YASMEEN.

Por JannatMN

1.2K 63 13

Labari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin... Más

Page 1 ✍🏻
Page 2✍️
Page 3✍️
Page 4&5✍🏻
Page 6&7✍🏻
Page 8&9✍🏻
Page 12&13✍🏻
Page 14&15✍🏻
Page 16&17✍🏻
Page 18&19✍🏻
Page 20&21✍🏻
Page 22&23✍🏻
Page 24&25✍🏻
Page 26&27✍🏻
Page 27&28✍🏻
Page 29-30✍🏼
Page 31-32✍🏼

Page 10&11✍🏻

105 5 0
Por JannatMN

YASMEEN.



*_Story & writing_*
*_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_*

*Wattpad_@Realtakowa*

*_Dedicated to my sister_*

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_


_*01 March , 2020😍*_

_*RIBACI RAYUWARKA DA AYYUKAN ALKHAIRI*_

_*•Ka k'ara zage damtse wajen ganin ka ninninka ayyukan alkhairi a wannan rayuwa ta duniya, domin itace kad'ai mafita ga rayuwar tabbas ta gobe alk'iyama.*_

_*•Kasancewa cikin ayyukan alkhairi da wuraren da ake aikata alkhairi, tare kuma da aikata alkhairin gami da yi don Allah shine ke datar da bawa duniya da lahira.*_

_*•Don haka kada ka raina aikin alkhairi komi k'ank'antarsa ribace shi kaga ka fa'idantu da shi, sai ka samu guzuri mai tsoka da zai taimake ka ranar da zinari da azurfa ba sa anfani, sai wannan kyawawan ayyukan ne kad'ai zasu yi anfani.*_

_*•Allah ya ba mu ikon aikata alkhairi a dukkan tsawon rayuwar mu ta wannan duniya, ya ba mu ikon tuba daga zunubanmu, ya kuma sanya mu daga cikin bayin sa nagari.*_

*ALLAH YASA MU DACE. AMEEN YA ALLA👏🏻*

_*Page 10&11✍*_

_________Bud'a baki sukayi da niyar zasuyi magana amma ya dagatar dasu ya hade fuska yace,

"Kada kuce zaku yi min godiya inba haka yanzun nan rayukanku zasu b'aci......"

"Toh..! Ayi mana afuwa Dady insha Allah bazamuyi maka godiya ba"

"Yauwa Allah yayi muku albarka"

"Ameen ya Allah"

"Abu na biyu da zan fad'a muku shine, yanzu nasan kun mallaki hankalin kanku kunsan maike muku ciwo da kuma abinda ya kamata, dan haka nake so nan da wani lokaci kuma ku aje naku iyalan, nima naga 'yan jikina.........."

Murmushi suka yi gaba d'ayansu harda shi daddyn Nabil ne yace,

"Insha Allah daddy sai ma ka aurar da su bama ganinsu ba."

Wannan karon dariya daddy yayi saboda maganar Nabil ta bashi dariya, suma su Yassar sai da suka dara.

"Allah yasa to, amma ni ai bani da matsala da Kabir da Yassar, saboda su ina so na had'asu da k'annensu, amma bazan takura muku ba in kuna da wad'anda kuke so sai ku fad'amin."

Batare da wata gardama ba suka nuna amincewarsu akan zancen cikin farin ciki, gaba d'aya sunyi farin ciki da wannan had'in da daddy yake so yayi.

"Gaskiya nayi farin ciki da amincewarku, insha Allah su Safrat da Safnat suna kammala karatu sai ayi auran, kai kuma Nabil sai je ka dai daita da Fadwa 'yar wajen gwaggonka."

Shima amsawa yayi cikin fari cikin da girmamawa ya amince da had'inshi da Fadwa 'yar gidan gwaggonsa.

Abinda Dady bai sani ba shine, tun Nabil na secondary school a lokacin tana yarinya yake san Fadwa,

Amma bai tab'amin nunawa ba koda da wasane, ya binne san da yake mata a cikin zuciyashi, yanzu da yaji Dadyn shi ya zama mishi ita a matsyi matar aurenѕa har akace yaje su daidaita,

Sai yaji yafi kowa farin ciki da wannan had'i, duk da yasan cewa suma su Yassar suna soyayya dasu Safnat a boye, amma basu san ya sani ba.

Dan bazai tab'a mantawa da rananan da ya d'auki phone d'in Kabeer zai yi wani abu da ita, yaga sak'on da ya turawa Safrat itama ta turo masa wanda yake bayyana tsantsar so da suke wa juna su.

Tsakani Yassar da Safnat ne har yanzu baida tambacin akansu, dan duk yadda zaiyi ya gane meye a tsakanisu ya kasa ganewa, dan kusan halin Yassar da Safnat d'ayane minskilayen kansune na bugawa a jarida ma kuwa.

"Insha Allah nan da 2months za'ayi bikin naku, tunda nan da 1month nasan su Safnat sun kamala jarabawarsu, mu dai kunga a shirye muke sadai ko bansan ku ba, in kuna gani yayi kusa sai kuyi magana a d'aga bikin zuwa sanda kukeso......"

Sai sannan ya bud'a baki da niyar yayi magana wanda tun zuwansu tunda suka gaisa bai k'ara cewa ta tafasa ba,

"Mai halidai baya fasa halinsa" a cewar Nabil ya fad'a murya k'asa k'asa mai kama da rada,

Shiko murmushi kawai yayi yace

"Dady 2months d'in ma da kuka saka yayi mana, basai an k'ara ba muma a shirye muke. Abinda kawai zamuce shine Allah ya tabbatar mana na mafificin alheri a cikin wannan lamari, Allah ya kore duk wani sharri da abu marar kyau a cikinsa, ya kuma karo mana duk wani alherin dake cikinsa. Mu kuma Allah ya bamu ikon zama mazaje nagari masu adalci ga matayenmu."

Kusan a tare suka had'a baki wajen fad'in.

"Ameen ya Allah"

Wani irin k'asaitaccen murmushi yayi acikin ransa yake k'ara yaba halin Yassar domin yarone mai hankali da bazak'a a duk abinda yasa a gaba, ga sani yakamata, ilimi, tarbiyya da girmama na sama dashi ko da kuwa bai san mutum ba indai ka girmemishi sai ya baka girmanka.

Shi babu ruwansa kuma gashi baida 'kyashin yiwa wani abu komai tsadarѕa kuwa indai ka tunkareshi, in kaga bai yi maka abu ba tofah sai dai idan Allah bai riga da ya k'addaro zaiyi maka abun ba.......

"Gaskiya nayi matukar farin cikin da dukkan ninku kukarb'i zab'in danayi muku hannu bibbiyu, batare da d'aya daga cikinku ya nuna rashin amincewarsa koda akan fuskarsa ne. Gaskiya naji dad'i haka Allah yayi muku albarka, Allah shige mana gaba. Zaku iya tafiya dama neman danaye muku kenan"

"Ameen ya Allah"

"Toh..!" tashi sukayi "mun barka lafiya Daddy"

Fita sukayi kowane da abinda yake sak'awa a cikin ransa, da ka gansu zaka gane suna cikin farin ciki dan fuskar kowanen su d'auke take da murmushi, amma banda gogan naku duk da bai had'e ransa yayi ba, amma kuma bai saki ransa ba saifa saifa dai.

Ko da suka koma part d'insu babu abinda suke yi sai firar yadda bikin nasu zai kawance cikin happy, kallon bakinsu sai kace yana kallon TV, lura da suka yi ne yasa suka dakata da abinda suke yi, Nabil ne ya dafa kafad'arsa cikin yanayi da yake nuna tsantsar damuwa yace

"Dude mai ya faru ne?"

Murmushin ya'ke ya 'kwa'kwalo dan ganin yadda jikinsu yayi sanyi, suka kuma shiga cikin damuwa yace

"Babu abinda ya faru, mai kuka gani ne?"

Kallon juna Nabil da Kabir suka yi, dan tambayar rainin hankalin da ya jefo musu, Kabir ne yace

"Komai ma mun gani, tunda kana cikin damuwa ka'ki ka gaya mana."

"Damuwa.! A irin wannan lokacin??"

Yace da su tare da tashi yabar musu parlor d'in gaba d'aya, bedroom d'insa ya shiga, kwanciya yayi bed ya d'aura sana'arsa daga inda ya tsaya.

★★★★★★★★★★

Rayuwa tana tafiyar wa Yasmeen yadda kowa ya sani, babu cigaba da ta samu in ba na ba'kar izaya da wahalar da take sha a wajen Mama ba.

Tashi tayi tunda sassafe ta fara had'a kayan wanke² tayi, ta share gidan ta gyarashi tsaf kamar wata babba ce tayi aikin, sannan ta fara shirin tafiya tahfiz ta gama shirinta tsaf ta fito lokacin garin ya gama wayewa rana ma ta fito.

Takar gida ta fito lokacin Mama ta tashi har ta gama dama koko da d'umamen tuwo tsugun nawa tayi tace,

"Mama ina kwana?"

"lafiya"

"An tashi lafiya?"

"Da ban tashi lafiya ba ai da bazaki ganin a haka ba, munafuka wani sabon salon munafinci kika fito dashi kenan, to bari kiji duk abinda zaki fito dashi bazai sa na canza ra'ayina akanki ba. Bari kiji ma ki fara shirin barin gidan nan na kusa ba da jimawa ba, d'an ko kinaso ko ba'kyaso sai kin barsa wannan alk'awari na d'aukarwa kaina."

"Toh! Mama Allah ya kaimu lokacin"

"Hhh! Yooo ko baki amsa ba ai sai kin barshi"

Tashi tayi tace,

"Na tafi makaranta"

"Kin dai tafi yawan iskanci zakice bakin tafi makaranta ba, baki wanke kayan da nayi amfani dasu ba zakice wani zaki tafi, to jeki na gani d'in."

Tsugunawa tayi ta d'auki kayan da ta b'ata ta tafi ta fara wakenwa ta gama tsaf ta gyara inda ta b'ata.

"Mama na gama na tafi"

"Ke zo nan, shi wannan sai nace ki d'auka ki kaiwa Jafar da Adam ko? Sannan zaki d'auka, wai me yasa ke 'kwa'kwalwarki ta kifice kullum kina abu amma kin kasa rik'ewa."

D'auka tayi ta nufi d'akinsu Jafar

"Assalamu Alikum"

Shiru babu wanda ya amsa mata, dama da san za'arin dan kullum haka suke mata. Shiga tayi ciki ta aje a inda ta saba ajewa juyawa tayi zata fita......

"keeee"

Jiyuwa a d'an razane "Yaya Adam ina kwana?"

"Lafiya, maza ki d'auko tsintsiya ki share d'akin nan tas"

"Yaya Adam makaranta zan tafi na kusa makara inna dawo zan share insha Allah"

"Keee ni zaki yiwa rashin kunya, to kada Allah ya baki ikon sharewa yanzu, ga hanya nan ki fita a gidan na gani."

Fita tayi taje ta d'auko tsitsiya ta fara shara da sauri² takeyi ta gama, 'kwashewa tayi taje ta zubar da dattin a abin zuba shara.

"Na tafi makaranta Mama"

"Kindai tafi yawon iskanci"

Bata ce komai ba ta fita daga gidan tafiya take cikin nutsuwa, amma tunani take hawayene suka fara bin kuncinta bud'ar baki tayi tana cewa,

"Shin yanzu idan Mama ta koreni ina zani, bani da kowa sai Yayana da Ummata kuma yanzu suma ban san inda suke ba. Ya Allah ka bayyana min Yayana da Ummata, kona samu rangwame a wajen Mama."

"Ameen ya Allah K'anwata"

"Yaya Ahmad kaine ina kwana?"

"Lafiya lau K'anwata, kin tashi lafiya?"

"Lafiya k'alau Yaya Ahmad"

"Tun daga 'kwanar Baba Lami mai k'osai na hangoki kin taho nayita kiranki, amma shiru ko kallon kinda nake ba bakiyi ba, jikina ya bani ba lafiya ba shine na taso na biyoki naji lafiya meke faruwa."

"Hmm!" Yalwata murmushin ta tayi wanda yake k'ara bayyana kyawunta, dimful d'inta dukka biyun suka bayyana. Dum² gabansa ya fad'i takiyanke yaji bugun zuciyarsa ya k'ara k'arfi.

"Innalilahi ya ilaihi alamin, K'anwata me yasa? Da kinsan yadda wannan murmushin naki yake tarwatsa zuciyata da bazaki k'ara yinsa ba mundun muna tare"

Duk a cikin zuciya yake wannan magan........

"Kayi hak'ura Yaya Ahmad wallahi banji kira... "

"Bakomai K'anwata ai nasan baki ji ba, yanzu dai kin karya ne kika fito?"

"Aa! Ban karya ba"

"Me yasa?"

Shiru tayi bata ce masa komai ba, girgiza kansa yayi yace,

"Zo muje.... "

"Toh!"

Bayansa tabi, wajen Baba Lami mai k'osai yaje yace

"Baba bani k'osai na 100 amma a leda zaki saka min."

"To Ahmadu."

Kamar yadda yace haka Baba Lami tayi, a leda ta zuba k'osan ta basa, kar'ba yayi ya mik'awa Yasmeen yace

"Ga wannan k'anwata in kinje makarantar sai ki ci."

Godiya sosai tayi masa, ya nuna mata cewa ai babu komai ita d'in k'anwarsa ce.

Tafiya take amma gabanta in banda luguda babu abinda yake yi, saboda tasan makarar yau tafi ta kullum, addu'arta d'aya ita Allah yasa Mal.Rabi'u baya nan, dan tasan suka had'u da shi toh sai dai buzunta.

Hankalinta ne yayi mugun tashi, yawun bakinta ya 'kafe 'kaf, idanunta suka fara ganin duhu, kunnenta ya toshe dimmmm, k'afafunta suka yi nauyi ta yadda har suka fara barazanar kayar da ita.

Ba komai ne ya janyo haka ba illar ganin Mal.Rabi'u da tayi a bakin k'ofar makaranta, fuskarsa babu alamun rahma ballantana sassauci, yana binta da wani matsiyacin kallo mai tattare da tsana tare da 'kyama.

Da Yasmeen tasan abinda zai faru a wannan ranar da batayi gigin zuwa ba, domin a ranar rashin imanin Mal.Rabi'u ya fito fili, domin dokan da yayi mata yayi yawa wanda yasa har sai da jini ya ri'ka zuwa, ya 'bata mata kod'ad'd'an hijab d'inta.

Tara mata yara 'yan uwanta wadan da ta girma dama wadanta suka girmeta, suka ringa yi mata ihuu dariya da kuma gwalo. Yaci mata mutunci sosai a k'arshe kuma ya koreta daga makarantarsa, kora irin ta kare mai tattare da wulakanci.

Tafiya take tana kuka dan wannan karan iya kacin k'arfinta take kukan, tun daga nesa ya hangota da gudu ya taho gareta, hankalisa in yayi d'ubu ya tashi, taki yanke yanayinsa ya canza, kwallace ta fito a cikin idonsa tsabar bak'in cikin abinda ya ga anyiwa Yasmeen d'insa.

"Ya.. Ya.. Yasmeen k'anwata wanene yayi miki haka?"

Cikin fushi yake tambayarta, amma bata bashi amsa ba kuma batayi shiru ba kukanta kawai takeyi, ai ko hakan ya k'ara dugun zuma zuciyarsa idanunsa suka k'ara kad'awa sukayi jajir.

Jikinsa ta fad'a ta cigaba da kukan da takeyi rungumeta yayi ya fara bubuga mata bayanta, ya d'au lokaci yana mata haka sannan tayi shiru ta fara sauke a jiyar zuciya, sai a lokacin yaji hankalisa ya fara kwanciya da yaji tayi shiru ta dai na kukan.

"Yi hak'uri kinji k'anwata, gaya min wanene yayi miki haka kinji."

Janye jikinta tayi a nasa ta fara bashi labarin abinda ya faru a makarantarsu, ranshine ya k'ara baci yaji gaba d'aya ya rasa inda zai saka kansa, kama hannunta yayi ya fara tafiya ganin makarantarsu ya nufa yasa tace,

"Yaya Ahmad kada muje mu barshi da Allah kawai, indai makaranta ce ni na hak'ura bazan k'ara zuwa ba, kuma kaga ya koreni ai shikenan."

Shiru yayi ya tsaya yana kallonta yarinya k'arama da ita, sai sanin ya kamata da hankali tunani da hak'uri.

"Toh! K'anwata mun barshi da Allah, Allah ya saka miki ya kuma bi miki hakk'inki"

"Ameen ya Allah"

"Yanzu dai kada ki gayawa kowa an koreki a makaranta, kinga sai na cigaba da koya miki da kaina kuma a nutse, kinga har lesson d'in exam d'in da zaku fara, sai muyi ko?"

"Eh! Hakane insha Allah bazan gayawa kowa ba"

"Yauwa k'anwata Allah yayi miki albarka"

"Ameen ya Allah"

"Zo muje gidan mu"

"Toh!"

Tafiya suke yana janta da hira har suka isa gidan.

"Salamu Alaikum! Gafaranku dai masu gidan sunana kuwa"

"Eh! Sunanan maraba² k'awalliya, yanzu nan nake shirin zuwa wajenki sai kuma gashi Allah ya kawoki"

"Ai wallahi Maimuna baki da zumunci, ba'kya zuwa gidana sai wani abun ya sha miki kai, nima na kusa na daina zuwa gidanki."

"Kiyi hak'uri Jummai kinsan yadda malam yake baya san yawo, duk yadda muka kanainayeshi sai abinda nace yayi yake yi, amma har yanzu indai akan yawo ne ba zaiyi ba. Wannan abun na cimin tuwo a'kwarya, na sara ya zan masa na cire masa wannan ak'idar tasa."

"Kice dai har yanzu bai.... Gaskiya k'awata dole ki k'ara tashi tsaye, dan indai kika tsaya a haka tofah wata rana alkadarinki sai ya karye wallahi."

"Hakane to yanzu ta ina zan bullo masa ne?"

"Hhhhh! Ta inda aka hau aka sauka tanan za'a k'ara hawa k'awata"

"Hhhhh! Gaskiya Jummai baki da 'kyau wallahi"

"Sai yau kika sani, wai da baki sani ba?"

"Aa! ni kuwa na sanki farin sani ma kuwa mu tashi tare, ace ban sanki ba ai da nayi asarar zama da nayi dake ba amfani."

"Hhhhh! Kema dai 'kya fad'a, yanzu dai meye labarin da zakije gidana?"

"Hmm!"

Nan ta 'kwashewa duk abinda sukayi ita da Jafar na barin Yasmeen gidan ta fad'awa Jummai, girgiza kai Jummai tayi tace,

"Ai ko kinsan nima da wannan maganar nake tafe, kinsan duk abinda zamu yiwa yarinyar nan bazai kamata ba, koda kuwa wanda zamu bata tacine. In baki sani ba bari na fad'a miki har kurciya nace ayi mata, amma ance babu abinda zai kamata, kuma ance indai muka takura akan illata wannan yarinyar k'arshe kanmu abin zai dawo."

"Yanzu Jummai kina nufin hak'uri zamuyi"

"Hhhhh! Amma ke dai Maimuna baki da...., Ke yanzu dan ga fad'i haka harkin sare cab! Lallai da sauranki. Ai ja da baya a filin yak'i baya nuna ka tsorata ne, kuma kinsan masu iya magana na cewa in hagu ta k'iyya sai a koma dama."

"Hmm! Har naji sanyi a cikin raina eh! Hakane, yanzu ya zamuyi?"

"Kawo kunanki"

Mika mata tayi ta rad'a mata wani abu, tsorone ya bayyana a kan fuskar Maimuna dan har wata razana sai da tayi, dajin abinda Jummai tace zasuyi.

"Jummai anya kina da imani kuwa?"

"Hhhhh! Lallai ma Maimuna ai duk rashin imanina ban kaiki ba, ko kin manta manya² abubuwan da kika aikata ne? da har kika razana da jin wannan k'aramin abun."

"Ai da kikace Jummai ba yanzu ba, kuma da banbanci da wannan, baki gani tayi yarinya da yawa?"

"Ikon Allah Maimuna yaushe kika fara tausayine har haka? Ashe kuwa kinasa san ki k'ara rasa d'anki a karo na biyu kenan?"

"Aa! Wallahi bana"

"Toh! Dole ki aikata haka indai kuwa bakya so"

"Shikenan zan aikata, amma ina d'an jin tsoro"

"Hhhhh! Toh! Ki hak'uri kawai"

"Aa! Yanxu ta ina zamu fara kenan"

"Baki da damuwa........... "

*Shin me Maimuna da Jummai suke kullawa kan Yasmeen? shin zasu cimma burinsu kuwa?*
*Shin Yasmeen zata had'u da Yayanta kuwa?*
*Shin ne zai faru da itane?*
*Duk wadan nan amsoshin zaku samesu a page na gaba*

_See me next page✍🏻_

_*Vote*_
_*Share*_
_*Comment*_
_*#Realtakowa*_

Seguir leyendo

También te gustarán

83.9K 2.1K 82
an eighteen-year-old boy, trying his best to save his ass from being whipped by his soon-to-be husband, and at the same time, he wants to get away wi...
33.5K 553 10
This story is based on village story with lots of smut...
106K 206 84
Erotic shots
54.1K 1.4K 191
Disclaimer : This is not my story. No plagiarism intended. The credit goes to original author. ◆◇◆◇◆◇◆◇ The entire Yunzhou knew that the Ye Family h...