🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 55-56

684 45 8
By SiyamaIbrahim

🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

5⃣4⃣➖5⃣6⃣

_The next morning_

Ji na yi ana tapping ɗi na farkawa na yi na ga salma ce zaune next to me a kan gadon gefe babyn ta ne kwance tana ta wutsil wutsil murtsuke idon na na yi ina murmushi dan yadda ta kumbure fuska alamun bala'in da ta dade bata yi irinshi ba ne ke taso mata kafin ta ce wani abu na tari numfashin ta

"Yi haƙuri na san ni mai laifi ce amma ki min uziri mrs umar abubuwa ne suka min yawa shi yasa baku ga na dawo da wuri ba jiya forgive me please"da fuskar tausayi na ksrasa maganar harara ta jefo min na saka dariya ina tsokanar ta daga bisani na ɗau babyn ina mata wasa dan ta fara wayo yarinyar tuɓur tuɓur tubarkallah ana haka muka ji sallama amsawa muka yi falmata ce da cikin ta a gaba wata muguwar dariyar na saka ina mata waƙar mai ciki ga ta nan tafe

"Mtsww Allah ya bar rai naki na nan zuwa banza"dariyar muka saka ni da salma zama ta yi a kan kujerar dakin ta fara bambami

"Wai ke Aisho me yasa baki da halin kirki ne wai jiya daga ina zuwa kika yi tafiyar ki baki dawo ba har taro ya kare an tafi dinner mun ta zuba ido dan ganin ki amma kika bar mu mu kadai akai ta kiran ki ba'a gan ki ba haka kawai kika saka matar mutani zubda hawaye hankalin angon ta ya bi ya tashi da kyar aka rarrasheta sannan yanzu kin zo kin kalailaye a gado kina zuba barci har 12noon ba ki ma yi niyar tashi ba malama yi ki shirya mu je gidan amarya dan ni kam miji na zai dawo daga tafiya yau ina da girke girken da zan yi anjima kadan"murmushin fuska ta ne ta gushe sakamakon jin time ɗin da ta faɗa 12noon a hanzarce na mikawa salma babyn ta na ce

"Ungo babyn ki subhanallahi wani irin barci ne ya kama ni haka"da sauri na diro daga kan gadon ina sauri har na so misding step na wuce toilet na bar su zaune da baki a buɗe dan mamaki ina jiyo su suna gulma ta 5 minutes bath na yi na fito ina ta sauri daukar waya na yi na ce ma mai girkin gidan ta kawo mana abinci mamaki ya gama kamasu ni na sani kuma ban da explanation da zan masu sai na dawo wata material royal blue da touches din yellpw a jikin ta na dauka na saka riga ce doguwa ɗinkin fitted da off shoulder hannun doguwa ce a bakin hannun sai aka zagaye shi da kyali kyalin duwatsu ban taba saka kayan ba dan a dinkunan bikin jiya yake plain neck chain na saka na saka ɗankunnen shi da abin hannu yellow veil na dauka na ajiye a gefe abincin aka shigo mana da shi a babbar tray da plates zaunawa na yi na yi serving kai na rice and stew ne sai coleslow da fresh fruit salad zubawa na yi na kalle su na ce
"Malamai ku sauko dan ni sauri nake yi ina da wun zuwa"daga haka na fara cin abincin sai tambaya na suke yi amma na kasa basu amsa ko rabin abincin ban yi ba na miƙe na kara touching makeup ɗi na gyalen na yafa na saka flat D&G shoe ɗi na mai jakar shi yellow ƴar karama car key ɗina na dauka na yi saurin isa bakin kofa sai na ji muryar salma

"Aisha wai wani irin halin wulaƙanci ne haka kike nuna mana tun jiya ha'an"!!

"Am so sorry sweethearts ba zan daɗe ba zan dawo ku min haƙuri please"na juya zan fita muka yi karo da aunty mama kallo na ta yi fuskar ta a ɗan haɗe

"Ina kika shiga jiya kuma yanzu ina zaki tafi"? ban ba ta amsa ba dan 12:30 har ya yi kawai matsar da ita na yi ina dariya

"Aunty mama zan sanar da ke in na dawo yanzu ba lokaci"da gudu gudu na karasa saukowa daga kan steps ɗin ina kokarin fiddo car key ɗin da zuwa na ban tsaya ɓata lokaci na shige motar na kunna ta reverse na yi aka buɗe min gate ɗin na fita da sauri ina ɗaga masu hannu tafiyar 15 minutes na yi kafin in iso wurin da sauri na fito na shiga ciki ban tsaya a nan garden ɗin ba na wuce ciki inda na fi kyautata zaton zan same shi ban gan shi ba sai hankali na ya fara tashi na shiga blaming kai na for not going early kamar in kurma ihu haka na yi ta ji kusan mintuna biyar ina neman shi ban ganshi ba sai a sannan na yi tunanin kiran wayar shi dialing numbern na yi na kara a kunne na sai na fara jin ƙara kamar ta wayar sa juyawa na yi sai na ga wayar a saman wata carpet da ban lura da ita ba a jiyan sai yanzu magana na fara ti da kai na

"Shi kuma a nan ya bar wayar"? Na ɗan sami relieve ganin ba fushi yayi da ni ba yana nan sai na zauna a wurin zaman jiran shi ban dau lokaci da zama ba sai gashi ya zo cikin shigar blue kaftan shadda ƴar asali sai maiƙo shaddar ke yi da hula blue colour mai adon zare kalar silver da agogon rolex mai kyau a hannun shi palms takalmin fata ya saka baƙa designer turaren shi ne ya fara mai sharan fage kafin isowar shi shakar turaren na yi na lumshe ido na ina daɗa godewa Allah da ban yi asarar wannan kyakyawar saurayi ba dan wani irin kyau yayi kasancewar yau ce rana ta farko da na gan shi cikin shigar gargajiya ina ta analysis ɗi na ni kadai sai ga shi ya karaso yana zuba min murmushi zama yayi kusa da ni tare da ce min

"Assalamu alaikum beautiful soul"jin kai na na yi kamar wata sarki cikin rausayar da kai na amsa da

"Wa'alaikumul salam kind creature"lumshe idanun shi yayi alamun ya ji daɗin sunan buɗe idon yayi ya zuba min su ya ce

"Tun ɗazu nake ta jiran ki ban gan ki ba me ya faru"?yana maganat ne yana tsare ni da ido sai na yi murmushi

"Baccin ne ya min kamu mai tsanani"shiru na yi ban kuma cewa komai ba sai ya murmusa a kayace

"Humairah ai dole bacci ya maki kamu mai tsanani ko kin manta jiya kika sauke nauyin da ke ran ko you made a confession last night kin tuna"?? Sunkuyar da kai na nayi ƙasa dan kamar da gayya yayi maganar sai na bashi amsa a bazzata

"Eh ai ina sane da hakan kawai dai baccin ne ya fi karfi na saboda sha'anin bikin nan"ban kuma ce mai komai ba na ja baki na na rufe murmushi mai sauti ya yi ya jingina kadan

"Humairah ko zaki iya sanar da ni ainihin tarihin ki dan wanda na sani bai gamsar da ni ba"?? A wannan stage ɗin bana jin zan iya musanta mai wani request da zai yi dan haka na numfasa na fara bashi labarin rayuwa ta babu abin da na boye mashi ko da na kai karshen labarin sai na ga ya miƙe daga kishingidar da yayi yana kallo na kamar wani soko har ya saka ni yin ƴar takaitaciyar dariya ina tonan shi

"Haba Humair irin wannan kallo haka ko dai ka manta ni ne"?ajiyar zuciya ya sauke ya fara magana

"Humairah i thought duk labarun da na samu game da ke were fake ashe da gaske ne kin shiga irin waɗannan matsalolin rayuwa amma baki taɓa nunawa ba kin san me"? girgiza kai na na yi

"You are more courageous than me kin yi overcoming duka hurdles kin tsaya a matsayin face of women a duniya baki ɗaya kin jajirce kin sadaukar da abubuwa dayawa saboda ba ma wasu farinciki a rayuwar su kin manta da kan ki yet baki tsira ba Aisha"

Numfasawa yayi kadan sannan ya cigaba

"You see ban san cewa akwai ranar da wani abu zai shiga tsakanina da ke mai suna so ba sai a yanzu da son ya kama ni sai nake ganin ya kamata in sanar da ke duk wani sirri na wa dan na yarda da ke fiye da yadda na yarda da kaina"kallon kwayar idon shi na yi son shi na daɗa fizgata ga tausayin sa mai tsanani da ke dawainiya da ni gyara zaman sa yayi

"Ban taɓa neman abu na rasa ba a rayuwa ta abin da na nema na rasa shine iyaye na da yaya ta kin san tun lokacin da na rasa su ban kuma samin madaɗin su ba?my grandparents are my strength na rasa iyaye na a dalilin son zuciyar wasu waɗanda suka dauki duniya a matsayin komai a gare su i lost my big sis sakamakon son zuciya irin ta mutani ban taɓa sanar da kowa wannan sirri na wa ba but yau ina jin na yarda da ke har zan iya sharing sirri na da ke Aisha"ɗan tsagaitawa yayi yana kallon ƙasa kafin ya ɗora

"Majeed was my friend tun a business trip din da muka haɗu na bashi yarda da aminci na to the extent that na sanar da shi sirruka na babu komai da na ke ɓoye mai toh kafar da ya samu kenan har ya ke min yankar baya but kin san wani anb? girgiza kai na na yi ina kallon shi cigaba yayi "ban taba yarda da shi ba sirri na da ya sani were all fake yarda da amanar da na bashi duk na yi hakan ne dan ya faɗa a trap di na saboda ya kasance prime suspect ɗi na for years duk abin da yake yi akai na ina hankalce abotar da na hada da shi nayi ne dan in yi sourcing information  da evidence da zan iya amfani da shi against him da gangar nake tura shi business meetings ɗi na dan ya sake jiki da ni da sani na nake cewa a bashi 2nd ko 3rd a gasar mazana na duniya in an je yi ina biyan kudade akan a yi signing contracts da shi duk dan saboda ina so ya faɗa tarko na a lokacin da ya riga ni zuwa wun ki nemar wa kan shi hada aiki da ke ni na yi plan ɗin dan ni na binciko ki na tara isasun bayanai a kan ki na adana su ranar da ya kawo min visit sai na fitar da informations din ki na bar shi a fili ta yadda zai gani ya kuma san cewa kamar kuskure na yi na bar su unknowingly sai na kawo maganar ki ina kokarin nuna baki min ba ke da paintings ɗin ki na nuna mai baki da ilimi da fasahar da zan hada wani al'amura na da ke ba nuna mai nayi baki da characteristics din da zan yi collaborating da ke karshe na wurgar da informations din naki a kasa na tashi ina maganganu akan har kina kokarin dusashe tauraro na da zuwan ki ke da karantawa kika yi da ni da a jini na yake sai da na ruɗa shi ya yarda na tsane ki na tsani paintings ɗin ki sai ya dage wai mu gwada in ya so sai mu dusashe tauraron ki a karshe mu kashe sunan kamfanin a duniya baki ɗaya kina matsayin mace bai kamata a ce kin sami ɗaukaƙa har haka ba daga mai murya nayi na nuna mai rai na ya baci kuma ba zan taba hada hannu da ke ba sai dai in shi ne zai yi hakan shi a nashi wai bugun ciki na yake yi bai san tuntuni na harbo jirgin shi ba sai na bar shi a kan ya daina kawo min maganar ki gabaɗaya sai ya ce ai shima babu inda za shi me zai kai shi collaborating da ke Allah ya kiyaye shi da yin asara a haka muka rabu koh da na duba ban ga wasu vital info da na ajiye ba sai na yi murmushi dan na san ya gani kuma ya dauka next kuma zuwa zai yi wurin ki shi yasa na jinkirta neman ki da mu yi collaborating har sai na ga inda rashin wayyon shi ya kai, dan halas sai ya dawo min da labarin ai kina nan kina yaɗa sanarwa akan mina neman companies da zaki hada hanmu da su saboda bunƙasa aikin ki jin shi kawai na yi dan na san shi ƙarya yake yi dan kusan duk investments din da muke yi da wasu kamfanoni a kasashen duniyar nan shine ke taka rawar yin hakan dan shi ne ya kasance so desperate  to make name and fame a faɗin duniya the secrete is that bai da komai a kwakwalwar shi instead ya rasa biyu sai ya nemi hanyar haduwa da ni dan ya san duk yadda za'a buga a kai a kawo matuka yana tare da ni toh ya gama zaga duniya kuma dama burin shi kenan toh ni dama chan ina neman hanyar shiga rayuwar su sai gashi ya kawo kan shi abin sai ya min sauƙi na rinƙa amfani da shi ina tara evidence a kan shi shi da mahaifin shi bai sani ba,, yin banza nayi da maganar nashi da ya kawo dan a duka investments ɗin mu cikin kashi ɗari ina da 96% while shi yana da 4%share a ciki amma da ya ke shi ɗin empty barrel na he make a lousy noise bai damu da ƙanƙanuwar share ɗin da yake da shi a investments ɗin mu ba.  a karshe a wurin PA din shi nake jin wai ya koma gida ya kori duk ma'aikatan shi ya sha giyar shi yayi tatil saboda ya kawo maki invitation amma kin raina mai hankali kin ce zaki neme shi baki neme shi ba karshe da ya koma kika wulaƙanta shi kika mai korar kafiri da annabi abin da ran shi bai so ba dan a nashi so yayi ki yarda sai ya dawo ya ce min kin yarda zaki haɗa hannu da mu in ya so sai in yarda kamar yadda na saba yarda that information was the sweetest information i got a kan shi jin hakan sai na yi saurin tura maki Ashiru  a matsayin wakili na na gama making analysis akan duk wasu amsoshin da zaki bayar in kun haɗu da ashirun so even when he returns and told me duk yadda kuka yi sai na yi murmushi kawai dan analysis ɗi na ya tabbata irin hakan yakan faru ne kawai a kan CEO's da suka san aikin su saboda na gwada hakan a kan CEO's babu adadi kuma duk ina samin positive feedback.. I was amused da karfin zuciyar ki duba da yadda kika yi disqualifying Majeed amma kika ba da chance a kai na na in zo da kaina bayan baki bani appointment ba kai tsaye na turo amma shi ya haɗa appointments da ke sau da dama kafin ki amince mai ya gan ki i don't know why kika hana shi but ni abin ya min daɗi dan haka na daɗa respecting ɗin ki ban tsaya jan abin ba na tura maki da email na kuma gwada patience ɗin ki by urging you to fix appointment for me kafin 2days kuma kija yi hakan sai na ga kin wuce matsayin sauran ma'aikatan da na yi investing da su kasancewar ki very young and sharp when it comes to thinking capacity in kin tuna ko ranar da na zo i was behaving so humble da ke dan in ga reactions ɗin ki kuma na sami abin da nake so"

"Ko da labarin ta riski Majeed zuwar min yayi uninvited yana son buɗe min wuta amma ban bar shi ba na tare shi ta hanyar ce mai ai kin turo min invitation kina roƙa na sai abin ya daɗa hargitsa shi ya fara ganin ai shima he is famous zai iya yin abin da zan iya yi shine PA din na shi ya ce min ya aike shi da letter of invitation na dinner da ya aika miki dariya abin ya bani dan na ga rashin wayo ƙarara a tattare da shi sai na cigaba da saka mai ido har zuwa ranar da muka yi conjunction party ɗin mu duk abubuwan da suka faru tsakanin ku a ranar ina kallon ku amma i pretended not to see you dan ina son ganin wayon ki da dabarar ki to my greatest surprise sai na ga kin tsallake tests din da na maki karshe ma har da taimako na kika yomi ta hanyar nuna min abubuwan da suka faru tsakanin ku since from that precious day i began to develope love and attraction towards you amma na rasa ta yadda zan fahimtar da ke until incidence ɗin nan da ya faru wanda ya zame min babbar mabuɗin kofar sanar da ke amma sai kika yi rejecting ɗi na i felt very bad and embarrassed shiyasa na nisanci kai na da ke for month because you need space to think wun grandparents di na na koma ba tare da sanin kowa ba sai su last week na dawo still bam sanar da kowa ba har jiya da na zo daurin auren ummi a nan na gan ki kin fito and i felt i can't ignore you shi yasa na kira ki na ce maki you look beautiful daga nan na dawo nan har kika shigo a hanyar fitar ki muka hadu har Allah ya sa kika sami ikon confessing min feelings ɗin ki i was the happiest person tun jiya i couldn't sleep coz it was like a nightmare to me ko yau da na yi ta jiran ki ban gan ki ba sai na fara tsoron koh dai mafarki na yi until now that you are present"!!

Ajiyar zuciya na yi irin wannan labarin al'ajabi da na ji ya rikida ni matuka toh dama ya san waɗanɗa suka yi sanadin iyayen shi amma ya ƙi kai karar su?

Gyara zama na nayi ina facing ɗin shi

"Dama ka san waɗanda suka yi sanadin iyayen ka amma baka kai kara hukuma ba me yasa"? dago kan shi yayi yana murmushi

"Humairah har yanzu yarinta bata gama sakar ki ba ai in mutum na farautar maƙiyin shi a sannu ya ke bi har ya saka wannan mutumin ya kama kan shi da kanshi kafin mai farautar ya yi exposing din shi kar ki manta har yanzu zargi nake yi zato na bai gama zama gaske ba but kin san wani abu"? girgiza kai na na yi ya cigaba"wuth you in my world i will be able to expose all my enemies kawai ki taya ni da addu'a dan wasu abubuwan sai na aure ki zaki gani da idanun ki right now i only have you and my grandparents dan haka ki riƙe ni amana Humairah it's been long da na saka trust ɗi na akan wani kar kiyi betraying trust ɗi na Aisha please"kamar zai yi kuka ya ida maganar ni ko da hawayen bai cika yi min nisa ba sai ga su sun fara saukowa zir zirr tausayin shi ke dawainiya da ni dan a yanzu bai da kowa kowa ma is a suspect a gare shi dan haka na yi wa kaina alƙawarin kare shi ko ta halin ya ya yarda da ni da yayi babbar abu ne i promised never to let him cry ko da ni zan kasance cikin baƙin ciki ne ba zan taɓa barin shi ya cigaba da zama a rayuwar kaɗaici ba

Dariyar shi na ji sai na dawo cikin hayyaci na ina tambayar shi me ya faru

"Anya Humairah zaki iya battling da enemies ɗin mu kuwa? ji yadda kika zauna kina kuka and it seems like you are lost in your thoughts me ke faruwa"?

Ba zan kira amsar da na bashi da suɓul da baka ba dan iya gaskiya ta na furta

"Humair kana bani tausayi ne ganin irin cakwakiyar rayuwar da ka shiga da yadda kake mu'amalar ka da maƙiyan ka amma baka damuwa da ka nuna shi a fili yet ba'a bar ka ka sha iska ba you are under pressure din maƙiyan ka me yasa wai duniya ta zama haka ne"? Da digon hawaye na ida maganar sai yayi murmushi kawai ya ce

"Saboda that is how it was designed haka Allah ya ƙaddara abin dan haka dan adam baya tsallake ƙaddarar sa kina cikin kaddara ta Aisha shi ya sa Allah ya haɗa mu all thanks to your ex and your friend who is his wife"da murmushin gefen baki ya ida maganar ni kuma na dada bude idanuna ina mai kallon mamaki wani irin gesture ya min kafin ya ce

"I know kina son tambayar inda na san maganar ne koh ba haka ba"? Cigaba nayi da kallon shi sai ya cigaba

"Well kin ga ni tun lokacin da na ji interest a kan ki na fara tracing ɗin ki sai da na tabbatar da cewa na sami cikakken love life history din ki abin da ya sa na daɗa respecting ɗin ki kenan you sacrificed your happiness to your friend so why shouldn't you be happy as well kina ganin ni da ke ba haɗin Allah bane? of course ikon Allah ne i have been with khadijah for so long amma daidai da rana ɗaya ban taba daukar ta a matsayin macen da zan iya yin rayuwar aure da ita ba babu abin da ta min haka kawai na ji bana son ta kuma ba wai dan bana kaunar ta bane a'a kawai hakan nufin Allah ne in ya so sai ya bar ka da dabarar ka karshe sai ya aiwatar da abin da yake daidai wanda kai bawa a da zaka dauka koh bad luck ne ke ta samin ka dan haka nake so mu fara gina *soyayya mai garɗi* tsakanin mu mu gudanar da soyayya mai tsafta i was never what you thought of of me you called me all sort of names kamar second hand,saur...., ban bari ya ida ba na ce

"Please ka daina maimaita abin da ya wuce na ce ka yafe min tun jiya i withdraw my words amma baka yafe min ba me ya sa"? Kamar zan yi kuka na yi maganar

Zuba min idanu yayi daga bisani ya ce

"Aisha ke zaki ba wa kanki amsoshin tambayoyin ki dan ni kaina ban sani ba koh na yafe maki ko ban yafe ba amma ke ke kadai zaki san hakan dan haka you should stop asking me such question"? A fizge na so fahimtar maganar sa amma sai na ga ai shi ɗin ba irin sauran mazan zamani bane at least yana da kunya tattare da shi he won't talk like that da haka na share maganar sai ya tambaye yi

"Humairah koh zaki iya sanar da ni dalilin ki na rejecting Majeed a lokacin da ya kai maki proposal"?

Murmushi mai ciwo na yi kafin in warware mai komai akan labarin Majeed din da ya iso ni kafin shi da kan shi ya zo da kuma dalili na na hana shi aiki da ni wanda dalilin kuwa shine bana so ya cigaba da cutar da Abdulrahman ɗin not knowing that shi Abdulrahman ɗin da kanshi yake abin da yake yi har shi Majeed din ya kai kanshi kenan Abdulrahman na shimfida mai gadar zare shi kuma yana hawa ya faɗa ba tare da ya yi la'akari ba koh da na gama ba shi labarin sai yayi zugum ya yi cupping hannayen shi a chin din shi yana kallo na kamar zai haɗiye ni ganin kallon yayi yawa sai na hada yatsu na kada su dab da idanun shi rufe idon yayi ya buɗe sai na ga kamar yana ƙoƙarin ɓoye wani abu

"Toh me yasa kika ji kamar ya kamata in sani kuma kina da bukatar taimaka min despite the fact yhat you knew ba ni da sauƙin kai"?

Murmusawa na yi ina jin sabuwar son shi na ƙaruwa min a zuciya kallon kwayar idanun shi na yi

"Kamar yadda ka ce ne Humair ikon Allah ne ya haɗa mu sau biyu ina mafarki da kai na farkon was terrible dan a mafarkin a halin wahala kake kana bukatar taimako sai ga wasu mutani da ban san su ba na ga kana magana da su a kan su taimaka maka but they were all laughing at you ni da ke gefe ban san me ke faruwa ba ga ka a kwance cikin jini ga babbar trailer tana nufo ka amma ka kasa tashi su kuma waɗannan mutanin sun ƙi taimakon ka ka tashi sai na yi saurin nufo ka na ja ka da iya ƙarfi na ina jan ka trailer ɗin na hawa kai na daga haka na tashi daga barcin ina ta mamakin toh ni kuma meye haɗi na da kai, a karo na biyun kuwa mafarki na yi wai muna dokar daji ana bin mu da bindigogi ba zan iya tuno fukokin su ba amma ba su gi su huɗu zuwa biyar ba da suke bin mu har suka cin mana suka zagaye mu you were trying to protect me amma su kuma sun ƙi yarda so suke su same ni ganin ba za su same ni ba sai suka ɗaga bindigar da niyar sakar maka harsashin cikin ta da sauri nikuma na juyo zuwa gaban ka suna sake harsashin sai ya same ni ganin ba kai suka samu ba sai suka kuma saita bindigar da niyar sakar maka a nan ma na kuma tarewa ya same ni ina maka murmushi na bar numfashi daga nan ma haka na tashi daga barcin shiyasa nake ta ji a jiki na ya kamata in sanar da wani ko zai iya fassara min mafarkin da na yi ban samu ba sai da aunty mama ta ta tasa ni gaba na sanar da ita shine ta ke ce min duk yadda aka yi kana bukatar taimako kuma ni kadai ce zan iya taimaka maka da fari a shirme na dau maganar ta yaya zan taimaka maka me ya hada ni da kai da har za'a ce kana matsala kuma ni ce zan taimaka maka share maganar na yi sai da na ga mafarke mafarken na daɗa dami na sai na yanke hukuncin sanar da kai in ya so sai ka san abin yi amma aunty mama ta riga ni sanar da kai a lokacin da ban shirya gaya maka ba jin nauyin abin na yi sai na yi shiru ban faɗa maka ba but every night i usually have that nightmare it keep on disturbing me to the extent that i thought of letting you know maybe zan sami sa'ida a rai na"

Sosai na ga ya shiga wani hali sai na ji wani iri

"Humairah all those hurtful moments ke ya ke samu kuma yake faruwa da ni kuma ina bacci na peacefully a kullum?why?i guess matsaloli na ne ke shafar ki ina mai neman yafiyar ki Humairah ni ɗin mai laifi ne a gare ki but please find it in your heart to forgive me kina zaman zaman ki na saka ki a sabga ta ki yafe min Humairah kin ji"?  Maganganun na sa sai ya ba ni kunya meye kuma na neman yafiya a gare ni bayan Allah ne ya hukunta hakan

"Kana saka ni jin kunya saboda duk abin da ke faruwa Allah ne ya hukunta hakan toh menene na neman yafiya na dan na shigo rayuwar ka ni ban dauki hakan a matsayin zunubi ba ko laifi na dau hakan a matsayin kaddara ta ce dan haka ina rokan ka da ka daina neman yafiya na dan yin hakan kamar butulcewa fate ɗin mu ne wanda Allah ya tsara mana daga ni har kai"

Doguwar ajiyar zuciya yayi daga bisani ya ce da ni

"Aisha ina son ki ina maki so da ban taɓa yiwa wata ƴa mace ba ina son ki daga nan duniya har darul salam Aisha kin kasance fitila a rayuwata ban taba sanin ki ba baki taba sani na ba amma hikimar ubangiji ya haɗa mu wanda wayo ko dabarar mu bata isa ta hada mu ba for that am praising Allah in a special way for bringing such an angel into my life without my knowledge,i love you so much and i promise to be with you only you alone Aisha Murad ba zan taɓa barin ki ba ko da mutuwa zan yi akan ki zan mutu in bar ki ki rayu ki kular mana da ƴaƴan mu da za mu haifa i won't let anything happen to you zuciyar ki tsarkakake ne yadda kike kyakyawa haka kike da kyakyawar zuciya rashin mijin aure a gare ki ya zame min babbar garabasa nikuma inshaAllah ba zan taɓa saka ki kuka ba is a promise from me to you we are MTB Humairah and i respect that ki so ni koh da kwatankwacin son da nake maki ne hakan ne kadaumi zai mayar da ni namiji a idon duniya baki daya dan sai kin samar min da kwanciyar hankali da natsuwa ta hanyar kula da ni da bani shawarwari masu kyau sannan duniya zata yi recognizing ɗi na a matsayin cikakken namiji as for me baki da matsala in dai yarda da so da kauna kike nema Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor Sadauki ya baki su tuntuni saura ke kuma ki ja ragamar akalar shi"

A sa'ilin da yake furta min waɗannan zafaffan kalamai rasa planet ɗin da nake na yi is it Jupiter Saturn or earth ji na yi duk duniya in aka cire iyaye na da kanwata sai aunty mama bana jin ina da wani wanda yake da muhimmanci a rayuwata sama da Abdulrahman dan haka har suman zaune na yi a da na yi tsammanin yaya kabeer was everything na yi zaton yayi hitting to the top har nake ganin na rasa wani jin daɗi da rayuwar *soyayya mai garɗi* sai ga shi ashe shi ɗin ɗalibi ne a fannin soyayya bai kai ga zama malamin ba wani hanin ga Allah baiwa ce na rasa masoyi duk aminaina biyu sun yi aure amma ni ban san fate ɗi na ba sai gashi cikin ruwan sanyi Allah ya jefo min sauƙi ba tare da na wulaƙanta ba wani hikimar sai ubangiji

"I love you too Humair i love you so so much and i promise to hold on to you till my last breath"a lokacin da a ce muna da aure a tsakanin mu ni na san babu abin da zai hana shi rungume ni dan iya control yayi kokarin yi tambayar shi na yi

"Humair what about khadijah me zamu ce mata"?

Yamutsa fuska yayi ya ce

"Manta da khadijah Humairah she is out if the country na yi signing mata resignation latter din da ta kawo min and she is now free kuma babu abin da ta isa ta yi dan manyan ta ma dealing nake kan yi da su bare ita da yanzu ta fara shiga system ɗin dan haka ki kwantar da hankalin ki nothing negative is coming our way as faemr as we will hold on to each other humm"? Ɗaga mai kai na na yi though ina jin guiltiness na ɗan kama ni amma wata zuciyar sai ta rinƙa tunzira ni akan in share abin kawai komai na faruwa ne da sanadi dan haka sai na share maganar na kuma jefo mai wata tambayar

"Amma me yasa kullum in ka zo nan ba ka barin motar ka a waje saidai ka kira a kawo maka daga baya"? Dariya ya ɗan yi

"Ahh lallai wannan budurwar ta wa akwai hikimar tambaya"dariyar muka sakar wa juna a lokaci ɗaya

"Saboda security purpose kon ga nan wurin da muke babu wanda ya san da shi ke ce mutum ta farko da na fara kawowa nan wurin  nan ɗin ba ko ina bane illah gonar big sis ɗi na da nake kular mata da shi with the hope that in na gan ta zan damƙa mata" tausayi ya ba ni gudun kar ranshi ya yi ɗaci sai na ce

"Wow you are amazing Humair Allah ya bayyana mana su"da sauri ya ce

"Amin summa Amin Humairah"

A nan muka baje muna ta zuba soyayya har lokacin sallar la'asar ta yi ya tashi ya je ya kawo min butar alwala karba na yi na ajiye sai da ya tafi sannan na mayar da butar inda yake na dawo na zauna ko da ya fito ya same ni zaune sai ya ce

"Ba dai har kin idar ba ce mai eh na yi sai naga yana min kallon ƙurila har na fara tsarguwa na ce meye ɗaga kafaɗun sa yayi ya ce babu daga haka ya ce min in tashi mu ɗan zaga gari miƙewa na yi muka fito shi ya ƙarɓi maƙulin motar ya ja mu da eatery muka fara inda yayi mana ordern lafiyayen meal muka ci tare tsabagen na sake jiki da shi har ban ji kunyar cin abinci a gaban shi ba tun daga eatery ɗin nan muks riƙa yawo a cikin garin Abj kasancewar glasses ɗin motar tinted ne sai muka zuge glass ɗin ta yadda babu wanda zai gane mu bamu bar yawon ba sai 6:20pm inda ya kawo ni har gida yayi yayi in shiga nikuma na ce sai an kawo mai motar shi sannan zan wuce sai da yayi da gaske sannan na wuce bayan tulin love and romantic words ɗin da muka yi showering junan mu da shi mun rabu akan zai kira ni by 9pm kafin in kwanta farinciki na na ranar ta fi ta jiya dan haka na shige cikin parlor ina ta zuba murmushi ni kadai sai ji na yi an ce min
"Daga ina kike"na tsorata sosai dan kuwa na san laifi na yi shi sai dai a yafe min ba yin kai na bane.........,,

*_🍒  S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama Ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

91.9K 816 12
အသက်ရွယ်ကန့်သက်ချက်တွေ လွန်လွန်ကြူးကြူးပါဝင်လို့ ကိုယ့်ဟာကိုယ် ဆင်ခြင်ဖတ်ပါ။
28.7K 2.8K 36
her life is ending becouse of her biogical brother,he rapping her the frist tym that he see her in his life
659K 23.7K 200
[FIXED/FAN TRANSLATION] A student who was preparing for the Civil Service examination for 4th year suddenly found himself in an unfamiliar body 3 yea...
1.9M 97.2K 38
Presenting the story of ISHIKA MEHRA Whose innocence made the king bow down to her AND ABHIRAJ SINGH RATHORE Whose presence is enough to make the per...