🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 53-54

604 41 0
By SiyamaIbrahim

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

*_ina miƙa ta'aziya ta ga daukakin jama'ar Nigeria da suka rasa ƴanuwan su da wasu na kusa da su a kasar South Africa sakamakon Xenophobic attack da ya faru a satin da ya gabata Allah ya jikan waɗanda suka rasa rayukan su ya kai haske kabarin su ya rahamta masu ya sa in tamu ta zo mu cika da kyau da imani su kuma family ɗin victims ɗin Allah ya basu hakurin rashi_*
5⃣3⃣➖5⃣4⃣

"Kee ni ne"!!! Natsuwa na yi daga mutsu mutsun da na ke yi sakamakon jin muryar shi a hankali ya cire hannun na shi daga baki na yana kallo na harda dai a cikin duhu ne amma ina ganin irin kallon kuril din da ya ke min nima shi din nake kallo duk a zato na wani ne ya zo sace ni sai na natsu na yi shiru duk da wurin ya fara duhu amma ina iya hango kallon kuril din da yake ni na da shi rasa abin yi dan kuwa guilty conscious ya gama kama ni sai na dukar da idanuna kasa

"Zo mu shiga ciki mana"!!

Haka na bi shi ina gaba yana baya har muka karasa shiga cikin province din ce min yayi in zauna na zauna kamar wata zombie shima zaman yayi ya kura min ido kasa kallon shi na yi dan abubuwan sun min yawa ga kunyar shi na ranar da abin ya faru ga tausayin sa da ke daɗa shiga na from no where ga wani mumunar so da kaunar shi mai tsanani da ke fizga ta ta ko ina kuma he is still gentile to me and kind guilty conscious din sai ya ƙaru maganar shi ce ta dawo da ni daga maganar zucin da nake faman yi

"Me ya kawo ki nan Ms Murad"?? Rasa amsar bashi na yi ga kunya da ya kama ni toh me zan ce mai yanzu ya kawo ni haka muka yi zaman shiru na wasu lokuta yana tsammanin amsa daga gare ni ni kuma ban san me zan ce mai ba sai da ya kuma tambayar a karo na biyu

"Tambayar ki nake yi akan me ya kawo ki nan kin yi shiru"!!

Shahada na yi kawai na fara magana dan ban san ta yadda zan fuskance shi ba

"Errr..rrmmm.. da... mmm.. aa.... hayaniyar gidan ne ta yi yawa shi yasa na ce bari in zo nan kawai"..

Kallon tsaf ya min kafin in ga yana min murmushi haɗeda shafa fuskar shi zuwa haɓar shi yana ta zuba murmushi sai guiltiness ɗin ya daɗu

"Me kuma na yi min murmushi haka"??

Faɗaɗa murmushin yayi kafin ya tanka min

"Toh ba dole in yi murmushi ba bayan na tambaye ki sime question amma kin kasa ba ni simple answer and ni ina ganin amsar tambayar da na maki a fili ke kuma kin kasa fiddo da amsar" cigaba yayi da murmushin sa nikuma kunya ta daɗa kama ni sai na ga is better in faɗa mai gaskiyar maganar than in zauna ina nuƙu nuƙu tunda har yanzu yana cikin mood ɗin jin daɗi

Gyaran murya na yi sai na fara magana

"Ni toh ba kawai gajiya na yi da zamar gidan ba shine na ce zan zo nan din dan in huta ba".
A yaddana ti maganar a haka maganar ta mai ma'ana amma sai na ga ya chanza fuska alamun bai ji daɗin amsar da na bashi ba next sai na ga ya miƙe zai bar rumfar ba tare da ya ce min ƙala ba da sauri na ce mai

"Ina kuma zaka tafi bayan kai ka ce min in shigo"!!?

Juyawa bai yi ba sai ya ba ni amsa da little pieced  voice

"Ai gudun hayaniya kika zo yi kuma at the same time kim zo hutawa ne right?dan haka ki huta lafiya ni na tafi".. 

Ko second bai ƙara ba ya daga kafar shi zai kara one step saurin dakatar da shi na yi

"Please don't go".. Da shaking voive na yi maganar sai na ga ko ya tsaya har ya juyo ya tsura min ido waiting for what i will say next shiru na yi dan kunyar shi nake ji a ce ina mace amma ni ce da furta kalmar so ga ɗa namiji kai abin bai yi ba sai wata zuciyae ta ce amma ai shi ya fara furta maki yana son ki ba ke ba dan haka just go ahead and say it in ba haka ba ke gari zai waya duk waɗannan tunane tunanen a rai na nake yin su kuma yana tsaye yana jiran amsar da zan bashi to his greatest surprise sai na furta

"Dawo ka zauna mana ina khadijah ta ke"?

In absolute amusement ya ce

"What"tsorata na yi da reaction ɗin sa sai na matsa baya kaɗan ina kokarin hana kai na zubda hawayen da ke son gangaro min dan ni kadai na san radadin da na ji lokacin da na kira sunan khadijah kafin in gama dawowa daga tunanin nawa na ji karar wurgi da abu a firgice na karasa dawowa duniyar tunanin na gwalalo idanuna waje bottle water da ke wurin yayi jefa da sannan ya juyo a matuƙar hargitse

"Damn it damn it"juyawa yayi ya fara tafiya a zuciye dan ran shi ya kai kololuwar baci

"I love you Abdulrahman"!!! Dif na dauke wuta kamar ba ni na gama furta kalmar ba yanzun nan yayin da shi kuma ya kasa sauke kafar sa kasa daga ɗagawar da yayi da niyar yin wani takun shiru shiru ni ban kuma furta 'a ba shi kuma bai juyo ba chan kusan minti ɗaya kalmar ta kuma kufce min daga baki na

"I love you"a wannan karon muryata na nuna alamun karaya dan a karon farko bai juyo ba yanzu ɗin ma ban saka ran zai juyo ba sai kawai na ƙara furta kalmar

"I Love you Abdulrahman"!! a nan ya juyo ƙaɗan ƙaɗan har ya karasa juyowar gaba ɗaya ya fara min wani irin kallo tun daga ƙasa har sama ni kuma na zuba mai ido ina kallon irin kallon da yake min ƙala ban ce mai ba sai na ga ya juya zai fita kamar in kwala ihu dan azaban da nake ji a rai na i don't know how but i found myself saying

"I said that i love you Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor please don't go".....

Da sauri ya juyo ya karaso gare ni ya ce
  "Kika ce me"?

Ban tsaya bata lokaci ba na ce

"I daid i love you"! Sai ya girgiza kan shi alamun bai yarda ba kallon shi na yi na kuma maimaitawa

"I love you Abdulrahman"..
hannuwan shi biyu a kan kugun shi yana kallo na ya ce

"Ban ji me kike cewa ba Ms Murad sake maimaitawa"

A wannan karon da kuka na furta dan ko na san mamaki ne ya cika shi duba da yadda na nuna mai ƙiyayya a ranar da ya furta min kalmar so ta ya ma zai amince son gaskiya nake mishi

"I said that i Love you mr Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor i love you i love you dearly""!!...

Girgiza kan shi ya shiga yi yana murmushin mamaki ni kuma na tsura mai ido ina kallon shi cikin tausayi da danasanin hali na

"Ƙarya kike yi Aisha ba kya so na bakin da ya furta ƙi ko ya dawo ya furta so toh tabbas yana da manufa amma ba har zuciyar shi ya furta ba dan haka ki sanar da ni dalilin ki na furta min wannan kalma"!?? A zafaffe ya kammala maganar hawayen da na ke boyewa ne suka tona kan su duk abin da min a halin yanzu ba zan ji zafin shi ba saboda ni na janyowa kai na komai

"Stop crying and answer me"!!.. kukan na cigaba da yi har da shesheka na kasa magana saboda karfin kukan ya rinjayi murya ta

"Goddamn it magana nake miki amma kin saka min kuka kamar wacce na daka"??

"Ce maka na yi ina son ka Abdulrahman kuma wallahi har cikin zuciya ta nake faɗa ba wasa nake yi ba dan Allah ka daina ja min rai yin hakan barazana ne ga zuciya ta"Da kuka na ida maganar cikin zaƙuwa da tsawa ya ce

"Ƙarya kike yi ki ce min kina so na kuma kiyi zaton zan yarda ahh me zaki yi da saura second hand sauran khadijah wanda bai da kyau wanda bai da ajin da zaki saurara wanda bai kai matsayin wanda zaki kalla ki nuna a matsayin wanda kike tare da shi har ki kira shi da saurayin ki ta ya kike tsammanin waɗannan yaudararun kalamai na ki zasu yaudare ni for the second time kuma never"!!! Ya ida yana girgiza kan shi nima girgiza kan nake yi ina kuka kamar rai na

"I take them back ka min uziri dan girman Allah those words were out of anger ba a cikin hayyaci na na furta su ba believe me ba da gaske na ke ba faɗa kawai na yi amma bai kai zuciya ta ba"!!..

Wani irin kallo ya min wanda ya saka ni a ruɗu dan na kasa fassara ma'anar kallon bai ce min uffan ba ya ce

"Hmmm Ms Murad kenan me ya sa kika iya yaudara ne wai haka kin kware a iya poisoning mutum gabaɗaya i can't trust you anymore"... Waɗannan kalamai nasa kamar saukar dalma na ji su ya zan fahimtar da shi ya gane cewa ko a da ɗin ba da gaske na furta kalaman da na masa ba duk ni na janyowa kaina

Sai da ya ga da gasken kukan da nake yi ba crocodile tears ke fitowa ba sai ya tausasa muryar shi

  "Aisha ki gaya min gaskiya ke ma turo ki aka yi dan in saba da ke in faɗa tarkon son ki sannan ki bayar da ni ga waɗanda suka turo ki"?? Subhanallah iya abin da nake ta nanatawa a zuciya ta kenan ba dai kallon rashin yarda yake min ba in ko haka ne toh na yi wa kaina a yadda ya taso cikin wata bahaguwar rayuwa ta rashin yarda har karshen rayuwar mu ba zai taɓa yarda da ni ba me zan yi dan in gyara wanna rift ɗin a brain ɗin shi kawai nuna mai so da kauna zaki na yi a ko da yaushe cewar ɗayar zuciya ta dan haka na haɗa dukka zantukar da zan gaya mai domin wanke mummunar taɓon da yake zuciyar shi a kai na..

"Abdulrahman kalle ni"kallon na wa yayi cikin ido sai da na tabbatar da mun sami good eye contact kuma mun yi maintaining ɗin shi dan ta haka kawai nake ganin zai fi yarda ya ba wa magana ta muhimmanci

"Abdulrahman ka yarda da ni ban taɓa zalintar ka ba ko daidai da second ɗaya ban taɓa yarda wani abin cin zarafi ko wulaƙantuwa ya same ka ba ban taɓa kuskuren yarda a yi amfani da ni dan a cin ma wani manufa ba ka yarda da ni Abdulrahman tun ranar da na maka waɗannan kalamai ban kuma samin isashiyar bacci ba dan da zarar na kwanta bacci ya fara dauka ta sai in tashi sabpda ban da natsuwar zuci hankali na kullum a tashe yake tun ranar har yau aunty mama ba ta sake min bata bani kulawar da ya kamata saboda fushi ta ke da ni duk a kan ka office na daina zuwa tun ranar da abin nan ya faru alakata da khadijah has fade away duk saboda kai Abdulrahman zuwa na nan na biyu kenan ina zuwa in zauna in yi kuka in yi danasanin abin da na gaya maka baka gani ba duk na chanza daga yadda nake zuwa wata iri na fita a kamannina na koma wata iri na rame kullum cikin tunani da nadama nake na gama rurufe kofofin alkhairai na ban taɓa tunanin zan buɗewa wani ɗa namiji zuciya ta ba tun yanzu saboda abin da ya faru da ni na ɗauka daga kan shi shikenan na dai na soyayya saboda shi ya nuna min *Soyayya Mai Garɗi* shi ya koya min komai daga baya na rasa shi tun daga kan shi ban kuma gigin yarda da wani ɗa namiji ba dan haka lokacin da ka zo min da wannan maganar a banbarakwai ya riske ni ban mai fahimtar fasali ba duba da cewa kai ɗin husband to be ne na aminiyata khadijah ba zan iya cin amanar ta ba shi yasa na ƙi yarda da kudirin ka amma bayan doguwar lokaci da na dauka ina tunani sai na gano ba a ranar na fara son ka ba Abdulrahman na daɗe da kaunar ka a raina tun ban san kaina ba amma ban taɓa ganin shi a matsayin so ba na fi dangana hakan da son da nake yi wa zane zanen ka wanda shi ya janyo min so da kaunar ka mai tsanani a rai na ka duba fah sunan kamfanina _'M MOTIVES'_ ka san wannan suna ya samo asali ne ta dalilin ka saboda kai ne ainihin motive ɗin na wa kuma kai ne motivator ɗin na wa shi ya sa na sanar da mahaifi na har ya min bazata ta saka sunan a matsayin sunan kamfanina,sai da na ga an juya min baya ta ko wani bangare sannan na farka daga baccin da nake ti dan i always put others first kafin kai na amma sai ya zama kuma ni ce a receiving end din dan duk halin kirkin da na ke yi bai saka ni na tsira daga kaidin jama'a ba ciki har da na kusa da ni kana gani mutani mafi kusanci a rayuwata aka nemi salwantar da rayuwar su saboda na nuna damuwa ta a kan ka ta ya kake tsammanin da zuwan ka da wannan maganar farat ɗaya zan amince da bukatar ba bayan abubuwan da suka gudana a tsakanin mu ban yi wani tunani ba na furta maka waɗannan kalamai saboda ba a cikin hayyaci na nake ba ni na yi hakan ne dan in gujewa faɗawa a wani halin daga ni har kai ban taɓa tsammanin abin zai zame min damuwa sai da na rasa ka a kusa da ni na tsawon wata guda a sannan na gane cewa son ka da kaunar ka sun yi overshadowing di na ba zan iya daukar rashin ka ba ko na kira ka baya shiga in na tura maka messages ta email baka responding hakan ya daɗa rikitani na rasa yadda zan yi biki ake yi a gidan mu amma hankali na baya tare da ni tun da na ji muryar ka a wayata na rinƙa neman ka ban gan ka ba na koma ciki aka ce min ka zo ka tafi hankali na ya daɗa tashi na ji gidan ya min tsanani da duhu kasa controlling kaina na yi shi yasa na zo nan ɗin ko zan sami sauƙin radaɗin da ke dami na a zuciya ta.. Abdulrahman kana gani bayan duk waɗannan abubuwa zan yarda a hada baki da ni in cutar da kai kai ɗin da ka zame min haske a rayuwata tun ina yarinya ta, kai ɗin da ta dalilin ka na zamo abin da nake preswntly,kai ɗin da na girma da sonka a jinin jiki na, ba zan taɓa cutar da kai ba na san duk halin da kake nuna min ni na janyo shi laifi nane ba ka da laifi ko kaɗan dan ka nuna min rashin yarda da ni ƙarara ba zan yi fushi ba dan son da nake maka yana da girma a zuciya ta kuma ina mutunta ka ina ganin ƙimar ka ta yadda ko ma me ka min bana jin zan iya fushi da kai Abdulrahman dan haka in har bayan waɗannam bayanai da na maka bai gamsar da kai ba kana ji a ran ka kamar ni ba mai son ka tsakani da Allah bane kana iya goge ni a zuciyar ka a kwakwalwar ka a rayuwar ka ma gabadaya Abdulrahman amma ka sani ni ɗin mai son ka ce har abada"!!! Kaiwa nan na juya da sauri dan wani irin kukan rabuwa da shi ne ya taso min ba sauƙi a nashi bangaren kuwa ƙamewa yayi sakamakon jin irin wannan bayanai da na mai bai yi zaton jin haka daga gare ni ba kenan dama na dade ina son shi ne?amma ne yasa ban sanar da shi ba tuntuni?  ashe ina matukar kokarin kare shi ne daga shiga wani tarkon miyagu amma ni nake takura kaina and still abin da ya saka min da shi kenan how could he be so heartless by playing with my feelings har ya nisance ni da shi tsawon wata har guda bai min adalci ba dan haka ya yanke hukuncin comforting ɗi na

"Aisha Murad"zirrr na ji sakamakon sunan da ya kira ni da shi sai na dakata na tsaya ina share hawaye na

"Aisha Murad ki tsaya kar ki tafi a karo na biyu a rayuwata"...

Numfashi na sauke ina jin wani baƙon yanayi yana shiga na juyawa na yi na zuba mai idanu takowa yayi kusa dani tsayin shi ya fi na wa dan ma na saka takalmi mai ɗan tudu sai na kusa kamo shi a tsayi fargaba ne ya shige ni dan shauƙin son shi ne ke fizga ta ga wani maganaɗisun kaunar sa da ke birkita min tunani daf da daf muka tsaya kamar zai ratsa ni numfashin mu a lokaci ɗaya yake fita yana garwaye space din da ke tsakanin mu gaba dayan mu bari jikin namu ke yi ni na tsoro ne shi kuma na shaukin so na ne da ke tsuma shi mun kai kusan mintuna biyu a haka kafin in ga yana lowering kan shi ƙasa kadan kadan dago idon da zan yi na ga yanayin da yake ciki gabadaya ya fita a hayyacin sa yana neman ya gusar da tunanin sa ko ba a sanar da ni ba na san me yake shirin yi dan ni ɗin ba karamar yarinya bace da sauri na kawar da fuskata ina sauke nannuyar ajiyar zuciya sakamakon baƙon yanayin da na riski kai na a ciki ban taɓa jin irin wannan yanayi ba sai yau dan haka nayi saurin korar shaiɗan dan yana kwadaitar da ni mugun abu daga ni har shi ganin abin da na yi sai ya lumshe idanun shi yana murmushin da bai cika yin ta ba dan kusan ko wani lokaci smirk ya ke yi murmushin zuwa zuwa ne bai buɗe idanun ba sai da ya dau lokaci with extended chin sannan ya juyo fuskar shi direction ɗin da na juya fuskata ya kuma matsowa da fuskar shi so close inalilahi wainailaihir raji'un muna ga rasulu abin da ya subce ya fito min kenan dam ban san ya fito ba sai ji na yi yana kyalkyace dariya kamar wani zarrare abin mamaki abin almara mutumin da ban taba ganin kyakyawar murmushin sa ba shine yau har da lyakyace dariya haka kallon shi na ke galala har sai da ya tsagaita da dariyar ya kuma naɗa min wani sunan da ragowar murmushi a kan fuskar shi

"Humairah"
  Subhanallah ko dai duk abubuwan nam da gangar yake min su dan na gama confessing mai zuciya ta shi yasa yake min haka dan ya ga iyaka ta why is he toying with my feelings?

Da serious tune ya kira ni a wannan karon
"Humairah me ya sa kike gudu na yanzu fah kika gama confessing mim komai then why are you avoiding me ko dai wari nake miki ne ban sani ba"?? Da sauri na dago na girgiza mai kai ina waro idanuna waje

Jijiga kan shi yayi yana pouting lips din shi ban ankara ba na kuma ganin shi kusa da ni ai a 360 na janye baya ina fifita da hannu na sauri sauri dan wata zufa ce ta kwace min ban san lokacin da ta balle min ba me zai yi sai ya saka wata muguwar dariya har da durkusawa sake baki na yi ina kallon ikon rabbi dama ya iya dariya har haka hala saboda matsalolin shi ya ke dadaure fuska bai son dariya a baya? Hmm

  "Humairah kina da abin dariya ban taɓa sani ba"ya dan dara kadan abin sai ya bani dariya nima dan sai a lokacin nake tuno tabargazar da na yi na furta wannan kalma da ta saka shi dariya haka

Zuwa wasu mintoci ya kalle ni da serious face ya ce

"Zo mu karasa ciki"yana gaba ina baya amma yana tafe yana juyowa yana duba ni ban ji wani abu ba ko ɗar sai muka cigaba da  ratsa cikin budaɗen wurin nan har muka iso wani wuri da ya ke kamar masallaci ne dan yanayin ginin shi bai da maraba da masallaci tun daga nesa nake hango ginin dan haka sai na kwaɗaotu da son ganin ginin muna karasawa ya tsaya daidai kofar masallacin ya juyo da ɗan murmushi a fuskar shi ya ce min

"Humairah bari in kawo maki kettle ki yi alwala kin ga lokacin sallah yayi" sai wani gentile gentile ya ke yi har na rasa gane shi sosai not quite long ya gama bambami amma yanzu yanzu wai har ya sauko ikon Allah kawo min butar yayi cike da ruwa wai in yi alwala muyi sallah da toh nagode na amsa mai sai da na bari ya wuce sannan na mayar da butar inda ya dauko dan ni ba sallar zan yi ba shi kadan shi ya gabatar da sallar shi ya fito ya same ni zaune kan dakalin masallacin tambaya na yayi ko na yi sallar na ce eh a nan waje na yi yana saka takalmin shi yana min kallon kurilla har ya gama ya ce

"Taso mu tafi gida kar a tafi a bar ki"ni ba abim da na so ji ba kenan dan haka sai na yamutsa fuska ta na ce

"Kar ka damu ai ni na kawo kai na nan ɗin"sai na yi gaba murmushi mai sauti yayi yana faɗin

"Someone will grab it dinner very soon"tsoro ne ya kama ni sai na kasa gaba na tsaya ina jin tsoro akwai namomin daji ne a nan ɗin

"Kin ga zo ki ga wani abu kafin ki tafi"ya fada yana kokarin saka hannun shi  aljihun shi wayar sa ce ya fiddo ya ɗan daddana kadan sai ya nuna min wurin zama karkashin wata rumfa mai hasken fitila saita wayar yayi ya ajiye ta muna facing wayar ban san ta ya aka yi hakan ba sai na ga ya matso kusa da miban kuma matsa ba bae in yi mai faɗar zuwa musa da ni muna zaunen babu dadewa sai ga fuskokin wasu tsoffi biyu mace da namiji suna murmushi ita tsohuwar ce ta fara magana kamar haka

"Sadauki yanzu ka rasa wacce zaka min kishiya da sai wannan mummunar ɗiyar baƙa da ita yoo ai na fi ta farin fata da tsufar ta wa hancin kawai da ido zata nuna min suma dan ƙuruciya ke yawo a jikin ta in ba haka ba ai bata kama ni a kyau ba,ke kuma mummuna kin bi kin kalailaye min jika kika saka shi jinyar sama da wata guda duk kular da nake bashi rainawa yake wai sai boss lady ta zo zai ji sauƙi ikon Allah kai sadauki ka gaya mata cewa jiy..... Ai a sittin ya ce

"No granny kar mu fara da ke ban fah ce ki min taɓara ba daga kira baki bari mun ko gaisa ba ba tambaya ta koh ya aiki kawai sai ki fara sakin magana?na cewa grandpa a kai ki home of the aged ya ƙi kema kike soyayya balle ni grandma"ya kare yana kanne mata ido ko nba'a faɗa ba na san kakarsa ce wacce ta karasa rike shi har ya gama girma dan ga kamannin nan shi da ita tsohon da ke zaune tuntuni yana ta zuba murmushi bai ce komai ba ya magantu

"Sadauki ya ayyukan ka da fatan ba su takura maka ko"?

Murmushin shima ya mayar masa yana shafa fuskar shi

"Aiki Alhamdulilah grandpa wai me ka bawa wannan tsohuwar take ta jin ƙarfi har take kiran wife to be di na da mummuna"dariya suka yi at the same time gwanin sha'awa sai tsohon ya min magana

"Aisha ya kike sadauki bai bar mu mun huta ba ko da yaushe in har ya zo garin nan magana ɗaya biyu sai ya kira Aisha mun yi mun yi ya haɗa mu da ke ya ce lokacin haɗa mu bai yi ba ina ganin yanzu ne lokacin ya iso koh sadauki"? Dariya suka kuma yi su ukun saɓanin ni da na murmusa dan sun burge ni sosai har nake tunanin nima da ina da ƴanuwa ko kakanni da haka zamu na yi da su muryar ta ya dawo da ni daga tunani na

"Ke mummuna nan gani nan bari ni da sadauki mutu ka raba dan ki sani kuruciyar ki ba zai saka shi ya chanza ni ba dan da tsohon zuma ake magana yawwa"dariya suka kuma yi dan grandma akwai kayan dariya

"Kai sadauki wai ita yarinyar kurma ce ko me tun dazu bata ce komai ba"!! Kallo na yayi yana murmushi dan a lokacin ji yake kamar ya ma rigada ya aure ni saƙe saƙen da yake yi a zuciyar sa sun fi karfin matakin da muke kai cige lips din sa yayi kadan hade da furta

"Grandma me yasa kika cika saurin yanke hukunci ne kina abu kamar ba ki san sadaukin ki ba yadda na ke haka itama take dan haka ki mata uziri tsohuwa zan roƙe ta tayi magana kafin mu tafi"

Kyaɓe baki tayi ta ce

"Inyee iyayi da rigima maganar ma ba za'a yi mana ba sai an roka? toh rike maganar ki mummuna kawai"a wannan karon har da ni aka dara dan kuwa ta ba ni dariya ba kaɗan ba toh shi dama dalin shi na haɗa mu kenan dan in ware kafin in koma gida kuma Alhamdulilah na sake da su mun gaisa sun tambaye ni jama'ar gida da taro na amsa masu da lafiya kusan 30minutes muna hira da su kafin mu yi sallama tsoffin na da kirki hakan daɗa kara son shi yayi a rai na tare da ƙimar shi da ya daɗu kashe wayar yayi ya ce min

"Humairah are you happy now"ban san lokacin da na ce mai

"Yes am happy Humair" da mamaki ya ce

"Ohh suna kika bani kenan Humairah"?? Ƴar dariya na yi na ce mai eh kamar yadda ya saka min sunan Humairah dariya muka yi mu biyun kafin ya ce min mu tafi dare na yi muka fito a tare har gaban motata ya rako ni tare da ce min
  "Take care of yourself for me Humairah humm"??

Da murmushi a kan fuskar sa ya ce min

"Gobe inshaAllah zan sanar da ke abunuwan da baki sani ba dangane da ni kin ji lets meet  here 12 noon dont bee late kin ji"?? Sai murmushi yake ta zubawa nima haka daga nan yayi waving ɗi na har na fara starting motar sai na ga ya matso kusa ya ce

"Humairah koma ɗayar seat ɗin lemme drive you home it will be more safer humm" girgiza mai kai na yi na matsan zuwa seat ɗin gefen shi kuma ya shigo ya tayar da motar muka bar wurin tun da ya fara tuƙin ɗaya biyu sai ya kalle ni ya rinƙa murmushi wani sa'in nakan taya shi murmushin wani sa'in sai in sunkuyar da kai na tuƙin da ya ke yi ba na mai niyar kai ni gida in less than 10 minutes ba ne sai seme seme yake yi kamar bai son tuƙin sai da ya hau kan titi sosai sai ya dan kara gudu kadan muna kawowa kusa da gida sai ya rage gudun ya gangara gefen titi saboda jama'a sun yi yawa a kofar gidan me alamu dai sun nuna dinner za'a tafi kashe motar yayi ya ɗan leaning da kujerar yana lumshe ido

"Humairah"!! sai da numfashi na ya ɗan yi skipping kafin in amsa mai

"Uhum"

"I will confess everything to you tomorrow i promise you" cikin calm voice yayi maganar sai muryar ta sa ta min tasiri na daga kai na ina murmushi daga haka ya fita ya buɗe min kofar motar na fito ya mika min wayoyi na tare da riga ni karasawa kofar gate din daya daga cikin masu aikin gidan ya kira ya zo ya shiga da motar ciki karbar car key din yayi ya shiga ya ja motar ya wuce mu ni kuma na sallame shi

"Sai da safe"
Sai ya saka moon face yana yi kamar wani karamin yaro da mamaki na kalle shi na ce
"Me kuma"??

"Sai da safe kawai zaki ce humairah"

Ohh in ya kira wannan sunan har cikin ɓargon jiki na nake ji ta sai na lumshe ido na dan na fahimci me yake nufi

Cikin fizgewar numfashi na ce

"Good night Humair"kaiwa nan na yi saurin juyawa na tafi ina jin kunya kunyar shi murmushi mai sauti yayi dan har ina iya jiyo shi  ya ce

"Same to you too Humairah"na isa bakin gate din na juyo na hange shi tsaye sai na mai alamu da ya tafi shima ya min wai in tafi abu kamar wasu yara shi ya ja nima na ja karshe dai ni na tadi na bar shi dan jama'a sun yi yawa a kofar gidan mu na shige ina murmushi ni kadai kamar sabuwar kamu saɗaf saɗaf na shige daki na dan ban so a san cewa bana gidan aka gama shagulgulan bikin da sauri na yi wanka na shirya cikin kayan dinner din na fito na bi ayarin ƴan zuwa dinner din motar karshe ina bude motar da nufin shiga na ji wayata ta dau ruri na daga na saka a kunne ba tare da na duba sunan ba karaf muryar shi na ji

"Humairah koma ciki ki huta dan bana so gajiya ta saukar maki da zazzaɓi dan gobe will be a special day just go and sleep good night"mamaki ne ya kama ni dama bai tafi ba ne ko ya ya san cewa na fito haka na koma ban san dalili ba kashe wayoyin na yi na yi addua'ar bacci na kwanta ina ta tunano sweet moments din mu ina murmushi hoping and praying for it to continue haka na yi bacci ina tunanin ko me zai sanar da ni a goben oho amma na san ko ma dai menene it will be special and zai bar tarihi a rayuwar mu gaba ɗaya.........

*Hmmm ina maki fatan samin special sunday Aisha Humairah Murad Abdulrahman Abdulsalaam*

*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

41.5K 2.3K 42
Labarin Yarima Hafiz da Ummuna Salmah
88.6K 786 12
အသက်ရွယ်ကန့်သက်ချက်တွေ လွန်လွန်ကြူးကြူးပါဝင်လို့ ကိုယ့်ဟာကိုယ် ဆင်ခြင်ဖတ်ပါ။
657K 23.6K 200
[FIXED/FAN TRANSLATION] A student who was preparing for the Civil Service examination for 4th year suddenly found himself in an unfamiliar body 3 yea...
28.7K 2.8K 36
her life is ending becouse of her biogical brother,he rapping her the frist tym that he see her in his life