🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 65-66

700 46 2
By SiyamaIbrahim

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

'''friendy surayyahms shafin nan naki ne Allah ya bar ƙauna ya ƙara mana kyakyawar alaƙa da fahimta a tsakanin mu u are indeed a good friend luv u dear'''

*INA MIƘA GAISUWA TA GARE KU MASOYAN SOYAYYA MAI GARƊI A DUK INDA KUKE GUDUNMAWAR KU YANA DA TASIRI A GARE NI ALLAH YA SAKA MAKU DA ALHERI YADDA KUKE BULBULA MIN ADDU'OIN ALKHAIRI KUMA ALLAH YA BAKU ABIN DA KUKE NEMA NA ALHERI ❤*

*_Ina taya ki murnar kammala littafin ki Asmeenat Xeeyan Allah ya baki ladan darussan da kika kawo a littafin_*
6⃣5⃣➖6⃣6⃣

Ji na yi an ja ni sai na kai duba na ga mai jan ashe ummi ce sai surutu take ta yi wai ana nema na na ɓace bin ta na yi a baya har muka karasa zuwa cikin harabar gidan mu inda ake gudanar da shirin gabaɗaya ƴanuwa da family friends kamar dai families  ɗin su aminaina biyu duk sun zo kuma sun min karamci anokanan aiki mata sun zo tunda taron na mata ne ina jin wani iri wani iri har aka gama taron dariyar yaƙe kawai na ke yi da ciwon kai na kwanta ranar dan sai da na saka ma aunty mama kuka ina cewa ita ta ja min gashi ana min auren dole ga khadijah sai kallon azzaluma take min ko bi ta kaina bata yi ba ta miƙa min wani pill na sha bayan ta sa an kawo min abinci wayoyi na ta kashe su duka ta rufe kofar da lock key ta waje dan in sami isashen barci babu daɗewa barcin ya ɗauke ni ban tashi ba sai wuraren 10am dan bana sallah shi yasa ta bani maganin na sha da na farka na yi wanka na koma na kwanta dan jiri jiri nake ji effect ɗin maganin bai gama sake ni ba kwanciyar ba dadewa wani barcin ya ɗauke ni sai 12 na tashi a lokacin na ji daidai na yi kokarin fita na ji kofar a rufe abin mamaki wayoyi na duk banu su salin alin na koma na zauna ina tunanin irin zaman auren da zamu yi nu da shi gashi dai muna son junan mu har mafarkin mallakar juna muke amma kuma babu kwanciyar hankali intruding factors su mana yawa ga koshi ga kwanan yunwa shi ne wannan al'amari ina tsaka da tunanin naji kici kicin buɗe kofa na daga kai ɗaya daga cikin matan nan ne masu min gyaran jiki ɗaure fuska na yi ganin shigowar ta dan zuwan ta bai cika kasancewar da alheri ba duk sadda za ta shigo da jiƙe jiƙe take shigowa kamar wata mai maganin gargajiya abin takaici yakr bani aunty mama ce ta bar mata wuƙa da nama sai ta ke son wuce gona da iri dan ta mayar da ɗure ɗuren kamar ruwan sha sai dai bata shigo ba daga tsuguna a kan wannan rushin sai shanye wannan sai tsotse wannan azaba kawai take gana min wai shi gyara gashi in ta fara murje min jiki kamar ta ga dutse ban yarda ta kai kirji na sai in ce ta tafi zan yi ba a son ran ta take incomplete work ɗin da take min ba kawai ta san ni ɗin ba yarinya ba ce bare ta min dole ta san zan yi ɗin aiko tana tafiya zan yi sama sama in rufe ƙofar minti goma mai kyau ban kaiwa nake zuwa in wanke in ta dawo in ce na yi saidai ta yi shiru toh a yanzu ɗin ma abinci ta kawo min ganin bana walwala ya sa ta ce
"Hajiya mamanku ta ce a kawo maki abincin ta ce tun jiya rabon ki da abinci"da toh na amsa mata ta tafi ina murnar bata kawo min surkullen da ta saba ba na buɗe abinci shar a ido na yi serving kai na na fara kaiwa baki ai da sauri na furzo shi waje na buga wata tsaki ina masifa ai dama na sani wannan mata babu alheri a zuwan ta wato ta san na gaji da shaye shayen magungunan da take kawo min shi ne ta saka min a abinci wannan wace irin jarababbiyar mata ce na buga wata tsaƙin na ɗau abincin a tray da ta kawo na yo ƙasa da shi sai hayaniya ake ta yi a gidan na wuce ɗakin aunty mama da abinci na ajiye mata a gaban ta

"Gashi nan ke kika saka matar nan ta raina ni ko wani lokaci cikin magunguna sai ka ce ni na ce mata ina laulayin ciwo da ko wani lokaci ban da shikir a gidan nan abinci magani ruwa magani da tana da hali ma barcin da nake samin yi magani zata bi ni da shi wannan wani irin takura ne ni fah na gaji"na ida ina kwafa jan hannu na tayi ta ce toh zauna baby na zauna kira ta yi aka kawo min wani abincin tsoron cin abincin nake yi ta ce in ci ba komai na kai spoon ɗaya na ji kamar ba komai sai na sake jiki na ci sosai har na yi rabi na ce na koshi ta miƙa min ruwa na sha ina ajiye cup din na ji ɗaci kamar na sha maɗaci sai na fara ƙaƙarin amai
"In kika fara zaki gamu da ni dan gidan ku"yamutsa fuska na yi na saka fuskar tausayi irin ana zalinta na din nan

"Yanzu shikenan ban da kwanciyar hankali a gidan nan komai magani"?

"Baki da sai kin je gidan mijin ki sai shi ya biye ma shiriritar ki amma a nan baki da shi shi kanshi in an kai ki sai ya saka mana albarka da gyara ki da muka yi shashashar yarinya"cikin ko in kula ta yi maganar kamar ƴar tsana a tsakiyar ƴan gida haka na koma  a gidan mu babu abin da aka fasa a ranar aka yi shuwa arab evening laffaya mai azababen kyau aka yane min jiki da anko muka yi da shi cream colour mai adon duwatsu masu kyau aka rankaɗa min kwaliya sai walwal na ke yi ko ina duwatsu ne a jiki na na ado extensive makeover aka min kamshi kamar kamfanin turaren maiduguri dan bari na ɗakin aunty mama matar nan ta zo ta rinƙa min turin turare ta tabbatar da turirin turaren nan ya biya koina a jiki na tun daga suman da aka kyalkyale shi har ƙafa na ƙamshi ne da aka gama kwaliyar aka buɗe ni da turare ƙarfe huɗu daidai aka fara gudanar da shagalin ranar ba african time tun fitowa ta aka saka slow kiɗa mai daɗi su salma da falmata ne a gefe na sun yi anko bayan mu ƴanuwan mu ne ban hango shi ba har sai da muka iso tsakiyar harabar wurin na hago shi zaune cikin rumfar a kan royal chair sai murmushi yake sakewa kamar wani wawa ya bi ya kafe ni da ido sai na rinƙa aika mai da harara amma bawan Allahn nan murmushi yake ta min kamar bai san me nake yi ba hAr muka karasa Inda ya ke da isar mu kafin in zauna sai yayi wuf ya miƙe ya fara zuba min kuɗi 1k note ya rinƙa zuba min sai da ya juye su duka tuni wurin ya ƙure da hayaniya ana ihu da mai kirari zama na nayi kamar ban san abin da ya yi ba shima ya zauna sai wani kallo na yake ni ni kunya ma ya rinƙa kama ni da irin kallon da yake min dan an cika a wurin mun zama tvn kallo flashes ta ko ina aka fara gudanar da program ɗin in har na ce bai yi kyau ba toh nayi karya dan ranar duk ya fita daban ko dan ango yake shi yasa yayi kyau na daban oho chan cikin rai na ina jin son shi na taso min da kishin shi amma ta wani gefen sai in ga kamar ina aikata rashin adalci ne

"Mrs Abdulsalaam kin yi kyau kamar kar in daina kallon ki ko dai a nan zan kwana yau"? Cikin calm voice yayi maganar wanda na ji maganar har chan cikin jiki na sai na yi shiru muryar shi na echoing a kunne na

"Are you shy of your groom Mrs Abdulsalaam"?? Banza na mai na yi kamar wasu nake kallo har da murmushin ƙarya sai ya juya dan ya ga ko da wa nake murmushin sai ya ga ba kowa juyowa yayi

"Ni kike nunawa attitude cutie"? Numfashi na sauke kawai dan na san magana yake son in yi mai ni ko fushi nake da shi

"Cutie ni ne fah so kike in saka maki kuka a taron nan"? Ƙala ban ce mai ba sai aka fara taka rawa a fili na mayar da hankali na ga masu rawan na yi kamar ban san da shi ba a wurin madaɗin ya kyale ni sai ya cigaba da min surutu da dai na ga bai da niyar yin shiru sai na ba shi amsa

"Humair dan girman Allah ka min shiru saka min ciwon kai kake yi"na ja baki na nayi shiru

Murmushi mai sauti yayi ya ce
"Toh na yi shiru Humairah"tsit muka yi har aka kira mu wai muzo mu taka rawa muka tafi filin kaɗan kaɗan muka taka yanayin daga ni har shi ɗin masu jin nauyin yin abu a gaban mutani ne sai muka yi abin cikin zamananci ana ta fesa mana turare da kudaɗe sosai aka cashe ba mazan ba ba matan ba abu dai yayi albarka around 7pm aka rufe taro lafiya aka sallami jama'a da kyaututtukar taron bai tafi gida ba ya tsaya jira na har na chanza kaya na same shi a jikin mota teasing ɗi na ya shiga yi

"Bar ganin ina kyale ki cutie zan haɗu da ke ne kawai barin ki fah nake yi saboda ban so hankalin ki ya rabu kashi biyu ki yi sha'anin ki cutie lokacin ki ne" hararar shi na yi na ce
"Damuwar ka"dariya ya fashe da shi ya ce

"Majeed zai zo gobe kar ki kuskura ki nuna mai auren nan ba cikin lumana ake yin shi ba dan akwai abin da na ƙulla mai kin ji cutie"? Sai na tsinci kai na da ce mai

"Wai har yanzu ba ka rabu da wannan majanunin ba heartthrob"? Smirk yayi ya ce
"Nahh sai mission ɗin mu ya cika cutie kawai ki bashi duk wani haɗin kan da yake nema dan shi zai haɗa mana dinner ya ce ya ɗau responsibilities ɗin komai na dinner"da mamaki na ce

"Shi ɗin ya ɗau ɗawainiyar dinner ɗin"? Murmusawa yayi ya ce

"Eh shi ne"
"Me yasa sai shi ni bana so"
Dariya yayi ya ce

"Cutie you are still childish ai baki san maƙiyi ba in yayi alƙawarin ganin bayan ka sai ya cinma burin shi a halin da ake ciki ya chanza plan yanzu nuna min yake yana supporting ɗi na kuma a yadda na gaya mai shine tunda kika mai wannan cin zarafin sai na wulaƙanta ki a duniya hanyar da zan rama mai hanya ɗaya ce shine in aure ki in mayar da ke a karkashi na sai yadda na yi da ke in ya so bayan na gama muzanta ki sai in kore ki daga gidan na kora irin ta kare korar wulaƙanci bayan na tabbatar da cewa na naƙasa ki na naƙasa maki businesses ɗin ki har rasa inda zai saka ranshi yayi ranar da muka haɗa plan ɗin dan murna toh Mrs Abdulsalaam kin ji abin da ake shirya maki ni kuma yana ganin ni ɗin wawa ne kamar shi na buɗe mai ciki na shi kuma yana chan yana haɗa min gadar zare wai zai mana komai na honeymoom ɗin mu a nan yake son ya cika burin shi dan so yake a hanyar mu na zuwa kar mu dawo kin ga ai babu wanda zai zarge shi da saka hannu a mutuwar mu kasancewar shi babban ɗa shine yake son cika burin mahaifin shi da bai karasa ba kuma fah na gaya maki suspects ɗi na har da wannan yayan ƙawar taki dan haka ki kiyaye su again i want to apologize ba zamu tafi honeymoon ba koh ya gama processing komai zan amsa in mai godiya amma ba za mu tafi honeymoon ɗin ba a nan gidan gonan nan zamu zauna har sai bayan 3months zamu dawo gidan mu a wurin kowa mun tafi honeymoon kin ga in ya ga plan ɗin shi bai yi working ba zai ɗaura plan B mu kuma a lokacin zamu tafi ainihin honeymoon ɗin mu a ƙasar da kika fi sodan haka ko da wasa kar ki nuna mai cewa you are not intetested in this marriage dan na gaya mai kin gama fadawa a tarkon so na kenan ki yi duk yadda zaki yi ki yi sourcing information a wurin shi kin gane ai"??

Doguwar ajiyar zuciya na yi
"Oh duniya budurwar wawa wai shi ya rantse sai ya ga bayan ka ne?bai ga duk yadda yayi Allah na nuna mai ishara ba ne?Allah ya raba mu da maƙiyan mu"da amin ya amsa min

"Kin san yau kyaun ki na daban ne cutie you were just like a glamour kin ki kyau dan haka dole in biya wannan kwaliyar"sai a nan na tuna ashe fushi nake da shi sai na haɗe girar sama da ta ƙasa na ce

"Riƙe kyautar ka ban so"kamar wata ƙaramar yarinya na yi maganar sai ya dara ya ce

"Cutie you can't ignore me ni na sani kawai jan aji ne irin ta ki"harara na maka mai na buɗe baki da nufin ba shi amsa sai ga ƴar saƙo wai in zo in ji aunty mama na ce toh

Kallon ƴar saƙon yayi ya kalle ni ya ce
"Wai rowar ki fah ake min ba damar in yi magana da ke ɗazu haka suka saka mana ido yanzu kuma sun aika a kirawo ki nine fah angon ko sun manta ne sun ɗauka sace ki zan yi ne"? kallon rigima na mai ina wani mar mar da ido na ce

"Wa ya sani abu a duhu ƙila nufin ka kenan shi ya sa suka gane suke kafa kafa da ɗiyar su"na ida ina kwafa  dariya ya rinƙa yi kafin yayi wani furuci na ce

"Sai anjima dan ban ga abin dariya ba a nan"fuu nayi gaba ina maganganu ya ma gama raina ni dariya yake ma maganata ko da na shiga ciki ummi da wasu matan da ke zaune a parlor suka rinƙa bi na da kallo har na ji na fara tsarguwa na cigaba da tafiya ta suma suka cigaba da kallo na na juya naga ni suke kallo muna haɗa ido da su suka yi saurin sunkuyar da kai suna magana kamar ba su ke kallo na ba except ummi da ta fashe da dariya haɗe rai na yi na ce

"Zo nan ummi"tashi ta yi ta tako har inda nake

"Gani yaya Aisha"
daɗa harɗe rai na yi

"uban me kika gani kije wa dariya halan"? Ai kamar na zuga ta sai ta tuntsire min da dariya kamar in buge ta

"Yaya Aisha ɗazu fah fuskar ki a murtuke kija rinƙa ƙunƙuni wai ba zaki fita ba yanzu kuma sai da aka aika ɗan saƙo ya kirawo ki awa fah ɗaya da ƴan mintuna kika ɗauka a waje fah shi yasa ake ta bin ki da kallo ana mutsmuts"ta ida tana dariya abin sai ya harzuƙa ni na ja doguwar tsaƙi na cigaba da tafiya ta ina cewa

"Ba na zama sa'ar ki ba da zaki na min dariya ba ba laifin ki bane"

***********

_kamu_

A kamun ma haka aka baza min ado da maroon ashobe mai kyau aka naɗa min ɗauri mai hawa hawa ya buɗe sosai aka sagala min mayafin ashoben aka kakama da pins dama zanin a kan rigar aka ɗaura min shi da takalmi mai tsini sai ƙwas ƙwas ƙwas sautin takalmin ke bayarwa na shiga motar ƙawayen amarya muka ja sai harabar da aka tsara dan gudanar da kamun angon da akan roke shi ya je kamu a namu case ɗin shi ne ke zumuɗin kasancewa a wurin dan ya riga mu tafiya haka a ranar ya ƙure ni da tambayoyi kamar ɗan jarida shagali aka yi sosai ba na wasa ba sai 6:20pm aka rufe taron bayan an raba gifts dan rigima wai shi zai maida ni gida ko sauraron sa ban yi ba na wuce na shige motar amarya ba saban ba sai ga sudden fever ya fara min sallama a taƙaice kusan kwana na yi ina rawan sanyi ga ciwon kai program ɗin da za'a yi washegari sai ɗaga shi aka yi zuwa ranar juma'a wato ƙaddararen bridal shower ɗin da na guji yi amma su ummi sarakan ƙauɗi suka assasa aka saka a wedding plan da kanshi ya ce bai yarda a yi wani bridal shower ba dan bana jin daɗi ranar thursday was a free day to me until around 5pm da Majeed ya zo wu na da fara'a ta na same shi muka gaisa ya tambaye ni kamar guest nawa zasu halarci dinner ɗin nace mai thousands dan daga ni har shi angon ƴan jama'a ne ina ankare da shi ya bini da wani mugun kallo

"Majeed ina bala'in son abokin ki Allah ya sa shima ya na so na hakan nan dan in ya ƙi ni toh tabbas wataran za'a neme ni a rasa"wani kallon banza ya jefe ni da shi sharewa na yi yana min tambayoyi ina bashi anmsa lokaci zuwa lokaci nakan yi deviating in shiga maganar son da nake yiwa Abdulrahman shi kuma ya ɗauka ni ke wahalar sai ya rinƙa murmushin mugunta akai akai sai da ya gama kiyastsin shi ya min sallama ya tafi nima na koma ciki da mamakin hali irin na Majeed kiran shi na so yi sai na tuna faɗa ma muke yi na yi buris na kyale

Ranar juma'a da ya kasance ranar ne ya kamata a yi walimar bikin amma aka ɗaga zuwa ranar bikin a ranar a ka yi bridal shower abin ya yi dan har hotuna aka ɗauka aka tura ma angon ba tare da sanina ba doguwar riga ce aka buɗe ta daga waiat har ƙasa sai yayi kamar Cinderella gown har abin balancing shape aka saka min ta ciki wanda ya taimaka ma rigar ya daɗa buɗew kamar lema high heels na saka pink dan gown ɗin ma pink colour ne sauran kuwa ankon chiffon gown suka saka da falmararta kamar dai nightgown kowace ta riƙe abin da nuni da ita ɗin wa cece salma married ta saka haka falmata ummi ƴar duniya ta riƙe taken ta yi ni kuma na riƙe bride to be aka min wani kwaliyar chanza kamanni dan ni kaina da na kalli kai na a mirror har tsorata na yi dan cewa na yi ya zata min over makeover bayan na hana ta yi min chaɓachaɓa da fuska cewa ta yi wai ai haka ake yi in dai ana bridal shower jin ta kawai na yi dan kar in bata ma bakin mu rai na yi shiru har aka fara gudanar da bridal shower ɗin it was actually fun dan na ji daɗin abin sosai ƙiɗa aka sake ai manta cewa amarya nake na chanchare rawa ganin duka taron mata ne ba maza an yi farinciki da annashuwa an rufe taro lafiya duk masu tsokana ta ina jin su na yi kamar ban ji a ranar na yi wankan tsarƙi na fara sallah lokaci zuwa lokaci na kan tsinci kai na cikin faɗuwa gaba wanda ban san dalili ba na kan yi tunanin maganganun firgitatwar da salma ke gaya min akan maza da rashin sanin da suke nuna ma mace da zarar an kai ta gidan su dan bijirewa suke yi su nuna basu san ki ba dan in har fagen auratayya ne toh maza ba su da ta ido duk shekarun su in na yi wannan tunanin sai in yu saurin kawar da shi ai shi Abdulrahman ba haka yake ba he is gentile he won't play rough with me not at all da haka na rinƙa saƙa ina warwara kwatsam ina zaune na sai ga kira wai daga hajiya mai gado wato mahaifiyar aunty mama na ji mamakin kiran nata dan bata taɓa min kira cikin dare haka ba tsoro ne fal rai na ga tsoron abin da zai faru a washegari na aure na ga fargabar da ban san dalilin ta ba haka na tafi na same ta muka yi cracking jokes ɗin mu kafin ta natsar da ni ta fara karanta min rayuwar aure daɗi da ɗacin ta sadaukarwar da ke cikin ta ladduban da ke cikin ta haƙƙin junan mu akan ɗanuwan sa haƙuri da tawakkalin ta sai na ji jiki na yayi sanyi kamar a ranar za'a kai ni sai ga hawaye dan maganar nata ya shige ni ba ƙaɗan ba duk sai na ji auren ya gundire ni dama ga kira da laƙabin da na ma sunan na auren dole sai na ji komai ya ishe ni rarrashi na ta yi ta ce ta san me nake ji amma wannan ba kwakwaran dalili bane da zai saka ni kuka shar ba kamar dole ake son yi min ta ce sanin zan bircike da yawa ya sa ta ce a kirawo mata ni tun ranar dan in na kwanta zan sami mafitar makomar aure na kafin washegarin auren komai zai min sauƙi ta gama ta ɗora da cewa

"Mummuna huɗubar ƴan zamanin kuma iyayen ki zasu maki dan wannan sai su ba ni ba"da raha ta yi maganar na san me take nufi sai na ji kunyar ta wato duk girman ka da ilimin ka in ka kasance kamilale wanda bai bada darajar shi da ƙimar shi ga wani da ba mijun shi ba rahama ne dan sai nake jin kamar sabuwar ni aka halitta dan waɗannan nasihohin nata sun saka ni jin ni da Abdulrahman mun rigada mun zama ɗaya saboda na san ba yadda za'a yi yayi tarayya da ni ya kalle ni ya ce min marar tarbiya dan ban zubar ba na adana mai

_*(virginity ɗin mace shi ne maƙullin duk abin da ta budewa kanta in ma alkhairi ko akasin haka dan wata macen duk talauci duk tsanani ta gwammaci ta zauna a cikin halin kakani kayin da ta taso a ciki amma mutuncin ta ya fiye mata komai wata kuwa kishiyar zuciyar ta ya fi karfin kyakyawar zuciyar ta dan haka ba zata iya copping da halin da ta taso a ciki ba na ƙuncin rayuwa dan haka ga hanya mai sauƙi da zata sami jin daɗin rayuwa kawai sai ta biye wa kishiyar zuciyar ta a karshe ko ta manyanta auren ba wani muhimmanci zata ba shi ba dama dan hutu ne kuma tana samu toh me zata yi da auren alhalin ba haka bane dan aure ya kasance rahamar ubangiji ne ga wanda ya so most of mata da ke zaune a gidajen mazajen su basu kai masu martabar su ba amma mazan ba su nunawa ba wai dan basu sani bane sai dan kawai wata dalili tasu da suka barwa kansu kuma mu sani we shall be accounted for all what we did here in dunya kuma duniyar zata ƙare to da me zamu kare kan mu a gaban mahaliccin mu kunyar har ina zamu kai shi gwara ki mutu a talauci da ƙimar a a wun mahaliccin ki da ace kin mutu cikin daula babu hijabin martabar ki kuma ki je chan ki rasa abin suturta kanki dan tun a duniya kin ɓata aljannar ki dan Allah mata mu rinƙa tsoron ubangijin mu abin da ubangijin ki bai baki ba waye shi mutum da zai ce maki zai baki kuma ki yarda zai ba kin har ya ja ki da shiga hallaka da haka nake rokon mata da su riƙe ƙimar su da mahaliccin mu ya bamu da rahamar da ya mana dan shi kadai ke da ikon yi mana hakan ba wani ɗan Adam na kuma duk tsanani yana tare da sauƙi sai dai in bamu iya karbar jarabawar ubangijin mu ba Allah ya yaye mana son abin duniya ya kare mu daga jefa kanmu cikin uƙubar rayuwa da zamu dawo muna da na sani Allah ya kiyaye mu da zuri'ar mu baki ɗaya amin)*_

da tunanin maganganun hajiya mai gado na kusa karar da daren saloli kam ya aure ni a daren ban dawo cikin hayyaci na ba na tunanin auren mu a matsayin auren da ke ɗauke da hakkin kowa ba sai da na gama salolin nafilfilu na ɗaga hannu na na roƙi Allah da ya tabbatar min da alheri in dai yin auren shine alheri a gare mu baki ɗaya Allah ya tabbatar na shafa sai a sannan na fara jin sanyi na cewa eh fah ina ji a jiki na auren nan akwai alkhairi kuma zaɓin ubangiji ne a gare ni sai na rinƙa jin baƙon al'amari tattare da ni i have no any other choice but keep on blushing ganin saura ƙiris in yi wa kaina kunun kanwa barci mai rai da lafiya ne ya ɗauƙe ni tun 12 sai past 4am na asubahin safe garau na tashi da jin daɗi da ban san dalili ba tun wuri aka fara kwaramniya da hayaniya sallah na yi na kwanta na bi lafiyar gado sai na tsinci kaina dazaƙuwa in ji an ɗaura auren ɗaukar wayata na yi na danna mai kira ringing biyu ya ɗauka

"Amarya ba kya laifi ko da kin sace sadaukin granny ne ya daren ki"tsintar kaina na yi ina murmushi na ce

"Angon amarya amarya ta kwana lafiya da fatan angon ta ma ya kwana lafiya"? Sai na ji yayi shiru na san mamaki ne ke ɗawainiya da shi sai na murmusa na ce

"Kana mamaki ne"? Da sauri ya ce

  ""Of course cutie ina mamaki ya aka yi haka"? Dariya na yi na ce

"Ka manta dare ɗaya Allah kan yi bature"? Sai yayi murmushi mai ƙayatarwa
"Ni ko na san haka tunda gashi Allah ya haɗa ni da ke ta inda ban taɓa tsammani ba har haɗuwar tamu ta zamto alkhairi tunda saura awowi uku da mintuna arba'in da biyu da seconds talatin da shida"exclaiming na yi
"Whoa lallai ka cika zumuɗi angon zamani"gabaɗaya muka yi dariya

"Ina son boss lady  ɗi na"
"Nima ina son Humair ɗi na"wani farinciki ne ya ziyarce shi sai kawai ya ce

"Is this real cutie"? Dariya na yi kawai na ce

"Saura ƙ
Kaɗan ka tabbatar da hakan"

"Can't wait for that moment Humairah"saurin sallamar shi na yi ganin aunty mama ta shigo tare da matar nan aiko ya rinƙa kira ina ta sakawa a silent sai aunty mama ta ce in ɗauka mana ɗaga wayar na yi na kara a kunme kafin in yi magana ya riga ni

"Cutie you looked precious yesterday da fatan complement ɗi na yayi maki daɗi"? Da uhum na amsa na yi saurin kashe wayar ajiyewa nayi ai tuni jarababbiyar matar nan ta nufo ni wai hayaƙi zata min dan haushi kasa furta komai na yi na yi shiru ta gama haɗe haɗen ta ta fara lulluɓe ni ina ji ina gani ta banka min hayaƙi kuma ta hana ni fita sai da na daɗe a ciki kafin in fito aunty mama ta bani breakfast na ci duk abin haushi ɗacin tsiya na gama ci ina yamutsa fuska dan haushi daga nan na shiga wanka ruwan wankar ma dan iyayi shima turaren ne dai a ciki har dasaka min ƙaidar yadda zan yi a ciki hakan na yi na fito aka fara lailaya kwalliya shigar farko da na yi na atamfa ce Hollandaise mai zanen crayfish riga da zani sosai na fito a amarya ta ni kaina ina ta admiring kai na zuwa lokacin ƴan zuwa biki sun fara cika gidan hotuna aka fara yi mana bayan wani lokaci na chanza zuwa swiss lace maroon  colour da zanen lemon green shima da zanin ne aka yi hotuna daga shi na saka wani boyel lace baƙa mai adon duwatsu a nan ne kuma wata ta rankaɗo guɗa har cikin kirji na na ji guɗar tana shelar an ɗaura aure sadaki mai albarka Allah ya albarkaci auren sai guɗa ake ta sambaɗowa nikuma na ji ni wani iri sanyi sanyi na fara ji kokartawa na yi na gama shiryawa sakamakon jin kiran da Abbu ya min ni da su ummi da wasu ƴanuwa muka tafi hotuna ne aka rinƙa ɗaukar mu har dai aka shiga ɗaukar video ƴan ma'aikata na duk sun zo mazan sun halarci ɗaurin auren matan sun shigo ciki duk an mana hotuna da su ana tsaka da daukar hotuna na ji kiran shi na ɗauka

"Officially Mrs Abdulsalaam Abdulshakoor"

Rasa bakin magana na yi sai kawai na ce

"Uhumm"murmusawa yayi ya ce
"Ba dai har kin fara tsoron angon na ki ba"da sauri na ce
"A'a" tuntsirewa yayi da dariya dan ya san a tsorace nake

"Alright sai mun haɗu a wun dinner kin san wai rowar ki ake min"daga haka ya katse kiran dan ina jin ana ta kiran sunan shi..

An yi yinin biki lafiya inda zuwa karfe uku da rabi aka gabatar da walimar bikin har sai karfe biyar aka tashi zuwa karfe shida da mintuna talatin aka saka ni nayi wanka da alwala aka shirya ni cikin doguwar riga da mayafin shi babba aka fara kai ni wurin Abbu inda ya rinƙa min nasiha akan sabuwar rayuwar da zan je in tarar da haƙurin da zan ɗaɓaƙa daga nan aunty mama ce ta rinƙa min nasiha har da sharar kwalla nima ta saka ni yin kwallar daga nan manyan matan suka min nasu nasihar daga nan aka saka ni a mota tare da hajiya mai gado da wasu manyan mata motoci biyar suka raka ni har tanfatsetsen gidan mu da ke maitama sai zumuɗi ake yi da wasa gidan ba laifi da shigar mu aka saka ni yin sallah dan za'a min shirin dinner sallar na gabatar na ƙi tashi har sai da aka yi isha'i na sauke sannan aka fara chanchara min adon dinner mai ɗaukar hankali white and blue open gown na saka aka min wani ɗauri ta gaba aka buɗe shi ta gefe kamar fanka ƴar pose ce a hannu na mai kyalli white colour da takalmi mai tsini shima white ras na fito mota ɗaya muka shiga da ango ni ban sani ba sai da aka rufe kofar na ji an ja min hannu wani faɗuwar gaba ne ya riske ni da sanyi sanyi kafin in ankara na ji ya kai hannun baki yana kissing

"You are looking just like your name cutie"sauke numfashi na yi na ce
"Thanks"daga haka aka ja mu har zuwa hall ɗin bai sakar min hannu ba har sai da aka buɗe kofar motar inda a nan ne ya sakar min hannu muka fito ƙaɗan kaɗan nake takawa har muka haɗe da shi inda ya kuma riƙe min hannu na har cikin hall ɗin khadijah da ke gefe da ango ta fara fetso mai turare nima ummi ta fara fetso min da mamaki na kalle ta ta kashe min ido muka cigaba da takawa har ciki inda muka zauna a kujerar da aka tanadar mana abin ƴan boko aka fara gudanar da program tiryan tiryan har aka yanka cake na bashi ya bani muka ɗau hotuna kala kala aka ci aka sha daga karshe ya ja ni muka fito inda a nan na kare mai kallo yayi bala'in kyau shima shigar shi lusan irin tawa shigar ce muna fitowa ya saka ni a mota ya ja wai kan shi ya fara ciwo wanda na san karya ne dan abokan hurɗar shi duk sun zo kuma da gani akwai ƴan duniya a cikin su duba da yadda suke ta bi na da kallo shi yasa ana gama yankar cake ɗin ya ja ni waje wai kan shi ke ciwo bai tsaya ko ina ba sai gate ɗin gidan mu ya danna horn aka buɗe mai ya shiga yayi parking ya fito jin yana bada instruction na ji wai a rufe mai gida kan shi na ciwo baya son hayaniya gefe na ya iso ya buɗe kofar ɗan kankwafowa yayi ya manna min peg a kumatu kawai sai ya saka hannu ya ɗauko ni in a bridal style da kafa ya tura murfin motar muka zo ƙofar falon duk nAuyiN shi nake ji
"Yi sallama ki shiga gidan ki Mrs Abdulsalaam"sallamar na yi muka shiga ciki ya rufe kofar yana min wani irin kallon kurilla......

*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama Ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

158K 9.9K 45
Elizabeth has been ruling her kingdom for 3 years now. She's gone through countless advisors in those 3 years. When she's finally ready to give up on...
840 127 34
BA KYAU BANIBA ABUN DAMUWA DA ABUN ALFAHARI ƘYAN HALI DA KYAKYAWAR ZUCIYA SHINE CIKAKKEN ƘYAN FUSKA! KOWANNE BAWA DA TASHI JARABAWAR ITA KUMA LATYFAH...
657K 23.6K 200
[FIXED/FAN TRANSLATION] A student who was preparing for the Civil Service examination for 4th year suddenly found himself in an unfamiliar body 3 yea...
1.9M 97.2K 38
Presenting the story of ISHIKA MEHRA Whose innocence made the king bow down to her AND ABHIRAJ SINGH RATHORE Whose presence is enough to make the per...