YASMEEN.

By JannatMN

1.2K 63 13

Labari ne da ya k'unshi abubuwan ban mamaki kama daga kan:-Hak'uri, juriyar, tausayi, soyayya, yaudara, cin... More

Page 1 ✍🏻
Page 2✍️
Page 4&5✍🏻
Page 6&7✍🏻
Page 8&9✍🏻
Page 10&11✍🏻
Page 12&13✍🏻
Page 14&15✍🏻
Page 16&17✍🏻
Page 18&19✍🏻
Page 20&21✍🏻
Page 22&23✍🏻
Page 24&25✍🏻
Page 26&27✍🏻
Page 27&28✍🏻
Page 29-30✍🏼
Page 31-32✍🏼

Page 3✍️

114 6 0
By JannatMN

YASMEEN.



*_Story & writing_*
          *_by_*
*_Jannat mn(Real takowah)_*

*Wattpad_@Realtakowa*

*_Dedicated to my sister_*
     

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM*_
     
         _*6 January, 2020😍*_

  _*Kyautatawa Allah zato!*_

_*Wata Rana wani mutum ya tambayi Abdullahi D'an Abbas r.a "Waye zaiwa mutane hisabi ranar kiyama?" Sai yace "Allah ne" sai mutumin yace "Na rantse da ubangijin Kaaba mun Tara."*_

_*Haka an taba cewa wani mutumin kyauye "Lallai zaka mutu" sai yace "daga nan sai wajen WA?" Akace "Wajen Allah" sai yace "Bamu taba ganin alkhairi ba sai daga wajen Allah ta yaya zamuji tsoron tafiya gareshi?"*_

_*Dan haka yan uwa mu ringa kyautat zato ga Allah shine zai isar mana komai. Ina rokon Allah ya yi min rahama ni daku da iyayenmu da malamanmu ya samu cikin inuwarsa ranar alkiyama ranar da babu wata inuwa sai tasa. Ameen Summa Ameen👏*_

_*Page3✍️*_

"Ke wace irin dak'ik'iyace da kika dawo nan kika kwanta kina barci,  wa kika ajiye ne da zai hura miki wuta. Zaki tashi koh sai nayi boll dake.....? shashsha kawai, mutum kullum yana abu amma saboda tsabar kwakwalwar ta kifice baya iya rikewa"

Tashi tayi ta fita had'o yayi da ledoji tayi ta dawo, madafar ta nufi ta fara had'a wuta muntin kad'an ta d'auka ta gama had'awa, saboda inda sabo ta saba tun batakai haka ba Mama ke sata hada wuta, tun tana k'onewa har ta saba bata k'onewa. 

Wata tukunya ta d'auko wanda tafi k'arfinta tana rinjayarta, amma ahaka ta d'agata da kyar ta daura a saman murhu takawo murfinta ta rufe sannan ta fita tabar madafar.

"Mama na had'a wutar"

"Toh..! Wa kika ajiye ne zaizo ya d'aura miki a saman murhun ne? Koh Ubanki ne zaizo ya d'aura miki ne? Koh shegiyar uwarki kikeso ta dawo ta d'aurane? Nama gane ni marainiyar wayanki kike so na tashi na d'aura.....?"

"Assalamu Alaikum"

"Wa'alaikassalam"

"Baba sannu da zuwa"

Banza yayi da ita bai tanka mata ba koh kallonta ma baiyi ba,

"Andawo lafiya baba?"

"Inda ban dawo lafiya ba ai bazaki gani anan ba, bafa nasan munafunci banza dana hofifa, ki fita a idona rufe Yasmeen, Uwarki ma tayi nata ta gama kuma ta gushe babu riba."

"Yauwa malam,  dama kai nake jira tun d'anzu"

"Allah yasa lafiya dai"

"Inafa lafiya, wai malam yanzu kamar ni nasa Yasmeen aiki wai tace mun bazatayi ba wai ni ba uwarta bace, kajifa dan Allah? Yarinya k'arama da ita, koh ina ta koyo wannan rashin kunya haka? Abin na ban mamaki wallahi dan ranan har zagina ta kusanyi...."

Sai kuma ta fashe da kukan munafinci harda hawayen k'arya, itadai Yasmeen tunda ta fara magana take kallonta da tausayin kanta, dan tasan babu abinda zai hana babanta dukanata yau.

"Inalilahi wa'ina ilaihi raji'un yau naga ta kaina ni habu, yi hak'uri Maimunah yi shiru daina kukan akan wannan hatsabibiyar yarinya."

"Ai dole nayi kuka Malam, yanzu indan yarinya nan ta lalace, me mutane zasuce akaina? Cewa zasuyi dagayya na bari ta lalace dan naga ba 'yata bace. Allah ne shedata akan wannan yarinya inayi iya bakin k'ok'arina akanta, amma abu yak'ici yak'ciyewa kaga kuwa dole nayi kuka tun yanzu kafin kuma nan gaba jinina ya hauu, saboda zagin jama'ar garin nan da ma......"

"Yanzu kee.....wallahi sai yau na k'ara dana sani auran uwarku danayi, dama masu iya magana nacewa "tsintacciyar mage bata tab'a zama mage," kuma haka abin yake yanzu gashi daga taimako na janyo uwarku daga rana na sata a innuwa, gashi yanzu ta turani cikin rana da ta haifamin...."

"Nima Malam abinda na gama fad'a dazu nan kenan, kasan ance kaddara ta riga fata babu yadda zamuyi, mu kuma haka jarabawar tamu take....."

Tashi yayi ya shiga d'aki bace komai ba, take jikinta ya fara haurawa, saboda tasan maizai biyo baya, fitowa yayi da murtukekiyar doriyanarsa yayo kanta.

Ta tashi zata gudu Mama ta faki idan Malam tasa k'afa ta hard'eta, aikuwa ta fad'i ta kife hab'arta ta daki k'asa, hak'oranta suka datse mata halshe wata irin k'ara tayi saboda azaba.

Dauk'ota yayi babu koh almar tausayinta da fad'uwar da tayi, ya fara zuba mata dorina nan a jikinta, banda ihun neman d'auki babu abin take, amma babu mai taimakonta saida ya daki san ransa sannan ya rabuta anan.

Juyawa yayi kan Mama sai wani huci yake sai kace wata salansa,

"Dan Allah Maimunah duk lokacin da ta kuskura ta k'ara miki rashin kunya, koda mai kama da ita ne ki sanar dani, kada ki k'ara rufa mata asiri bazan lamurci wannan iskancin a cikin gidana ba."

"Insha Allah malam anyi na farko anyi na k'arshe bazan kara rufa mata asiri ba, ai in ta lalace nice aciki, kuma inta gyaru sai nafi kowa farin cikin, domin Yasmeen tamkar 'yar cikina na d'aura"

"Ai nasan ni Maimunah, shiyasa kwata²  bana da shayi akanki, indai akan wannan hatsabibiyar yarinyar nan ne."

"Na gode Malam da irin wannan kyakyawar shedar da kayi min, yanzu nasan ko mai zai biyo baya marar kyau zaka goya min bazaka ce laifinane."

"Hakane ai nasan jini ne,  gado tayi kisan masu iya magana nacewa "Barewa bazatayi gudu ba d'anta yayi rarrafe" dan haka kidaina tunanin komai indai dakwai jini Kubrah a jikin wannan yarinya, tofah sai munyi hak'uri amma nasan me zanyi zanyiwa tufkar......"

"Ke kuma bazan ce kada ki k'ara ba koh nace kidaina abinda kike ba, aaa kada kiyi koh d'aga aciki, inkinga zaki daina kinceci kanki, inkuma akasin haka shima dai kanki, ba damuwata bace nidai abinda zance kawai shine muzuba mu gani nidake aga......"

Yana gama farin haka yayi hanyar waje, "Na fita saina dawo"

"Toh...! Adawo lafiya Malam"

Yana fita ta kallin inda Yasmeen ke kwance ta kwashe da dariyar mugunta, sannan tace "Yarinya kad'an kika gani indai bazaki bar gidan nan ba  tofah yanzu na fara sa Ubanki yana dukarki, kinga koh kasheki yayi shi yayi asara, ba Maimunah bace tayi, dan haka inamai shawar tarki kiyi gaggawar barin gidan nan indai.... Maza ki tashi ki had'o kayan wanke² kiyi sannan ki gyara gidan tsafa, inko ba haka ba kindai san kwanan......"

Tashi tayi da kyar tana jan k'afa idanun nan nata sunyi jajir dasu, abinka da fara fata duk inda Malam ya daketa yayi jajir dashi, kuma ya kumbura dan wani gurin har borin jini yi.

Had'o kayan wanke² ta farayi bata wani dauki lokaci ba ta gama gaba d'aya har gyaran gidan, alwala tayi sboda a lokacin an fara kiraye² sallar magriba, itama Mama lokacin ta gama abincin har tama zobawa kowa kwananshi.

Tashi tayi ta nufa d'aki gabatar da sallah, fitowa tayi ta nufi madafa d'auko abincinta tayi d'aki ta koma, zamatayi a saman tabarmarta ta faracin  k'anzoneta dan Mama bata, bata abinci saidai kanzo, ci take hankali kwance har tagama tasha ruwa, sannan tace  "Alhamdulillah."

"Ke Yasmeen²"

"Na'am..!"

Fitowa tayi da saurinta tace "Gani Mama"

"Kinaji ina kiranki shine kikayi bazan, kamar bakiji ba koh?"

"Aaa..! Wallahi banjiki bane kiyi hakuri...."

"Yoo..! aiko kinji cewa zakiyi baki ji ba dani kike magana zanki gane kuranki ne, karb'i maza kije shagon Audu ki krb'on ashana da sigari, kiyi sauri saura kuma ki dade...."

"Toh..!"

Karb'a tayi tasa takalmi tayi waje, tana fita taci karo da Yaya Ahmad, aiko da gudu tayi kansa ta rugumeshi wani irin kuka da fashe dashi mai tsuma zuciyar mai sauraro, rintse idonsa yayi  jin kukanta yake har cikin ransa, takiyake idanonsa suka kada sukayi jajir dasu, babu abinda yafi tsana a duniya sama da kukan Yasmeen tun bata kai haka ba.

Dan bazai tab'a mantawa ba wasu shekaru kad'an sa suka wuce lokacin Yasmeen bazata wuce shekara uku ba a duniya, shi da Kabir da Yasar suna hira Yasmeen na hannunsa yana mata wasa, Yasar ya kallesu yayi murmushi ya d'aga hannu sama yace "Alhamdulillah" kallashi sukayi shida Kabeer.

Kabeer yace "D'an uwana lafiya, mai yasaka farin ciki haka?" K'ara yalwata murmushinshi yayi sannan yace "D'an uwana sai yau na k'ara tabbatarwa da ko yau na bar duniyar nan, bazan tafi ina mai dana sani ba, domin nasan K'anwata bazata tab'a kukan rashin d'an uwanta ba. Saboda na san Kai da Ahmad bazaku tab'a barin Yasmeen dinta tayi kukan maraici ba zaku tsaya mata a komai nata kamar yadda ni zan tsaya mata...."

Shiru yayi kukane ya kub'uce masa, ba  k'aramin razana sukayi ba da gani kukan Yasar dan ba k'aramin abu bane zai sashi kuka, dan Yasar jarumin ne yanada dakiya akan komai, amma gashi yanzu shine yake kuka abinda basu tab'a gani ba.

Bakinshi na rawa cikin rauni murya shima kamar zaiyi kuka yace, "Ya kai d'an uwana menene dalilin wannan kukan naka?, ko zan iya sani abinda yasa jarumin d'an uwana kuka? har nima yake shirin sani kukan."

"Kabeer kasan duk duniyar nan babu abinda nafiso sama da k'anwanta sai kuma Ummata koh?"

"Eh..! Na sani d'an uwana"

"Inaji ajikina wani dalili yannan zuwa ya rabani dasu, akoda yaushe na kwata mafarkin nakeyitun ban d'auki abun gaskiya ba har yanzu takai na d'auka kuma nasawa raina abun. Duk lokacin dana tuna sai nayi kuka domin basan ya rayuwata data k'anwanta da kuma ta Ummata zasu kasance ba. Kabeer Yasmeen itace duk wani farin cikina, indai na rasata bansan ya rayuwata zata kasance ba ina tausayin Ummata. Kai kanka shedane domin kasan yadda muke rayuwa a cikin gidan mahaifin mu tamkar a gidan kurku, Allah nai kadai gatanmu kuma nine bangon jinginasu. Kasan indai Ummana na cikin gidan nan bazata tab'a samun farin cikin ba, ganin mu ke rage mata damuwarta kana gani rashin mu a kusa da ita bazai haifar mata da wata babbar damuwa ba, wannan kadai na tuna sai nayi kuka, dan haka tun yanzu kafin lokaci ya k'uremun zan bar muku amanar Ummana da K'anwanta dan Allah ku kulamin dasu kada ku bari suyi kukan rashina....."

Kuka ya kuma fashewa dashi, tausayi ya basu sun kuma gasgata da dukkan kalaman da Yasan ya fad'a, kawai Suma sai suka fashe da kuka  aka rasa mai lallashi wani acikinsu.

"Yayana me akayi maka kake kuka Mamace koh?" Kawai ita saita fashe da kuka dan bata san ganin kukan yayan nata, shiru yayi ya jawota jikinshi ya fara lallashinta yace "Yasmeen dinta me waya tab'aki kike kuka nunamin na rama miki "nunashi tayi tace "Ba kaine lake kuka ba" murmushi yayi yace "Toh..! Na daina kema ki dai..." Dariya  tace "nima na daina "yauwa 'yar K'anwata wata kokefa kin mafi kyau a haka" 

"D'an uwana kadaina damuwa akan wannan inadai ina raye bazan tab'a barin su Umma ba zan tsaya musu adukan lamuransu Insha Allah nayi maka alk'awa."

"Na gode d'an uwana, kuma  na san zaka iya yiwa su Umma komai Kabeer amma Mama bazata tab'a yarda da haka ba kayi hak'uri ni ban daura maka wannan dauyin ba ka kasance mai yin biyayya ga mahaifiyarka bana sa tana yawan fushi dakai akanmu, kaji d'an uwana?"

"Eh..! Naji kuma Insha Allah zan kasance mai biyayya a gareta."

Dafa kafadarsa yayi yace, "Abokina nayi maka alk'awari zan kuna maka dasu Umma da Yasmeen koda kuwa k'arfina zai k'are ne zan kula ma dasu insha Allah bazan tab'a gazawa ba..."

"Na gode Ahmad Allah ya bar zumunci"

"Ameen ya Allah"

Lallashin ta ya farayi tare da bubuga mata bayanta, "Yi hak'uri Yasmeen dinta Yi shiru daina kukan, me ya faru? Me kayi miki? Waya tab'amin 'yar k'anwata ne? Gaya min yanzun nan na rama ma miki koda kuwa k'arfina zai k'are....."

Ajiyar zuciya kawai take saukewa, cikin kuka ta kwashe duk abunda akayi mata ta fad'a masa, rashi ya b'aci idanowansa sukayi jajir dasu.......

_See me next page✍🏻_

_*Vote*_
_*Like*_
_*Comment*_
_*#Realtakowa*_️

Continue Reading

You'll Also Like

1.8M 117K 26
#Book-2 in Lost Royalty series ( CAN BE READ STANDALONE ) Ekaksh Singh Ranawat The callous heartless , sole heir of Ranawat empire, which is spread...
40.3K 3.6K 19
A Royal family renowned for their illustrious name and fame, A family full of pride and rage, A Family for which everyone bows their head - The Agnih...
192K 4.7K 111
As the Maid of Evil, Y/n sacrifices her life for her twin brother. As the Mist Hashira, Y/n sacrifices her life for humanity. But not anymore will Y...
77.5K 2K 71
"mom, dad, Im married!" lahat ng relatives namin ay nagulat sa announcment ko. Sino ba naman kasi ang mag aakala na ang unica ija ng pamilyang Letpr...