๐Ÿ’๐Ÿ’SOYAYYA MAI GARฦŠI๐Ÿ’๐Ÿ’

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 69-70

919 55 4
By SiyamaIbrahim

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

_kuna rai na my dearies_

_maimunah🌹my maimu_
_deeja_
_jiddah_
_miss thomas_
_Mrs daddy_
_Halima bello_
_Farida mpape_
_Fatima garba_
_My maman mubeena_
_Ummu safwan_
_Allah ya ƙara zumunci_

6⃣9⃣➖7⃣0⃣

  Mun yi landing safely a nan na farka inda ya riƙo hannu na aka saka mana kayan mu a cab muka shiga na yi mamakin abin da ya hana shi sakawa a zo a ɗauke mu saidai na yi shiru dan zai iya yiwuwa duk a cikin sirrin da yake ɓoyewa ne a motar ma bacci bacci nake ji dan haka na kuma kwanciya a jikin shi while shi kuma yana ta shafa fuskata yana min sannu tafiyar da ɗan nisa dan haka kafin mu isa inda zamu sauka wata baccin ta kuma ɗauka ta sai shi ne ya fito da ni rungume a jikin sa kaɗan kaɗan na ke buɗe idanuna har na buɗe su tar na ga a kofar gida muke yanayin environment ɗin ya saka ni sakin jiki ban yi tunanin saukowa ba ƙaramar kofar gate ɗin ya buɗe mana muka shiga a babbar falon gidan muka tsai da madakata ya sauke ni haɗe da kwantar da ni ina ta kallon shi har ya cire min doguwar abayar da na saka ya rage daga riga sai wandon da ke ciki ya ɓalle boturan rigar exposing my chest ya cire rigar gabaɗaya cire jeans trouser ɗin ya yayi yana yi yana min tsiya wai jikin yayi yawa dole ma mu fara tafiya gem kafin mu koma murmushi kawai na iya mai bayan ya gama cire min kayan ya ya shiga yi min tausa ina ta lumshe ido na wani baccin ke son ɗauke ni ganin haka ya daina tausar ya ɗauke ni muka wuce zuwa bedroom ina iya cewa a yawan kayan alatu wannan bedroom ɗin ya fi na mu na Abuja sai dai a tsari da scanty room decorators na Abj ya fi.

Na yi tsammanin kwantar da ni zai yi sai yayi bathroom da ni kamar in saka mai kuka haka na rinƙa ji a lokacin da ya sauke min ruwan shower tun daga kai na kafin in ankara shima sai gashi ya yi joining ɗi na a shower ɗin babu alkhairi a tsayuwar mu dan sai da na gwammaci ƙiɗa da karatu babu abin da ya min amma wani irin muguwar rough play da yayi min har yana so ya shafe azaban da na ji a jiya amma na daure ban yi kuka ba karshe dai baccin na mai a shower ɗin dan kamar wacce ta sha wani abu na rinƙa ji ban san yadda ya karasa min wankan ba amma na farka na ganni kwance saman royal bed ɗin ɗakin ni kaɗai sanyin ɗakin a appropriate temperature da salati na farka na yi miƙa na ɗan ji dama daman jiki na dan haka kallon agogo na yi na yi saurin miƙewa na yi hanyar bayi na yi alwala na dawo na tantance gabas na tada iƙama bayan na idar na rinƙa zuba idon ganin shi amma ban gan shi ba dan haka na cigaba da karatun alqur'ani da nake yi a zuciya ta

Kamar bayan mintuna kaɗan na fara jin ƙamshi na daɗa buɗe hanci na sai na ji eh fah da gaske ƙamshin ne rasa ta ina yake fitowa na yi sai na fara bin ɗakin ina neman ta inda ƙamshin ke fitowa har na kai bakin ƙofar ɗakin ssi na ji ƙamshin ya daɗu a hankali na rinƙa saukowa har na iso tsakiyar falon na juya na ga wata ƙofa na tura kofar me zan gani..

My hubby in a complete chef attire hular dogo irin na masu girki da apron ɗaure a jikin shi ya saka wata karamar boot hannun shi sanye cikin abin sauke girki ga shi kitchen ɗin tsaf tsaf da shi kamar ba namiji ke aiki a ciki ba ƙamshin ya daɗu ina iya cewa ban taɓa jin ƙamshin flavour ɗin nan ba sai a ranar dan haka na ƙarasa cikin sanɗa na rungume shi ta baya sai ya sake murmushi ya riƙe hannu na ya ce

"Wify har kin tashi"? ban amsa mai ba sai na daɗa lafewa a bayan shi zai juyo na ce

"A'a cigaba da aikin ka"sai ya murmusa ya cigaba da aikin na shi na ƙi sakin shi in ya juya ina biye da shi kwance a bayan shi in wun oven zai je ina bin shi har ya gama kammalawa ina ta kallon shi komai cikin tsari da ilimi yake yin su ya tsara komai a muhallin shi ya jer su a dinning ɗin kitchen i was eager to taste the dish dan haka na taya shi haɗa kayan a saman dinning ɗin ya ce min

"Gracies sanyòra"darawa na yi kaɗan na ce

"Wow my hubby is now a Spanish chef"muka yi dariya shi ya ja min kujerar baya kaɗan kamar wata special kwai ya rinƙa treating ɗi na har ya gama buɗe dishes ɗin da waɗanda ya yi kafin in zo kitchen ɗin i was salivating already ganin i was eager sai ya rinƙa ja min rai kafin ya zuba min a plate kusan 5 course ga white rice an barbaɗa mai wasu irin ganyayyaki ƙanana a saman shi ga wani irin garnished fresh fish da aka yi roasting aka ajiye mai lemon ga graded pepper da yankakun tomatoes da chili ga wani irin pepper soup na catfish sai wani babbar plate da aka rufe da babbar food cover ban san me a ciki ba

"Woow hubby did you prepare all these"? Sai ya faɗaɗa murmushin sa ya na girgiza min kai buɗe food cover ɗin yayi sai na ga kamar chicken ne a ciki na tambaye shi

"Hubby wannan kuma me ye shi"? Yayi serving ɗi na kafin ya bani amsa

"Chiken Casablanca"
"Whoa chiken Casablanca""da amusement na kira sunan sai na ga yana ta murmushi kafin ya ce
"Mrs can you please taste and rate the dish"? Da sauri na ce "yes of course chef"muka dara tare sai ya saka suspense face irin yana jiran jin markin da zai samu.

First bite da na kaiwa chiken Casablanca ɗin nan sai da na lumshe ido na dan daɗin da na ji a baki na buɗe idon na yi na sauke su akan fuskar sa sai na ga tension a fuskar sa dariya na yi na ce

"Are you nervous"? Girgiza kai yayi sai na kyale shi na yi tasting sauran abincin duk iya girki da garnishing abinci na ban kai wannan matakin ba ni da aka bawa judge akan in yi rating girki sai na ɓige da cin abinci na bar participant a tsaye sai da na kai rabi na ɗago na kalle shi shaf na manta

"Ohh ya salam hubbu ka min afuwa wallahi na manta da kai a tsaye"madaɗin in gaya mai feedback sai na cigaba da kai abinci baki na

"Cutie for Goodness sake kin bar ni cikin anxiety"ɗagowa na yi da da spoon a baki na sai da na gama tauna abincin na sha fruit drink ɗin na miƙe tsaye na isa gaban shi ina murmushi

"Hubby in ka ga judges ko judge na tasting abincin da ka yi suka ɓige da cin abincin ba tare da sun ɗago ba ya kamata ka san cewa baka buƙatar wani rating saboda da abincin bai yi ba ba zasu cigaba da cin abincin ba dan haka albishirin ka hubby"!! da murmushi ya ce
  "Goro ma'am"

"Am happy to announce to you chef AA that you are the best chef and the best Cook i have ever seen the cooking method the garnishing and the taste most of all the appearance all are fantastic superb"na ida ina tafa mai rungume ni yayi yana jin daɗi

"For the first time i cooked for my wife and she likes it thank you cutie"ƙanƙame juna muka yi na ce

"Amma hubby wa ya koya maka girki har ka iya waɗannan girke girken haka ka san har kamar ka doke ni a iya girki"? ɗan dariya yayi ya ce

"Cutie kin san ni ɗin rainon big sis ce so whenever am home for vacation ina taya ta aikin gida in na ga tana girki nakan taya ta tun ina grating onion pepper har na turje rannan na ce ni girki zan yi ta ƙi na kai ƙarar ta wun hayatin ta sai ya saka baki shine ta bar ni na fara joining ɗin ta a kitchen gradually i began to get more knowledge a yin abinci and i made a promise to myself that daga ita sai matata da ƴaƴa na zan rinƙa yi wa girki  unfortunately an ɓatar min da ita an raba ni da ƴaruwa ta and she wasn't here to taste the food i made amma Alhamdulilah you are here kin yi tasting i just pray and wish to see her very soon saboda ta ci abincin da  ƙaramin ƙanin ta yayi"muryar shi a raunane ya karasa maganar nima sai na ji kamar in yi kuka

"Shhhh is okey hubby zaka gan ta zamu ga big sis very soon InshaAllahu ka kwantar da hankalin ka hubby"sai ga hawaye na ɗiga daga idanun shi abin sai ya firgita ni hawaye haka abin yayi tsanani

"Hubby stop ka daina kuka na faɗa maka zamu same ta very soon ka ji"?? Girgiza kai yayi ya ce

"Ko wanene ke da hannu a ɓacewar ƴaruwata wallahi wallahi ba zan bar shi ba that is a promise"

Zaunar da shi na yi na zuzzuba abincin a plate na fara bashi a baki yana ci a hankali har dai na ga alamar ƙoshi a tattare da shi sai na dakata na goge mai baki na taya shi tashi muka koma parlor na kunna mai plasma tv da ke bangon parlorn na kai mai BBC world news na koma kitchen ɗin na gyara na wanke sauran kayan na maida su ma'adanin su na dawo na kwanta a kafar shi yana kallon news ɗin ni kuma ina ta mai wasa da botir ɗin rigar shi ina yi ina mai surutu kaɗan kaɗan har dai ya dawo da kallon shi kai na

"Cutie you are looking for trouble i guess"!? Jin abin da ya ce sai na rufa ma kai na asiri na natsu dan hango azaban da na ji jiya da ranan bana fatan ƙara fuskantar su dariyar mugunta ya min dan ya san na tsorata

Shiru na yi ban kuma cewa komai ba har bacci ya ɗauke ni bai tashe ni ba sai lokacin da aka kira sallar magrib dan zai tafi masallaci ya raka ni har wun alwala sannan yayi shima ya tafi kafin ya wuce sai da yayi min wani hot and romantic kisses ya tafi yana min dariya nima dariyar na yi na koma ciki..

***********

Zuwan mu lagos was a very sweet and fantastic idea dan babu wanda ya san muna chan illah iyaye na watan mu kusa biyu da rabi saura mana sati biyu mu koma Abj wanda ban so hakan ba a zaman mu bai taɓa kai ni gun grandparents ɗin shi ba na yi borin ma yi lallamin bai saurare ni ba karshe dai akan saura kwanaki biyar mu wuce zai kai ni mu gana aka bar maganar..

Labarin dija nakan ji kaɗan kaɗan a wurin shi a halin da muke ciki ya sanar da ni cewa tana running wani mini painting organization kuma abubuwa na tafiyar mata smoothly matsalar ta ɗaya shune tana son ta tafi wani ƙasa ta ƙaro ilimi amma mahaifin ta ya hana gudun kar ta je ta yi wani abin tunda basu kusa da ita..

Wani faithful Saturday muna zaune ni da shi muna  rigimar ya kai ni kitso na gaji da barin kai na haka nan shikuma ya dage ba zai kai ni ko ina ba sai dai in jira har mu tafi gidan granny wai akwai wata bahaushiya da take ma granny kitso sai ta min amma shi ba giyar wake ya shawo ba da zai bar ni matan yarbawa su jagwalgwala min kai ba nima sai na botsare na ce ai ba kan shi za'a jagwalgwalan ba kai na ne shikuma ya ce bai san zancen ba sai dai in in bar kitson ba zan iya ganin samu in ga rashi ba dan haka na turɓune fuska na wuce bedroom ɗin mu a zuciye bai biyo ni ba dan dama haka muke yi in mun yi faɗa baya biyo ni sai na sauko kuma ya san laggo na bana iya fushi da shi da zarar ya fara lailayo min kalamai sai in ji jiki na yayi laƙwas bana iya doguwar fushi da shi

Bai biyo ni ba sai da aka idar da sallar isha'i faɗan tun safe sai bayan isha'i aka zo neman sulhu da fari shima haɗe fuskar yayi nima na haɗe yayi yayi mu sasanta na ƙi sai daga baya ya fara bani haƙuri

"Cutie bana son ƙazaman matan yarbawan nan suna taɓa maki suma they irritate me kin ga in aka ce kitson za'a miki wannan mai tsinin za'a miki ni me sunan shi na ji big sis na faɗa"!?? yayi shiru alamun nazari sai na taya shi bada amsa

"Shuku"?? Da sauri ya ce
"Yess cutie kuma irin na su zasu miki a ta tsakiyar kai babu tsari shi yasa na ce ki bari in mun je gidan granny sai a miki amma duk kin birkice min cutie uhum toh yanzu dai zo in kai ki gyaran suma a nan kusa ne ba nisa""

Da mamaki na ɗago na kalle shi na ce
"Ka san lokaci kuwa"?? Ya ban amsa

"This is just past 8 suna nan har safe 24/7 saka hijabin ki ki zo mu tafi"da yake ina son yawon nima sai na yarda na zumbula hijabin na ce mai na shirya muka fito tare da yake a Victoria island gidan namu yake babu yawan hayaniyar jama'a..

Da kanshi ya cire min hijabin ya warware ribbon ɗin ya tsaya jaddada ma matar kar ta jagwalgwala mai kan mata ni dariya abin ya bani dan da ganin matar professional ce amma wai shi ke koya mata yadda zata yi aikin ta..

Sosai ta min gyaran suma aka ƙyalƙyale suman aka gyara shi sai ɗaukar ido yake ina kallon irin mayen kallon da yake bi na da shi amma na yi alƙawarin ba zan bar shi ya hargitsa min gyaran suma ba sai dai yayi bala'in da zai yi ya bar ni.

Biyan su kuɗin su yayi muka kama hanya zamu tafi gida mun fito kenan wata mata ta bige ni sai ta ɗago ta ce min

"Sorry dear"murmushi na mata na ce

"Ba komai"da murmushi nima a fuska ta har zan wuce sai na dawo na ƙura mata ido dan a tsaye ta ke tana jiran a miƙa mata wani abu matar ta min kama da wata sai dai na kasa gane wacece dan haka na yi gaba abi na ina ta son tuno inda na san ta saidai na kasa...

tun a hanya ya fara nuna maitar sa amma na yi biris kamar an ce kar mu dawo gida muna dawowa kuwa tun a falon ya fara demonstration ɗin shi na ƙi biye mai amma inaa da yake ya iya seducing mace mutumin nan sai da ya san yadda yayi ya saka ni ɓannata gyaran suman nan kasa wanka na yi saboda takaici sai ture turen baki nake yi ganin ban da niyar yin lagwas sai ya kuma rikita ni ya rikita kan shi muka shige wani zangon a wannan karon har kukan takaici sai da na mai dan konda tsiya ko da arziƙi  dole in sakawa kai na ruwa..

Bayan mun yi wankan ina zaune ina busar da kai na da hand dryer ina share hawaye da jan hanci dama ga laifin ƙin kai ni gidan kitso da yayi kuma bai bani haƙuri ba ya bige da yi min wayo dan rai na yayi sanyi gashi yanzu ya kuma aikata wani laifn dan haka na rinƙa sharar hawayen baƙin ciki ina bysar da kai na ta mirror nake ta maka mai harara yana ta min murmushin mugunta tashi yayi ya zo kusa da ni ya karɓe hand dryer ɗin ya cigaba da busar min da kan ƙala ban ce da shi ba har ya gama ya binciko stretcher na gyara suma ya haɗa ya nemo cutting comb ya fara tsagawa yana shafa min oil yana stretching kamar dai yadda ya ga matar nan na yi ban tanka mai ba har ya gama yayi parking yana ta admiring ɗi na har ya furta

"Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan kyakyawar mata tawa"harara na aika mai da na miƙe na cire bath throb ɗin na rage da ƙaramar transparent nightie na wuce na kwanta ina hamma ya san laifin shi na ranar babba ce dan haka shima biyo ni yayi bayan ya gama drying suman shi jan duvet ɗin yayi ya shige ciki haɗe da kashe mana bedside lamp janyo ni yayi ya kwantar a kirjin shi yana ta wasa da kumatu na ban ce da shi komai ba a haka muka yi bacci dan it was already past 12 kusan 1am na dare dukkan mu muna buƙatar bacci..

  Fushin mata da miji musamman irin na mu daban yake dan haka a washegarin ranar muka shirya abin mu komai ya cigaba yadda ya kamata kwatsam muna kallo ranar sunday sai gashi an baza pictures ɗin mu ni da shi wai ana neman mu ba'a gan mu ba tun ranar da muka tafi airport ba'a kuma jin ɗuriyar mu ba dan haka an saka ga wanda ya gan mu yana iya kawo rahoto ga kuma kuɗin da aka saka ga duk wanda ya gan mu naira miliyan biyu da rabi,,,

Miƙewa zaune na yi cike da al'ajabi
  "Hubby ana so a kashe mu da ran mu ka ga abin da suka saka"?? Ɗan rausayar da kai yayi ya ce

"Kina tunanin wa zai yi irin wannan shirmen"?? Shiru na yi ina nazari caraf na ɗago kai na

"Majeed"!??

Jinjina min hannu yayi
"Good kina da brain cutie shi yasa na ke ƙara son ki yanzu tunda an buga ana neman mu kin ga sai mu gudu zuwa gidan granny dama delay ɗin da na tsaya yi kenan dan na san ko mu jima ko mu daɗe sai an yi hakan shi yasa na bari sai na ji me za'a kai media sai mu san next plan ɗin mu kuma gashi an yi hakan dan haka a yau da dare zamu wuce gidan su granny a nan zamu zauna har abubuwa su lafa sannan mu koma gida in an nemi sanin ƙasar da muka tafi har aka neme mu aka rasa sai mu sanar da su chanza ra'ayi muka yi saboda gudun ƴan aɗawa da ƴan ƙarƙashin ƙasa kin fahimta"? Girgiza kai na yi ina mamakin irin wannan rikiɗaɗen rayuwa da muke yi cikin hideout kamar wasu waɗanda suka yi kisa..

A daren muka haɗa yanamu yanamu muka wuce arean su granny  kafin mu tafi dama ya sanar da old man akan tafiyar mu dan haka da muka isa gidan sai kakkare mu yake yi bai son rasa jikar sa da matar sa granny mai ran ƙarfe ita ta saka aka kawo mana dinner dan dama bamu ci abinci ba bayan mun gama tsohuwa ta rinƙa ja na da hira har dai su suka gama nasu hiran da grandpa mu bamu gama ba da zata shige ɗakin ta ta ja hannu na muka dhige tare ta juyo ta na magana da hubby ɗi na

"Toh sadauki Allah ya tashe mu lafiya"tana kaiwa nan ta rufo ƙofar ta ta bar shi tsaye da al'ajabi shi fah yana ɗaya daga cikin dalilin da ya sa bai yarda ya kawo ni gidan ba dan sarai ya san halin granny tana iya hana shi matar shi dan ba zai manta ba duk sadda big sis ta zo ita da mijin ta toh sun rabu kenan sai dai su haɗu a wun cin abinci amma da dare yayi babu ruwanta tafiya take da ita shi yasa shi ya rinƙa dodging ɗin ta amma gashi ta sami galaba a kan shi in ba dan muna cikin halin tsaro ba da babu abin da zai hana shi ɗauke ni duk rana muna zuwa wun hutawa ba shi da yadda zai yi sai haƙuri haka ya wuce makwancin shi ya kwanta dan grandpa ya tafi nashi makwancin thinking that matar shi zata sake ni in dawo wun miji na bai san ta yi captivating ɗi na ba.

Yadda na ga rana haka na ga dare i couldn't sleep miji na baya kusa da ni haka na rinƙa juye juye na har dai asuba ta kusa sannan na sami bacci shima a nashi gefen haka ne dan mun saba da juna sabo mai tsanani.

*************

Washegari kuwa da sassafe ya shigo gai da granny abin ya bata mamaki
"Sadauki lafiya kuwa ka tashi da wurwuri haka ko dai akwai matsala ne'? Ɗan shiru yayi kafin ya bata amsa

"Babu komai granny kawai kishiyar ki na zo gani"sai ta ce

"Auuu ai tana bacci oh ni maryama na ga yaran zamani wai yarinyar nan ta ƙi yin bacci jiya sai juye juye take ta yi ita daddawa daɗi miji ko"?? dariya ya mata kawai ya miƙe yayi gaba ya barta tana ta surutanta

Da shigan shi ya hango ni ina bacci sai ya rinƙa sauke min wani calm kiss a forehead ɗi na har na farka na gan shi sai na yi kamar zan saka mai kuka

"Hubby i couldn't sleep last night "rungume ni yayi yana rarrashi na

"Cutie shi yasa nake ta delaying zuwar mu nan dan kin ga tsohuwar nan ta yi suna wurin raba ma'aurata believe me grandpa bai sani ba shi yasa but i will report her to him i couldn't sleep either last night ina ta tunanin cute wify ɗi na"shiru na yi ina sauraron shi har dai muka ji gyaran murya

"Yanzu kai sadauki haka ka ɓaci rana tangararas ka zauna kana rarrashin wannan mummunar ƴar? toh nima a zo a rarrashe ni"ta karasa tana son yi mai tsirfar tsoffi sai muka saka mata dariya itama ta ɗan dara kafin ta kora shi waje bayan ya fitan ne take sanar da ni wai ai sadaukin ta baya son zuwa wun dangin shi na ruga ya ce abin da suka mai baya jin zai iya yafe masu nan kusa ita ke sanar da ni wasu abubuwan da dija bata sanar da mu ba ashe akwai ƴaƴan baffanin shi da ke aure a ruvar tsakanin shi da su abin arziƙi da yame aika masu da shi amma shi baya zuwa..

Hira tai daɗi sai ga shi an zo kiran ta wai in ji grandpa a hankali ta lallaɓa ta tafi a ranar na ga faɗan tsoffi dan grandpa ya ce lallai lallai ta mayar da ni ga miji na ita kuma ta dage sai dai ya haƙura har mu koma gidan mu faɗar rashin gaskiya har da iƙirarin shi ai bai san wahalar da sadaukin ke ba ni ba shi yasa ita ta gano ta ke son hana shi matar sa bai da yadda zai yi da ita dan ta fi shi baki saidai haƙuri ya ba shi...

A haka muka yi zaman sati biyun da ya rage ba tare da mun sami keɓewa ba ran mu bai so ba a ranar da zamu bar garin madaɗin jirgin yamma rescheduling yayi ya mayar na safe ana idar da asubahi ya haɗa kayan shi ya ce in haɗa na wa we are leaving ana gama breakfast ya sanar da granny cewa akwai wata aikin gaggawar da ta zo mai dan haka he need to go  bata fahimce shi ba ko nufin shi dan haka ta mana fatan alkhairi haɗe da jaddada min in rinƙa amfani da abubuwan nan fah na amsa mata muka yi filin jirgi inda muka ɗaga zuwa Abj a ranar babu wanda ya san da dawowar mu sai a washegari baza love muka yi iya son ran mu kusan all night muka yi muna soyayyar mu...


*************
_2 days after_

A nan fah media suka cika mana gida ana son jin ainihin labarin komai yadda ya ce zai gaya maau toh haka ya gaya masu a ranar da haka ya yi sealing bakin su suka tafi bayan sun ɗau iya abin da suke son samu daga gare mu.

A ranar da yamma sao ga Majeed wai ya zo yi mana sannu da zuwa ya nuna kamar bai da masaniya da yaɗa neman mu da aka yi a kafafen yaɗa labarai ba jin shi kawai muka yi basu wuri na yi dan su samu su tattauna bayan na cika su da abinci..

Bai tafi ba sai almost 9pm bayan tafiyar shi ne hubby ke gaya min ai ga yadda suka yi ya ce ai ya ce mai da gangan ya chanza plan ɗin tafiyar muka tafi Thailand dan in ƙara yarda da Shi in bar komai a hannun shi a karshe ya sanar da shi wai ai next week zamu yi resuming office a nan zai saka ni signing important documents ɗi na na aiki ya koma sunan shi kaɗan kaɗan har ya karya ni a cewar shi wai da murna suka rabu da juna tirr na yi da hali irin na Majeed.

Satin gabaɗaya baƙi muka rinƙa yi babu ƙaƙautawa saboda ba'a zo mana ba bayan biki shi yasa aka rinƙa zuwar mana a satin bamu huta ba sai ranar ƙarshen mako..

***************
_One month later_

Mun koma bakin aikin mu ni da shi komai  a tafiya daidai muna da good relationship tsakanin mu da juna ya fahimce ni na fahimce shi Majeed na ta zuba ido bai ga wani changi ba sai ma ya ga kamar wasa da hankalin shi muke yi dan daga ya ji Abdulrahman yayi signing min contract kaza sai ya ji ya yi awarding ɗi na da abu kaza kaɗan kaɗan ya fara zargin mu har ya saka mana ido ya gano duk abubuwan da muke yi a gaban idon shi ƙarya ne so yayi ya yi mai gabaɗaya amma mahaifin shi ya taka mai burki bai so hakan ba dan dole ya haƙura ya cigaba da setting traps ba tare da mun sani ba..

Bayan dawowarmu Lagos da watanni huɗu muka shirya tafiya real honeymoon ɗin mu a kasar Paris inda zamu yi spending wata biyu sannan mu dawo wannan tafiyar babu wanda ya san da shi dan koh shi Majeed mai ƙididdigen bai sani ba except our family ko wurin aiki ma kawai ɗaukar hutu na yi ba tare da na sanar da su inda zan tafi ba..


***************

Rayuwar tsafta da jin dadi muka yi a ƙasar paris nan muka yi honeymoon ɗin babu tsoro koh fargaba mun zaga mun buɗe idanun mu mun yi hotuna mun ga abubuwan tarihi watan mu ɗaya a kasar ranar muna wun shaƙatawa ya miƙo min tab ɗin shi  na karɓa na duba hotunan motoci ne birjik ya ce in zaɓar mana sai na rasa wanda zan zaɓa ƙarshe wata baƙar Land Cruiser vx8 na zaɓar mana iri ɗaya na miƙa mai transferring kuɗin yayi yayi placing ordern motar rungume shi na yi ina ta godiya ba wai dan kyautar da ya min ya zame min abin mamaki ba a'a sai dan mutunta juna da ke tsakanina da shi da kuma rayuwar ƴan boko da ya ratsa mu dan duk ƙanƙantar abu kalmar 'thank you' bata mana nauyi kuma zuciya ta kan so mai kyautata mata a yai koh duniya na tara in har miji na ya min kyautar tsilin tsinƙe ne yana da muhimmanci a gare ni bare kyautar mota kuma a bazata da haka nake ƙara bashi daraja da mutunta shi nake kuma jin babu abin da zai raba mu sai dai mutuwa..

Mun cinye honeymoon ɗin mu lafiya kalau mun dawo a dawowar ne ya yanke hukuncin sanar da Majeed duka plans ɗin nan saboda he wants to put an end to all those mess a ƙarshe ya ba da shi ga hukuma su hukunta shi shi da mahaifin shi dan during our honeymoon he was able to get enough evidence akan mahaifin Majeed ne ya saka aka bankawa iyayen shi wuta a gida dan har su granny ya sanar da su kuma a nan ya ke ƙara jin faɗar da ya shiga tsakanin abokan kafin rasuwar iyayen shi akan shi mahaifin Majeed ya dage da sai dai Arch Abdulsalaam ya yafe mai gasar da za'a yi tunda shi ya saba yi kuma yana lashewa amma shi bai taɓa yi ba sai dai ya bada contribution shi kima Arch Abdulsalaam ya ƙi ya ce kawai su haɗu a filin daga toh shine aka sami rashin fahimta a tsakanin su har ya kai ga mahaifin Majeed ya nemi gurbin shiga gasar amma ya san ko da yayi ɗin ba zai kamo Arch Abdulsalaam ba dan haka jin sun yi tafiya kuma dama ya san tarihin ƴan gidan su Arch da superstitious believe sai yayi amfani da wannan damar ya aika ala bankawa gidan wuta  ta yadda za'a yi tsammanin ƴanuwan Arch ne ke da alaƙa da yin hakan secretaryn Arch Abdulsalaam ke sanar da granfpa dan kusan komai a gaban shi ya faru sai dai rashin isashiyar evidence ya sa bai sanar da kowa ba ya ce ya bar ma Allah toh yanzu da ya ga Abdulrahman ya dage akan bincike kuma yana son a sami zaman lafiya ta hanyar gurfanar da mai laifi gaban hukuma ta yadda peace will reign ya san ya gama da su ya yi focusing on family ɗin yaya umar..

Weighing all this evidences sai ya ga kawai ya fara bin su ta salama in suka ƙi sai ya yi ta ƙarfi dama dan kar a sami mishkila a next targete ɗin shi ya sa ya ce zai bi su sannu a hankali dan haka bayan komawar mu da sati uku ya gama tsara yadda zai yi approaching ɗin su na bashi kwarin gwiwa da full support ɗi na

A wannan lokacin na fara jin chanji a jiki na wanda da chan ba haka nake jin kai na ba na dai share abin ina cigaba da attending aiki na by then mun yi expanding paintings ɗin mu ya faɗaɗa so abubuwa sun mana yawa ina handling na nan Nigeria shi kuma yana handling international businesses ɗin mu matan yayyen shi kan zo mana muma in mun sami lokaci sun zo hutu mukan tafi musu visiting family relationship ɗin mu was very strong haka friends ɗi na sune dai abin su muna mutunci da juna families ɗin mu na maintaining good relationship da juna time to time mukan yi video call da su granny ƙalau muke zaman mu lafiya babu matsala sai dai wanda ba za'a rasa ba..

  Wani tafiya ya taso mai na gaggawa zuwa ƙasar Germany akan wani business ya so sanar da Majeed abin da ya yi planning ni na kai shi airport muka yi sallamar da muka saba yi

"Hubby am gonna miss you alot amma ka san me"? Ya girgiza kai na cigaba

"In ka dawo akwai babbar albishir da zan maka trust me wannan ba kamar sauran bane i promise"moon face ya saka min dama a ko da yaushe alƙawarin kenan amma tunda ya ji na ce wannan na daban ne sai ya ɗau abin da gaske

"Cutie kar fah ki min ƴar hali dan Allah in kika min this time around ni da ke ne"!! Dariya na mai kawai na kai lips ɗi na daidai kan lips ɗin shi deep interlock kiss na mai kusan 5minutes muka rabu da juna yanayin mu na neman chanzawa muka ƙurawa junan mu ido

"You see,am serious about it in ka dawo zaka yi alfahari da surprise ɗi na"rungume juna muka yi kamar waɗanda zasu yi gamon ƙarshe da haka ya fita ya shige jirgin suka tashi zuwa ƙasar Thailand ni kuma na koma gida

A tsarin tafiyar kwanaki huɗu zai yi wanda yayi daidai da saura kwanaki biyar da birthday ɗin shi wanda a ranar na yi niyar sanar da shi cewa ina ɗauke da cikin babyn mu the product of our pure love..

Tafiyar was successful a rana ta huɗun ya dawo da yamma shigowar dare yayi dan haka ban da kula da shi da na rinƙa yi har ya sami bacci ba wani abin da na mai dan dama ban so in sanar da shi sai a washegarin ta yadda abin farincikin zai mai daɗi rungume miji na na yi muka kwanta tare...

********
_The birthday morning_
 
   Duk wasu shirye shirye da ya kamata in yi na yi dan dai birthday ɗin ya zama one in million masu decorating event centre na ɗauko aka tsara mana harabar gidan mu ta gefen garden komai yayi tsaftsaf har 12noon yana baccin gajiya bai tashi ba sai 1pm da na tashe shi ya tashi yayi sallah a nab yayi wanka ya tafi masallacin cikin gidan yayi sallar shi ya dawo abinci na ba shi yana ci yana min bayanin yadda abin ya kasance ina ta praising ɗin shi duk ya matsu ya ji surprise ɗin amma da zarar ya tambaya amsar ɗaya ce

"Wrong timing hubby saura ƙiris"da haka har ya fidda rai akan surprise ɗin muka cigaba da zaman mu har la'asar yayi ya tafi ya yi sallar shi ya dawo bai duba wayar shi ba bai kuma yi tunanin duba su ba ana haka har magrib yayi ya tashi ya tafi masjid yayi ya tsaya haɗawa da isha'i kafin ya dawo gida kasancewar code ɗin birthday ɗin fari ne sai na fiddo mai sabuwar white complete suit ɗin shi nima na fiddo wani doguwar farar rigar da na siyo mana tare da suite ɗin shi na ajiye mai nashi dama tun bayan sallar magrib aka min makeup ɗi na na yi isha'i aka kuma min touche up na saka kaya na aka naɗa min ɗaurin net scarf fara komai na jiki na fari ne shigowar shi kenan da tambaya a bakin shi sai ya ga kwaliyar da na yi zai yi magana na riga shi

"Hubby bamu da time mu je mu shirya ka"da mamaki ya ce

"i don't understand you cutie"?? Tura shi gaba na yi na ce

"Your surprise ko baka so ne"? Da sauri ya ce

"Of course not ina so mana"
"Yauwwa sadaukin granny mu je"bai tsaya min doguwar tambaya ba ya yi shiru har na yi undressing ɗin shi na shirya shi cikin white suite ɗin nan na yi leveling mai sajen fuskar shi na gyara mai sumar kan shi  na rinƙa fesa mai turare kala kala white half cover shoe na saka mai na ɗaura mai necktie shi dai yana ta bi na da kallo har na kammala na ɗau wayata na saita na bamu one shot sannan na riƙo hannun shi muka sauko har garden ɗin gidan muka isa babu haske sai ya ce

"Cutie saboda Allah me kuma zamu yi a nan ɗin babu haske me ya sami fitilun wurin"? Sai na ɗan murmusa na ce

"It seems like aiki ya saka wani manta special and important day a rayuwar shi dab haka nake son tunatar da shi"shiru yayi alamun nazari sai dai kafin yayi magana hasken da ya dallare wurin ya hana shi furta komai

"Surprise"aka faɗa in harmony he was surprised sai dai bai tsinƙe da lamarin ba sai da ya ji ana wishin ɗin shi

"Happy birthday Arch Abdulrahman"juyowa yayi ya kalle ni da annashuwa a kan fuskar shi nima fuskata cike da farinciki

"Happy birthday hubby"kamar ya rungume ni dan maganar gaskiya ya manta da ranar ne birthday ɗin shi kuma bai ma iya nemar wayar shi ba if not da ya ga one to two notification

"Thank you Mrs Abdulsalaam"murmushi muka sakarwa junan mu kafin ya ɗago ya kalli crowed ɗin wanda duka family ne sai abokan hulɗar mu na kusa ba'a yi inviting Majeed ba but abin mamajisai gashi a wurin shima cikin shigar farar suit yana shu'umin murmushi ban so hakan ba ya ce masu
"Thank you so much am great full for the love and care Allah ya mayar da ku gidajen ku lafiya"tafi aka saka daga nan aka fara gudanar da ƴar wasannin da aka shirya mai sai nan nan yake ta yi da ni har aka gama wasar aka kawo cake ɗin wanda ya kasance fari ne aka mai matured design ɗin logo ɗin kamfanin shi aka bi logo ɗin da HBD ARCH ABDULRAHMAN tafi gurin ya kaure da ana ta baza hotuna da videos har muka yanka cake ɗin ya saka min a baki sannan nima na saka mai ya ɗiba ya saka ma ƴaƴan shi madaɗin ya fara da big daddy sai ya fara da Asiya wato big sis sannan ya bama sauran yaran aka saka tafi

Gifts aka rinƙa bashi kala kala har dai ƙarfe 11pm na dare ya kai aka rufe taron inda ya keɓe shi da abokin shi ya sanar da shi komai amma mutumin nan babu kunya ya nemi sainsa da Abdulrahman har ya kai yana ce mai wai ya mai ƙazafi kuma sai ya gani a taƙaice a tsiyace suka rabu a inda Abdulrahman ya ce shi kuma sai ya maka ƙarar Majeed da mahaifin shi ga hukuma shima ya ce bismillah shege ka fasa a haka suka rabu ya dawo ya sanar da ni yadda suka yi na yi comforting ɗin shi muka share chapter ɗin Majeed dan at that veey moment i was eager to tell him the surprise dan shi ya zata ko birthday party da na haɗa mai ne surprise ɗin har muka gama wanka muka saka pyjamas ɗin mu iri ɗaya muka kwanta sai na tashi na zauna ina son gaya mai amma na rinƙa ja mai rai har dai ya ce min

"Cutie kin ga wallahi ki daina ja min aji dan Allah in kika saka wasa sabuwa dal zan kawo miki ƴar yarinya dan na gaji da wannan shirmen da kike min"a lokacin da ya faɗi maganar har cikin rai na naji dumm sai na ɗau maganar a gaske har na yi zuciya na ce

"Haka ka ce koh? wato ka gama da ni sabuwa zaka ɗauko wato koh"? Ya saka serious face ya ce
"Eh kuma ni kin ga sai da safe ki riƙe surprise ɗin ki ban so"ya kwanta ya ja duvet ɗin har kai sai na saka mai kuka ya yaye duvet ɗin ya keƙo ya ce

"Kin ga cutie in kuka zaki yi maza fita parlor ki yi dan am exhausted already i need to sleep"ya koma ya kwanta ni kuma na ƙara sautin kuka na sai yi nake yi ina maganganu

"Tunda ka gaji da ni gidan mu zan koma dama ni na san ba damuwa kayi da ni ba"surutai barkatai na san har ga Allah a gajiye yake amma ban yi tsammanin zai yi saurin bacci ba sai na ji numfashin shi ya ƙaru na ja duvet ɗin na ga bacci yake yi sai na shige nima na kwanta a jikin shi na rufe ido ina ta mutsu mutsu sai na ji kamar dirar mutum na yi saurin miƙewa na ƙunna bedside lamp na ga babu kowa na tashi na leƙa parlor ban ga kowa ba sai na dawo ɗakin mu na rufe na je zan kwanta sai na ga wasu ƙartin maza har su huɗu fuskokin su babu rahama na zazzaro idanuna zan saka ihu suka min alamar in yi shiru tare da ɗora bindiga a kan miji na tsit na yi ina faman hawaye fesa mai wani abu suka yi ban san ko menene ba sannan suka juyo gare ni suna gaya min magana wai ni ce mai saka shi bin diddigi har da barazanar maka boss ɗin su ga hukuma toh kafin ya maka shi su zasu maka shi dan an yi da iyayen shi ma bare shi a nan na san cewa Majeed was behind it zan yi magana suka frsa min nima daga nan ban farkaba sai a gadon asibitin psychiatric da ban san ta yadda na zo ba...................

*_CIGABAN LABARI_*
Wani irin wawan kuka ta fashe da shi yayin da ta kai aya a labarin al'ajabi ban mamaki da tausayin da ta bamu daga ni har Metron mun riƙiɗe ni mai saurin hawaye kamar teku har na tsiyayar da hawayen ido na kamar famfo dan tun da nake tun da nake bincike bincike na ban taɓa cin karo da abin juyewar tunani ba irin wannan tana kuka Metron na rarrashin ta ni kam kasa cewa komai na yi dan abin ya fi gaban tunani na...................

*_🍒S,Ibraheem_*
Follow@siyama ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

77.3K 4.4K 23
โ๐™ˆ๐™–๐™œ๐™ž๐™˜๐™–๐™ก ๐™ž๐™˜๐™š ๐™˜๐™ง๐™š๐™–๐™ข ๐™ฉ๐™๐™–๐™ฉ ๐™™๐™š๐™จ๐™˜๐™ง๐™ž๐™—๐™š๐™จ ๐™ฎ๐™ค๐™ช๐™ง ๐™จ๐™ค๐™ช๐™ก๐™ข๐™–๐™ฉ๐™š? ๐™ž๐™ข๐™ฅ๐™ค๐™จ๐™จ๐™ž๐™—๐™ก๐™š.โž โ๐™”๐™ค๐™ช'๐™ก๐™ก ๐™ฃ๐™š๐™ซ๐™š๐™ง ๐™ ๐™ฃ๐™ค๐™ฌ ๐™ž๐™›...
1.4M 96.4K 24
#Book-2 in Lost Royalty series ( CAN BE READ STANDALONE ) Ekaksh Singh Ranawat The callous heartless , sole heir of Ranawat empire, which is spread...
28.7K 2.8K 36
her life is ending becouse of her biogical brother,he rapping her the frist tym that he see her in his life
1.4K 423 36
A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishada...