Page 41-42

630 46 0
                                    

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

4⃣1⃣➖4⃣2⃣

  Da sasarfa ya karaso inda na ke tsaye kamar an dasa ni yana zuwa daf da ni ya dakata yana min wani irin killer smile yadda ya saba yi da sauran mata in yana bukatar wani abu daga gare su a jin shi ban san ko shi din waye ba yana ta faman zuba murmushin ƴan duniya.

"Ms Murad ko zaki iya bani aron lokacin ki ko da mintuna 10 ne akwai muhimmin abin da nake so mu tattauna dake akai"

  Tsaf na kalle shi har ya fara jin tsarguwa na kama shi kafin in ce mai

"Ka dawo gobe dan yanzu na gama activities di na a office ina da wani abin yi"
  Na juya zan shige mota ta ya yi saurin shan gaba na yana kokarin dakatar da ni

"Not so soon ms Murad abin da na zo da shi zai amfane ki ya kuma amfane mu baki daya so just create 10 minutes out of your time for the discussion"!!

  Rufe murfin motar na yi na yi gaba yana bi na a baya har muka dawo office din dama gidan su salma zan tafi dan na damu in gan ta sai shi kuma ya hana ni tafiyar kamar yadda na tsara

"Have a seat please"
  Zama yayi yana murmushin yaudara

"Yes ina jin ka"
  Kallon ya haka ya min ya zata zan yi offering din shi wani abu ne kamar yadda na yi ma abokin shi sai ya ga akasin hakan zai fara min doguwar zance na introducing kan sa na dakatar da shi
"Pls just go straight to the point na rigada na san ko kai din wanene dan haka a cikin 10 minutes din ka ka yi exhausting 4 minutes"

Bai yi tsammanin ina da zafin kai har haka ba amma ya aka yi na san labarin shi har nake neman hana shi gabatar da kanshi

"Ms Murad tunda kin ce kin san ni va damuwa ba sai na gabatar da kaina ba a gun ki so nake ki bani aron hankalin ki da tunanin ki kina ji na"?

"Ina jin ki make it snappy?

Gyra zaman shi yayi yana murmushi kaɗan dan a ganin shi ya riga yayi nasara dan babu wanda zai ji wannan tsararen labari na shi ya ƙi yarda da shawaran da zai bayar

"Kin ga ke mace ce na daya kenan na biyu baki gama zaga duniya kin ga yadda ake gudanar da gasar fasaha ba abu na gaba shine ina son ki fahimci cewa duk ilimin ki da hikimar ki bazaki taba zama wata mai muhimmanci ba sai kin hada karfi da irin mu sannanu dan kin ga mun dade a harkar mun taso cikin jin dadi da arziki bamu san wahala ba iyayen mu na mana komai da kudi zai siya unlike wasu shi yasa na ga ya kamata in kawo maki wannan shawarar in zaki taimaki kanki ki tsira da mutuncin ki"

Tabdijam wannan gogagen ɗan iska ne ya zo gona ta ya zage ni stylishly ya goranta min rashin arziki da gata da a baya amma shi gani yake duk a cikin hikimar magana ce i didn't blame him a tarihin shi ya kasance wawa a ahalin su shi yasa ko tsara magana bai iya yi ba shi a nashi rashin fasahar tsara ni yayi ba komai dama in bera bai iya kama mage ba shi magen sai ya kama berar bari in bishi a yadda yake so

"Wow interesting ina jin ka"
  "Yauwa ƴar gari kin ga in kika kwantar da kai kika daina displaying zafin kan nan da kike yi da mutani zamu tsallake wata mataki tare da ke wato a last week ina zaune tare da aboki na na ga ya saka wayar shi a hands free ta yadda zamu iya jiyo komai da ake faɗa a wayar luckily enough muryar ki muka ji akan meeting din da kuka yi da Ashiru duk mun ji komai and as at then Abdulrahman ya kasa controlling fushin sa a matsayin sa na babba a ce ke kina sabuwar tasowa ki yi rejecting proposal din sa i have to calm him saboda banzar zuciya ce da  shi kamar ta kafiri ko ni dake tare da shi hakuri nake yi da shi saboda Abdulrahman is too selfish and arrogant ni na yi convincing din shi akan ya zo da kansa ya baki hakuri akan rashin dai dai da ya maki na karan tsaye da yayi na zuwar maki babu appointment shi yasa kika ga ya zo amma saboda bakin ziciya irin ta sa sai ya kasa baki hakuri instead ya miki zafin kai ya fito abin shi  shi yasa na ce kawai tunda na bashi shawara ta yadda zai shawo kan abin amma ego da pride ya hana sa ni bari in zo kawai kin ga in yaso sai mi haɗa hannu mu biyu kawai abin mu mu tayar maki da kamfanin ki dan kema ki zama wata shaharariya kamar dai mu kin ga babu wata mace a arewacin kasar nan da ta yi himman zama mai zane kamar ke so am advising you ki manta da maganar Abdulrahman dan in har ba ke kika neme shi ba toh ba zuwa zai kuma yi ba ba kuma zai aika miki da invitation ba sai dai ma ya ɓata maki suna ta hanyar yadawa cewa ai kin so hada hannu da shi amma ya ƙi yarda daga nan ma ai kin ga ya gama da ke ya bata miki tauraron ki tun kafin ki fara haskawa a duniya so is better to be safe than sorry ms Murad ai kin san me nake nufi ba sai na kai ki chan cikin issue din ba huh"??

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒Where stories live. Discover now