🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 57-58

656 44 3
By SiyamaIbrahim

🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

'''This page is for you my wattpad fans thank u for the love i really appreciate it'''

5⃣7⃣➖5⃣8⃣

Juyowa na yi kamar mai jin tsoron haɗuwa da kumurci kaɗan kaɗan na karasa juyowan ina jiran saukar kwandon faɗa daga gare shi sai na ji yayi shiru runtse idanuna na yi a tunami na ko ma wari na zai yi sai na ji shiru da sauri na buɗe idanun na zuba mai a yadda ya dan daka min tsawa da na shigo na yi tsammanin zai min wani abin sai na ga akasin hakan instead sai ya kwantar da muryar shi ya ce

"Mama na daga ina kika fito tun dazu ake kiran layin ki ba ki dagawa an kira ƴar uwar ki ta ce bakya gidan ta maman ku ta yi ta kiran layin ƙawayen ki sun ce basu san inda kika shiga ba secretary din ki ta ce baki da appointment da kowa dan haka ba ki je office ba ina kika tafi"?? Tsuru tsuru na yi da ido dan na rasa amsar bashi in yi ƙarya ne ko dai in faɗa mai gaskiyar lamarin tunda tsakanina da Abbu babu boyewa sai na gyara tsayuwa zan fara jero zance karaf aunty mama ta fito tana magana

"A'ah baby har kin dawo daga meeting ɗin kenan na na ɗauka kin ce min sai 7pm zaku gama kun taƙaita kenan"? Da wani irin non verbal eye gesture ta ida maganar wanda ya saka ni gane cewa taimako na tayi daga hell ɗin da na kusa shiga a wun Abbu sai na yi saurin amsa mata

"Eh kin ga ai ba ni kadai ba ce musulma lokacin sallah ya gabato shine muka ce su takaita in ya so gobe sai mu karasa kawai shiyasa kika ga na dawo da wuri"gaba na sai bugun tara tara yake yi dan ƙarya ba hali na bane a ranar da na yi shi sai nake ji kamar Abbu zai dago mu sai na ji ya ce

"Amma mama na an yi shirmammiya shine kika kasa sanar da ni emergency meeting kika tafi attending kika bar ni ina ta tambayar ki"? Toh how was the meeting da fatan komai ya tafi daidai? Saurin amsa mai na yi ji Abbu da wata magana wai ban mai bayani ba bayan bai bar min breathing space ba ya rinƙa min tambaya
_(jan hankali dan Allah kar budurwar da ta yi gangancin yin abin da Aisha ta yi na bin saurayi su haɗu a wani wurin daban sannan ta dawo gida ta yiwa iyayen ta karyar wani abu mai muhimmanci ne ya tsare ta har ta sami goyon bayan matar mahaifin ta itama ta ce eh haka ne yin hakan bai da ce ba a zamanin nan ba'a cika samin matan uba masu hallaya irin ta aunty mama ba sai ɗaiɗaiku dan haka ita a nata nufin ta fitar da Aisha ne daga zargin da mahaifin ta ke son yi mata saboda ta san hallayar Aishan kuma duk abubuwan da ke faruwa da Aishan ta sani kuma ta masu kyakyawar fahimta dan tana da ilimi da hikima kuma ta san Aisha ba zata taɓa aikata mummunar abu ba shi yasa take kare ta bayan haka wallahi wasu matan uban ba za su taɓa kare ki ba sai dai su ƙara wa barkono raɗaɗi wasu kuma zasu karen amma ba dan tsakani da Allah ba dan in nasu ƴaƴan ne da suka haifa ba za su taɓa yarda hakan ya faru ba dan haka wannan scene ɗin is necessary to the story shi yasa na saka ƙalubalen mu mata kar ki taba daukar wasu abubuwan littatafai ki ce suna faruwa a reality kice zaki yi practicing if it worked for the star a littafin it might not work oit for you dan haka nake jan hankalin ku da ku guji biyewa makauniyar soyayyar da zai saka ku bin ɗa namiji a zaman da ya kasance mace da namiji ne waɗanda ba muharramai ba ne na ukun su shaiɗan ne koh a fannin su Aishan haka ne amma Allah ya kare babu abin da ya shiga tsakanin su amma suna jin bakon yanayi wanda sai da suka yaƙi zukatan su kafin su rabu kenan in su sun iya yaƙi da zukatan su ku fah? Ba lalle bane ku iya yakar zuciyar ku da abin da yake kwaɗaita maku dan haka ni Siyama Ibraheem ina mai gargaɗin ku da kar ku yo practicing abin da Aisha ta yi da waɗanda zata yi nan gaba kafin su zama muharraman juna ita da Abdulrahman dan kar wata ta zo ta yi kuka da ni ta ce ai na saka a littafi na my hands are clean and my mind is pure Allah ya sa mu dace)_

Tambaya na Abbu yayi koh na ci abincin na ce mai eh dama fita masallaci zai yi sai ya karasa fita muka mai a dawo lafiya yana fita aunty mama ta ɗaure fuskar ta ni kuma da sauri na rungume ta ina mata godiyar taimako na da ta yi ture ni ta yi daga jikin ta ta fara min faɗa

"Wai Aisha yaishe kika zama haka ne eyye? jiya bikin kanwar ki amma ki ƙi halarta har ƙarshe an yi dinner babu ke a wurin kin saka yarinya yin kukan dole a ranar farincikin ta kin kwanta bacci baki tashi ba sai shabiyu saura sannan kina tashi ƙawayen ki da kika bari a jiyan suka kuma zuwar miki da auren su fah amma haka kika tsallake su kika fita mun haɗu da ke ina tambayar ki matsar da ni gefe kika yi kika yi tafiyar ki irin waɗannan sabbin halayar da kika dauko kin ga sun dace dake kenan ko kuma rayuwar ki? eyye"? A tsawace ta karasa maganar wanda hakan ya birkita ni har na ɗan matsa baya ɓacin rai ƙarara na hango a idanun ta sai ba kwantar da murya na ce

"Dan girman Allah ki yi haƙuri aunty mama wallahi ba da gangar na yi hakan ba na so ne in kawo maki good news sai dai ban san cewa track ɗin da nake bi bai dace ba ki min haƙuri ba dan hali na ba please"na haɗa hannaye na wu ɗaya ina roƙon ta dan na san na kai ta maƙura sai ta sasauto tana min kallon ban gama yarda da ke a duk sanda na ga irin wannan kallon toh na san me take nufi could it be that nima na shiga sahun ummi kenan dan a duk lokacin da ummi da yaya Ib suka ɗan ƙeɓe toh ta ringa kiran ummin kenan kokuma ta rinƙa kai kawo a inda suke har sai sun haƙura da hiran kokuma su karasa a fili in ta dawo ciki kuwa a falo zata tarar da ita iza kan ta take yi zuwa toilet ta mata thorough vaginal examination sannan ta mata head to toe mishkila ƙadn tana samu ta rinƙa ɗaga jijiyan wuya kenan har sai ummin ta yi bayanin dalilin mishkilan a cewar ta namiji in ba mijin ka ba ne ko ana gobe ne ɗaurin auren ku babu wata yarda a tsakanin ku toh ganin irin kallon da take min Sai  na yi saurin tarar ta da cewa

"No noo don't think of that da hankali na da wayo na ba zan yi wannan abin ba never"sheƙeƙe ta kalle ni wanda ya daɗa birkita no

"Da yake kin san shi feelings ɗin duba girma da wayo yake yi koh? hmm ki fah kiyaye ni Aisha ki fitar min daga ido tohm"su aunty mama rai ya baci nima sai ban kuma cewa komai ba juyawa tayi ta wuce tana ce min

"Abincin ki na ɗakin ki ki je ki ci ki yi wanka"ta wuce nima sai na wuce ɗakin nawa

Wanka na fara yi kafin in zauna cin abincin ina yi ina tuno da sweet moments ɗin mu na ɗazu gefe guda kuma ina tuno tabarar da na so yi a gaba Abbu da taimako na da aunty mama ta yi at the same time ina tuno faɗan da ta yi min sai na ga 90% ban da gaskiya a matsayi na na ƴa mace da aka sani da kunya bai kamata in je wun namiji ba kai tsaye babu ƴan rakiya what if something had happend me zan cewa Abbu me zan cewa aunty mama ohh ya salam Allah nagode ma da kasa babu abin da ya faru toh da chan ma ni me ya kai ni yin abun kai tsaye ba tare da na yi shawara da kowa ba? Wani sashe na zuciya ta ta ce min "ai so babu abin da bai saka mutum yi"sai na daɗa damƙe pillow ɗin da na rungume a kirji na da a lokacin tsumin son shi ne ke ratsa ni ni da aka gama yi wa fada not quite long amma har na manta da faɗan na faɗa duniyar tunani mai zurfi kawai sai na ji buɗewar kofar daki na na dago na ga aunty mama ne daga tsakiyar ɗakin ta ce min

"Go to sleep already gobe in Allah ya kaimu zaki bani amsoshin tambayoyin da zan miki kuma that shall happens kafin ki tafi office got it"? Na ce yes ma harara ta min ta kashe light ɗin dakin tare da jamin kofa ta fita cigaba na yi daga inda na tsaya har sai da na ga waya ta ta dau ruri dan a silent na saka ta da sauri na janyo karamar hijabin da na ajiye a gefe na saka sannan na ɗanna answer bottom bayan na yi positioning wayar charming face ɗin shi ne yayi appearing a screen ɗin wayar yana sakar min kayatacen murmushi nima sai na mayar mai da martani

"Mrs Abdulsalaam kin karasa shiga gida lafiya"yanayin yadda yayi maganar sai da tsigar jiki na ya tashi yarr lumshe ido na nayi dan jin daɗin sunan na buɗe idon na zuba mai kamar in janyo shi daga cikin screen ɗin haka na yi ta ji

"Lafiya kalau Mrs Abdulsalaam  ta karasa shiga gida da fatan Mr Abdulsalaam ya isa gida lafiya"? A wun shi shima haka ne wun amsa min tambayar sai da ya lumshe cat eyes din sa masu burge ni a ko da yaushe sannan ya amsa da

"InshaAllah Mrs Abdulsalaam"daga haka shiru muka yi muna kallon juna muna sakarwa juna murmushi sai chan na ce mai

"Mr Abdulsalaam ina jin bacci dan gobe akwai office da fatan kaima baka manta ba"? Cikin sanyin murya na yi maganar wanda ya haddasa masa rufe idanun dole

"Mrs Abdulsalaam in kina cigaba da min magana da irin wannan muryar toh tabbas wataran a bayan windown kin zan kwana"abin ma dariya ya bani wai a bayan window na zai kwana akan me dariya na yi sosai har da ƴar hawaye na shikuma ya yi zugum yana kallo na sai da na gama ya ce

"Wato dariya na baki righ? i was saying my mind amma kike min dariya"? moon face ɗin da ya saka ya daɗa tunzira ni na rinƙa sheka dariya ina share hawaye ni duk na ɗauka fushi zai yi sai na ga ya min murmushi kawai ya ce

"Alright tunda yau dariya Mrs Abdulsalaam ke jin yi wa Mr Abdulsalaam bari in bar ki ki kwanta gobe in mun haɗu sai mu yi maganar da na so yi da ke good night cutie"tsagaita dariyar na yi na ce mai

"Good night Humair"exchanging smile  muka yi sannan muka rabu i can say that night was the most perfect night that i got dan sumul na yi bacci na...

****************"""

Zaune muke ni Abbu da aunty mama muna breakfast Abbu ya riga mu gamawa dan yana da appointment da wani chines company akan wasu kayan da suke so ya fara supplying masu sai ya dawo muka mai sai aunty mama ta kallo ni tana ɗan hahaɗe ido

"Ina jin ki explain inda kika tafi a shekaranjiya da jiya"?

Ban ɓata lokaci ba na shiga yi mata bayanin komai da suka gudana except of our little secretes da na ɓoye she wss happy sai dai har da hakan bai hana ta yi min faɗar kar in sake zuwa wun wani ba da sunan na yarda da shi ba zai min komai ba  na ce mata na ji kuma ta min haƙuri ba zan sake ba ta ce ta hakura kuma in sanar da shi washegari ya zo muyi dinner tare as family tunda ya fara neman ƴar ta dariya muka yi ni da ita kafin ta min fatan alkhairi na fita har masu aikin gidan sun san ina cikin farinciki dan kyautar kuɗi na masu saboda murnar da nake yi ba zan iya daukar ta ni kadai ba shiyasa na raba tare da su ina tuƙi ina tunani wai dama ashe haka soyayya yake da daɗi ban taɓa sani ba hmm lallai ni kam na yi testifying so abu ne mai girma da haka na karasa zuwa company ɗin tun daga gate ɗin na fara hango attracting balloons da write ups kala kala ban karanta ba na karasa shiga ciki na yi parking gabaɗaya ma'aikatan suka taru a compound din kamfanin ɗaya bayan ɗaya suna min welcome back  ma'am haɗe da miƙa min flower wasu gift ne well packaged abin sai ya saka ni nishaɗi da jin daɗi sai thank you nake ta yi masu har na karasa zuwa ciki nan ma duk welcome back ɗin ake min cikin office da na shiga kuwa har tsorata na yi ganin su jabir su biyar sun saka ihu suna cewa
  "Welcome back boss lady"dariya me ya kufce min yau ina zan saka kai na dan daɗi sai ga hawaye gogewa na yi ina masu godiya ban gama tsinkewa da lamarin ba sai da na hango wata ƙatuwar red yellow and white bouquet ana turo shi zuwa office ɗin sai ƙamshin flower ɗin ya buɗe ko ina so fresh and attracting ban hango na bayan mai turo bouquet ɗin ba sai na ga ɗaya bayan ɗaya su safwan sun fara zilewa sai da suka fita kaf sannan aka karasa turo da bouquet ɗin gefen refrigirator ɗin da ke office ɗin aka cire daga abin turawar aka ajiye shi a kasa dama cikin modernized pot ya ke mai adon daukar hankali juyawa nayi dan ganin wanda ya ke bayan mai turo bouquet din sai na ga Abdulrahman ne i was short of words dan haka sai kawai na cigaba da kuka dan farinciki da so da kaunar da aka nuna min not every staff will show it to their boss i felt loved

Karasowa yayi towards me yana girgiza kai alamun kar in yi kukan share hawaye na nayi ina murmushi at the same time

Cak ya tsaya daidai inda na ke just few inches ne tsakanin mu kowanne na shaƙar kamshin turaren ɗan uwan sa well dressed in ocean blue suit kamar dai yadda ya saba a ko da yaushe kyaun shi na saurin ɗaukar min hankali dan haka so da yawa ban cika son haɗa idanu da shi dan gudun sharrin shaiɗan

"Mrs Abdulsalaam good morning"numfasawa na yi na bashi amsa

"Morning"sai da ya ɗan ja fasali kafin ya kuma jefo wata tambayar

"And your night how was it"? Ya rasulilah da gangar fah yake min irin waɗannan salon maganganun kwakwalwata ba zai ɗauka ba sai na yi saurin amsa mai

"It was perfect yours"?

Ganin kamar ina tsoron shi ne sai yayi murmushin gefen baki sannan ya amsa da

"Terrible so terrible cutie"da sauri na dago muka haɗa ido daman abin da yake so kenan dan haka ganin tension ɗin dake tattare da ni sai ya ɗan fadaɗa murmushin sa ya ce

"Yes i got you now"lura da cewa nemana faɗa yake son yi sai na harare shi cikin wasa na juya abi na zan zauna sai karaf ya ce

"Lalalaa nima ikon mulkin za ki min dan na zo office ɗin ki boss lady"? Samfurin tambayar dariya ta ba ni ba kaɗan ba dan irin yaran da aka wa laifi suna son expressing disapproval din nan haka yayi sai na ɗan dara na ce

"Wai da me ka zo ne yau Mr Abdulsalaam kana ta cinye min time ɗi na da shirme"da biyu na yi maganar ɗan dai ya yi fushi ya zauna ne kawai aiko sai ya haɗe rai ya karaso ya zauna yana facing ɗi na na zuba mai ido ina jiran ganin reaction din  sa abin dariya sai ya fara mazurai irin ran yara ya baci ɗin na n hana su yin abin da suka yi niyar yi dariya na saka mai ganin zunkudeɗen saurayi da abin yara dama haka yake so jovial ban sani ba lallai maganar da ake yi na never judge a person by mere looking instead judge him by his character na yarda da saying ɗin dan gashi nan karara ina gani a wun shi zai yi magana na ce
"Please yi hakuri Sadaukin granny da grandpa ba zan sake babyn big sis"sai na ga ya washe yana ta murmushi ikon Allah wato dai da gaske namiji wawan mace ne in macen ta iya tafiyar da shi ba dai wani serious issue bane ya bi ya bata rai amma ɗan kirarin da na mai sai ya sanya shi farinciki

"welcome back boss lady"da murmushin ƙauna na kalle shi na ce

"Thank you so much"
  "dama so na yi tun jiya in gaya maki wani magana but you were laughing at me all through"murmusawa na yi kawai na ce

"Toh yanzu gashi na baka time ɗin maganar ka yi kawai abin ka"

Gyara zaman sa yayi ya zama serious sai ya fara magana

"Gasar mazana na duniya ya gabato kuma kin ga a ko da yaushe ina yin gasar ina kokarin lashe kambun gasar a wancan gasar ban lashe ba dan ban yi claiming position ɗi na ba sakamakon dalilai na biyu na farko saboda ina son ki yi representing di na a gasar saboda so nake sunan ki ya zaga ko ina a faɗin duniyar nan ta yadda za'a san cewa budurwar Abdulrahman ta na da hazaka da ilimi na biyu saboda ina so Majeed ya dandana kuɗar sa dan so nake ku hadu kuyi gasar tare ta yadda ko da anzo wurin tattara scores za'a kama shi dumu dumu da rashin iya aikin shi sannan a bata mai suna saboda Kamar culprit za'a kama shi daga nan zai fara jin kunyar shiga jama'a babu wanda zai sake bashi contracts kuma maga zai fito fili na ni din dan gado ne na ilimin zane shi kuma din karantawa yayi dan ya kara da ni saidai kash bai kai labari ba kuma ba zai kai labarin ba dan haka ina so ki shiga karatu da research ba bacci da yawa ayyukan office ki barsu a side ni zan iya kukar maki da su but make sure you study very much dan i really wanf you to score the overall gold medal gasar zai kasance ne dab da bayan azumin watan nan da zamu shiga i want you to produce something extraordinary again bana so in ji kin ce a'a bazaki yi ba it's gonna be taking place in Cairo city sauran information din zan tura maki ta system din ki kuma i shall teach you all the techniques dan so nake Majeed ya dusashe at once hmm"? Da twinkling din hannu ya karasa maganar da murmushin irin har ya ci nasara din nan

Digesting maganganun shi na yi sai na dago da pen a hannu na ma saka a baki ina nazarin shi kafin in yi magana

"Mr Abdulsalaam in na fahimci maganar ka da kyau so kake kayi amfani da ni a matsayin weapon da zaka yaƙi Mr Ja'afar amma a baibai ba tare da masaniyar cewa kana da halaƙa da failure ɗin shi ba sannan zaka nuna mai cewa kana working mai akan yayi beating ɗi na tunda is my first time of emerging with him and sauran mazana na duniya dan haka zaka taya shi da komai since you won't be competing right"?

Tafi ya saka yana murmushi kafin ya ce
  "Kan ki na ja Ms Murad shi yasa nake daɗa daraja ki dan kina da brain na ji daɗin fahimta ta da kika yi kuma zan baki babbar kyauta in kika ti beating Majeed is a promise and you will love the gift"da murmushi ya karasa maganar nima sai na mayar mai dan kuwa a wannan stage din ina jin babu abin da ba zan yi wa Abdulrahman ba saboda ceto shi daga mummunar past din shi da ke bibiyar shi wanda ba alheri ba ne a nan nayi tunanin sanar da shi akan maganar salma na abduction din iyayen ta da aka yi wanda mijin ta ya ce yana suspecting wani ne da abduction din

"Yauwa akwai maganar da nake son sanar da kai"
"Yes ina jin ki"

Sai da na dan dau lokaci sannan na fara

"A ranar da aka aiko min da sakon bacewar iyayen salma har na tafi yi masu jaje salma ta sanar da ni wata magana wanda na ji mamakin maganar yanzu da na san makiyan ka na da yawa sai na ce zan sanar da kai in yaso sai ku hadu ya sanar da kai wanda yake zaton ko shine ya yi abduction din"dan tsagaitawa na yi sannan na cigaba "according to yaya umar ya ce yana suspecting wani ne na kusa wanda yayi wannan abin sai daumi shima ya saka ma wannan ido dan ya tabbatar da zargin shi amma shi bai san ainihin maganar ba kenan letter din nan babu wanda ya san abin da ke ciki daga ni sai kai sai shi wanda yayi abduction din dan haka nake tunanin sanar da kai zai fi saukaƙa mana binciken mu a cikin ruwan sanyi ya ka gani"? Ga mamaki na sai na ga yana murmushi ya ce

"Barrister Umar Amodu the great barrister a supreme high court Abuja right"? Mamaki ne ya kama ni jin yadda ya karanto sunan yaya umar gabadaya sai ya dada yin murmushi

"Na san kina mamaki na ta ya na san shi right"? "Toh kar ki ji mamaki duk wanda nake tare da shi ina bincikar mutanin da yake mu'amala da su dan haka barr.umar is my suspect as well ki manta da wannan maganar kawai all i want you to do for me shi ne ki taya ni saka ido akan shi shi da matar shi ok"? Girgiza mai kai na yi ina mamakin shi dama ya gama sanin maƙiyan shi ashe zan yi magana na riga ni

"Lets talk about love"dariya kawai na yi na biye mai hira muka yi sosai ban yi aikin kirki ba ranar mun yi concluding zuwa next week zai fara koya min techniques din har na sanar da shi saƙon aunty mama sai murna yake yi wai aunty mama na kaunar shi apart from his elder brothers and grandparents bai da wani family that cares about him kamar aunty mama dariya kawai ya bani sai 11am ya yi dropping ɗi na a gidan salma har da jaddada min akan in saka mata ido sosai koh da na shiga cikin gidan sosai ta min bambami amma da yake ban da gaskiya hakuri na rinka ba ta kafin ta hakura ta tambaye ni yaushe zan tafi gidan ummi na sanar da ita ina barin gidan falmata zan tafi mun yi magana akan bikin hasina wanda saura watanni uku sai 2pm na bar gidan da kaina na tafi gidan falmata ita ma hakurin na bata dan ta zazzaga min bala'in kafin ta hakura daga gidan ta gidan ummi na nufa da farko wai fushi ta ke da ni sai daga baya ta sauko dan ni har wani kumatu naga ta min ina ta teasing ɗin ta hirar mu muka sha sai yamma na koma gida a nan aunty mama ke tambaya ta favourite dish din sa ce mata na yi ban sani ba harara ta dankara min wai ban san abincin da ya fi so ba dariya kawai na mata na wuce

*******************

_7:30pm_

Ni Abbu aunty mama da Abdulrahman gaba daya muna kan table muna cin abincin kadan kadan suka magana da Abbu lokaci zuwa lokaci aunty mama na jefo mai ɗan tambayoyi duk dan ta san wasu abubuwa akan shi a nan ya sanar da su akan gasar da zan yi suka tambaye ni ko zan yi na ce eh suka min addua'ar samin nasara around 9pm muka yi sallama ya tafi bayan mun sha hirar mu ko da ya koma gida ya kira ni ya ce in kara yi wa aunty mama da Abbu godiyar karrama shi da suka yi na ce na ji hirar muka kuma yi kun san halin sabon shiga abin sai dadi yake min kamar kar ya kare

*****************

_Three months later_

  Bayan sallar azumi saura sati 1 gasar ya fara duk tension da phobia ya gama dami na ba wai tsoron rasa gasar nake yi ba sai dai gudun kar in watsawa Abdulrahman kasa a ido alhalin ya saka burin zan yi winning gasar kuma bana so in ba wa wancan wawan chance ɗin lashe gasar dan haka na kara zama very busy at that time shima yayi tafiya zuwa wata business meeting dan haka Abbu da aunty mama kadai ke encouraging ɗi na zuwa lokacin bikin hasina ya gabato amma sakamakon wannan gagarumar gasar ba zan sami daman halartar bikin ba sai dai after bikin in na dawo falmata was able to deliver a baby boy a ranar da zan tafi a ranar za'a yi suna abin bai yi min daɗi ba amma dole in tafi wannan gasar dan fidda Abdulrahman daga wannan kishin da ake yi da shi

Ana saura kwanaki huɗu a fara gasar nikuma na gama shirye shirye na komai was ready a ƙaida ana saura sati biyu ya kamata in tafi dan akwai special classes da ake koyawa new competitors amma sai Humair ɗi na ya hana ni tafiya ya ce duk abubuwan da yake koya min za su koya min dan haka in ce ba zan zo ba sai ana saura kwanaki uku a cewar shi in na yi hakan zan fi drawing more attention din judges ɗin dan zasu so sanin wacece wannan painter din da bata yi attending special classes ba kuma ta zo competing da sauran da suka daɗe suna yi da waɗandan duka halarci special classes da haka ya rinka kwantar min da hankali akan kar in damu hakan kawai da na yi zai ƙara min marks bare a ce na yi emerging first position..

*********
_Friday 10am_

Yayi mana a airport su aunty mama ummi da yaya ib ne suka raka ni suna min fatar alkhairi da samin nasarar gasar 30 minutes da arrival ɗin mu jirgin mu ya ɗaga zuwa kasar cairo few hours muka yi arriving already akwai hotel room da ya min booking dan haka da saukar mu chan na wuce na yi wanka tare da rama salolin da suka wuce ni daga nan na sanar da sauran ƴan uwa arrival ɗi na daga karshe na kira shi na gaya mai cewa mun isa lafiya muka ɗan yi hira ƙadan most of hirar akan gasar ne ya ce kar in kuskura in bari Majeed ya san na tafi saidai ya gan ni ranar gasar dan dama bai san zan yi gasar ba na ce mai inshaAllah da haka muka rabu tun ranar har sunday night yana kokarin kwantar min da hankali akan kar in damu zan ci gasar

************

_The competition day_

Filin cike yake da jama'a ga over headed projectors nan wuri kusan hudu duk abubuwan bukata na gasar an tanada judges ɗin were well set kusan mu hamsin da bakwai ne a cikin 57din  nan 5 competitors kawai zasu lashe gasar komai daidai ga kujerun mu nan jere a angle shida na field ɗin a takaice wuri ya cika maƙil jiran sauran competitors ɗin ake jira su gama isowa a fara gabatar da gasar by 11am an gama cika wani balarabe ne da Majeed suka shigo a karshe sai annashuwa yake yi dan ya san Abdulrahman mai hana shi cin 1 zuwa 3 baya nan dan haka shi zai maye gurbin shi duk a zaton shi ilimin shi ke bashi 4-5th position din da yake samu tunda kuwa babu mai tare mai hanya ya san zai lashe not knowing that ni ina wurin balaraben ya kasance daya daga cikin judges ɗin dan haka da zuwan Majeed angle ɗin mu ya dosa dan nan zai zauna da zuwan shi ya zauna yana washe baki kamar gonar audiga mutani hudu ne a tsakanin mu dan haka bai lura da ni ba sai da ya je gyara zama irin yayi gaba kaɗan din nan sai ya hango ni zaune ina kallon shi da fari har ya juya sai ya kuma juyowa ganin ni ɗin ce dai sai ya gwalalo idanu ni kuma na kaahe mai ido ina murmushi na daga mai hannu biyu alamun all the best na juya kaina.......

*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama Ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

432K 18.1K 123
SYPNOSIS Reading Purifying Love made Rachelle D'magiba feel very insulted. The ending that the author had written didn't go well with her expectation...
840 127 34
BA KYAU BANIBA ABUN DAMUWA DA ABUN ALFAHARI ƘYAN HALI DA KYAKYAWAR ZUCIYA SHINE CIKAKKEN ƘYAN FUSKA! KOWANNE BAWA DA TASHI JARABAWAR ITA KUMA LATYFAH...
26.9K 1.4K 29
LABARI NE WANDA YAKE DAUKE DA BOYAYYAR SOYYYAH, BOYYAN HALI MARA KYAU,DA TSANTSAR BIYAYYA.
1.4M 96.9K 24
#Book-2 in Lost Royalty series ( CAN BE READ STANDALONE ) Ekaksh Singh Ranawat The callous heartless , sole heir of Ranawat empire, which is spread...