๐Ÿ’๐Ÿ’SOYAYYA MAI GARฦŠI๐Ÿ’๐Ÿ’

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78

Page 79-80

1.8K 72 9
By SiyamaIbrahim

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

*_Grand Finale_*>>>>>

*_IF I SAY THAT I DON'T LOVE,CHERISH,APPRECIATE AND RESPECT THE LUV U HAVE FOR ME AM DEFINITELY DECEIVING MY SELF WORDS OR EXPRESSION AREN'T ENOUGH FOR ME TO SHOW U ALL MY GRATITUDE TOWARDS THE LOVE,CARING,STRONG BOND AND ATTACHMENT U GAT FOR ME RIGHT FROM THE VERY FIRST BEGINNING OF THIS BEAUTIFUL NOVEL TO THE VERY PRESENT END OF IT I DON'T KNOW HOW TO SAY IT ALL BUT I LOVE U ALL I SINCERELY DO FROM MY HEART AM SAYING IT AGAIN I LUV U ALL,,IT WASN'T AN EASY JOURNEY,FOR SOME IS OK WHEREAS FOR SOME IS A NO NO BUT NEVERTHELESS I AM IN LOVE WITH UR LOVE TOWARDS ME IT'S ACTUALLY MY FIRST BOOK BUT UR LOVE AND ENCOURAGEMENT MADE ME FEEL AS IF I WASN'T NEW TO THE WORLD OF WRITERS MAY THE GOD ALMIGHTY CONTINUE TO BLESS AND SHOWER MORE LOVE THAT WILL SPRAY ALL OVER US AM REALLY HONOURED MY CUTIE FANS_*

*_🅱WA I WANT TO SAY A BIG THANK U ALL FOR SUPPORTING ME,ENCOURAGING ME THROUGHOUT THE JOURNEY IT WAS A WOW THANK U SO MUCH MAY WE BE A CATARACT TO OUR ENEMIES OUT THERE I LUV U GUYZ_*

*_THE GIANT OF ALL SOYAYYA MAI GARƊI FANS GROUP YA ALLAH AM SHORT OF WORDS BUT KEEP IT IN MIND THAT I SIYAMA IBRAHEEM RESPECT AND HONOUR U ALL THANKS FOR THE LUV AND GIGANTIC PRAYERS_*

*_SIYAMA IBRAHEEM FANS PAGE I REALLY APPRECIATE THE LOVE AND CARE THANK U_*

*_SPECIAL THANK U TO U MY HEART LISTENER MY MENTOR MY MOTIVATOR MY FRIENDY SURAYYA MUHAMMAD SULE AKA SURAYYAHMS OFFICIAL CATTY🐈 U ARE EVERYTHING THAT IS SO SPECIAL TO ME U NOT BEING SELFISH MADE U A VERY WELL RESPECTED HUMAN TO ME U ARE KIND SELFLESS AND A MOTIVATOR TO EVERY SENSIBLE HUMAN BEING CAN'T LOVE U LESS MAY GOD CONTINUE TO ASSIST U AND INCREASE UR BRAVERY AND KNOWLEDGE AS U CONTINUE TO UPDATE US WITH THE GREAT LATEST AHUMAGGAH_*

*_AT LAST AM HONOURING ALL MY LOVELY FANS WHERE EVER U ARE AM HAPPY FOR THE LUV U SHOWED TO ME MAY ALLAH SWT INCREASE THE BOND BTW US AMIN❤_*

*_This final page is for the cat and rat of Brilliant Writers Association no one i mean no one no body can come btw the two of u ummerherny Nersallah the rat and Surayyahms official catty the cat i luv u guyz_*

7⃣9⃣➖8⃣0⃣

A matuƙar ruɗe big sis ta juya zuwa direction ɗin hanyar waje inda ta hangp Abdulrahman na ƙoƙarin saka Aisha a mota cikin sauri ta biyo su ita da mijin ta duk ta rikice sai tambayar shi take me ya sami Aishan amma ya kasa bata amsa duk ya ruɗe shi tsoron shi bai wuce kar yayi lossing babyn shi ba sai ga hawaye wanda ya dasa wa big sis tausayin sa a zuciyar ta dan haka ita ta karɓi car keys ɗin ta miƙawa mijin ta akan yayi driving ɗin su zuwa asibiti ya karɓa suka tafi zuwa babbar asibiti wato national hospital Abuja inda aka yi emergency room da ita sai zirga zirga yake yi a kofar emergency room ɗin duk ya gama fita a hayyavin shi sai da big sis ta riƙe shi ta zaunar da shi haɗe da kwantar da kan shi a kafaɗar ta tana rarrashin sa kamar ƙaramin yaro dan kuka ya ke yi babu ji babu gani sosai Dr Abubakar ke bashi maganganu masu daɗi da sanyi kusan awa biyu da mintuna ashirin da biyar aka ɗauka a emergency room ɗin kafin babban likitan ya fito ai ko kamar jirar shi yake yi da fitowar shi ya yi hanzarin ƙarasawa gare shi ya fara tambayar shi

"Dr my wife,our baby how are they"?? Da fari likitan ya so yayi scolding ɗin sa sai kuma ya ga yadda ya birkice sai ya fasa ya kirawo shi zuwa offishin sa dan yana so ya sami natsuwa bayan sun shiga ya bashi wun zama sannan ya miƙa mai bottle water wai ya sha kallon ruwan yayo kafin ya ce mai

"I don't need water i want to know the current health situation of my wife and our baby"!! a ɗan dame yayi maganar sai likitan ya kalle shi da kyau

"Your wife,has she been on a bed rest instructions"?? Saurin girgiza mai kai yayi

"Then me yasa ka bar ta ta tsallale ƙaidar likita"? Kasa bashi amsa yayi shi dai kawai ya ji ya ce mai matar shi da babyn su na cikin ƙoshin lafiya

"Well minor abu ne da ya kusan zama babba ba dan kun kawo ta da wurwuri ba da damage ɗin sai ya fi haka,, yanzu dai mun mata cervical circlage wato an mata ɗaurin mahaifa har sai ranar da zata haihu kafin a kunce ɗaurin dan hakan ne kaɗai zai taimaka maku dan kar ku rasa babyn ku because the baby is suffering from so many distresses already dan haka dole za mu riƙe ta a nan in kuma kana ganin akwai inda zaka kai ta inda ba za ana damin ta dayawa ba fine in ta farfaɗo sai a tafi da ita brcause yawan bugun zuciyar da take experiencing ya sa har ya fara affecting cikin ta wanda yake ta barazanar dissolving gradually a kiyaye dokokin farko da aka baku dan saving wannan precious baby ɗin da fatan ka fahimata"? Idanun shi duk sun yi luhu luhu ya amsa da
"Eh na fahimta Dr kuma mun gode"Allah sarki gwanin tausayi haka ya koma actually he was happy komai haa come to end amma bai yi yi tunanin celebrating happiness ɗin a wannan halin ba da rayuwar matar shi da unborn baby ɗin su ke cikin wasi wasi ba.

Ko da ya koma gun su big sis explaining komai ya masu a inda suka yanke shawarar tafiya da ita gida kawai in ya so sai a ɗauko special permanent domiciliary nurse da zata rinƙa kula da ita har ta haihu a kan wannan shawarar aka tsaya.

Zaman jiran farfaɗowar ta suka koma yi yayin da shi kuwa ya shiga ɗakin hutun da aka kai ta ya zauna haɗe da tsura mata ido yana mai jin tausayin ta dan ya san ba abu mai sauƙi bane a gare ta a ce babbar aminiyarta ta kasance mai yaƙin ganin downfall ɗin ta it wasn't easy for all of them sai tunani yake ta yi jin turowar ƙofar ɗakin ya sa yayi saurin goge hawayen da ya silalo mai ya juya dan ganin wanda ya shigo..

Salma ce da ummi wace sai kuka take yi tana mai jin tausayin yayar ta matsowa kusa ta yi ta tambayi lafiyar ta ya ce mata da sauƙi ya mata bayanin anin da likitan ya faɗa sai ta daɗa fashewa da kuka tana cewa
"Ai ni na san yaya Aisha ba saurin fushi ne da ita ba amma sai da wannan annobar ta tura ta bango yanzu in na ja mata Allah ya isa ina da laifi"? Tana maganar ne tana kuka saurin girgiza ta salma ta yi dan ita kanta ba a hayyacin ta take ba
"Me kuma na Allah ya isa ummi baki ga hukuncin da aka yanke mata bane?you should forgive her she is going for good"itama dauriya kawai take yi dan har lokacin furucin alƙalin ke mata yawo a kunne inda yake cewa an yankewa falmata hukuncin kisa kuka take ta yi har dai ta fita dan kar ta tayar da Aisha

Jikin shi sai yayi sanyi ƙalau shi sai ma a lokacin yake tuna judgement ɗin alƙali sai kuma ya ji tsausayin falmata ya kama shi mai tsanani dama haka duniya take in ka yi mai kyau ka gani in akasin haka ne ma duk zaka gani.

Su aunty mama ne da maman salma suka shigo ɗakin wanda yayi sanadiyar tashin shi ya bar ɗakin ya basu wuri aunty mama kam ta rasa yadda zata yi tashin hankalin ya mata yawa close family friends kawai aka bari su gan ta ko da su Ahmad da su safwan abokan aikin ta suka zo ba'a bar su sun shiga ba dan tana buƙatar hutu mai tsayi dan haka fatan samin lafiya suka mata suka tafi a kan zasu dawo in ta ware ba laifi dija ta kawo mata ziyara sai dai still tana bacci bata farka ba dan ita ta sanar da su safwan abin da me faruwa kasancewar kiwannen su ya mallaki ma'aikatar kan sa sun daɗe da rabuwa da kamfanin M Motives suma suna da na su sai dai lokaci zuwa lokaci sukan yi colliding in wani aiki ya kama wanda zai amfane su sai su haɗa hannu tare su yi.

Ba ta farfado completely ba sai second day ɗin ta a asibitin around 10pm wanda da kuka ta farfado dan ta saka abin a ran ta shi kadai ke ɗakin a lokacin da ta farfado ɗin dan haka miƙewa yayi a sittin ya nufe ta ya shiga rarrashin ta yana ƙokarin hana ta yin kukan dan ya san abin ya mata nauyi da yawa tana kujan ta tambaye shi

"Hubby ina take ina falmata"? Shima cikin mutuwar jiki ya bata amsa da
"Cutie she is gone almost 27hours ago"

Sabuwar kuka ta fashe da shi ta faɗa jikin shi ta shiga raira kuka mai tsuma zuciya encouraging ɗin ta ya rinƙa yi har dai ta ɗan tsagaita da kukan ta ɗago tana Kallon shi cikin ido

"Hubby shikenan ta tafi ba zata dawo gare mu ba kuma?itama ta tafi inda Ammahn mu ta tafi kenan ba zan ƙara ganin ta ba"?? Girgiza mata kai yayi yana share mata hawayen da ke zirarowa daga idon ta sai ta kuma tambayar shi

"hubby ai na yafe mata ko"? Ganin duk a ruɗe ta ke alamun har yanzu bata gama recovering daga state of shock ɗin da ta shiga ba saurin haɗa jikin su yayi ta yadda ba zata sami damar yin wani mutsu mutsu mai ƙarfi ba kuka take yi sosai sai da ta yi mai isar ta sannan ta yi lamo tana furta

"Ya Allah ka gafartawa aminiya ta ka sauƙaƙa mata ka ji ƙan ta da rahamar ka ya ar hamarrahimin"ta ida tana fitar da silent tears daga haka bata kuma furta komai ba sai numfashin ta da ya ƙaru leƙa fuskar ta yayi ya ga bacci ne ya sace ta dan haka gyara mata kwanciya yayi ya fita ya sanar da Dr cewa ya basu sallama zasu tafi gida...

Back at the court kuwa kuka kabir yayi sosai ko babu soyayya a auren shi da matar shi akwai kyakyawar shaƙuwa ta aure da ya shiga tsakanin su wanda ya saka shi jin tsananin kewan ta tun a lokacin haɗe da ba ma kanshi laifi akan halin da ta shiga wanda ya fi ƙarfafa laifin ga kanshi akan cewa da ya mata uziri da duk hakan bai faru ba,ranar ta kasance mai rana mafi duhu a ranakun rayuwar shi amsar ƙaddarar shi yayi ya koma gida haɗe da rungumar ɗan shi yana kukan rasa matar sa da yayi wanda rashi ne na har abada tsakanin shi da ita kuwa sai dai addu'a..
°°°°°°°°°°°°°°°°°°

_5months later_

Alhamdulilah komai yayi ma families ɗin daidai dan a yayin da cikin Aisha ya shiga watanni takwas sai girma yake yi wanda mutum zai yi tsammanin ko ƴan biyu ne amma ba hakan bane dan kuwa single viable fetus take ɗauke da shi a jikin ta kukawa da jin daɗi babu wanda mijin ta bai bata dan ma ayyukan sun mai yawa ga nata ga nashi duk shi ke running businesses ɗin na su saboda he tries as much as possible as he could to strike a balance tsakanin aikin shi na office da duties ɗin shi as a responsible husband and a father to be.

Domiciliary nurse ɗin da ke kula da Aisha na iya ƙoƙarin ta wurin ganin ta cika dukkan ƙa'idojin kula da complicated pregnant mother wanda hakan ya sa Abdulrahman sakar mata amanar matar shi a yayin da baya nan.

Big sis na sauke responsibilities ɗin ta na babbar yaya wace ita kaɗai ce uwa kuma uba ga ƙannin na ta ta koma bakin aikin ta na ma'aikaciyar gidan talabijin kuma tana jin daɗin hakan because she have passion for her career wanda kuma mijinta wato Dr Abubakar yana matuƙar kula da ita kuma baya nuna mata tsangwamar wai dan bata haihu da shi ba shikenan babu sauran nutuncin ta a idanun sa he believes that komai nufin Allah ne kuma dan adam bai isa ya bama kan sa abin da ubangijin sa bai ba shi ba dan haka bai cire ran samin zuri'a da kamilar matar sa Asiya ba ita kan ta abin na damin ta sai dai ta san duk yadda ya dame ta bai kai yadda ya dame shi ba amma daidai da rana ɗaya bai taɓa nuna mata ba toh dan me ita zata tunzira shi she once gave him the advise of taking in a second wife maybe Allah ya sa a dace a ranar ƙaurace mata ne kawai bai yi ba dan ya san damuwa ce ta saka ta yin hakan amma kam ta ga ruwar masifar da bai taɓa yi mata shi ba sai daga baya kuma ya shiga bata haƙuri kafin su sasanta da sharaɗin ko da wasa kar ta ƙara kawo irin wannan shaiɗaniyar tunanin a ran ta dan shi dai as far as he is concern he is created just for her ba dan wata ba.. At times takan zauna tayi nazari da tunanin me tayi da Allah ya bata miji irin wannan mai gudun ɓacin ran ta wanda ta san da wasu ne shekarun su na goma shashida kenan da aure da ya auro mata kusan huɗu ma ko tunda in dai kuɗin ne yana da shi in kyawu ne da ilimi duk Allah ya hore mai sai dai bai kasance ɗaya daga cikin masu aƙidar ba godiyar ta ga ubangijin ta ba mai ƙarewa bane dan ya azurta ta da abin da ko kuɗi bai isa ya bata ba in-laws ɗin ta are very nice to her babu alamun nuna damuwa akan ta wai dan ta daɗe bata haihu ba they always make her feel important wanda hakan ya sa take bin su da addua'a da fatan alkhairi.

Ƙannen ta na bata girman ta na babbar yayar su haka ma matan su ƴaƴan su kuwa sai dai weekend ko vacation bai zo ba amma yaran nan a gidan ta suke yin shi itace mamar su ita ce baban su ita ce baabar su tana matuƙar ƙaunar yaran dan jinin ta ne jinin ƙamnen ta ne wanda in ba dan haka ba da bata da ikon yi ma ƴaƴan wasu Alhamdulilah ta gode ma Allah ko yanzu ta bar duniyar ta san tana da masu yi mata addu'a because the bond is very strong..

Kusan duka delivery preparation ɗin Aisha ita ta yi shi sai dai waɗanda ba za'a rasa ba wanda Aishan da mijin ta kan yi ta online tunda babu damar fita yawo da yawa..

Ummi ƙanwar Aisha kuwa Allah ya azurta ta da wani kyautar dan a halin yanzu ciki ya fara bayyana wanda yake kimanin watanni huɗu da ɗoriya yayin da yaya Ibrahim ɗin ta ke ɗoki da azarɓaɓin cikin wanda ya sa aunty mama taka mai burkin kusantarta tun da itama an gindaya mata sharruɗan zama lafiya da cikin..

Abbu babu abin cewa sai hamdala with his two blessed kids da Allah ya azurta shi da su ya sami farinciki rayuwa wanda a da yake ganin ba zai taɓa samu ba sakamakon rasa natsatsiyar matar shi Farida with hajiya Nafisa aunty mama in his life presently he feels that his world is complete dan jinkirin shi ya zame mai alkhairi.relationship tsakanin shi da Alhaji Habib sai abin da ya ƙaru dan sun gane cewa haɗuwar su daga Allah ne wanda ƴaƴan su ne sanadin silar haɗuwar ta su haka ma matayen su na maintaining good relationship kamar yadda mazajen su ke yi ciki kuwa ba su bambanta mahaifiyar falmata ba dan sun cigaba da kyakyawar hulɗar su ta matan abokai da kuma iyayen ƙawayen ƴaƴan su..

Yayin da Aqeeb da matar sa wato mufeedah ke da arziƙin ƴaƴa uku dan na farin ƴan biyu ne duka maza ƴan shekaru huɗu a duniya sai macen da ke da shekaru biyu a duniya wacce suke kira da nabila..

Kabir na ƙoƙarin dauke ɗawainiyar ɗan sa mai suna Hakim wanda yake da shekaru biyu a duniya kusan kan su ɗaya da nabila ɗiyar Aqeeb yaron natsatse ne bai da hayaniyar yara ƴan shekarun sa dan babu inda ya rago mahaifiyar sa tun daga kamannin har ɗabi'ar wato kamewa da natsuwa most of the time mahaifin shi kan tasa gaba ya rinƙa kallon shi yana share hawaye dan tsananin kamannin shi da mahaifiyar shi da fari yaron na yawan kuka da tambayar inda mamar shi ta tafi sai daga baya kuma ya daina ganin ko yayin ba amsa shi ake yi ba har school aka saka shi yana play class shi da nabila yakan zauna a gidan grandparents ɗin sa wasu lokutan kuma yakan yi ma Abban shi kwanaki kafin ya koma gidan granny ɗin sa.. tun umma na mai maganar lallami akan ya yi aure saboda tarbiyar ɗan shi yana share maganar har dai ta koma yi mai cikin zafi wanda ta saka shi tilast ƙauracewa zuwa gidan ta sai da Abba ya mata faɗan abin da ta mai ya nuna mata ba'a takurawa namiji especially shi da ke da past heartache ta bar shi har ya sauko ya zaɓo zaɓin shi dan haka ta kirawo shi ta ba shi haƙurin strictness ɗin da ta nuna mai haɗe da bashi goyon bayan zaɓo duk wacce yake so ya kuwa ji daɗin saukowar mahaifiyar ta shi sai dai bai san ta yadda zai faranta mata ba dan shi har lokacin bai ga macen da ta kwanta mai ba but he is still praying for God best to come his way..

Hajiya salma da mijin ta kuwa Barrister Umar mai nasara kamar yadda jama'a suka laƙaba mai tun bayan shaida cases ɗin da yayi handling few months back suna zaune luɓus a gidan su ɗiyar su mai shekara ɗaya da watanni kusan bakwai na samin kulawa da tarbiya dan a ko da yaushe in salma ta kalli yarinyar fuskar aminiyar ta ke dawo mata babu inda ta baro ta shi yasa in suka haɗu da Hakim suna wasa takan kalle su in admiration takan masu hotuna kala kala in suna wasan su ba amsu san tana yi ba dan jinin su ya haɗu da juna ko sauran cousins ɗin su are not as close to them as the two are Allah ne ya haɗa jinin su fatan salma bai wuce ta ga ranar da ta haɗa ƙaƙƙarfar relationship tsakanin su ba dan ta ɗau alƙawarin cigaba da gina incomplete relationship ɗin da falmata ta bari alƙawari ne wannan wanda yake ajiye a rubuce ko da wasa bata taɓa revealing ma mijin ta intention ɗin ta ba sai dai tuni ya gano ta dan shi ɗin kwararren alƙali ne mai saurin fahimta sai dai ya bar wa kan shi in bai so a sani ba dan haka shima ya rinƙa taya ta rainon alƙawarin nata ba tare da sanin ta ba dan shima yana son ya ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ahali biyun..

A ɓangaren su granny kuwa har yanzu dai sun ƙi yarda su dawo kusa da jikokin na su suna nan a Lagos ɗin su sai dai a kai masu ziyara kuma suna bin jikokin nasu da addu'a kyawawa ɗa ɗaya Allah ya azurta su da shi wanda ya bar duniyar amma ya bar kyawawan reshen da ya shuka wanda su ne ke ta multiplying suna ganin su suna jin daɗi dan dai dangi da ƴanuwa da ke garin membila ba duka aka gama sabawa ba sai dai dan family ne lokaci zuwa lokaci akan haɗa family function na sanin juna wanda ta nan families ɗin ke ƙara ƙarfafa bond ɗin su sai dai still they were born and brought up there so they find it difficult to leave there dan haka babu wanda yayi gigin barin membila sai dai alkhairi kam ba'a magana dan suna samu daga wun ƴanuwan su na jini babu tsangwama ko hantara sai daraja juna da mutunta juna wanda yayi creating good rapport a tsakanin families ɗin abin da grandpa ya so yi kenan tun ɗan shi Arch Abdulsalaam na da rai sai dai hakan ya yi mai wuyan yi but now with the present trends da yayi adopting na haɗa family function ɗin nan komai ya daidaita sai dai godiyar ubangiji..

As for dija she is moving on with her life smoothly babu hallayar da na rashin ji da shaye shayen kayan calming mood da takan ɗan taba a baya her businesses and career are more important to her than shiriritar ƴan matan zamani because she learnt alot ftom Aisha's experience ba ta fatan hakan ya faru da ita a rayuwar ta dan haka ta kama kan ta time to time ta kan kai ziyara gidan yayan ta wasu lokutan har werkend takan yi masu a chan kuma suna jin daɗin hakan sai dai maganar rashin sauraron ko wani saurayin da take yi yana damin su hatta ga iyayen ta sai dai ba ɗabi'ar su ba ce takurawa ƴaƴan su dan sun tsumu da boko ba laifi amma har da haka mahaifiyar ta is disturb dan sau biyu tana samin yayyen dijan da maganar ko sun haɗa family meeting a kan ta ƙarshe ba a wanyewa da wani kyakyawar sakamako dan ita dai amsar ta ɗaya ce "on Allah ya kawo mijin auren ai ba zan ƙi kawo shi gare ku ba"da haka aka zuba mata idanu kawai dan lamarin nata sai ita ta yi committing rayuwar ta da time ɗin ta ga aikin ta about relationship da friendship ɗin su da Aisha kuwa an sami chanji dan takan yi visiting ɗin ta sukan yi waya akai akai wanda hakan ya fara rufe rift ɗin da ke tsakanin su..ganin bata da niyar fidda mijin aure gashi kuma shekaru na ja dan ta kai ashirin da shida kuma ba baya take komawa ba dan haka sai yayan ta ya nemi alfarmar haɗa ta da Dr kabir kasancewar suna aiki wuri ɗaya kuma wani lokaci ta kan kai ma yayan nata ziyara sukan haɗu a chan toh dama akwai mutunci a tsakanin su kasancewar first love ɗin ƙawar ta Aisha kuma sun ɗan san juna a baya kafin yanzu sai suka ɗan saba dan har gajeruwar hira na haɗa su ganin haka sai Dr Abubakar ya ga kawai ya mata mai gabaɗaya muddin Dr kabir ɗin zai amince toh itama haka zata haƙura da haka ya sanar da matar sa shirin sa sai ta nuna mai kar ya mata tallan ƙanwa ita bata yarda ba amma da yayi convincing ɗin ta ya nuna mata dalilan shi sai ta amince ta yi fatan Allah ya sa ita khadijar ta yarda toh fah shine ya je har gida ya kai ma Dr kabir ɗin ziyara ta musamman a inda kafin ya tafi ya shaida mai manufar sa surprisingly sai ya ga ya amince babu gargada ya mai godiya ya koma gida ya sanar da matar shi ta yi murna sai dai fah ita inda gizo ke saƙa ne matsalar ta wato uwar gayyar ko zata yarda oho dan haka sai da suka tsara kalaman da zasu sanar da ita kafin su fuskance ta da maganar amma me? haka itama ta yarda kai tsaye babu gargada abin ya ɗaure masu kai sai dai sun yi farinciki at least itama zata yi aure ta fara haɗa nata family ɗin they were happy but unknown to them cewa dama chan ƙanana ƙananan hirar da ke gudana tsakanin dija da kabir ɗin ya saka sun ɗan fara shaƙuwa da juna sai dai basu yi confessing ba wanda kaɗan kaɗan abin ya rikiɗe ya koma so but still they weren't ready to confess until lokacin da aka same su da maganar sai daga baya masu haɗin suka gano hakan sun kuwa yi murna dan a da har suna tsoron kar alkhairin da suke niyar haɗawa ya janyo matsala..babu wanda ya kai iyayen su jin daɗin wannan lamari dan haka babu wano doguwar janjani aka yi magana a inda magabata suka shiga lamarin a halin yanzu kam biki ya rage saura watanni biyu cif cif a ɗaura shi wanda an yi haka ne dan du ƙara fahimtar junan su sosai Aisha ta taya ta murnar wannan babbar al'amari da ya same ta.

Kwatsam ana zaune sai ga big sis da ciki wanda babu wanda yayi tsammanin shi dan kowa ya cire ran zata haihu a wannan lokacin daɗi bisa kan daɗi kenan ko da Dr Abubakar ya gano hakan azumi na musamman yayi dan nuna godiyar shi ga Allah swt mai bayarwa a sanda ya so mai azurta bawan sa da rahamar sa ba tare da sanin bawan ba wanda duk kuɗin bawa bai isa ya bawa kanshi ba sai mai yi ma kowa ya bashi,,kukan farinciki bai ƙauracewa idanun big sis she never expected it amma sai gashi haƙurin ta ya janyo mata ni'imar ubangiji ashe dai itama zata zama uwa wacce za'a rinƙa kira da mama bata gajiya da yi wa Allah godiya da wannan babbar kyautar,su Abdulrahman uncle ɗin unborn sai rawar kan shi ma ya fi wanda yake yiwa cutie ɗin shi da unborn ɗin ta he can't just believe that his one and only big sis is gonna become a mother Alhamdulilah he is happy for her..

**********************

Dawowar shi daga office kenan ya tarar tana baccin gajiyar minor exercise ɗin da nurse ɗin ta ta saka ta yi murmusawa kawai yayi dan ya lura yanzu da ta shiga watar haihuwar ta wanda a lisaffe EDD ɗin ta ya faɗa ne a 4/10/19 sanyin jikin ta yayi yawa bacci bai mata wuyar kamu kuma shi a yau da begen ta ya dawo gidan dan yana jin displaying love da matar shi dan haka bai ma bari ta san ya dawo gidan ba ya wuce yayi wankan shi ya shige ɗaya part ɗin gidan da suka yi fake honeymoon a ciki ya shiga gyara babu ji babu gani har sai da ya ga atmosphere ɗin is conducive mashi sannan ya wuce part ɗin su it was already 6:47pm dan haka any moment from then za'a kira sallar magrib dan haka tayar da ita ya shiga yi ta hanyar da ya saba wato kwanciya kusa da ita ya rinƙa goga hancin sa a wuyan ta ta hakan ne kaɗai take tashi cikin lokaci kuma da ta juya ta fi so a ce da shi ta ci karo laying next to her abin da ya matan kuwa kenan sai gashi ta fara buɗe idanun ta ta sauke su kan charming cat eyes ɗin sa murmushi suka sakar wa juna

"Hubby har ka dawo kenan i wanted cooking your favourite sai dai baccin nan ya fi ƙarfi na wallahi so sorry"faɗaɗa murmushin sa yayi kafin ya ce

"Ummu Asiya kar ki damu matuƙar ba ke ce ke buƙatar in aikata miki wani abin ba bana so ki rinƙa yi min wasa da kafiyar ki and our baby too humm"?? Ɗaga mai kai tayi alamun ta gane dan haka sai ya taya ta tashi duk ta kumbura ko ta ina tafiyar ma da kyar take yin shi dan ko ɗan gajeruwar zama ta yi sai ta yi bayani dan haka in ta kwanta bacci da kyar ake tashi.

Taya ta alwala yayi ya shimfiɗa mata sallaya ya zaunar da ita dan yanzu sai a zaune bata iya yin sallar a tsaye hijabi ya saka mata ya ce bari ya je ya dawo ta mai Allah kiyaye hanya ya sakar mata side cheek peck sannan ya fita ita kuma ta fara sallar ta.

Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i wanda yana dawowa ya shiga chanza mata kaya ita dai tana kallon ikon Allah dan bata san inda zai kai ta da wannan tulelen cikin nata ba ta yi shiru har ya gama saka mata red maternity gown wanda ta ke free a ciki babu takura ya barbaza mata suman ta ya taje shi tsaff tana bin shi da kallo har ya gama shafa mata powder ya goga mata matte red lipstick sanna ya yi complimenting ɗin ta ya roƙe ta da ta bashi 5 monutes he will be back ta ce mai sai ya dawo ya tafi ya shirya shaf shaf cikin red suite mai ɗaukar hankali kalar exactly irin kayan ta ya shirya tsaf ya fito a Abdulrahman Abdulsalaam ɗin sa cikin hanzari ya dawo ɗakin ta sai bin shi da kallon mamaki take yi har dai ya magance mata mamakin nata ta hanyar ɗagata a hankali ya mata side hug ya ƙi sakin ta ta balcony ɗin back door exit suka fita tana son tambayar shi amma ya hana ta tambayar dan haka ta mai shiru kawai tana baza ido dan ganin inda zai kai su.

Basu tsaya ko ina ba sai a garden ɗin part ɗin wanda ya sha gyara da red roses ta ko ina zuzzube a ƙasa ga candle lights nan ya haska ko ina wurin bai fiye dyhu ba haka ma bai fiye haske ba so cool and silent gefe ga table da two chairs table ɗin na ɗauke da cups biyu haɗe da champaign sai wasu wrapped snacks da aka yi masu wasu ado da ƙyal ƙyal masu kyawun kallo

She was speechless dan haka ta kae shi ta sakar mai murmushi tana mau cewa
"Thank you hubby you are too gentile"shima murmushin ya mayar mata da shi kafin ya tambaye ta
"Did you like it"?? Ta mai irin surprise look ɗin nan kafin ta ce

"I don't like it i love it"daɗi ya ji sosai ya saka cutie ɗin sa annashuwa dan haka ya ce mata
"Shall we"? Ta murmusa haɗe da jijjiga mai kai sakin hannun ta yayi ya tafi ya kunna masu Bluetooth ɗin da ke wurin yayi regulating sound ɗin daidai yadda su zasu ji abin su.. sautin kiɗar wakar shahararriyar mawaƙiyar nan ne ya fara amo wato Celine dion a waƙar ta mai take _"My heart will go on*_

Dawowa yayi cikin natsuwa ya ɗaga hannun ta a hankali ya ɗora a kafaɗar shi shi kuma ya kai ɗaya hannun shi kan waist ɗin ta yayi grabbing ɗin ta firmly and gently ɗaya hannun ta kuma ya haɗa da nashi suka fara takawa kaɗan kaɗan suna bin waƙar sau uku yana juya ta sai su sakarwa kan su murmushi kawai su cigaba haka suka rinƙa yi har tsawon lokaci kafin su zauna su ɗan taɓa abin da ke kan table ɗin cikin ƙauna da son juna suka enjoying night ɗin daga ƙarshe ya ɗauke matar sa ya shiga da ita cikin bedroom ɗin inda nan ma duk romantic arrangement yayi rose flowers ta ko ina ga romantic bed sheet bai sauke ta ko ina ba sai kan gadon tmya taya ta cire kayan shima ya cire nashi loss nightie ya saka mata shima ya saka night wear ɗin shi suka shige cikin blanket rungume da juna bacci mai daɗi yayi gaba da su basu farka ba sai washegari a inda bayan sun idar da sallar asuba suka koma baccin har sun yi nisa amma kuma sai me?? Wani irin azababen rhythmic uterine contractions suka saka Aisha gaba ta shiga jiyi kamar zata sauka a gadon a son ta ta bar shi ya huta amma inaa juye juyen ta ya sa ya farka ganin halin da take ciki ya sa shi miƙewa a 360 yana tambayar ta

"Cutie are you in labour"?? Bata bashi amsa ba sai wani irin muguwar damƙa da ta kai mai wanda ya saka shi ruɗewa yayi saurin sauka daga gadon ya shiga nema mata kayan sakawa da sauri ya dawo ya saka mata doguwar riga ya saka mata hijabi shima ya chanza zuwa kayab mutunci yayi saurin dawowa gare ta yana mata sannu car keys ya bincika yayi nasarar samin wani wanda tsabagen ruɗewa bai bar shi ya san na wacce mota ya ɗauko ba ɗaukar ta yayi suka fito har car park lot ɗin a nan ya rinƙa danna key ɗin har yayi nasarar gano motar cikin hanzari ya dhogar da ita gidan baya ya shiga motar ya fusge ta a tsiyace yana gudu yana mata sannu har suka iso asibitin inda ya shiga da ita a rikice yana kiran sunan nurses ɗin wurin da sauri aka taimaka mai aka karɓeta zuwa ciki inda aka mata emergency dressing zuwa kayan masu haihuwa ya so shiga ciki amma suka bashi haƙuri dan haka ya tsaya a waje yana ta zirga zirga basu yi planning haihuwar ta a nan ƙasar ba a ƙasar Dubai suka yi booking delivery ɗin ta sai dai gashi kafin lokacin haihuwar ya kai har labour ya kana ta a lissafin su saura almost a week + ta haihu yana ta addu'oin da ya zo mai a haka wata midwife ta leƙo ta ce mai ina kayan baby sannan ya ce mata ya baro su gida dan haka ta saka shi komawa ya ɗauko ta lissafa mai abubuwan da zai taho da su da sauri ya kuma figar motar ya koma gida sai a nan ya tuna cewa kayan babyn gabaɗaya na wun big sis dan haka ya danna mata kira karfe 10am dan haka basu tashi daga baccin ba kasancewar weekend ne kiran shi ya tashe ta ta yi saurin ɗauka a nan yake gaya mata cutie is in labour suna asibiti wuf ta tashi mijin ta ta sanar da shi ko wanka bata bari sun yi ba suka haɗa kayan suka kamo hanya shi kuma sauran abubuwan ya kwasa ya koma kusan tare suka isa asibitin shiga suka yi gabaɗaya aka mikawa midwife ɗin kayan yana juyawa ya ji ihun ta ai a sittin ya juya ya bankaɗa ƙofar ya shiga sai ganim shi suka yi a gefen ta sun yi sun yi ya fita ya ƙi fota dan haka suka kyale shi sai hura mata iska yake yi yana sannu tare suka yi labour ɗin tana ihu yana ce mata sannu in zafin ya ragu sai ya saka ta yin addu'a tana cikin yi kuma sai ta ida da ihu dan azaba a taƙaice sai da suka ɗau awa ɗaya da rabi a labour room kafin Allah ya taimake ta ta yi pushing wata ƙatuwar bouncing baby girl wacce ta shigo duniyar da ƙarfin ta ɗayar midwife ɗin ta amshi babyn ta tafi gyarawa ɗayar kuwa ta shiga ɗinke ta dan ta sami bilateral tear the baby is very huge ko da ɗayar midwife ɗin ta gama weighing babyn ta juyo ta ce
"The baby weigh 5.4kg"sai exaggerating suke yi wai babyn is healthy yana wurin aka gama ɗinkin aka gyara ta haɗe da babyn su aka shigar da su observation room akan bayan 2hours of monitoring in babu komai sai a sallame su gida sai a sannan ya rungume babyn shi yana share hawayen farinciki yayin da ita kuma mai jegon ke baccin ban gajiya addu'a yayi mata ya mata huɗuba da sunan Asiya sannan ya fito waje da babyn a kirjin shi rungume yana share hawaye how he wished his parents are alive to see their grand daughter his own blood da sauri big sis ta iso gare shi haɗe da karɓar babyn wacce ta kwaso kamannin Abban ta sak sai dai hasken fatar na maman ta ne sai yaba babyn ake ta yi daga nan fah gari ya ɗauka the great painter matar world best painter kuma Architect ta haihu ta haifi bouncing baby girl dan tuni aka ɗau hoton babyn a waya aka yi uploading ɗin shi a social medias sai ga jama'a ana ta kiran familyn ana ta masu congrats

Su aunty mama an zama granny da su Abbu sai washe haƙora ake ta yi 2hours na cika bau bari an ƙara mintuna ba ya ce za su tafi gida dan haka suka rankaya suka dawo gida da sharaɗin zata na yin sitz bath saboda suturing da aka mata a gidan ma ba'a bar ta ta huta ba sai tururuwar jama'a babyn kan ta ba'a bari ta gani ba sai da ta ɗau kwanaki uku kafin ta sami natsuwar kallon babyn ra tsaff da abin da ke haɗata da babyn breastfeeding ne da zarar ta gama sai a tafi da ita wun jama'a kuma da dare yayi baccin gajiya take saurin yi.

A haka ranar suna ta zagayo aka raɗa ma baby sunan ta wato Asiya inda big sis ta rasa inda zata saka kan ta dan murna da jin daɗin karan da ƙannen nata suka mata.

Bikin suna yayi albarka MashaAllah sai dai fatan samin inganttaciyar rayuwa..

Kamar wata ɗaya da rabi da haihuwar babyn aka yi bikin dija da kabeer babu daɗewa hasina ta haifo baby boy ɗin ta very healthy families ɗin were very happy da ƙaruwar arziƙin da suke ta samu..

*******************

_5 years later_

Wata astonishing cute baby girl ce ƴar kimanin shekara huɗu da watanni sanye cikin baby pi nk top da blue jeans trouser kan nan ya sha parking a tsakiyar kai da ribbon pink colour ta sauko cikin rigima da iyayi irin ta yara tana ta ƙunƙuni tana cewa

"Umma,,,,umma"!!! Wacce take kira da umman na zaune tana abu a cikin tablet wanda da gani abu ne mai muhimmanci amma fitinar yarinyar ya hana ta bada full attention

cigaba da kiran sunan ta yi
"Umma,,ummah,,umma"ta ida tana mai girgiza umman aiko a harzuƙe ta ɗago ta ce

"Wai hibba uban me ke damin ki ne yau ɗin nan haba dan Allah kin ƙi bari na in ƙarasa abin da nake yi tun ɗazu sai fitinata kike yi me ke damin ki ne wai"?ta ida tana mai daka mata tsawa ai ko sai yarinyar ta fashe da kuka sai kuma ta bata tausayi sai ta ɗan rage murya ta ce

"Toh zo nan hibba gaya min me ke damin ki ta faɗa tana jan yarinyar jikin ta aiko yarinyar ta fincike tana cewa

"Umma tambaya ta kike me ke dami na bayan tun ɗazu nake ta miki magana kika min banza"!! Ta cigaba da kukan ta sai ta saka umman nata dariya ta ɗan dara dan in da sabo toh ta saba da halin rigimar hibba yarinyar akwai daru sai dai akwau ta da tausayi tana ƙanƙanuwar ta amma ta san in maman ta tana cikin damuwa ta tambaye ta in ma abinci ne bata ci ba saboda ayyuka sun mata yawa itama sai ta ce bazata ci ba sai mahaifiyar nata ta ci abincin kafin itama ta ci..

"Haba baby na yi haƙuri ayyuka ne suka min yawa kin ji forgive your umma"share hawayen ta tayi dama she just wanna get her mom's attention kuma ta samu ɗin

Yarinyar da bata da maraba da mahaifin ta hatta da cat eyes ɗin wanda ke saka umman ta tasa ta gaba tana kallo saboda fuskar mijin ta da ke dawo mata buɗe baki yarinyar tayi ta ce

"Ummah bread na ke jin ci wallahi ki ce ma momma Karin ta raka ni mu siyo kin ji"?? Dama ta sani babu wani abu mai muhimmanci da zata faɗa sai shirme in ba haka ba bread na nan a kitchen kamar zai ci kan shi amma tsabaragen fitinar Hibba ya sa take son dagula mata lissafi"

Haɗe fuska ta yi ta ce
"No hibba you are going no where koma ciki akwai bread ki ce ta baki ki ci bana son rigima"aiko yarinya ta saka ihu wai an hanata cin bread

Saukowar shi kenan daga staircase ɗin ya ga tana kuka a guje ya ƙarasa saukowa ya nufe ta yana cewa

"Sweetheart me ya faru wa ya taɓa min ke halan"?? Duk ya birkice ganin haka sai ta rage sautin kukan banzan da take yi ta ce

"Ummah ce na ce ta sa a raka ni in siyo bread amma ta ƙi"cikim shagwaɓa ta karasa maganar sai ya juyo yana kallon ta ya haɗe rai ya ce

"Cutie me yasa kika chanza ne da yawa yanzu wai?babu halin yarinyar nan ta zauna tun safe har dare a gidan nan ba tare da kin taɓa min lafiyar ta ba directly or indirectly also emotionally me ya sa kin san she is my big sis my blood amma kike mata haka"?? dariya kawai ta masu ta yi gaba abin ta dan haka suke haɗe kai su rinƙa guma mata wai dan ta ji haushi..takawa take yi a hankalo saboda yanayin jikin ta dan tsohon ciki ne da ita yayi saurin dawo da ita baya yana cewa
"Cutie am not done talking"kallon shi ta yi kafin ta ce

"Hubby am tired i need to rest please"daga haka tayi gaba abin ta ta bar ɗiya da mahaifin ta suna ta gulman ta wai wannan cikin ya sa duk ta zama masifaffiya dakatawa ta yi kaɗan ta juyo su kuma suka yi saurin yin shiru kamar ba su ke gulmar ta ba yanzun nan kallon su tayi tsaff ta girgiza kai tana murmushi kafin ta ce

"And ki koma ciki ki ce ma karine ta baki abincin ranar ki ki cigaba da ci bana son surutu dan bacci zan tafi yi"
Daga haka ta cigaba da tafi amma sai muryar hibba ya dakatar da ita

"Toh ni wani abinci aka bani?babu wani abincin da aka bani ummah"ta faɗa tana pouting bakin ta so cute and lovely banza ta mata ta cigaba da takawa abin ta ta bar su a nan..

**********

_17years after_

Juyawar ta yayi daidai da ajiye mata table ɗin breakfast ɗin ta a kan gadon miƙa tayi tana murmushi kaɗan

"Good morning wify how is your morning"? ta ƙara murmusawa sannan ta bashi French kiss ta ce

"Just like this"murmushin gefen baki yayi ya ce
"Good toh tashi ki ci breakfast ɗin ki"miƙewa ta yi ta zauna ya rinƙa feeding ɗin ta cike da ƙauna har ta gama ya goge mata bakin ta kafin ta sauko daga gadon ta nufi hanyar toilet tana ce mai

"Thanks for the breakfast Humair"sunan da ta daɗe bata kira shi da shi ba sai ya sakar mata da murmushi ya sauko daga gadon ya tare ta daga shiga toilet ɗin ya yi blocking mata hanya ya matso daf da ita yana kallon ta ido cikin ido

"Why are you avoiding me cutie"? Ɗan murmusawa ta yi kafin ta ce

"Mr Abdulsalaam it seems like you have completely forgot that you are in your mide 40's"darawa yayi irin ta shahararrun manyan ya ce

"Mrs Abdulsalaam it seems like you have forgotten that you came to me first did you remember"?? Wani hararar masoya ta aika mai da shi ta zame ta ƙasan shi ta wuce toilet tana me ce mai

"Mr Abdulsalaam is like you forgot that you always screem argggghh"cije bakin shi yayi lallai cutie ta same shi yau da yawa dole ya nuna mata cewa duk yawan ƴaƴan ta bata fi ƙarfin yayi seducing ɗin ta ba dan haka wani irin wicked grin yayi ya fita abin sh..

_10:20am_

Cikin shigar alfarma da kamala suke saukowa daga staircase ɗin duka members ɗin family ɗin are present in the dinning dan haka da zuwan su yaran suka miƙe suna gaida su amsawa suka yi cikin ƙaunar ƴaƴan na su kafin su basu izinin zama suma zaman suka yi aka yi serving ɗin su abincin su except her da ta rigada ta ci nata tun ɗazu a bedroom ɗin ta.. Ganin empty chair ya sa ta kalle su ta ce

"Ina yayar ku ta ke"? Dakatawa suka yi da cin abincin ɗaya daga cikin yaran da ya ke matashin saurayi kyakyawa son kowa ƙin wanda ya rasa very chubby ya ce

"Ummah ba ta fito ba ne"! Yana rufe bakin shi wata angelic creature ta ɗaga murya tana magana
"Ohh common Abdulsalaam sau nawa zan na hanaka yin ƙarya baka son ji why"? Cikin shigar riga da wando mai matuƙar faɗi wanda in ba lura mutum yayi ba zai ɗauka ko skirt ne rigar baƙa ce marar ado ko ɗaya plain deep black mai buɗaɗɗen hannu wandon kuwa mai multi colours ne red,white,black and orange wata heels ce baƙa a ƙafar ta ta yafa ƙaramar baƙar gyale ta yafa irin na zamani hannun ta riƙe yake da jaka wanda kamar tare suke da wandon jikin ta saboda irin colours ɗin da ke jikin shi hannun nan ya sha manya manyan hand accessories fuskar nan tarr da shi an fiddo da kowani contour da ke cikin ta orange red lipstick ta yi amfani da shi wanda ya fiddo da beauty ɗin kwalliyar tata sai ƙamshi take bulbulawa ɗaya hannun ta riƙe yake da ƙaramar mug tana sipping abin ciki cikin hanzari take saukowa

Juyawa suka yi suna kallon ta wanda ta kira da Abdulsalaam ne yayi saurin durƙusar da kan shi ƙasa dan ya san yayi laifi da zuwan ta kuwa ta kama mai kunne

"How many times did i warned you not to be telling lies"?? Haɗa hannuwar shi yayi yana bata haƙuri kafin ta rabu da shi ya gaida ta ɗayan ma da yake kamar kan su ɗaya da wanda aka kira da Abdulsalaam ya gaida ta ta amsa sannan ta juya ga iyayen na ta ta ce masu

"Good morning ummah"ta amsa da
"Morning dear"
"Good morning Abba"shima ya amsa da
"Morning hibba"

Ɗaukar burger ƙarama ta yi ta sa kai zata tafi cikin hanzari tana cewa

"Am off sai na dawo yau na yi latti da yawa yau"kafin ta yi nisa shi ɗayan da bai cika magana ba ya miƙe ya ce

"Big sis kin ga ki ce ma Abdulsalaam ya daina irin tuƙin da yake yi a kan titi wallahi jiya ba dan wata yarinyar da ke son shi ta taimake mu ba da sai dai ku ji Abdulrahman da Abdulrashid are no more kuma in na ce zan tafi school a wata motar sai ku hana ni"ya ida maganar kamar wani ɗan 5-6years alhalin ya kai 17years ajin farkon shi kenan a jami'a yayin da ɗan uwan shi mai shekaru 19 ya ke aji na biyu going to na uku a jami'a dukkan su Architecture suke karantawa dakatawa ta ɗan yi

"Ohh ya Allah Abdulsalaam ina ka ɗauko rashin jin magana ne wai haka ban hanaka yin reckless driving ba wai"? Cikin in inaa ya ce

"Kin hana big sis"ta harare shi kafin ta ce
"Fine ka shiryawa punishment ɗin ka anjima" gyaran murya Abban na su yayi ya ce

"Ai barewa ba ta yi gudu ba ɗan ta yayi rarrafe"daga haka ya ja bakin shi yaran basu gane ma'anar maganar shi ba amma ita mahaifiyar su tsab ta gano shi wato ita ce mai reckless driving a baya koh lallai abban su hibba ya raina ta

cigaba da tafiya ta yi sai ta jiyo muryar Abban ta yana cewa

"Sweetheart amma fah kin san baki wani ci abinci ba ko and na san in kika tafi office ɗin ma ba ci zaki yi ba"ɗan murmushi ta yi kafin ta juyo ta ce

"Don't worry Abba ka san duk lokacin da world competition din nan ya taso ban cika samin natsuwa ba sai an gama i will eat later hmm"?? Girgiza mata kai yayi alamun shikenan kafin umman ta taso ta bata good luck kiss kafin ta ce mata

"Kar fah ki manta ki dawo da wuri saboda akwai family function"girgiza kai ta yi ta tafi sauran ma suka sallami iyayen na su suka fita

Asiya Abdulrahman Abdulsalaam kenan ƴar kimanin shekaru ashirin da biyu a duniya wace ta kasance her daddy's favorite ita ce babbar ɗiya ga Arch Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor wanda a yanzu ya ke ɗan taya ɗiyar tashi da wasu ayyukan dan she has taken over everything har ma da na mahaifiyar ta wato Hajiya Aisha Murad Abdulsalaam, ƙannen ta biyu duka dukan su kenan uku wanda Allah ya bama iyayen su kuma Alhamdulilah sun sani ingantarciyar rayuwa mai cike da tarbiya dan ita kan ta Asiyar wacce suke kira da hibbatullah kokuma hibba wato gift of God field ɗin mahaifiyar ta ta karanta wanda ya saka iyayen ta alfahari da ita ta riƙe girman ta ta kama mutuncin ta na babbar yaya.a halin yanzu family kam ya cika tamm dan Big sis haihuwan ta biyu ɗaya namiji ɗaya mace kuma duk sun girma suna aiki dan kusan a jere ta haife su,dija da kabir ɗin ta sun sami arziƙin haifar ƴaƴa huɗu uku maza ɗaya mace wanda babban yayan su wato hakum ya kama girman shi na babban yaya,salma ma haka Allah ya bata ƴaƴa har uku bayan mami kenan ƴaƴan ta huɗu itama alƙawarin da ta ɗaukarwa kanta kuwa yana gab da cika dan dai ta yi nasarar jefo son ƴaƴan a zuciyar junan su halin da ake ciki ma da zarar ta kammala karatun ta na jami'a za'a yi settling komai na bikin,hajiya ummi da yaya Ibrahim kuwa iyayen love ƴaƴan su biyar biyu maza uku mata Allah ya albarkaci family ɗin Abbu,yayin da Majeed ya fito daga 15years imprisonment ɗin da yayi barin ƙasar yayi baki ɗaya zuwa ƙasar oman a chan ya auri wata ruwa biyu inda suma Allah ya basu arziƙin ƴaƴa biyu.

Su aunty mama an zama granny ga jikokin nan ta ko ina masu albarka abin ba'a cewa komai sai hamdala.

Hasina ma ƴaƴan ta biyar duka huɗun maza me sai ɗayar ve autar ta mace ƙawancen su da ummi na nan sai abin da ya ƙaru na alkhairi

A kowani lokaci in aminai biyun suka tuna da aminiyar su da ta riga su gidan gaskiya sukan mata addua'a su yi kukan rasa ta dan ga ɗan ta nan ya taso with the impression that his mother died as a result of heart attack ba'a bari ya san maganar ba dan karatun shi baki ɗaya a waje yayi shi..

Bayan tafiyar ƴaƴan na su ya juyo gare ta ya mata wani mayen kallo tare da cewa

"Cutie you want to defy me right"? Dariyar manya ta mai kafin ta ce

"Hubby ko ɗaya kawai dai na tuno da ne"sai suka yi ma juna murmushi ya kalle ta ya ce

"Kin tuna da soyayyar mu kenan cutie"?girgiza mai kai ta yi kafin ya ɗora da

"Cutie ke ɗin ta daban ce you came into my life without a notice and through you i was able to face all the challenges in front of me kin gwada min *_Soyayya mai garɗi_* cutie ga product of pure love ɗin mu nan duk sun girma i can't stop thanking Allah almighty for bringing you into my life cutie thank you for loving me thank you for standing by my side thank you for protecting me thank you for everything Humaira I LOVE YOU AISHA MURAD ABDULSALAAM"daɗi kalaman nashi suka saka ta ji dan haka ta mayar mai da martanin
"I love you more my Mr Abdulsalaam the most arrogant caring husband and father i can't love you less Humair"ƙanƙame juna suka yi suna tuno shekarun baya da abubuwa suka kacame masu gashi yanzu kamar ba'a yi ba sai labari........................

_*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILAH A NAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFIN NAN MAI TAKEN SOYAYYA MAI GARƊI INDA NA YI KUSKURE YA ALLAH KA YAFE MIN*_

NAGODE DA ƘAUNAR KU ALLAH YA BAR ZUMUNCI

MU TARA A SABUWAR LITTAFI NA MAI TAKEN _*IYA RUWA FIDDA KAI*_ WANDA ZAI ZO MAKU DA WANI SALO NA DABAN

TAKU HAR KULLUM SIYAMA IBRAHEEM

~ONE LOVE~
_*🍒S,Ibraheem🍒*_
Follow@siyama ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

83.2K 6K 67
a love story, this is a love triangle between 4 lover's.
77.3K 4.4K 23
โ๐™ˆ๐™–๐™œ๐™ž๐™˜๐™–๐™ก ๐™ž๐™˜๐™š ๐™˜๐™ง๐™š๐™–๐™ข ๐™ฉ๐™๐™–๐™ฉ ๐™™๐™š๐™จ๐™˜๐™ง๐™ž๐™—๐™š๐™จ ๐™ฎ๐™ค๐™ช๐™ง ๐™จ๐™ค๐™ช๐™ก๐™ข๐™–๐™ฉ๐™š? ๐™ž๐™ข๐™ฅ๐™ค๐™จ๐™จ๐™ž๐™—๐™ก๐™š.โž โ๐™”๐™ค๐™ช'๐™ก๐™ก ๐™ฃ๐™š๐™ซ๐™š๐™ง ๐™ ๐™ฃ๐™ค๐™ฌ ๐™ž๐™›...
28.7K 2.8K 36
her life is ending becouse of her biogical brother,he rapping her the frist tym that he see her in his life
541K 17.6K 157
Genre: Space, Doting, Farming, Time travel, Healing Synopsis: Xu Linyue from the 21st century crossing over with the heavenly space soul penetration...