UMAIMAH!

By xinnee_smart1

64.8K 5.1K 604

Dad! Mi... ji.. n... UMAIMAH.. ne! ****ta Yaya musaki yasan soyayyah? Wannan wani salon munafurcin ne! More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
17
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36
37
38
40 MURFI TARE DA KAMMALA WA

39

1.4K 104 14
By xinnee_smart1

Lokacin da su Abba" suka samu labarin mutuwar Jamila"sosai hankalin su yatashi,, jiki na rawa suka je ga gawar ta bayan hukuma ta gama aikin ta aka basu gawar gidan Abba akayi mata komai na wankan gawa da sallah wanda shine gata na karshe a duniya da mutum yake samu, (Allah kasa mucika da Imani, amin) daga nan aka sada ta da gidan ta na gaskiya gidan duk wani mutum da aka Haifa a duniya,

Su Ummi" basu samu komawa ba saboda rasuwar Dad ne kawai ya koma kashe garin rasuwar,,

******
Rahamu"har zuwa lokacin tana hannun police"banda surutai babu abunda take gaba d'aya ta zare, ta fita hayyacin ta,

d'an gashin da yayi saura tabi ta tattazge"

ga uban ba'ki data 'Kara,, kamar an shafa mata shuni, Sam tayi babu kyan gani.

***
Yau kwana ukku da rasuwar Jamila"inda Abba yake zaune a d'akin sa yana duba wasu takardu,, Mami ce tayi sallama had'i da zama kusa da abban,,

duban ta yayi bayan ya amsa sallamar,,

Murmushi tasakar Masa kafun tasoma magana,

Abba"dama nace anya baza mu raba auren mus"ab da UMAIMAH"ba?

da sauri ya dubeta, akan me?

A gaskiya ina ganin UMAIMAH da Zaid suna son junan su,, haka kuma kaga shi mus"ab d'in ba sonta yake ba, ni ina ganin UMAIMAH da Zaid ta dace!

hannun matar sa ya kama kafun yace kin tabbatar da abunda kika fad'amun?

Insha'Allah Abba"...

Shikenan zanyi tunani.

Parlour Mami takoma inda ta samu ummi ta shirya,, dan tafiya Abuja, ga baby sai rigima take wai sai ta bita,, itakuma tace baza ta je da ita ba saida izinin mijinta,

Mami ganin ummi yasa ta ce kardai har kin shirya a mamakance,,

dariya Mami tayi aikuwa na shirya insha'Allah!

baby... Lafiya naga sai kumbura baki kike?
dariya ummi tayi tana duban babyn da sai sake cuna baki take kamar zatayi kuka.

Wai Lallai sai ta bini, ni kuwa nace bazani da itaba.

Habadai"sai ki  'ki zuwa da ita? Akan me?

dan Allah hajiya kuje tare itama ai zata so taga dangi,, dariya baby tayi, yawwa mamina mai sona....

Da gudu ta nufa d'akin ta dan had'a kayan ta.

Su Ummi kuwa fira suka shiga yi.

Suna cikin firar ne mus"ab da Zaid suka shigo,, da sallama.

Amsawa sukayi Mami sai murmushi take tana mai kallon yaran nata cike da kauna a ranta tana godiya ga ubangiji da ya azurta ta da wad'anan zaratan samarin. Sosai take jin kaunar su na sake ratsa ta.

Muryar su da taji suna gaisheta ne yasa ta duban su cike da murmushi ta amsa musu gaisuwar.

zama sukayi a kasa,, ummi"cikin muryar ta mai sanyi tace to Zaid mus"ab muna sake jaddada godiyar mu ga Allah sub'hanahu wata'ala, haka kuma muna yi muku godiya da irin wannan karamci naku.

Allah yasaka da alkhairee.

Amin kowa ya amsa kafun Mami tace.... Ai kuma kun cancanci godiya,, da irin rikon da kuka yiwa Zaid hakika samun mutane kamar ku a wannan lokacin zaiyi wuya ba kowa bane mai zuciya irin taku fatanmu dai Allah yabiya ku da alkhairee. Ya kuma sake kiyaye mu daga dukkanin sharri.

Amin suka amsa gaba d'aya har Abba dake shigowa parlourn.

Zama yayi a d'aya daga cikin kujerun.

Shima dai godiyar yasake yi da kuma addu'a.

Mus"ab ne ya d'an muskuta kad'an kafun yace,, dan Allah iyayena ku gafarce ni da hukuncin da na riga na yanke wanda ni a nawa tunanin shine daidai,, saidai zuciya ta ta amince da hakan da nayi shine abunda ya kamata.

Kowa a gurin ya kura masa ido dan jin mai zai fad'a.

Sake sunkuyar da kansa yayi kafun yace.... tun daren ranar da na gane UMAIMAH"ba cikakkiyar mace bace...... Na....
Sake..... Ta!

Ya karasa fad'a kirjin sa na bugawa, dan baisan yadda iyayen nasa Za su karbi maganar tasa ba.

numfashi Abba ya sauke kafun,, ya shiga yi masa nasiha da bin umarnin iyaye duk yadda ba'a son abu matu'kar iyaye suka ce ayi tofa ayi matu'kar bai dabawa shari'a ba. domin biyayya ga iyaye tana gaba da komai a rayuwar ko wani d'an Adam.

Sosai yayi musu nasiha dukan su, har baby wacce ta dawo parlourn da jakar kayan ta.

Daga bisani yace mus"ab ya kira driver dan yakai su ummi airport.

Zaid"najin haka yace, ai ban hado kayana ba.

dariya mus"ab ya sheka, Abba ne yace to waye yace maka da kai Za'aje?

Kai ai kana nan tukuna.

d'an Sosa keya Zaid yayi yana hararar mus"ab, a gaskiya shi a ransa ba haka yaso ba. so yayi kafar sa kafar yarinyar sa saidai kuma babu yadda ya iya.
dan haka yana ji yana gani suka tafi,
Sai fatan Sauka lafiya.

******
Bayan kwana biyu!

Mus"ab ne cikin mota yana jiran,, Zaid ya fito dan rakashi gun favorite d'in sa.

Sai duban agogon dake hannunka sa yakeyi,, dan yau tunda yace zai je gun ta yake jin wani irin zumudi da kewar ta na shigar sa, wani irin Allah Allah yake ya ganta.

Zaid"yake ne ya bud'e d'ayan side d'in ya zauna, ko gama rufewa baiyi ba mus"ab ya fizgi motar saida Zaid ya tun tsira.

Malam meye haka wai?

Mus"ab dai tukin sa kawai yakeyi cikin kwarewa,

Wai ba magana nake maka ba?

cewar Zaid.

So hauka ne? Zaka dinga fizgarmu sai kace abun banza,, ni kaga kawai ka sauke ni indai da wannan uban gudun zamuje sauke ni bazani ba.

Mus"ab dai ko ci kanka baice masa ba.

Ganin dai bazai kula shi bane yasa yaja bakin sa yayi shiru.

*****
Sun isa gidansu budurwar mus"ab inda sukayi parking a bakin gate.

Wayar sa ya d'auka yayi dialling number ta,, har ya katse ba'a d'auka ba ya koma kira, cikin ikon Allah aka d'auka,, tana d'auka jiki na rawa tasoma cewa... Mus"ab Kai..... Kaine? tana maganar muryarta na rawa,, daga ji dama kuka take.

a hankali yace cool down"favorite.

yanzun dai ki fito gani a bakin gate.

Yana gama fad'in haka ya katse wayar,

Zaman mintina goma sukayi kafun ta fito.

Sanye ciki jallabiya Yar asalin Saudi, kanta yane da mayafin jallabiyar.

Idan bakasan ta ba tsaf zaka ce balarabiyar saudiya ce dan tafi kama da su.

hangota da yayi ne yasa yace da Zaid dake dannar wayar sa muje.

Banza Zaid yayi dashi.

ganin haka yasa yace Kar Allah yasa ka fito, yana gama fad'in haka ya fice daga motar Kai tsaye gurin bugun zuciyar sa ya nufa.

Assalamu"alaiki" ya habibty"

d'an murmushi taimasa had'i da fad'in Wa"alaikissalam" ruhy.

Khaifa haluk?

Alhmdllh"

Aaaa bil"munasaba, ana......

Hey" hold on...

Mus"ab ya fad'a yana dariya,, daga gaisawa? garki kaini inda banje ba,

Itama yar dariyar tayi,,

Favorite"!!

Yanayin yadda ya fad'i sunan yasa ta dube shi, idanuwan ta na kawo ruwa.

Shima cikin asalin qwayar idanun ta yake kallo,, yana jin kirjin sa na wani irin bugu.

Maike faruwa ne?

Ya jefa mata tambayar,, dan sam hankalin sa bai kwanta da ramar da tayi ba.

Asalima lokacin da ta amsa wayar sa Koda yaji muryar ta, ya d'auka ko duk kewarsa ce da farincikin jin sa a lokaci d'aya.

Saidai ganin da yayi mata yanzun yasa ya karya ta wancan tunanin nasa.

Kasa cewa komai sideeefah tayi sai hawaye da take faman sharewa.

hannun ta yakama kai tsaye ya nufi mota da ita bayan ya bud'e had'i da nuna mata ta shiga babu musu ta shiga dan tana bu'katar hakan wato kebancewa suyi magana.

Shima shiga yayi,, ba tare da laakari da Zaid dake motar ba ya ri'ke hannuwan ta duka biyu,,

Zaid lokacin da yaji alamun shigowar su tsaki yayi a ransa yace duk wajen bai ishesu ba har sai sun shigo mota dan iskancin mus"ab. Bai dago kansa ba Sai dannar wayar sa da yaci gaba dayi.
Sidde Sam bata lura da mutum a motar ba saboda damuwar da take ciki dan haka ganin nata ma sai a hankali.

Favorite"look in to my eyes and told me what's going on.

Kinga yadda kika rame kuwa Kinga yadda kika koma?

Please talk to me! am here for u.

Wani hawayen ne ya sauko mata,

Kafun a hankali tasoma magana.

Mus"ab u hv no idea how much I love you.

numfashi ta sauke kafun taci gaba da cewa tun lokacin da naida na jinka na shiga damuwa,, saidai tashin hankalin da ya tunkaro ni yafi komai damuwa a gurina.

Alhaji mijin mahaifiya ta,, kuma uban riko na,, ya sameni da zancen in fidda miji.

Mus"ab mai zance masa a wannan lokacin? Ince Inada wanda nake so yake sona saidai bansan inda yake ba? Ince yadaina kirana a waya? Ince idan na kira bana samun shi?

ban San mai zance ba, dan haka kawai na amsa da zan fitar,, bayan kwana biyu yasa ke tuntuba ta da zancen. shirun da nayi shine matsalar domin kuwa kasa ce wacce komai nayi,, daga nan yaje sanar dani da ammi na ya fitar mun da miji.

Zai aurawa d'an sa ni!!

ta karasa zancen da wani irin kuka,,

What!??

Cewar mus"ab jikin sa na wani irin kyarma.

Cikin kuka seedifah tace.... Me yasa bakazo da wiring ba? Ina kaje ka barni cikin wannan tashin hankalin? Yanzun haka fa saura sati d'aya a d'aura aurena da Hafiz.

sunkuyar da kansa yayi had'i da dafe shi da dukkan hannayen sa wanda ke nuni da kan na masa ciwo.

tunda suka soma maganar,, yadaina gane abunda yake a wayar sa dan komai da suke fad'a yana ji,, sosai Shima yaji babu dad'i da wannan rashi da d'an uwansa zaiyi. Shi shaida ne akan yadda mus"ab yake tsananin kaunar yarinyar.

Jin sunyi shiru sai sheshekar kukan ta dake tashi a motar, sai numfashin mus"ab akai2,

Shi yasa ya juya a hankali dan kwantar musu da hankali.

Saidai idanuwan sa na Sauka kan yarinyar yaji gaban sa ya fad'i.

a hankali yace seddi!!

itanma d'agowa tayi dan ganin mai ambatar ta da wannan sunan,, mutum d'aya ne mai kiran ta da seddi"saidai bata ta'ba tunanin sake ganin sa a rayuwar ta, dan mai kama dashi ma data sani mutum d'aya ne wanda shine makullin zuciyar ta.

Haka kuma bai taba kwatanta kiran ta da sunan ba.

Waye wannan?

karaf idonta ya Sauka akan nasa daya zuba mata,, wanda mamakin sa yakasa boyuwa a cikin su.

Mu had'e a murfi....Insha"Allah 🤗


Xinnee smart 😍😘

Continue Reading

You'll Also Like

320K 4.4K 31
Rajveer is not in love with Prachi and wants to take revenge from her . He knows she is a virgin and is very peculiar that nobody touches her. Prachi...
39.4K 2.4K 47
It's all about love betrayal of trust and bargaining
1M 78.3K 39
"Why the fuck you let him touch you!!!"he growled while punching the wall behind me 'I am so scared right now what if he hit me like my father did to...
1.3M 32.5K 46
When young Diovanna is framed for something she didn't do and is sent off to a "boarding school" she feels abandoned and betrayed. But one thing was...