Page 17-18

597 45 0
                                    

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

*_HAPPY EID EL MUBARAK TO THE ENTIRE MUSLIM UMMAH IN AND ACROSS THE UNIVERSE WISH U A VERY SWEET CELEBRATION_*

*PLS KAR A MANTA DA NAMAN SALLAH NA INA JIRAN KU AGAIN A AJIYE FLAGYL KUSA SABODA IN AN YI BUDA BAKI CIKIN YA HAUTSINE SAI A SHA A SAWWAKE*😄😄



1⃣7⃣➖1⃣8⃣

Rayuwar mu ta kasance rayuwa ce ta yan boko da wayewa ba wai wayewar tanbaɗaɗu ba wayewa irin ta fahimtar juna da karantar halayar juna hade da kau da kai akan abububuwan da bai shafe mu ba girman kai ba namu bane amma miskilanci ga duk wanda yake mana gani gani ba abu ne mai wuya a wurin mu ba

Kwatsam sai na fara bayyana wasu halayya wadanda da bani da su abu na farko shine yawan kyaliya abun da a da har tsoron tambaya na ake yi akan magana daya sai in yi tambayoyi sama da goma har guje ma tambaya ta ake yi a baya ce min ake yi aikin jarida zai fi dacewa da ni saboda yawan tambayoyi na amma yanzu da muka kai wannan marakin na aji uku a makaranta sai kuma na fara jajan aji maganar ma sai na ga daman yi koh tambaya na aka yi in bai min ba toh bana wani bayar da amsa sai na ji ra'ayin yin hakan wannan sabuwar hali na wa ya na damin kawaye na matuka dan har su abin bai musu dadi abu na biyu kuma shine tunda muka shiga aji na biyu nake mayar da hankali na akan zane wato painting abu kamar wasa tun suna min dariya wai aikin maza nake son yi har dai suka daina suka zubama sarautar Allah ido dan kuwa sun ga ni da sukewa dariyar abin baya dami na toh shigan mu aji na uku wanda yayi daidai da shigan mu shekara sha hudu (14yrs) a lokacin ne na fito da ainihim kaunar da nake yiwa harkar zane a gida koh da su falmata suka gayawa iyayen mu sun matukar jin dadin haka ganin ga ni mace amma ina da sha'awar zane zane kuma ban damu da duk wani kalubalen da nake fuskanta daga wun jama'a ba

Yayin da na tsunduma a harkar zane zane yaya kabeer na dada fitomin da manufar sa karara da farko ban gane ba gani nake yi duk saboda zanen da nake yi ne dan yana daya daga cikin mutanin da ke nuna jin dadin su akan abin da nake yi amma koh da wasa baya bari in gane wani abu dangane da kulawar shi a gare ni falmata so ne take mai kamar zata hallaka kanta amma alkunya da kama kai baya bari ta nuna mai koh kadan duk yanda zata yi ta danne feelings dinta in ta gan mu tare tana yi saidai in ta koma daki takan ci kuka ne kamar ba gobe tun mama na mata fada akan kukan da takeyi har ta zo ta fara rarrashin ta dan kuwa bata taba gaya mata sirrin zuciyar ta ba itama bata takura mata tsoronta daya ne kar ta rasa ƴar ta dan tana gani kamar falmata tana boye mata wani abu ne babba wanda ta rasa yanda zata yi ta gano wannan sirrin

Yaya kabeer a yanzu ya fara aikin shi a National Hospital dake cikin garin Abuja a matsayin gynaecologist(likitan mata)

Alhamdulilah yana jin dadin aikin shi kuma yana kokarin kare mutuncin shi baya bari aikin shi ya jayo mai raini daga wun patients din sa koh colleagues din sa ya zaɓi aiki a nan ne farko dan ya kware ya kuma kara samin ilimi kafin ya fara a asibitin shi wanda ake kan gina shi saura kiris a gama koh da Abba ya ajiye shi ya tuntuɓe shi akan batun aure sai ya ce ai ya kusa ne kar ya damu baba ma sai da ya mai maganar amma amsar shine ai ya kusa ne abin na damin umma ganin shine fah babba nan gaba kaɗan za'a fara maganar aurar da su salma dan ita bata so salma ta ƙara wasu shekaru masu yawa a gida dan girman jikin ta ya wuce misali ga tsayin ƙafa a duk sanda ta tuno wannan abin takan nutsar da shi ta gaya mai duniya fah ba wurin zama bane kuma ya bar ganin shi wai shi dan boko dan mai kuɗi a duk ranar da aka ce ya fadi ya mutu to lallai wadannan abubuwa basu da amfani a gare shi illa abin da ya bari wandanda su zasu kasance masu yi masa addua'a wadannan kuwa ba komai bane face sadakatul jariya wato sadaka mai gudana,auilmul yantafa'u bihi wato ilimin da aka amfana da shi,auwwaladul sahle wato ƴaƴa na gani masu kokarin yi mai addua'a wannan nasiha nata yakan sake mai jiki dan ya san da a yau zai zauna da ita ya gaya mata ga wacce yake so tsab zata amince ta taimaka mai dan ya aure ta amma matsalar shine shi so yake ya sami soyayyar ta da kanshi ya wahala da kanshi a wun nemo soyayya ta so yake muyi *soyayya mai garɗi* kafin mu yi aure dan hakan ne kadai zai samo mishi zaman har abada da yake son yi shi da iyalin shi a nan gaba..
fannin soyayyar da yake min kuwa yana nan babu abin da ya canza amma shi har a lokacin jira yake wai in na daɗa girma sai ya fito min da manufar sa

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now