40 MURFI TARE DA KAMMALA WA

2.2K 129 30
                                    

Hhhhh ji da yawan ku kunsaka ni dariya 😂da masu cewa kansu ya qulle akan sidde da Zaid(to idan baku manta ba, bari mu d'an koma baya kad'an, lokacin Zaid yana gidan marayu ai anyi masa sharri yayi wa wata yarinya fyada yarinyar da ya d'auka matsayin kanwar sa, yawwa Fatn kun tuna yanzun to itace wannan yarinyar da mus"ab yake so ya akayi suka had'u da mus"ab? Sai ku biyoni Yar mutan RIJAU dan jin yadda abun yake 😀🤗)

Hhhh kuma wanda baku gane Murfi ba kunsani dariya fa sosai,, harda mai cewa wani novel d'in ne Murfi? Hhhhh to qarshen labarin😂

Thank you all for reading my story😍abunda yake daidai Allah yasa mu amfana wanda yake kuskure Allah ya gafarta mana,

Anan na kawo karshen wannan labarin na UMAIMAH🤗 masoya na na whatsapp da kuma Wattpad, babu abunda zance muku sai dai Allah yabar zumunci domin sunan ku bazai taba lissafuwa ba, Ngode sossai da qaunar ku a gareni hade da addu'o'inku, Allah yabar zumunci 😘😍😘

Sosai jikin ta yake rawa... ta dubi mus"ab ta dubi Zaid" ta kasa cewa komai.

Zaid ma sosai yake al'ajabin ashe zai koma ganinta a rayuwar sa?

Mus"ab jin shirun yayi yawa ne yasa ya shiga duban su, ganin irin kallon mamakin da sukeyi wa juna ne yasa yadan taba Zaid"hey what?

Numfashi Zaid ya sauke had'i da fad'in Allah mai iko.

bro dama kasanta ne?

madadin yabawa mus"ab amsa sai ya dubi siddifah had'i da fad'in ina ammi?

Sai yanzun tasamu nutsuwar amsa masa da tana cikin gida.

Yaya Zaid ina ka tafi ka barmu?

Na dade ina zargin mus"ab d'an uwanka ne amma tun lokacin da nafara ganin sa na zaci Kaine" saidai kuma yayi mun bayanin shi baima San wanda nake fad'a, Ammi ma tana ganin sa ta zata Kaine saidai amsa d'aya yabamu baisan wanda muke magana akai ba hasali ma shi kad'ai iyayen sa suka Haifa, a kullum ammi cewa take wannan kamar tayi yawa.

Gyada Kai mus"ab yayi had'i da fad'in hakane gaskiya ne na tuno lokacin da nafara ganin ki hakan kika hakikance kan Zaid ne saida na tabbatar miki da banma San wanda kike nufi ba,, kafun kika yarda a tsorace.

Allah sarki ashe d'an uwana ne.

Numfashi Zaid"ya sauke, kafun yace mai ya faru bayan Bana nan.??

Hawaye ta sauke masu d'umi kafun ta fice daga motar Kai tsaye cikin gida ta nufa.
Ido suka bita dashi.

Ammi.... Ammi.... Ammi kizo ga Zaid d'inki.

d'akin mahaifiyar ta tanufa tana kwala mata kira,, Ammi dake gyaran kaya a closet da sauri ta ajiye kayan hannun ta ta taro siddefah.

Ke lafiyar ki kuwa?

Tana haki kamar wacce tayi gudun klm 30

tace Ammi yau dai Allah ya karbi addu'ar ki ga Yaya Zaid"!!

Wani irin gingirim ammi taji maganar.

Za... Z... a... Zaid?

gyada Kai siddi ta shiga yi kamar qadangaruwa.

Ke siddifah kin tabbatar kuwa shine?

Wlh ammi shine har munyi magana dashi yana ma kofar gida ashe d'an uwan mus"ab ne.

Fiddo ido ammi tayi Kai haba? Koda naji ai biri yayi kama da mutum.

Maza bude musu d'akin baki,, bari in d'auko mukulli.

mukullin ta d'auko ta bata.

Itakuma waya ta d'auka ta shiga kiran,,  mai gidan yana d'auka ta nemi izinin shi kan tanada bako yaron da tasha bashi labarin ya bace a gidan marayu yau shine a gidan, (kasancewar ta boye asalin abunda ya faru)

UMAIMAH! حيث تعيش القصص. اكتشف الآن