39

1.4K 104 14
                                    

Lokacin da su Abba" suka samu labarin mutuwar Jamila"sosai hankalin su yatashi,, jiki na rawa suka je ga gawar ta bayan hukuma ta gama aikin ta aka basu gawar gidan Abba akayi mata komai na wankan gawa da sallah wanda shine gata na karshe a duniya da mutum yake samu, (Allah kasa mucika da Imani, amin) daga nan aka sada ta da gidan ta na gaskiya gidan duk wani mutum da aka Haifa a duniya,

Su Ummi" basu samu komawa ba saboda rasuwar Dad ne kawai ya koma kashe garin rasuwar,,

******
Rahamu"har zuwa lokacin tana hannun police"banda surutai babu abunda take gaba d'aya ta zare, ta fita hayyacin ta,

d'an gashin da yayi saura tabi ta tattazge"

ga uban ba'ki data 'Kara,, kamar an shafa mata shuni, Sam tayi babu kyan gani.

***
Yau kwana ukku da rasuwar Jamila"inda Abba yake zaune a d'akin sa yana duba wasu takardu,, Mami ce tayi sallama had'i da zama kusa da abban,,

duban ta yayi bayan ya amsa sallamar,,

Murmushi tasakar Masa kafun tasoma magana,

Abba"dama nace anya baza mu raba auren mus"ab da UMAIMAH"ba?

da sauri ya dubeta, akan me?

A gaskiya ina ganin UMAIMAH da Zaid suna son junan su,, haka kuma kaga shi mus"ab d'in ba sonta yake ba, ni ina ganin UMAIMAH da Zaid ta dace!

hannun matar sa ya kama kafun yace kin tabbatar da abunda kika fad'amun?

Insha'Allah Abba"...

Shikenan zanyi tunani.

Parlour Mami takoma inda ta samu ummi ta shirya,, dan tafiya Abuja, ga baby sai rigima take wai sai ta bita,, itakuma tace baza ta je da ita ba saida izinin mijinta,

Mami ganin ummi yasa ta ce kardai har kin shirya a mamakance,,

dariya Mami tayi aikuwa na shirya insha'Allah!

baby... Lafiya naga sai kumbura baki kike?
dariya ummi tayi tana duban babyn da sai sake cuna baki take kamar zatayi kuka.

Wai Lallai sai ta bini, ni kuwa nace bazani da itaba.

Habadai"sai ki  'ki zuwa da ita? Akan me?

dan Allah hajiya kuje tare itama ai zata so taga dangi,, dariya baby tayi, yawwa mamina mai sona....

Da gudu ta nufa d'akin ta dan had'a kayan ta.

Su Ummi kuwa fira suka shiga yi.

Suna cikin firar ne mus"ab da Zaid suka shigo,, da sallama.

Amsawa sukayi Mami sai murmushi take tana mai kallon yaran nata cike da kauna a ranta tana godiya ga ubangiji da ya azurta ta da wad'anan zaratan samarin. Sosai take jin kaunar su na sake ratsa ta.

Muryar su da taji suna gaisheta ne yasa ta duban su cike da murmushi ta amsa musu gaisuwar.

zama sukayi a kasa,, ummi"cikin muryar ta mai sanyi tace to Zaid mus"ab muna sake jaddada godiyar mu ga Allah sub'hanahu wata'ala, haka kuma muna yi muku godiya da irin wannan karamci naku.

Allah yasaka da alkhairee.

Amin kowa ya amsa kafun Mami tace.... Ai kuma kun cancanci godiya,, da irin rikon da kuka yiwa Zaid hakika samun mutane kamar ku a wannan lokacin zaiyi wuya ba kowa bane mai zuciya irin taku fatanmu dai Allah yabiya ku da alkhairee. Ya kuma sake kiyaye mu daga dukkanin sharri.

Amin suka amsa gaba d'aya har Abba dake shigowa parlourn.

Zama yayi a d'aya daga cikin kujerun.

Shima dai godiyar yasake yi da kuma addu'a.

UMAIMAH! Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon