🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

Per SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining Més

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 63-64

631 47 4
Per SiyamaIbrahim

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

6⃣3⃣➖6⃣4⃣

Miƙewa tsaye na yi na matsa baya ina kallon shi ban san ta ina ba amma wani mugu mugun ƙaunar shi ke shiga na ina jin ba zan iya rabuwa da shi ba amma dole in kiyaye son zuciya da son kai na tare na gansu da khadijah da ita ya fara soyayya ni tsakanin su na shiga ban ma soyayya adalci ba in har na amince da auren shi dan tun yanzu ga halin da ta shiga duk a dalilin son da take mai tana neman salwantar da rayuwar ta duk dan na shiga tsakanin ta da masoyin ta me ya kaini shiga tsakanin su tun farko me yasa na kasa bude idanuwa na tun farko sai na bar su a rufe ina biyewa son rai na yanzu ga abin da ya janyo min ta ina zan fara ga son da nake mai ga tausayin dija da nake ji na katsalandan da na mata yayin da take tsaƙa da jin daɗin soyayyar ta anya na yiwa kaina adalci kuwa? na kyautawa kaina da rayuwar ƴaƴa na kuwa? zan iya cigaba da zama da haƙƙin wata a kaina while nikuma ina chan ina rayuwa cikin sukumi kuwa? kaii a'a ya kamata in roƙi afuwar dija sannan in bata haƙuri i think iya damar da nake da shi kenan na wanke kaina a wurin ta in banda wannan bana jin zan iya yafewa kaina abin da na mata dan na cutar da ita da wannan tunanin na tsaya chak na zuba mai ido na wasu lokuta

"Ina so zan je gidan su khadijah dan ina buƙatar magana da ita"a gigice ya miƙe

"Cutie har yanzu baki fahimce ni bane?ko bayan wannan bayanin ma kina fushi da ni ne"? Murmushin da ya fi kuka ciwo na yi na ce

"A'ah duk na fahimta kawai ina buƙatar ganawa da ita ne"tsayawa yayi yana mamaki na
"Kenan bukata na bai iso ki ba kike nufi"?

"Bukatar ka ta iso ni amma amincewar bukatar lies on so many factors wanda ban isa in tantance su kai tsaye ba"

Kallo na ya ke yi yana jin mamaki

"Me kike buƙatar bincikawa akai na? sanina ne baki yi ba ko baki gamsu da yardar da ke tsakani na da ke bane?menene baki sani akai na ba da har kika tunanin ba zaki iya amince min ba har sai kin bincika"?

"Hmm sanin ka da sanin tarihin ka ba matsalata ba ce in ni da kai mun san gaskiya wasu na bukatar a ganar da su ainihin abin dan haka ina buƙatar ganawa da dija"kaiwa nan na dau car key ɗina na dau wayata na fara tafiya tare min hanya yayi

"Banu inda zaki tafi Aisha me yasa baki da tausayi ne a duk lokacin da wani kofar farinciki ta bude min burin ki ki rufe kofar forcefully kawai kan ki kika sani babu ruwan ki da feelings ɗin wani i cared about you shi yasa na jure duk wasu abubuwa dan dai kawai in mallake ki a matsayin abokiyar rayuwa amma duk hustles ɗina ba kya gani kan ki kawai kika sani"

Kwayar idon shi na kalla na ga bacin rai amma duk yadda zai ɗau maganar sai dai ya ɗauƙa in ya so ma ya cigaba da min kallon selfish being amma ba zan iya cin amana ba

"Kana iya cewa duk abin da ran ka ke so akai na amma hakan ba zai sage min gwiwa ba dan ni na san abin da muke yi akwai ayar tambaya in kai baka yi la'akari da hakan ba"

Kaiwa nan na kama hanya na buɗe ƙofar na fita ina jiyo shi yana cewa but i said i wanna marry you na yi shiru na cigaba da tafiya a daidai lokacin da na hau kan titi a lokacin na ankara da shima bi na yake yi ina gaba yana baya ƙara speed ɗin motar na yi dan kar ma ya kamo ni haka shima ya ƙara gudun nashi motae kamar masu wasan tsere haka muka rinƙa sharara gudu da motocin mu a kan titi ban ankara ba na hango babbar motar kwashe kaya na dunfaro ni at the same direction da na ke tuƙi a 360 na juya hancin motar Allah ya kiyaye babu abin da ya same ni shima ganin hakan daga nesa ya rinƙa danna min horn amma na zata kokarin hana ni yake yi buɗewar kofar motar na ji na juyo kamar zai make ni ya ce
"Fito"babu musu na fita daga motar girar sama da ta ƙasa a haɗe ya fara masifa

"Are you out of your senses Aisha so kika ki yi committing suicide? kina jan mota kamar ba mace ba don't you care about yourself and people around you that love you? yarinyar da kike son halaka kan ki  saboda ita ba damuwa ta yi da ke ba amma ke duk kin bi ki takurawa kanki kina ganin ko mutuwa kika yi tana da asara ne? Why don't you care about your wellbeing? Am tired of all this drama act show   ki amince ko kar ki amince Aisha zan tafi neman auren ki in kin so ki yi abin da ya fi maki daɗi a ran ki tunda baki da brain ɗin da ke hasaso maki masu son ki da maƙiyan ki"yana kaiwa nan ya shige motar shi yayi gaba kuka ne ya ci karfi na sai yi nake a karshe shiga motar na yi na cigaba da nufan hanyar gidan su dija ko da na isa gidan na kai kimanin mintuna talatin zaune ina jiran ta kafin daga baya ta sauko da stick ɗin da ke taimaka mata wurin tafiya cikin shigar doguwar abaya brown color da gyalen shi ta yafa a gaskiya ta sacce dan ta rage jiki ba kamar yadda na san ta ba a da sai ta daɗa haske ta ƙara min kwarjini.

Karasa saukowa tayi tana yi kamar bata san ta bar mutum yana jiran ta ba ban damu ba da ta karaso na je na rike mata hannu dan im taya ta zama amma me sai ta fizge hannun tana kallon wani gefe ta dogara ta zauna abin ta na san hakan zai faru dama zama na yi kusa da ita

"Khadijah ya jikin ki"?
  Murmushi ta yi ta kalle ni kyar ta ce
"Idanun ki basu nuna maki amsar tambayar ki bane"? jim na yi kadan duk cin kashin da zata min bata da laifi ni na janyo

"Allah ya ƙara lafiya"
  "Amin in ya kai zuciya"ta bani amsar tana kallon gefe guilty conscious na dami na da attitude din da take nuna min shiru ne ya ratsa wurin kafin in yi magana

"Khadijah na san ni mai laifi ce dan girman laifukan da na maki basu kirguwa bare a faɗe su a baki amma ina mai neman yafiya da afuwar ki gare ni dan alhakin ki shi ke bibiya ta duk na kasa saƙat bana son tunowa dan ba abu mai daɗi bane ki yafe min ni kuma na maki alƙawarin barin Abdulrahman har abada kuma zan gyara maku alaƙar ku ya dawo kamar da ki yafr mim shi kaɗai nake buƙata a yanzu"ido na sun kawo ƙwalla a hankali ta juyo ta zuba min ido babu alamun wasa a fuskar ta

"Hmm Aisha kenan ashe dai kina sane da cin amanar da kika min har ma abin na damin ki wonderful da kike neman yafiya na akan wani laifi?boss lady you rule komai kike so kina samu a plater of gold me kuma ya rage?kin kwace min komai kin saka ni na shiga halin da ba na wa ba na shiga aikata ɗaɓi'u da ba'a haifo ni da su ba the fact that gudan mu free home ne ba'a koya mana rashin ji ba ni nikadai na fita da ban ni ce mai bin maza ni ce mai shaye shaye ni ce marar madafan dafawa duk saboda Abdulrahman da ya ke nuna min halin ko in kula akan ki a dalilin ki Aisha Murad hmm,sannab kina tsammanin zan yi saurin yafe maki? wani hisabin sai a lahira game da ce min da kike zaki rabu da shi har abada kuma zaki haɗa mu kamar da dama ba tare kika same mu ba kika shiga tsakanin mu? ko kin manta un tunasar da ke?ni ba jaka ba ce da zan auri gangar jikin mutum ba alhalin na san zuciyar shi da hankalin shi na gun wata macen daƙiƙanci na bai kai nan ba dan haka ki tafi ku cigaba da shirye shiryen auren ku ko Abdulrahman ya kasance autan maza a duniya baki ɗaya na yafe maki shi na bar shi har abada dama ai matar mutum ƙabarin sa in da rai da rabo a tsakani na da shi ko bayan shekaru da auren ku zan dawo muyi aure komai yawan yaran mu komai tsufa dan haka ki tafi kawai na san cewa zai aika neman auren ki gidan ku komai na sani ina maku fatan samun zaman lafiya a rayuwar auren ku na bar ki lafiya"..

Miƙewa tayi ta wuce ni kuma na zauna kamar saƙago dan mamaki da rashin jin daɗi na so mu yi doguwar magana ko da zagi na zata yi ta yi in dai zata yafe min amma wannan kamar daɗa ƙara rura min garwashi ta yi a zuciya ta game da matsalolin da ya faru a tsakanin mu kenan har zuwa lokacin akwai rift tsakanin mu inalilahi wainailaihir raji'un ya zan yi a haka na fita na bar gidan gidan mu na wuce na tarar da aunty mama zata fita cikin sauri tana amsa waya da ƙaraji na karasa na faɗa mata a jiki tare da sauke wani zazzafar kuka

"Ta ƙi yafe min aunty mama ta bar ni da haƙƙin ta bata yafe min ba ina zan saka rai na me ya kai ni aikata wannan aika aikar"sai kuka rungume ni ta yi dan ta gano dija nake nufi ita ta ma manta da wata dija ɗago ni ta yi ta

"Ya isa haka baby sai me dan bata yafe maki ba? ke ba yafewa wata farincikin ki kika yi ba a baya?toh sai me dan wata ta ƙi barin ki ki ji daɗi kin damu da ita ne meye haɗin ku?kashe mata nata kika yi ko ita kika kashe da kike takura kan ki saboda ita? kar in kuma jin wannan shiriritar kamar ba mace mai ilimi ba? "

Ɗagowa na yi ina kallon ta
  "I killed her silently na hana ta farincikin ta fah aunty mama baki san abin da ya faru da ita ba ta sanadiya ta"a nan na shiga labarta mata komai ina kuka sai jikin ta yayi sanyi

"Baby dama ba'a jin daɗi farat ɗaya sai an shiga jarabawar ubangiji  dan haka baki da masaniya a kan kaddarar ki kawai ganin su kike yi bare ki ce zaki hana waɗannan matsalolin afkuwa baki da laifi ko kaɗan hmm"? Jin ta kawai na yi ya zata ce ban da laifi

"Baki fahimce ni ba amanar ta fah na ci"

Murmushin manya ta yi ta ce
"Kece dai baki fahimta ba har yanzu dan kamar kina son ja da ikon Allah ne dan haka tun wuri ki yi istigfari da shirmen da kike kokarin yi komai zai wuce kin ji"? Girgiza mata kai na yi ta min murmushi ta ce

"Ina da appointment ba zan dawo da wuri ba sai 2 dan haka ki kula da kanki"ta yi saurin fita nikuma na karasa ciki throughout tunani nake ta yi kuma ya ƙi kira na nima haka kusan kwanaki biyar a tsakani ranar weekend na ga ana shirye shirye a gidan mu ɗora wannan sauke wannan girki kala kala na tambayi wani sha'ani ake yi suka ce babu kawai in wuce in huta it was so wired to me na dai yi gaba abi na ba su suka kimtsa ba sai wuraren azahar  a inda babu daɗewa ina ɗaki na na ji horn ɗin motoci har biyu na leƙa ta window ban hango komai ba na koma na zauna ina jiran ganin ko su waye baƙin da ake ta yi wa hidima tun safe amma still ban hango su ba haƙura na yi da gadin sai chan na ji hayaniyar su ummi da sauri na miƙe ina mararin ganin ƴar uwata ta riga ni shigowa rungume juna muka yi kamar in yi kuka ko ba komai naka ai sai naka hira muka shiga yi tana ta vani labarin gidan auren ta da yadda mijin ta ke kula da ita abin sha'awa  sai na ji mata daɗi ina ma nima haka zan sami mijin auren

"Yaya Aisha wai ya na ga kamar ba kya cikun walwala ne"? Da mamaki na ce

"Ummi me kika gani"?
"Gani na yi ya kamata ace farinciki ya ƙaru ko dai ba kya murnar yau ne"? sai na ji wani iri kar fah damuwa na ya shafi marainiyar Allah bata ji ba bata gani ba sai na sake fuska ta

"Of course not ummi ni ke farincikin wannan rana kuwa"sai ta sake jiki muka cigaba da hiran mu chan aunty mama ta shigo ta same mu ni da ita ta ce mata mijin ta na jiran ta yana so ya tafi wani wurin ba kunya ta miƙe tana

"Ohh ni farida yanzu mine ɗin na bari yana ta jira ni subhanallah yaya Aisha barin zo"da dariya muka bi ta da kallo yarintar ummi bai sauya ba fitan ta aunty mama ta juyo ta kalle ni da serious face

"Aisha"jin ta kira sunan kai tsaye na san da akwai wata a ƙasa dan in har ta kira ni da sunana akwai muhimnin magana

"Na'am"riƙe hannu na ta yi

"Ƙila ki fe ba's maki daidai ba amma yin hakan shi ya fi zama daidai da rayuwar ki dan ina so ki sani matar mutum ƙabarin sa duk nisan daɗewa in Allah ya ƙaddara ya kuma hukunta sai kin auri mutum toh duk wayo da dabarar ki fah sai kin aure shi dan haka ina so a matsayin ki na ƴa mace mai ilimin addini da na zamani da ki karɓi ƙaddarar ki da hannu bibiyu nikima ina mai shaida maki da ba zaki taɓa kukan da kij sani ba"da sauri na ɗaga ina kallon ta ina maganganun ta suka dosa

"Aisha a yau mahaifin ki ya bada ikon auren ki ga Abdulrahman nan da watanni biyu masu zuwa sun kawo gaisuwar su da sadaki haɗe da kayan na gani ina so ga shi wannan ma cikin kayan na gani ina son ne"ta saka min maƙulin mota a hannu na ta rufe bata bani chance ɗin magana ba ta ɗora

"Bana son jin ja in ja dan na san me kike shirin yi kafin nan ina so kiyi wa mahaifin ki biyayya dan ya gama yarda da ke ya kuma amince da tarbiyar da ya baki shi yasa ya tambaye ni kina da masaniya akan batun na ce mai eh bai tsaya doguwar bincike ba ya yarda da sun ganin daga ke har shi ɗin masu mutunci ne dan haka bana so ki watsawa mahaifin ki ƙasa a ido baby auren nan shine kwanciyar hankalin ki da shi kan shi ki cire tsoro da zargin kan ki dan ba zai kawo maki cigaba ba da wannan nake so ki riƙe martabar ki da ƙimar ki na ƴa mace mai tarbiya ki rungumi wannan lamarin da wannan abin hukuncin Allah ne kawai ba na mutum ba da fatan ba za mu sami saɓani daga gare ki ba dan shi bai da matsala"!! Kamar a dasa haka na yi a wurin ban fah dawo hayyaci na ba ta ɗora

"Ki tanaji wanda zai yi taking over a offishin ki dan daga gobe karshen satin nan kin ajiye zuwa aiki sai bayan bikin ki ai kin san me nake nufi ko mamana"? Ta ida tana murmushi menan gyaran amare za'a min tun ban yarda da auren ba ikon mai duka hmm ɗaga mata kai kawai na yi alamun na gane daga haka ta fita sai ga ummi ta dawo ta ga ni a wani yanayi

"Yaya Aisha lafiya kuwa"? Kallon ta na shiga yi
"Wai koh dai har kin fara gundura da zaman jiran ranar ne yanzu fah aka gama yanke ranar zai zo ne ai wata biyu kamar awa biyu ne fah yaya Aisha"ta ida tana murmushi imagine wato itama ta san komai kenan amma ta kasa gaya min

"Dama kin sani"? Da mamaki ta ce

"Eh mana ai shi yasa muka zo ni da mine kuma nake tambayar ki koh ba kya farinciki ne kika ce kina yi"kenan bata san cewa ba da amincewa ta Abdulrahman ya turo gidan mu ba lallai ana shagali shiru na mata ta yi ta surutun ta ta kwanta wai bacci take ji kallon ta kawai na rinƙa yi

Amma Abdulrahman ya riƙa ban yarda ba ya min shigan bazata straight wun iyaye ba tare da amincewa ta ba ko ya ɗauka wasan yara ne abin bai ma damu da kallon maciyiya amanar da za'a min ba kawai kan shi ya sani hmm akwai sauran aiki muddin aka ce auren nan will take place..

Sai dare su ummi suka tafi a rakiyar da na mata ne take min tsiya
"Yaya Aisha ki fa tsaya aunty mama ta jiƙa ki da kyau kar kiyi wa kanki ƙeta dan Allah nima haka na so yi i never knew taimako na take yi dan haka mu dai ki tsaya ki jure wahalan gyaran nan dan zaki ji daɗin shi in kika shiga daga ciki"ta karasa tana kashe min ido tare da yin dariya daƙuwa na mata ina murmushi
"Ummi kin raina ni wallahi kar fa ki manta yayar ki ce ni"ta juyo tana dariya ta ce
"Kuma mai sunan kakar mu ba"dariya muka yi baki ɗaya na ɗaga mata hannu suka wuce ni kuma na koma ciki

Komawa na ciki na yi zaman diris ina ta tunanin mafita me auren nan zai kawo alkhairi ko akasin sa da haka n kwanta na yi bacci ina ta mafarke mafarke barkatai a washegarin ranar da aka kai kuɗin aure na na rinka saka idon ji daga gare shi amma kamar ya san dama jiran kiran shi nake sai ya ƙi kiran kamar in yi hauka sai ga aunty mama ta shigo da tablet a hannun ta ta zauna kusa da ni

"Amarya ga wasu fah samples da na kawo maki ki duba na san ba zaki rasa taste ɗin ki ba"tana maganar ne yayin da take nuna min screen ɗin table ɗin kamar in saka kuka wai amarya wato ita babu ruwan ta da damuwar da na shiga kawai shirye shiryen bikin take yi.

Ignoring ɗin ta na yi tana ta magana ta ji ban bata amsa ba sai ta ɗago

"Baby lafiya kuwa ina ta magana kin min shiru ba kya jin daɗi ne"? Me aunty mama ke nufi tana nufin bata gano halin da nake ciki bane ko me? na yuwa kaina tambayar sai na dai cigaba da yin shiru

"Baby ko dai collection ɗin basu maki bane sai a yi ordern wasu samples ɗin ko ƙawar ki falmata ta turo wasu tunda ita ta bada shawarar a fara nuna maki waɗannan ta ce kin fi son su"?!

Imagine har falmata ta san da zaman wannan aure yaushe aunty mama ta zama PRO ban sani ba maganar jiya jiyan nan har ta gama yaɗa shi

Kamar zan yi kuka
"Wai shi auren nan dole ne sai an yi shi? na ce bana so auren dole fah zaku min da bai nemi izini na ba ya min shigar gadara da isa sannan madaɗin ki taya ni rejecting wannan violence ɗin har wani planning kike yi kuma kin gama sanar da friends ɗi na haba mana ni ya ake so in yi ne"? Da kuka na karasa maganar abin mamaki dariya ta min ta miƙe tana faɗin

"Toh tunda baby na har yanzu tana stage of shock game da auren ta har ta kasa zaban kayayakin ta na aure bari in tafi zan dawo bayan kwana biyu na san zuwa lokacin kin gama accepting fate ɗin ki see yah"ta yi gaba na ji kamar in kurma ihu wai babu wanda ya fahimce ni ne ko dai nba su son fahimta ta ne? shi kuma ya kira ya ƙi nikuwa na yi alƙawarin da zarar ya kira ni toh tabbas sai na zazzaga mai akan me zai saka a min auren dole sai ka ce wacce ta rasa masoya

********************

Abu kamar wasa har sati biyu ya wuce sai shirin biki na ake yi amma ni da ake yiwa ɗin bai ɗaɗa ni ba dan wani haushin angon nake ji ya san yayi laifi tun ranar da muka rabu da shi bai kuma kura na ba amma ban cire rai ba na san zai kira ɗin.

An fara min gyaran dole dan tun ina dojin fita har na fara kai kaina ɗakin dan na ga ran aunty mama ya fara ɓaci da ni Abbu ya bani zaɓin ƙasar da nake so a yi min siyayyar kaya na ce duk wanda aunty mama ta zaɓa yayi dan haka ita ta zaɓi ƙasar Dubai da china wasu kayan ta yi ordern su ne ta online wasu kuma ta shirya masu tafiyar musamman zuwa ƙasashe biyun wanda ta ce ba sai na tafi ba za ta na turo min pictures ɗin wasu kayan in zaɓa jin ta kawai nayi..

_4 days after_

Ana kan dilke ni da kayan chanza kalar jiki na gargajiya na ga haske a waya ta na kai duba na sai na ga sunan"Hubby"har ɓari hannun ke yi wurin ɗaukar kiran na ce masu su ba ni waje ina son amsa kira bayan fitar su na danna answer tun bai ce komai ba na fara mai ruwan bala'i

"In kana ganin wayo ko dabara ka min toh Allah kan ka ka mawa dan ni ba zan aure ka ba ba za a min auren dole ba dan ni ba kwantai na yi ba kuma bari in faɗa maka ka ji tun wuri ka je ka ce ma Abbu ba ka son auren ka fasa dan ni ba zan iya zaman aure da hakkin wata ba"sai nunfashi nake yi kamar wacce ta yi aiki sai na ji yana min dariya

"Cutie kina da kyau da ko da faɗa kika yi bai maki kyau sai dai ya rage maki kyau dan bai amshe ki ba kuma ni Allah in baki daina ja min layin nan da yawa ba ku biyu zan haɗa a rana ɗaya tohm dan ki ji kar ki ce ba'a maki adalci ba huh"? Wani dumm na ji gaba na ya faɗi da ya ce haɗa mu zai yi amma sai na daure

"Toh sai me in ka haɗan ni dai kawai ka janye maganar auren nan na gaya maka"dariya ya saka har da kyakyatawa abin sai ya daɗa harzuƙa ni

"Cutie kin san fah tsaɗa ne da ni kin sami dala a kala kina wasa da shi anyway i don't blame you har yanzu ke ɗin yarinya ce duk abin da zaki faɗa ba zasu hana komai ba dan haka tun wuri my Mrs ki shirya tarbon sadaukin granny"!! Abin haushi amma na kasa gasa mai magana ɗaya mai zafi un na yi kamar in faɗa sai in kasa zan kuma furta wata kalmae na ji ya ce

"Time to concentrate cutie ana gyara mana ke kar fa kiyi gardama dan so nake in gan ki kamar taurari a cikin jama'a in an fara shagalin bikin nan again in ban zo mun yi planning tare ba babban aboki na zai zo Majeed Ja'afar"da dariya ya ida maganar tare da ce min

"Sai na kira ki anjima my Mrs take care"kamar in yi me haka na rinƙa ji share shi na yi na cigaba da zaman juran bushewar dilƙar..

Tun wannan rana haka ya ke kira na ya rinƙa teasing ɗi na tun ina biye mai har na lura raina min hankali yake yi ga biki sai daɗa gabatowa yake yi ƴanuwa da abokan arziƙi duk an sanar da su dan har an fara tururuwa a gidan media sun ɗauƙa ana jiran a ga an sake pre-wedding pictures amma daga ni har shi bamu da wannan ra'ayin ba wai dan bamu waye ba sai dan muna bawa addini daraja da haƙƙin ta da na ɗauƙa kamar wasa ne sai da na ga saura sati ɗaya dan kuwa ana shirin fara gudanar da programs ɗin bikin a inda za'a fara da sa lalle wanda zai gudana ana saura kwana biyar da bikin an kawo akwatinan auren waɗanda suka kasance seti biyu 12peices dan Abbu ya hana harkar ƙarya ya ce duk abin da yake da niyar yi min ya bari har mu yi auren sai ya min da kyar ma ya amince da 12 pieces boxes ɗin dan aunty mama ta tsaya ta ce ai zamani ne da yake tana da dabara da hikimar magana sai ya amince..

Bai zo ɗin ba bai kuma damu da zuwan ba nima ban damu ba dan su salma sun tsaya a kan komai na bikin har da dai ni ɗin ban cika wani walwala ba amma babu wanda yake bi ta kaina duk sun share ni ni kadai ke bori na babu mai rarrashi na..

Ranar talata by 4:00pm za'a gudanar da sa lallen dan haka an tsara farfajiyar gidan d kyau sai ɗauƙar ido yake yi kalar decoration din wurin kalar kayan da zan saka wato yellow and blue dan haka zuwan lokacin ake yi dan an gama min lalle da gyaran fuska saura awa ɗaya a fara program ɗin a nan nake jin anguwar da za'a kai ni wato maitama a cikin Abj kwafa na yi na ce wato shi har yanzu yana kan bakar shi na auren nan bai fasa ba ko.

4:00pm prompt ba a gi African time ba aka fara program ɗin ba dan halin da nake ciki ba da lallai na ji daɗin wannan al'ada da aka gudanar a ranar ana ta shagali sai chan ma hango wata kamar dija da sauri na tashi na karasa inda take

"Dija dama zaki zo ashe"da fara'a ta na faɗa sai ta bani shocking answer

"Eh zan zo mana amma a matsayin ƙanwar ango ba wacce ta taɓa sanin wata wai amarya ba"tana kaiwa nan tayi gaba leaving me standing like a live statue.................

*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama Ibrahim
#vote
#comment

Continua llegint

You'll Also Like

1.9M 97.1K 38
Presenting the story of ISHIKA MEHRA Whose innocence made the king bow down to her AND ABHIRAJ SINGH RATHORE Whose presence is enough to make the per...
655K 23.6K 200
[FIXED/FAN TRANSLATION] A student who was preparing for the Civil Service examination for 4th year suddenly found himself in an unfamiliar body 3 yea...
KUN MAKARO Per Haermeebraerh

Literatura romàntica

26.9K 1.4K 29
LABARI NE WANDA YAKE DAUKE DA BOYAYYAR SOYYYAH, BOYYAN HALI MARA KYAU,DA TSANTSAR BIYAYYA.
87K 767 12
အသက်ရွယ်ကန့်သက်ချက်တွေ လွန်လွန်ကြူးကြူးပါဝင်လို့ ကိုယ့်ဟာကိုယ် ဆင်ခြင်ဖတ်ပါ။