🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 73-74

657 39 0
By SiyamaIbrahim

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

_Wannan shafin naku ne masoyan soyayya mai garɗi ƴan group ɗin Taskar surayyahms,Ajalin so fans,Surayyahms novel,Zauren brilliant writets,Siyama ibrahim fans page and soyayya mai garɗi fans nagode da soyayyar ku gare ni haƙiƙa SOYAYYAR KU MAI GARƊI CE nagode_

_ina alfahari da ku Faltex Farhana,Ameerahraji,Zara kyari,Zainab pindigi,Suwaiba,mmn bilal teemah aji_
7⃣3⃣➖7⃣4⃣

Kowa a wurin fuskar shi cike yake da tension except Barrister Umar wanda ya san wace ake zargin sai dai bai ambata ba salma da ke tsaye duk ta zaƙu ya furta sunan dan ta san ta inda zata fara gudanar da binciken ta an yi shiru ana jiran shi jiran ƴan mintuna kaɗan ya furta sunan wanda abin ya zo ma salma a riƙiɗe dan kuwa ji ta yi kamar hearing capacity ɗin ta ya ragu kamar jiyo sunan ta yi daga kan hanya an furta sai ta ɗauke wuta ta tsaya a wurin kamar mutum mutumi na wasu lokuta kafin wani irin muguwar zuciya ta zo ta ɗebe ta ta sauke mai wata mummunar marin da bai shirya karɓa ba ta nuna shi da yatsa

"Idan kana surkullen ka ka rinƙa sanin da waɗanda kake yi idan kana ƙarerayin ka da ka gado daga wun ubanka ka ka rinƙa bin turbar da yake bi dan shi baya fitowa ɓoro ɓoro sai ya ma ƙaryar tasa ado kafin ya fitar ta dan haka tun kafin rai na ya ɓaci hankali na ya gushe ka san ba da ƙaramar Human right archivist kake wasa ba dan yanzu zan maka abin da ba zaka taɓa mantawa da ni ba tun wuri ka gyara kalmar ka ka faɗi ƴar iskar da kuka haɗa kai kuka ɓatar min da aminiya"a matuƙar harzuƙe ta ƙarasa maganar dan ta ɗau maganar a matsayin shimdiɗar mafarin zance ne bata ɗau maganar a matsayin abin da kunne zai ɗauƙa ba bare har hankali ya aminta da shi..

"Calm down dear calm down bari ya kuma maimaita sunan maybe ya ruɗe ne shi yasa ya furta sunan". Wani tsaki ta saki gamida banka mai harara ta tsaya tana jiran shi bai fasa ba sunan dai da ya faɗan shi ya kuma maimaitawa wannan karon babu wanda ya lura da wani irin ɗamƙar da ta kai mai sai da aka ganta tana ƙoƙarin aika shi lahira dan tsabar baƙin ciki sai tari yake yi jan ta mijin ta yayi yayi waje da ita yayin da ɗan sandar kuma ya mai da hankalin shi akan Majeed da ke yashe kamar marar rai dan kuwa salma ba wasa ba in ta damƙi mutum ƙiba ne da ita kuma ƙibar ba ta iska ba dan akwai ƙarfi kamar wata mai jinnu..

An yi nasara yana numfashi amma ya jigata dan haka aka yi saurin kirar likita dan ya duba shi..

Sai fisge fisge ta ke
"Mine ka bar ni in koma in ci mai mutunci wannan wani irin wulaƙanci ne da cin fuska ta hanyar gidan uban wa ya san ta da zai saka ta a shirgin ahi wannan ai domestic abuse ne ba zan bar shi ba case ɗin shi biyu a hannu na sai ya gwammaci mutuwar shi da ƙaryar da ya min ka bar ni in tafi mine " ta fincike ta kama hanya amma muryar shi ya mata iyo a kunne ta juyo kaɗan ƙaɗan ta rinƙa bin shi da kallon tuhuma girgiza mata kai yayi ai ko ta yo kan shi da masifa

"Mine are you thinking properly at all? kaima wannan ɗan iskan ya juye maka kwakwalwa ne? did he"? ta daka mai tsawa ya haɗa ta da bangon wurin itama na daka mata tsawar

"Babu juye min brain da yayi Falmata committed this crime ita ta haɗa hannu da shi aka ɗauƙe Aisha come back to reality Mrs Amodu come back and accept the truth your Falmata is the culprit did you get that"?? Sulalewa ta yi ta faɗi ƙasa sai ga hawaye biyo ta yayi a ƙasan shima ya durƙusa yana facing ɗin ta ɗaga mata haɓa yayi ya rage murya ya ce

"Salma my blood sister my very own sister is the culprit ita ta saka shi ya haɗa plan ɗin shi da nata suka yi a lokaci ɗaya Falmata is the culprit ki daina takura kan ki kina kokarin karyara maganar shi dan iya gaskiyar shi kenan salma ki tuna fah cewa yayi her best friend in ba ita ta sace Aisha ba kenan ke kika sace ta?noo Falmata ce ni na sani kuma na daɗe da sani rashon evidence ne ya sa ban fallasa ba amma yanzu da ya faɗa da kan shi kin ga ai bana ɓuƙatar wabi shaida abokin aikata sharrin ta ne ya faɗa ko har kin manta da labarin da na baki ne jiya akan waɗanda suke da hannu a kisar mahaifan Abdulrahman? Zuba mai ido ta yi kamar statue tana bin shi da kallo cigaba da maganar yayi

"dan haka ki natsu ki dawo hayyacin ki muna da babbar battle a gaban mu we have to put family relationship aside and face the reality did you understand dear"?? Ƙala bata ce da shi ba ta yi shiru tana kallon shi juya kan da zata yi ta hango falmata a raɓe gu ɗaya a 360 ta miƙe ta nufe ta tana ɓarin baki wurin tambayar ta

"Falmata kin ji abin da suke faɗa?wai sunan ki ke ta zuwar masu baki sai furta shi suke yi wai  ɓacewar Aisha da saka hannun su har fah da yayan ki a cikin masu supporting ƙarerayin wannan ɗan iskan please dear je ki faɗa masu ba ke ba ce ki faɗa masu su daina ɓata maki suna"!! Tana hawaye ta ida maganar tana kallon falmata dan jin me zata ce ga mamakin ta sunkuyar da kai falmata ta yita kasa ɗagawa jijjiga ta ta shiga yi tana mata magana cikin tsawa

"Will you say something?ki je ki gaya ma yayan ki cewa ƙazafi ake son miki ki sanar da shi cewa baki da masaniya akan wannan sharrin da ake son laƙaba maki"!! Kusan duka mutanin dake wurin su suke kallo yayin da Barrister Umar ya karaso yana ƙokarin jan matar shi dan ya san ta shoga ruɗu ne ga gaskiya tana gani amma ta kasa amincewa ta gasgata gaskiyar riƙeta da yayi ai ko ta fincike ta damƙo falmata tana huci

"Ba zaki yi magana bane wai ko me falmata kina gani ana son ɓata miki suna amma kin kasa ƙaryatawa speak up will you"?? A tsawace ta karasa maganar sai dai abin da ya girgiza ta ta gani haɗe da birkita mata tunani dan kuwa kuka taga falmata ta fashe da shi tana sulalewa ƙasa ta saki hannun ɗan ta tana kuka mai cin rai da nadama haɗe da dana sani kasa cewa komai salma ta yi ta tsaya a wurin tana jallon falmata still tana so ta ji falmata ta karyata wannan allegation da aka mata amma ina kuka ya ci ƙarfin falmata sai yi take yi zuwa lokacin kabeer da iyayen su Barrister Umar sun rigada sun iso ganin falmata na kuka a durƙushe mijin ta ya karasa da sauri ya na tambayar ta lafiya

"Baby me ke faruwa haka me ya saka ki kuka what happened kid sis"? Ya ƙarasa tambayar yana directing tambayar zuwa ga salma da ke tsaye ƙiƙam kamar marar numfashi ganin babu amsa daga gare ta sai ya tambayi umar
 
"Umar talk to me meke faruwa ne wai ban gane ba duk kun min shiru what is going on"? a ruɗe ya ƙarasa maganar rasa abin faɗa mai Barrister umar yayi sai kawai ya sunkuyar da kan shi ƙasa cakumo Barrister Umar kabeer yayi ya ce

"Will you say something"?? Idanun Barrister umar yayi ja sosai kamar zai yi kuka yana jimamin sanar da shi matar shi ce ke da hannu a ɓacewar ex lover ɗin shi kuma babbar aminiyar matar shi haka zalika babbar aminiyar ƙanwar shi yana tir da irin halayyar ƙanwar ta shi yana da ya sanin haɗa jini da ita yana jimamin abin da zai aiwatar dan duk abin da za'a yi sai dai a yi amma alƙawari ya ɗaukar wa kanshi wannan extensive case ɗin shi zai yi handling no matter what and how the outcome may be dole ya juyawa family ɗin shi baya dan kare haƙƙin wanda aka zalinta ta nan ne ƙaɗai zai gyara sunan family ɗin shi daga ɓaci gabaɗaya da tarnizhinf image ɗin gidan su a idon duniya dan haka ya ɗago yana kallon Kabeer bai san ta yadda zai ɗau maganar ba

"Big bro she was behind everything she was behind her friend's abduction ita ta saka aka ɗauƙe Aisha"shock of his life da bai taɓa tunanin zai riske shi tun yanzu ba ya ji shiru yayi a tsaye yana kallon Barrister Umar kamar wani marar laka a jiki kafin daga baya ya ce mai

"Umar,ka saurari abin da ka faɗa kuwa? falmata my wife your blood sister jinin ka kake wa irin wannan zargin? anya ba biyar ka aka yi ba akan ka zo ka haɗa wannan ƙaryar ba tunda kai alƙali ne"?? Kafin a bada amsa sai suka ji murya na cewa

"Ko ɗaya babu wanda ya biya shi kuɗi dan nima shaida ne akan Majeed tare da falmata suke aiki"juyawa suka yi gabaɗayan su suka zuba mai ido wannan ɗin ba kowa bane illah Aqeeb wanda shigowar shi kenan tare da Ibrahim suka ji last words ɗin Kabeer..

Da azama ya ƙarasa gaban shi ya ce
"Aqeeb me kake faɗa ne haka she is your sister In-law koh dan ka rasa Aisha kake son saka kowa a blame game ɗin ka kar fah ka manta nima na rasa Aisha amma haƙuri na yi me ya sa kake son yi ma matata sharri Aqeeb are you insane"? A iface ya bashi amsa da

"No that isn't the fact bro you don't get it your wife is too selfish she snatched virtually everyones happines don't you get it Aisha was your heaet beat amma ta raba ku saboda selfish interest ɗin ta ta hana Aisha saƙat saboda son ran ta sannan kana haɗa ni da ita a matsayin sister in-law  ɗi na? ya tofar da yawu ya ce i reject that Allah ya kiyaye"..

Shiru wurin ya ɗauƙa ana mamakin kalaman Aqeeb domin gasganta gaskiyar lamarin sai aka juya ga falmata amma me? ta kasa ɗago kai sai hawaye da kukan kunyar abin da ta aikata rasa abin faɗa suka yi dan haka mahaifiyar ta ta ƙarasa gare ta ta tsugunna ta ɗago ta

"Falmata abin da yayan ku Aqeeb ya faɗa akan ki gaske ne"? Muryar ta na rawa ta ida tambayar dan tana tsoron jin amsar da falmata zata bata

Kasa ce mata komai ta yi sai kuka dan haka ta daka mata tsawa a rikice ta ce

"Mama ni ce bi na sa aka ɗauƙe Aisha ni na sa aka sace aminiyata"tana kuka mai tsanani tuni Aqeeb ya mai da mata raddi

"Kul ki kuma kiran Aisha da aminiyar ki Allah ya tsare ta ke ba aminiyar ta ba ce it would be better in kika yi addressing ɗin ta a matsayin maƙiyiyar ki than ki kira ta da aminiya because you are nothing but a wicked being very selfish"da anger a muryar shi ya karasa maganar

Ban da salati da wurin ya ɗauka babu abin da ake ji mama da ke tsugune gaban ta mari ta ɗauke ta da shi dan takaici da baƙin ciki miƙewa ta yi ta ce

"Na yi dana sanin haihuwar ki falmata na yi asarar haihuwa riƙe cikin ki da na yi a jiki na tsawon watanni tara asara ce kin cuci kan ki ki zalinci kanki ba ni ba"kuka ne ya ci ƙarfin ta sai yi take kamar ran ta zai fita barin wurin tayi tana kukan takaici.

Salma da ke sauraron su tun ɗazu komawa da baya ta yi ta zauna rigijif a kan kujera Kabeer da ke tsaye kamar wanda baya cikin duniyar ya jingina da bangon wurin yana salati haɗe da lumshe idon shi Ibrahim da Aqeeb tsaye suke kafin daga baya Ibrahim ya ɗaga ƙafar shi ya nufo inda take ya tsugunna ya ce

"Falmata ke kika aikata wannan laifin"? sai kuka ba bakin magana takaici abin ya bama Aqeeb ya ce
"Man ita ta aikata mana baka ji ta amsa da bakin ta bane"??

Kasa cewa komai yayi sai ya kuma tambayar ta
"Ina ƙanwata ta ke"?? Kuka take ta yi wani tsawa Aqeeb ya daka mata

"Ina kuka kai Aisha"a rikice ta ce

"Wallahi shawarar sagir ne ba shawara ta ba ce sai da na ce mai kar a kai ta amma ya ƙi"ta cigaba da kuka

Wata sabuwa waye kuma sagir?? Mijin ta ne ya juya ya ce

"Wa nene sagir kuma falmata"?? Shaf ta manta ta furta sunan a fili sai ta eufe bakin ta tana girgiza kai zata yi denying maƙure mata wuya yayi ya ce

"Wanene sagir"???  Idon ta na rufewa ta ce

"He is my sex mate"!! Ingiza ta yayi ta faɗi ya riƙe kan shi yana zirga zirga gabaɗayan su gwalalo ido suka yi what??  Ita kuma ta cigaba da kuka dan ta san shikenan tata ta ƙare mahaifin ta zai fita Barrister Umar ya dakatar da shi

"Baba ina kuma zaka tafi"? Jiki na ɓari ya juyo ya rasa abin faɗa sai kame kame

"Arrest him"ya bada oder polisawan da ke tsaye a wurin ne suka matso zasu saka mai ankwa tashin hankali da ba'a saka mata rana me?? Kowa ɗagowa yayi hatta da falmatan except salma da ta rigada ta san komai dan mijin ta ya sanar da ita da mahaifiyar shi wanna wace iroyar rana ce

"Umar am your father what the hell are you doing"??

"Am trying to make peace reign i want to balance the scale father ba zan iya cutar da al'umma ba saboda kai mahaifi na ne"ya girgiza kai idon shi duk ya ciko da ƙwalla"i can't  support you dad ka aikata laifi mai muni dan haka you shall be punished for your wrong deeds"

Ya kalli ƴan sandan ya ce masu

"Ku shiga da shi zamu haɗu a court dan bana buƙatar bincikar shi komai na riga na sani"muryar shi kamar zai yi kuka ya karasa su kuwa tafiya suka yi da shi yana ta jaddadaa Barrister Umar cewa shine fah mahaifin shi kar ya mai haka..

Abin al'ajabi,Barrister Umar bai ba su damar tambayar shi ba ya riƙe hannun matar shi ya ɗaga ta ya bada umarnin a tafi da falmata itama su bata horo har ta faɗi inda ta kai Aisha sannan ta sanar da su inda sagir yake dan shima a kamo shi har cikin ran shi yake jin babu daɗi amma ya zai yi Allah ya riga ya fitar da shi daga tsatson gidan bai isa ya guje su ba.

Barin wurin suka yi shi da matar shi haɗe da ɗaukar yaron falmata da ke tsaye yana kallon maman shi na kuka aka kama falmata aka yi ciki da ita Kabeer kuwa sai riƙe shi aka yi zuwa mota Aqeeb ya shiga motar ya ja shi kuma Ibrahim ya ja motar Aqeeb ɗin suka wuce.

***********

Ƙunna TVn aka yi cikin sauri haɗe da mayar da tashar zuwa na labarai daidai inda aka gama karanta headlines ɗin za'a fara karanta labarun in full da na wani siyasa aka fara kafin a saka na gano Matar CEOn D'AA paintings kuma shahararriyar painter mai kamfanin kan ta miƙewa tsaye yayi har aka gama karanto part ɗin a rikice ya juya ya ce

"Bro lets go someone just found my wife mu tafi"duk ya rikice dan haka suka zaunar da shi suna gaya mai yanzu dare ne kuma bai kamata a ce sun bi hanyar kaduna ba duba da yanayin rashin kyan hanyar ya bari har sai washegari ture su baya yayi ya ce

"Yanzu na san zama na da ku dama ba so na kuke ba matata ta ɓace a samo min ita in ce maku mu tafi mu ɗauko ta nan nan kaduna sanban ku ce min in bari har sai gobe? what if in an bi an ɗauke min ita fah kafin goben me zaku ce?please excuse me i need to get my wife in ba zaku taya ni ba is okey dama ba responsibility ɗin ku ba ce responsibility ɗi ta ce"yana kaiwa nan ya wafci car key da ke saman glass table ɗin falon yayi hanyar waje da sauri suka biyo shi

"Bro is okey zamu tafi zamu tafi tare ba sai ka saka kan ka cikin hatsari ba"sai kuma suka tsaya wani wawan tsaki ya ja ya cigaba da tafiyar shi da sauri ɗayan ya riƙe shi yayin da ɗayan ya koma ciki mintuna kaɗan sai gashi ya fito tare da matan sai kuka suke yi suna masu Allah ya tsare karɓar maƙullin motar yayi ya buɗe sauran suka shiga ya ja motar suka bar gidan suka kama hanyar kaduna....

*************

Isowar shi kenan ga motoci nan na juran shi shiga yayi duk ya ruɗe yana Allah Allah ya yi ido hiɗu da ɗan shi kiran layin yake yi amma a kashe hakan ba ƙaramin ɗaga mai hankali yayi ba ɗaga kan da zai yi sai ya ga ana bin hanyar station buɗe baki yayi da nufin tambayar dalili sai ya ga an kafa mai bindigar piston a goshi

"Kana furta kalma ɗaya zan sakar maka harsashin da ke cikin bindigar nan"tsit yayi dan kuwa wannan police officer ɗin da gani ba shi da imani dan fuskar nan sam babu sassauci bai kuma cewa komai ba har aka kawo station ɗin suka fitar da shi aka shiga da shi ciki aka zaunar da shi ƙala bai ce ba ya cigaba da ɓarin jiki kawai sai ga ɗan shi an fito mai da shi duk jina jina babu kyawun gani miƙewa yayi tsaye yana ɓarin baki ya nuna ɗan na shi yana magana

"My boy who did this to you wa ya muzanta min kai haka"?har karkarwar bala'i yake yi ya na ƙoƙarin rungume shi sai dai hakan ya ci tura dan kuwa ƴan sandan sun hana suka saka mai ankwa aka tasa ƙeyar shi zuwa wani VIP room ɗin nesa da na MJ ta yadda ba zasu na ganin juna babai san me ke faruwa ba kawai dai gani yayi ana rufe shi kwatakwata ya kasa hango cewa asirin su ne ya tonu sai da aka tafi aka bar shi sannan brain ɗin shi ya fara booting ya fara addua'ar Allah ya sa ɗan shi ba sakarcin shi yayi ba ya je ya tona masu asiri in ko haka ne toh lallai da Majeed ya janyo mai babbar asara da koma baya toh ta yaya zai kare kan shi in hakan ne ta kasance? haka ya cigaba da ƙullawa yana warwarewa har dai ya kwana a wurin..

Washegari da sassafe aka buɗe shi sai wani busa hanci yake yi a dole zai yi magana da lawyern shi haɗa su aka yi bayan ya fito aka basu privacy ya rinƙa jero magana shi kuma lawyern yana ta rubutu har dai lokacin da aka ɗebar masu ya cika aka mayar da shi cikin ɗakin shi aka rufe sai harare harare yake ta yi yana maganganu..

Chan sai ga wata mata ta shigo tare da wasu samari biyu sun shigo duk a hargitse matar sai kuka take yi kamar me ta ce ma ɗan sandar ita ce matar Arch Ja'afar kuma mahaifiyar Majeed ta ce ta zo ne ta gan su da kyar aka yarda dan kuwa ba lokacin visiting bane ana fito da su ta fashe da kuka ta shiga tattaɓa ɗan ta ta na tambayar shi ko ya ci abinci jiya da dare girgiza mata kai yayi alamun eh ya ci sai kuka take yi kafin ta juya ga mijin ta ta mai kallon wulaƙanci ta ce

"Tirr da hali irin naka ja'afar ga shi nan ka ɓata min ɗa na sha gaya maka da ka daina koyawa ɗan nan mugayen abubuwa dan baka san me gobe zata haifar ba me kake ce min? ba ce min kake yi in rinƙa fitar maka a harkar rayuwar ɗan ka ba?ce min kake yi da ina baƙin ciki da ɗan ka kamar ba ni na riƙe cikin shi ba har na haife shi na raine shi ba dan haka yau ka ga iya son ɗa ai gashi nan daga kai har shi kun kwana a jail kuma babu wanda zai fitar da ku sai an gama hukunci a gaban hukuma duk hukuncin da aka yanke maku sai ku karɓa"tana kukan takaici ta ida maganar sauran yara mazan suka yi saurin ƙarasawa suka rungume yayan na su suna tausaya mai dan kuwa sun san mahaifin su ne makasudin komai da ke faruwa ba'a basu damar cigaba da magana ba dan kuwa lokaci ya wuce haka suka fita matar na kuka su kuma mazan na assuring ɗin su akan cewa zasu yi ƙoƙari su ga an fitar da su ba tare da an kai maganar kotu ba.....

***************

Tun da suka koma gida ta ke abu kamar wacce bata cikin hayyacin ta dan abubuwan da suka faru earlier basu daina uaeo mata a kai ba gani take kamar mafarki take yi ba gaske ba ne she can't believe wai falmata ce ta yi waɗannan abubuwan ta ya ma ta haɗu da Majeed da har suka haɗa kai suka aikata wannan crime ɗin and issue kf sagir wanda ta kira da "sex mate"ɗin ta waye kuma shi what does that mean falmata na having affairs da wani namiji da auren ta?sexual relationship? Salati ta  rinƙa yi tana neman tsari daga sharrin shaiɗan dan ji take har yanzu kamar tursasa falmata ta yi ƙarya ta ke gani mijin ta ne ya rinƙa rarrashin ta shi kan shi yana buƙatar wanda zai rarrashe shi dan ba karamin namijin ƙoƙari yayi ba na saka a kama mahaifin shi da ƙanwar shi da ya sa aka yi ba sai rarrashin matar shi yake yi ga baby ɗin su da ke ta surutun gwalangwalan tana son samin attention ɗin iyayen nata amma babu wanda ya bi ta kanta dan haka ta shi tsala kuka dan dole shi ya ɗaga ta ya shiga jijjiga ta har dai ta yi shiru fita da ita yayi zuwa ƙasa dan yana buƙatar yin magana da matar shi mai muhimmanci kuma yana son su fahimci juna...



**************

   "Granny granny"!!!!!!!

Sai kwala kiran sunan take yi dan ta matsu ta gan ta,, kamar daga sama ta ji murya da ta daɗe tana addua'ar Allah ya kawo mata har inda take Allah ne ya amsa mata addua'ar ta kenan?

"Granny kina ina"ƙarasa jin muryar ya sa ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin fitowa tsaƙar gidan da sauri ta buɗe ƙofar tana fatar ganin mai muryar

"Granny ga ni na zo ki fito mana ba sace miki miji zan yi ba"har rawa jikin ta ke yi dan ta ƙarasa kusa da ita da ɗan gudu gudu ta karasa tana fargabar Allah dai ya sa ba gizo fuskar ke mata ba..

Tana kaiwa kusa da ita ta tsaya cak tana ƙare mata kallo kamar bata taɓa sanin ta ba itama kallon ta ke yiwa kakar tata kafin ta fashe da kuka ta faɗa jikin ta tana kuka rungume ta tsohuwar ta yi tana zubda ƙwalla tana jijjiga ta

"Ashe rai kan ga rai?ashe kuna nan da ran ku a duniyar nan?Allah na gode maka da ka dawo min da jikoki na gida lafiya"sai kuka shi dake tsaye yana bin su da idanu gwanin tausayi ya yi gyaran murya yace

"Please ku daina kukar haka nan lets all settled down"ɗagowa tayi daga jikin ta tana share hawaye ta ce

"Am sorry for leaving you standing for so long Hayati mu shiga daga ciki"ta faɗa tana ƙoƙarin jan hannun granny da ke ganin abin kamar drama falon gidan suka shiga suka zazzauna aka kawo masu abin motsa baki ba su taɓa komai ba dan ba su da buƙatar hakan gaggaisawa aka yi granny na riƙe da hannun jikan ta ta ƙi sakewa

"Ɗan nan Allah ya maka albarka da riƙe amanar ƴar nan dan da wasu mazan ne tuni da sun san yanda zasu yi da ita amma kai ka jure ka riƙe ta Allah ne kaɗai zai biya ka mun nema mun nema amma babu wani labari amma ni ban cire tsammani ba kullum ina roƙon Allah da ya bayyana min ku a yau Allah ya cika min buri na na bayyanar ku me ya faru bayan barin ku gida ɗan nan"?? Ɗan shiru yayi kafin ya fara bata labarin abubuwan da suka faru

"Granny a ranar da abun ya faru Abdulrahman baya nan ya tafi siyo magani bayan tafuyar shi babu daɗewa sai na ga gilmawar mutani ko da na tadi dan in duba sai ban ga kowa ba na dawo ɗakin mu amma sai na ga wasu maza su uku suna zagaye da Asiya ɗayan ya ɗora mata bindiga a kai ɗayan yana zaune a bedside drawer ɗayan kuma yana zaune akan sofa babu wanda na gane a cikin su na yi ƙoƙarin matsowa kusa ɗayan ya nuna min bindiga akan in na kuskura na matsa ko da taku ɗaya ne zasu bindige Asiya  dan haja ban kuma takawa ba amma na shiga roƙar su da su bar ta kar su mata komai duk abin da zaau yi su yi akai na amma suka min dariyar zalinci suka ce wai ni ne tantirin da na dage akan sanin wanene ya bankawa surukai na wuta har suka mutu ko toh kafin in tona asirin ogan su su zasu aika mu ni da ɗiyar mutanin da suka ƙonan kuma babu ruwan su da wani bamu dama bare ni sami bakin kai karar su hukuma dan basu gama cika ƙudirin su akan family ɗin Arch Abdulsalaam ba saboda haka zasu yi mai gabaɗaya kawai su aika mu inda suka aika surukai na nayi nayi su min uzuri akan zan janye binciken amma suka ƙi yarda wai su zan rainawa hankali ai an rigada an gama plan ko kawai aiwatarwa ya rage kuma su sun san ogan su zai yi alfahari da su in suka aika mu chan dan haka basu bamu damar magana ba ina ta roƙon su da su bar Asiya a ditar da ita kar su mata komai amma mutanin nan basu bi ta kai na ba na so jin sunan wannan ogan na su amma ban sami damar ji ba dan kuwa maganana ya yanke ne sakamakon wutar da suka bankawa ɗakin gabaɗaya bana ganin komai suka fita suka bar gidan ɗakin mu ya ringa kamawa da wuta kawai sai gidan ya cigaba da kamawa da wuta haka har na cire ran zamu rayu kawai sai wani daga cikin ma'aikatan gidan mu ya banko ƙofar ɗakin ya shigo kayan  jikin shi duk suna kamawa da wuta ya zo da sauri ya ce in kama uwargida mu fitar da ita ta kofar baya haka wuta na ruruwa a jikin mu na yi ƙokarin sagala ta a kafaɗa na shi kuma na ce mai ya duba drawern sama zai ga documents ɗi na da nataya fiddo min da su ni kuma zan fita da ita ta ƙofar baya da taimakon shi muka fito shikuma duk rabin jikin shi ya gama ƙonewa dan haka na roƙe shi da ya bari mu isa zuwa wani wuri in ya so sai in kai shi asibiti bamu fita da komai ba sai documents ɗin mu haka muka rinƙa tafiya ta bayan gari har muka isa zuwa wani asibiti sun gane ni dan nakan yi treating marasa lafiya in sun turo su toh roƙon su na yi da su bar maganar a tsakanin mu kar su fitar na nemi alfarma da su yi treating ɗin shi dan ni tafiya zan yi sun yi sun yi in tsaya na ƙi na tafi nearest POS na yi withdrawing kuɗi na basu ATM card ɗin Asiya da muka tsira da shi a daren muka nemi motar haya da ta ɗauke mu na rasa inda zamu dosa sai dai na yi tunanin mu zo Lagos at least akwai ƴanuwa a nan dan kuna nan amma tsoro na ɗaya kar su aiko masu leƙen asiri su gan mu a nan su biyo dare su hallaka mana ku dan zasu aika tunda dama sun ce basu gama ida ƙudirin su ba shi yasa na chanza shawara akan in ƙaurace ma hanyar gidan nan har sai komai dan haka ko da muka sauka gidan da na ke da shi a nan wanda ba wani daɗewa yayi ba da na siya akan in mun zo hutu sai mu rinƙa zama a chan a Banana Island gidan yake dan haka ko da muka iso taxi muka shiga na mai kwatancen gidan ya kai mu a nan muka kwana zuwa washegari na yi abubuwan da ya kamata mun ɗau kusan sati ɗaya a gidan ina kula da Asiya a lokaci ɗaya ina ƙoƙarin samin gurbin buɗe ƙaramar clinic wanda ba lallai bane ya zaga ko ina ta hakan ne ma na laƙabawa clinic ɗin sunan Asiya dan bana so a gane cewa clinic ɗin nawa ne dan haka ko a clinic ɗin da dr kawai ake addressing ɗi na bana bari a ji sunana da haka abubuwa suka fara yi mana sauƙi kaɗan kaɗan Asiya ta fara samin sauƙi har dai ta warware sai dai bata san yadda muka baro gida ba kuma bata yaɓa tamɓaya na wannan ya nuna min cewa har lokacin bata gama dawowa hayyacin ta ba dan haka nima bana kawo mata maganan ƴanuwan ta sai dai ni na maye mata gurbin ƴanuwan nata time to time takan yi mafarki wasu lokutan takan tuna wasu lokutan bata tunawa idan ta yi mummunar mafarkin na kan yi mata allurar bacci a haka muka cigaba da rayuwar mu da daɗi babu daɗi  nakan ga labarai da ke gudana akan Abdulrahman da cigaban da yake samu a rayuwa har lokacin bikin shi da matar shi duk na gani amma gudun kar mu fito a kai mana hari yasa na cigaba da ɓuya ni da Asiya har ɗazu da nayi kuskure na bar ta ta kalli tv ta ga abin da ke faruwa shine duk ta ɗaga hankalin ta ban da zaɓi sama da in sanar da ita tunda na ga an fara kama masu hannu a abin shine ta ce tana son ganin grandparents ɗin ta na ce toh muzo"....

Kuka sosai suke yi har da ƴar tsohuwar da ta rasa irin godiyar da zata mai na riƙe amanar jikar ta da yayi dan haka albarka ta rinƙa saka mai babu iyaka  koh da old man ya dawo ya gansu abin ya girgiza shi dan bai yi tsammani ba mayar mai da labarin granny ta yi shima ya rinƙa shiyimasu albarka a nan suka zauna kusan satin su ɗaya sannan suka shirya akan zasu koma gida wato Abuja dan sanin halin da ake ciki da addu'a suka rabu suka kama hanyar Abj by flight abin ban mamaki kwatsam sai iyayen Dr Abubakar Sadik Alhassan suka ga ɗan su tare da matar shi abin kamar almara haka ya zo masu kukan farinciki mahaifiyar shi ta yi ta rinƙa kiran ƴanuwa da abokan arziƙi tana sanar da su abin arziƙin da ya same su tuni gidan ya cike ana masu sannu da zuwa da barka da tsira da rayuwar su labari ya rinƙa zagawa Dr Alhassan ya dawo gida bayan ɓacewar su sama da dhekaru shi da matar sa kwanan su biyu a gidan duk ta matsu ta ga ƴanuwan ta amma babu su babu labarin su duk ta tayar da hankalin ta maganar da surukar ta ke gudun sanar da ita dai shi ta gaya mata dan bata so da dawowar ta a ce ta fara cin karo da mummunar labari dija bata garin amma labarin ya riske ta dan haka ta yanke shawarar dawowa kafin lokaci zaman ta a inda take ya ƙare,,da nasiha ta fara kafin ta warware mata kan komai sannan ta ɗora da cewa a halin da ake ciki sun ji ance an gano inda Aishar ta ke kuma Abdulrahman ɗin ya tafi neman ta dan ya dawo da ita gida ita dai baƙin cikin da ta shiga a rayuwa bata san yaushe zai goge mata ba a kundin shafin rayuwar ta ba..


***************

"Wanene sagir kuma ta yaya aka yi ya baki gurguwar shawara akan ki saka a ɗauke aminiyar ki a kai ta gidan mahaukata"?? Ban da kuka babu abin da take yi sai da ya kuma maimata mata tambayar sannan ta ce

"Nima ban san abin da yasa nabi shawarar shi sharrin shaiɗan ne"ta ƙi ƙarasa faɗar koh shi ɗin wanene a gare ta kusan awowin su uku kenan ana abu ɗaya dan haka aka bar ta har zuwa anjima da yamma in Barrister Umar da matar shi sun zo sai a kuma yi mata tambayar.....

******************

ba su suka shiga cikin Kaduna ba sai karfe uku da rabi na dare dan haka dole suka tursasa shi su kwana a hotel bai so ba dan haka kasa bacci yayi sai da gari ya waye bayan sun idar da sallah a sallayar bacci ya ɗauke shi babu abin da yake yi sai mafarkin ta dan haka ya ɗau lokaci a baccin sai 10am ya farka koh da ya farka ya ga time a ruɗe ya miƙe ya shiga masifar ya aka yi basu tadhe shi ba

"For Goodness sake bro ya zaku min haka you guyz seduced me to sleep right? damn it"duk ya ruɗe masu dan haka calming ɗin shi suka shiga yi dan ya kasa natsuwa wai ya tsaya ya yi wanka

"WTF wa zai yi wankan?ni?damn it ku bani car keys ɗi na am going damn it"

Ya shiga binciken inda car keys ɗin yake yayi nasarar hango shi wuf ya ɗauke zai fita dakatar da shi suka yi suka ƙarɓi maƙullin sannan suka roƙe shi da ya tsaya ya ci breakfast amma ya haukace masu wai anya ma sune yayyen shi da ya sani ko dai chanza masa su aka yi ne ganin ba natsuwa zai yi ba haka suka bar shi suka shiga motar suka kama hanya tiryan tiryan suna bin address ɗin da suka kwasa har dai suka sami nasarar isowa daneji street inda gidan matron yake da zuwan su ya fita a motar kafin su gama parking..

Wani irin wawan bugu yake ma gate ɗin wanda yayi sanadiyar fitowar wani ɗan saurayi ya buɗe kofar zai fara ruwan bala'i sai ya ga fuskar kamar ya san fuskar ai kafin ya tsaya yi mai doguwar surutu ya ture shi ya shige cikin gidan yana faman kiran sunan ta

"Cutie,, cutie,,  cutieeeeee"sai kira yake yi yayin da ƴanuwan shi ke bama ɗan saurayin da ya bangaje haƙuri kafin su nemi izinin shiga gidan ya basu dama shiga suka yi suna neman hanyar da ya bi basu gan shi ba sai muryar shi suka ji yana kwala kiran cutie

Kamar a mafarki ta jiyo muryar dakatawa tayi daga kunce kuncen da take yi ta miƙe tsaye ta ce mana

"Kun ji wani murya yana kiran sunan cutie"? Bamu ji ba dan haka muka girgiza mata kai

"No no nooo na ji sunana"ta faɗa tana bin hanyar waje har ta karaso falon ta tsaya cak sakamakon mutumin da take kwana take tashi da shi da ta gani tsaye yana kiran sunan ta juyawa yayi ya fara kiran sunan again

"Cuti......"""kasa karasa kalmar yayi dan tozalin da yayi da abar son shi matar shi hasken rayuwar shi mabuɗin kofofin farincikin shi kamar a mafarki ya buɗe baki ya na son yin magana amma ya kasa furta ko ƙala dan tsananin shock da ya shiga wanda a nata fannin ita na hakan ne dan haka tsayawa suka yi suna kallon junan su kamar hoto..............




*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama Ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

28.7K 2.8K 36
her life is ending becouse of her biogical brother,he rapping her the frist tym that he see her in his life
41.6K 2.3K 42
Labarin Yarima Hafiz da Ummuna Salmah
436K 18.1K 123
SYPNOSIS Reading Purifying Love made Rachelle D'magiba feel very insulted. The ending that the author had written didn't go well with her expectation...
661K 23.8K 200
[FIXED/FAN TRANSLATION] A student who was preparing for the Civil Service examination for 4th year suddenly found himself in an unfamiliar body 3 yea...