewarka sosai." Shima rungumeta yayi na ɗan wasu sakanni, sannan ya janye ta daga jinsa ya tsuguna a gabanta, suna haɗa ido da ita, ya ji wani irin abu tun daga kansa har zuwa ƙafarsa, wutar kansa ta ɗauke duf ya ringa ganin duhu a cikin idanuwansa, tun daga wannan lokacin bai ƙara sanin inda kansa yake ba sai ji yayi ana dukansa da itatuwa ta ko ina, shiga kare kansa ya ringa yi yana neman tseratar da kansa, Yasmeen ce ta faɗo masa a cikin rai tunawa da yayi suna tare da ita a ɗakin, a ransa yace _Ina Yasmeen take? Me yake faruwane? Me nayiwa su Adam suke dukana haka?_ duk wannan tambayoyin ya kasa ba kansa amsoshin su.
   
        Juyawar da zai yi idanuwansa suka sauka akan Yasmeen dake kwace cikin jini, tana fitar da numfashi sama-sama, kanta yayi a ruɗe da nufin ya je ya taimaka mata, yana faɗin, "Yasmeen!!! Meya sameki? Meke faruwa dake? Wayyoo Allah ƙanwata meta sameki?"
   
       Har ya kusa ƙarasawa wajenta suka jawoshi suna cigaba da dukansa, da yi masa munanan kalaman da ya ji dama ace shi kurma ne, da bai ji wannan munanan kalaman da yake ji suna shirin tarwatsa masa zuciya.
   
         "Kaiii! Har ka isa ka shigo har cikin gidan mu ka ketawa ƙanwar mu hadi, wallahi yau sai dai uwarka ta haifi wani ba zaka fita a gidan a raye ba."
   
         Dukansa kawai suke yi har sai da suka ga ya daina motsawa, sannan suka yi masa kama-kama suka fitar dashi daga gidan, duk Mama ce ta tsara musu yadda zasu yi, yadda tace su yi haka suka aikata ba su saɓa ko ɗaya a cikin abinda tace musu.
   
        Ƙauyen kam ya ɗauka Ahmadi ya shiga har gidan Malam Habu yayiwa ƴar sa Yasmeen fyaɗe.
   
        Tun da suka fitar da Ahmad a ɗakin Yasmeen ba su ƙara waiwayar inda take ba, hassalima mazan ficewarsu suka yi ita kuma Mama ta shige ɗakinta ta kwanta.
   
        A birkice Malam Habu ya shigo gidan tun daga soron yake kiran, "Maimunah! Maimunah!! Maimunah!!!" Tana jin maryarsa ta ƙaƙalo kukan ƙarya ta fito tana faɗi, "Malam kaga abinda yarinyar nan ta jawo mana ko?"

         Kuka take kamar gaske har da hawayen, Malam na gani haka ya kuma ruɗewa yana faɗi, "Ina shegiyar yarinyar take? Ta zo ta bar min gidana, wallahi zamanta ya ƙare a gidan nan, dan ba zan taɓa zama da ƴar iska ba a cikin gidana."

          Har cikin ɗakin da Yasmeen take kwance Mama ta raka sa, bai yi duba da halin da take ciki ba ya ringa janta har ya fito da ita daga gidan, ya yasar da ita a waje, ita ko Mama ƙara tunzurasa kawai take yi, ta hanyar amfani da kauraran kalamai cikin hikima.

        Yana fito ta ita yace mata ta bar masa gida, idan ta sake ya ƙara ganinta a zagaye layinsu sai ya yankata da ranta, kama gidansa ya karkame ya barta anan waje ko tausayinta mai ji ba a matsayinta na ƴarsa, kuma gata yarinya ƙarama dudu ba ta wace shekara 11 ba a duniya, gashi gari ya fara duhu mangariba ta kawo kai, duk bai yi duba da su ba ya kulle kofar gidansa.

         Da kyar ta iya tashi tana takawa, duk daku ɗaya idan tayi sai ta kwalla ƙara da ƙwallar avzaba ta fito mata, hanyar gangare tabi ta nufi titi, in ta gaji da tafiya sai ta tsuguna tana rarrafe gwiwoyinta duk sun fashe kafin ta ƙarasa titi, sakamakon jansu da take yi, amma duk da haka ba ta sare ba har sai da ta kai bakin titi, sannan ta zube a gefen titi tana fitar da numfashi da kyar, domin duk wani ƙarfin halin da take dashi ya ƙare mata a lokacin.
    
   
              _*<•>•<•>•<•>•<•>•<•>*_

        Zaune suke suna hira shida Safna, yaji kamar ana kiransa, tashi yayi a gigice ya nufi hanyar fita, ya duba duk inda zai duba amma bai ga mai kiransa ba, tambayar duniya Safna ta yi masa, amma bai bi ta kanta ba ballantana ma ya ba ta amsa. Safa da marwa kawai yake yi a falon yana dafe kansa da ke shirin tarwatse masa, ta rasa me ke damunsa kuma yaƙi kulata ba ballantana ma ta sa ran zai gaya mata damuwar sa, waya ta ɗauko ta shiga kiransu Kabir tana gaya musu abinda ke faruwa, yana jinta yayi banza ya rabu da ita har ta gama wayar bai kulata ba.

        Ko miti biyar bata yi da kira su ba sai gasu sun shigo hankalinsu a matuƙar tashe,  tambayar duniya ba wacce ba su yi masa ba, amma yaƙi musu magana ƙarshe ma da suka takura masa, sai dai kawai suka ga kwalla na fitowa a idonsa, nan fa hankali kowa ya ƙara tashi suka rasa inda zasu sa kansu, da ya ga sun takura masa ma kawai sai ya tashi ya tafi ɗakinsa ya sa mukuli ya rufe kansa.
   
        Yana zuwa kan gado ya zauna ya tallabe kansa yana kwalla, ba kiran da ba su yi masa ba akan ya buɗe amma yaƙi kulasu, wayarsa ma in sun kira sai su ji ta a kashe. Har Daddy da Momy suka kira amma duk mai bi ta kansu ba, haka suka haƙura suka bar baki ɗakin nasa, suka koma falo suna tattaunawa kana me ya haifar masa da wannan damuwar.
   
        A nan su Nabil suka shaidawa Daddy ai tun kafin a yi bikinsu yake fama da damuwa, amma bata yi tsamarin ta yau ba. Itama Safna ba su labarin yadda yake birkice mata wasu lokutan, ta kuma gaya musu komai ya faru a yau a tsakanin su, jinjina kai kawai Daddy ya shiga yi yana wani nazari, har aka yi sallar isha suna gidan Yassar bai fito ba.
   
        Sallama su Daddy suka yi musu, suka ce indai ya fito su kira shi, suka amsa masa da to suka bar gidan.
   
         Yassar bai fito a ɗakin ba sai wajen 11:30 na dare, sannan ya buɗe ɗakin ya fito tsaf dashi kamar ba shi ba, yana zuwa ya tarar da su zaune sun yi jigum-jigum kamar masu zaman makoki.
   
         Kawai sai dai suka ji ance musu, "Kun ci abinci kuwa?"
   
        A razane suka ɗago suka na kallanshi fuskarsa ba yabo ba fallasa, Kabir ne ya iya girgiza masa kai alamar a'a! ba su ci ba ɗan murmusawa yayi yace, "Okay!" Ya dubi Safna da take kallansa tsabar mamaki ta kasa buɗe baki yace, "Please Ƙanwata a haɗo mana kwanuka cin abinci, na yi mana order abinci yanzu za'a kawo mana."
   
       Tashi ta yi jiki ba kwari, ta nufi kitchen ta haɗo kwanukan da ya buƙata ta jeresu a dining, shi kuma ya nufi waje sai gashi ya dawo ɗauke da ledoji a hannusa, har dining ya kai su ya ajesu, sannan yace musu su taso a ci abinci, da kansa ya shiga zubawa kowa sai da ya tabbatar sun ci sun kika cikinsu sannan ya kyale su, su dai kallan mamaki kawai suke masa, kuma sun kasa yi masa magana, ya lura da irin kallan da suke masa amma kawai sai ya basar da lamari.
   
       Agogon dake jikin bangon dakin suka kalla ganin sha biyu tayi har ta ɗan gota, yasa suka yi musa sallama kowa ya nufi gidansa. Suma suka je suka kwanta Safna bata yi gigin ƙara tambayarsa bashi ma bai yi mata wata magana ba. Haka ya cigaba da al'amuransa har tsawon sati ɗaya ba yabo ba fallasa, kuma babu wanda ya ƙara takura masa ba, dan su ji taka-mai-main ainahin abin da ke sa shi damuwa.
   
   
   
                _*(•)(•)(•)(•)(•)*_
   
   
       Yau take ranar walimar da Daddy ya haɗa na mallakar Company da yaransa suka yi, kuma a yau ya shaidawa kowa a idan Company nin sa yake, na Nabil da Kabir a cikin gari suke, na Yassar ne yake wajen gari shima ba waje ba can sosai, sun yi murna da farin cikin faruwar haka, inda kowa zai gudanar da shagalin walimarsa a Company nin sa tare da ma'aikatansa, duk da ba su su haka ba amma haka suka haƙura ba su musawa Daddy ba.
   
   
      Tun waje azahar Yassar da Safna suka ɗauki hanyar zuwa Company nin su domin gudanar da walimar, da yake su sai sun dan yi tafiya kaɗan shiyasa suka fice da wuri, su kuma Nabil da Kabir sai bayan la'asar suka tafi nasu Company.
   
       Shi dai tun da ya tashi yake jin gabansa na faɗuwa, kuma jikinsa yayi sanyi sai bai nunawa kowa ba, dan gudun kada ya cike gurbin farin ciki zuwa damuwa, ya ringa ambata Allah yana yake kawai, yana zuwa wucewa ta wani ɗan ƙauye tun daga nesa yake kallan ƙauye zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, haka ya wuce ƙauyen ba dan ya so ba. Sun isa Company lafiya aka gabatar da walimar da ka shirya, kowa ya kasance cikin farin ciki, amma banbda Yassar, tun yana daurewa yana yin yake har ya zamo baya iya yaƙen, ƙarshema da ya ji ba zai iya jurewa ba, yace a yi shela antashi, ya kamo hanya yayo gidan.
   
        Tun daga nesa ya fara hango alamun wani abu a gefen titi, yana matsowa zuciyarsa na bugawa gabansa na faɗuwa, yana zuwa dede wajen abu ya ji zuciyarsa ta buga da ƙarfi, da sauri ya nemi birki ya taka ya ja hanbirek motar tsaya cak! Ya fito waje, Safna na tambayarsa lafiya amma ya yi mata shiru, ganin itama zama bai kamaceta ba yasa ta biyo bayansa.
   
   
        Kwance take sai nishi take tana fitar da numfashi da kyar da kyar, bakinta ne kawai yake motsawa tana kiran Yayanta, kanta suka yi a razane muryarsa na rawa yake cewa, "Safna ƴar mutum ce wallahi." Kama kanta yayi ya ɗaura kan cinyarsa yana kallanta kwalla na bin kuncinsa, ƙwallar da ya sara ko ta mecece. Safna ce ta yi ƙarfi halin cewa "Honey mu taimaketa mu kai ta asibiti."
   
        Ɗaukar ta yayi cankasa ya nufi mota da ita, baya ya buɗe ya shiga har a lokacin yana rungume da ita kasa rabata da jikinsa, gani hakane yasa Safna shiga mazauni direba ta ja motar suka nufi a asibitin cikin gari. Har suka ne asibitin ba ta daina kiran Yayanta ba, a duk lokacin da tace, "Yayana!" Sai yaji zuciyarsa ta buga da ƙarfi.
   
      Da kanshi ya kaita har cikin asibiti gaban Dr. Ɗauke da ita a hannu Dr ne yasa nurses suka karɓeta, shima da kyar ya ba da ita, suka turata a gado sai emergency room. Tun da aka shiga da ita ya kasa zaune ya kasa tsaye.....
   

   
   
   
_*See me next page✍🏻*_
_*Share*_
_*Comment*_
_*#JannatMN*_   

 
   
  

*©JANNAT M. NASIR•*

Continue Reading

You'll Also Like

175K 1.6K 175
δ½œθ€…οΌšζ‘ι‡Œηš„ε°ε‚²ε¨‡ Chen Xiaolin accidentally bleeds on the bracelet her grandmother left her, and she discovers a space inside. She then fills the space with...
22.2K 1.6K 34
"Say it. Say you hate me. Say you want to leave. But remember-no one will ever touch you like I do. No one will ever love you the way I do" "I hate y...
199K 5.9K 98
A villainess known by all as a wicked woman who has done all sorts of evil deeds-Ducal Lady Violet. She regained her memories of her previous life af...
22.2K 1.3K 200
DISCLAIMER: I do not claim ownership over this story. I only MTLed it. Original novel: https://www.jjwxc.net/onebook.php?novelid=5287959 Although Luo...