🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

Por SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining Más

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Part 49-50

612 44 1
Por SiyamaIbrahim

🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

4⃣9⃣➖5⃣0⃣

Tafi aka saka sai yi take yi tana mana kallon wulaƙanci kafin ta dakata ta tsaya tana ƙare mana kallo daga ni har shi shiru muka yi ni nafi kaɗuwa akan shi dan in ma ya kadun ma bai nuna ba unlike me da na kasa boyewa

Wannan matar ba kowa bace face khadijah wacce ta shigo mana a bazata ba tare da sanin mu ba sai da ta mana kallo tas ta zauna a kujerar ɗakin muka bi ta da kallo kafin ta ba ma wanda suke taren izinin shigowa shigowan yayi yana kallon mu irin zaku gane kuren ku ɗin nan shima zaman yayi a karo na biyu muka kalle su su biyun

"Hmmm Ms Murad boss lady mai kamfanin "M Motives da elegant Arch Abdulrahman Abdulsalaam Abdulshakoor the owner of "D'AA flame paintings most well known and popularly known as the number one best painter"tana isowa nan sai ta yi shiru na ƴan seconds sannan ta cigaba

"Kun ban mamaki wato hero ina nan ina mana yaƙi akan soyayyar mu amma kana nan kana shagalin ka da wannan?humm?hero ina chan ina ƙoƙarin ganin an yi fixing mana ranar auren mu da kai amma kai ko a jikin ka? na tsiyace na cire kunya ta na ƴa mace na zage na yi faɗa da aminiyata akan ka amma kai kai hero kaine ke backing ɗin ta ka gama nuna mata cewa dama chan nike ɗawainiya da son ka ni ke burin auren ka amma kai ba son hakan kake ba"ta ɗan ja fasali kafin ta ɗora

"Na san ni ke son ka amma kana ganin na chanchanci wannan wulaƙanci daga gare ka? eyye?sai ta saka kuka"

"Tun da nake da kai ban taba haɗa soyayyar ka da na kowa ba tun ina kankamuwa ta na tasho da son ka da kaunar ka a jinin jiki na amma haka ka zaɓi yi min?dan ni ke son ka?a da in na tambaye ka ko baka iya soyayya bane sai ka nuna min eh baka iya ba dan baka taba yi ba sai ni ce da ke mace na koma nuna maka soyayya a fili ko ba haka aka yi ba?yanzu da kake kokarin nunawa wata banzar so ai gashi nan ka san yadda ake ecpressing so a wurin wannan abin"..

Numfasawa tayi ta ɗora da
"Toh albishirin ki Aisha Murad daga ke har shi baku gaba na saboda baki isa in yi kishi da ke ba tunda kika dauke mar hankali a kaina toh na bar maki shi but ki tuna saƙon da na turo maki akan ki tanadi kayan yaƙi ki jira dawowa ta gashi na dawo unexpectedly yanzu kuma za mu fara dan na miki rantsuwa da mahallici na ke da kwanciyar hankali har abada bar ganin cewa na bar maki shi ki ɗauka wai ko bana son shi ne a'a na bar maki shi ne dan na fi ƙarfin haɗa abu da ke amma am telling you today ki rubuta ki ajiye tashin hankali ya buɗe babi kenan a rayuwar ki Aisha Murad"ta na kawowa nan ta tashi tsaye ta kalle shi ta ce

"And for you" tana mai kallon yaya Aqeeb da suka shigo tare

"Ga ta nan in zaka mayar da hankalin ka kan matar ka ka mayar dan ka gane ma idanun ka irin sheƙe ayar da take yi da sunan aiki kai bata bar ka ka zauna lafiya ba sannan bata bar ka ka aure ta ba tana wahal da kai amma kana chan kana azabtar da kan ka bayan kana da matar ka kyakyawa ƴar asali ba wasu ba da ba'a san asalin su ba mtsw" da tsaki ta karasa maganar tana mai dalla mana harara for the second time da na ji zafin yi min gorin rashin asalin da ake yi da farko aunty mufeedah ta min a yau kuma khadijah why me? ban san cewa na fara hawaye ba sai da na ji saukar hawayen a ƙirji na na kai duba na gun na ga hawaye na kai hannu na kan kumatu na na ji ruwa ruwa alamun hawayen ne ya fito min ba tare da na shirya ba a zuciye na goge fuskata na matso kusa da ita na ɗaga hannu na na nuna ta da yatsa na manuniya

"Khadijah ya ishe ki haka ba zan dau wulaƙancin ki ba for the second time ki bini har building ɗina ki gaya min magana son ran ki sannan kiyi tunanin zan bar ki ki tafi haka nan kin yi karya dan haka ki bude kunnuwar ki da kyau ki ji ni Abdulrahman is nothing to me because mazan da suka fishi kyau da aji ban saurare su ba ballantana shi shi da yake saura sauran ma sauran ki mutumin da na tsinta a hanya ba a gida na ba wanda ban san asalin shi ba ban san ko shi ɗin waye ba kike tsammanin zai yi tormenting ɗi na da wani abu da yake da shi?kina ganin ke ɗin kin cika mace ne da har zaki tsaya kina exchangimg words da ni a kan ɗa namiji? kenan baki cika mace ba dan ni ɗin nan da kika gani ban taɓa son namiji ba sai dai ni ya so ni kuma ai kin ga hakan da idon ki sau uku yaya kabeer shi ya ke mutuwar so na shima wannan ɗin na nuna yaya Aqeeb shima shi ke so na ban ma san yana yi ba jabeer ke shaida ce ban taɓa nuna mai so ba shi yayi ta bulaguron sa sai a kan wannan na juya na kalle shi ido cikin ido na cigaba wanda ban taɓa daukar lafuzan bakin shi da ƙima ba shi kike tunanin ni Aisha Murad zan tsaya ina chanza kalamai akan shi bai taka waɗannan matakai ko ba dan a second hand nake kallon shi mutumin da ke mu'ammala da second hand shima ai second hand ɗin ne"buɗe idanuwan shi yayi cikin nawa nima na cigaba da kallon cikin idon na shi for a moment kafin in cire idon na wa na mayar da shi kan yaya Aqeeb da ke tsaye kamar gunki

"Kai kuma Mr Habib ban san kwakwalwar ka bai gama nunar da zai dauki matsalolin ka ba amma har ka ke yaudarar kanka wai kai ɗin psychologist ne mai sanin hallayar ɗan adam tirr da bahaguwar tunanin ka kana namiji amma mace ce ke brainwashing ɗin ka har ka iya takowa ka zo nan tare da ita kana bin ta kamar mahaifiyar ka tirr"na tofar da yawu na juya ga ita khadijar na mata kallon tsana dan kuwa zuwa wannan lokacin ta fitar min a rai ta ba ni mamakin da ban taɓa tsammani ba

"Khadijah kin ba ni mamaki amma ko da yake ɗan duniya wanda bai sami isashiyar tarbiya ba yana iya yin abin da ya fi haka amma ni tunda na sami isashiyar tarbiya i won't say some of the dirty acts you portray ai kin gane me nake nufi"na dage mata gira ɗaya da yake marar kunya ce ita sai ta turje

"How dare you Aisha how dare you ki zagar min hero a gaba na ƙarya na maki ko ƙarya na faɗa?ba snatching din sa kika min ba?in ba salon duniyanci ba ta yaya zaki zauna ki tsara zane sannan ki rasa wa zaki zana sai wannan"ta yi nuni da board din wanda hoton shi ya fito sosai suffar shi ta kyakyawar ɗan boko ya fito sarari

"Kalli wannan zanen da kyau ki ƙaryata min cewa ba son sa kike yi ba Aisha"? Kunyar duniya na ji shi a wannan rana dan a gaskiya fasahar zanen ne ya zo min amma ban san cewa zan karasa zanen da fuskar shi ba dan haka ƙarfin hali na yi na yi interrupting ɗin ta

"So what dan na zana shi? sai me? ganin dama na ne fasaha ta ce ba taki ba dan haka fitar min daga nan kuma ki gaggauta bari min building kafin rai na ya daɗa baci in maki abin da zaki mutu kina da kin sani" a tsawace na karasa maganar ina mai nuna mata hanyar fita yaya Aqeeb da ya buɗe baki kenan da nufin magana na daka mai tsawa

"Outtt"tare da nuna mai hanyar waje wannan wace iriyar masiface da bala'ai ba'a fita a wannan ba an shiga wannan da hakan aunty mama ke cewa son juna muke yi ba mu sani ba tsaƙi na yi a daidai lokacin da ya fita dan dama shi bai da niyar zuwa ita ce ta zuga shi akan su zo su min ɗibar albarkar ta manta cewa shi ɗin mai mutunta nine mai bauta min kamar ran shi dan tsabagen kaunar da yake min ne yasa sama da shekaru biyu ya kasa tarawa da matar sa yana jira na ko zan chanza ra'ayi in dawo gare shi dan haka kanzil bai ce ba ya fita abin shi da ƙudirin gyara gidan auren shi dan ya san ya rasa ni har abada duba da irin tsantsar so na da ya gani a idanun Abdulrahman wanda shi kuma ya san bai taka wannan mataki ba dan bai da qualities din mijin da zan aura tunda har na iya furta me zan yi da sauran second hand a gaban su lallai na tsani namijin da ke harƙalla da mata kuma shi ya kasance mai bin mata dan koh bai taba kwanciya da su ba yana rage zafi da su kenan yana jerin second hand din kenan he can't associate with me shi yasa ya yanke hukuncin fitar da ni daga zuciyar sa...

Ita kuwa rikaƙiyar kin fita ta yi a dole sai ta ga reaction din shi wani banzan kallo na bi ta da shi wanda ya saka ta cire idanun ta daga kallon da take mai kallon kallo muka yi wa juna kafin ta fara takawa da nufin fita

"Aisha baki yi winning ba dan haka kar ki ji daɗi it will only last a little"smirk ɗin takaici ta yi sannan ta fita daga office din.

Shi da tun da aka fara hayaniyar bai ce ƙala ba sai ya cigaba da bi na da kallo masu manifofi kala kala ni ma shi na kalla na ce mai

"Please leave"cikin sanyin murya dan na rasa confidence din daga mai muryar har in mai rashin kunyar da na yi dazu ko gezau bai yi ba yana tsaya yana kokarin digesting furucin da na furta tuntuni kasa jurewa kallon na yi na juya da nufin barin mai dakin sai na ji muryar shi a salamce

"Aisha"ɗif na dauke wuta bai taɓa kira na da sunana ba bai taba kiran sunan a gaba na na ji ba sai dai yace Ms Murad a karo na biyu ya kira sunan

"Aisha dakata"har ciki cikin zuciya ta na ji sunan dan a kwanciyar murya ya kira sunan kamar mai jin tsoron furta sunan tsayawa kam na yi amma juyawan ne ban yi ba kuma ban yi niyar yi ba mun shafe wasu daƙiƙu a tsaye shi bai kuma cewa komai ba ni kuma ban fita ba kuma ban juyo ba sai daga baya na yi kokarin daga kafata dan barin dakin dan cigaba da tsayawa a ɗakin na daɗa tunzira ni yin abin da zai zo daga baya ya dame ni wata uwar tsawar da ya daka min wanda ko Abbu da ke mahaifi na bai taɓa min ba ya sa na juya a rikice na sauke idanuna a kan shi wanda sai a lokacin na lura da yanayin shi zufa ne sosai a kan fuskar shi ran shi ya kai kololuwar baci dan har a zahirance ya nuna idon shi ƙyam a cikin nawa kafin in ankara na ga mutum ya fara zuwa towards my direction a zafafe ya ke tafiyar cikin sauri yana iso ni na rufe idanuna dan the next thing i was expecting was a sound slap sai na ji shiru

"Open up your eyes will you"? A tsawace ya gama kai aya hawaye ne suka yi nasarar excaping daga idanuna wata tsawar ya min

"I said you should open up your eyes"!!

Buɗe idon na yi na sauke su a ƙasa because ba zan iya kallon shi ba

"Good now look at me"ban kalle shin ba ya kuma min ihu

"Look at me i said"a hankali na daga kwayar idanuna na saka cikin nashi babu abin da nake iya hangowa sai tsantsar wutar bala'i da bacin rai idanuna na cikin na shi at the same time hawaye na zubo min

"You see baki da courage da confidence din da zaki kalli idanuna ki furta min kalaman da kika fada ɗazu"daɗa buɗe idanun na yi cikin mamaki in ban manta ba i was looking straight into his eyes while i was saying all those words dan haka na share hawayen da nufin sake maimaita abin da na faɗi ɗazu

Jan hanci na yi kafin in buɗe baki

"You are a second hand to me,saura,sauran khadijah wanda ban san shi ba ban kuma san asal.... ban ida ba kawai na ji fashewar abu ko da na kai duba na sai na ga glasses farfashe a ƙasa Keenan glass bouquet ɗi na ya ture ƙasa har abin ya fashe da sauri na dago the next thing da na gani kawai sai ya tura ni na haɗe da bangon wani gefen ɗakin wanda yake dauke da enlargement ɗin paintings kala kala muna isa bangon ya kai ma ɗaya enlargement din bugu har sai da ya fashe ya fadi wanda karar ya ruɗar da ni na saka hannu na rufe kunnuwa na cire min hannun yayi yana huci

"Kika ce min ni second hand ne? Right"? ya kuma kaiwa wani enlargement din bugu na kuma rikicewa

"Kika kira ni da saura"right"? nan ma kuma kaiwa wani enlargement din bugu yayi a karo na uku

"Nine namijin da bai kai sauran maza kyau ba right"? Bugun wani enlargement din yayi wanda yayi sanadiyar tsala mai ihu

"You are going mad you are out of your senses how could you be doing all these to me me na maka da kake saka min damuwa"

Shima cikin ihun ya min responding

"Yes ina saka miki damuwa saboda ni kika saka a damuwar ɗazu"
Mayar mai da martani na yi a zafafe nima

"Ka dai na blaming ɗi na dan ba karya na faɗi ko dama na san ka ne? ko kai din ba sauran wata bane me zan yi da kai da har aka zo ana min wulaƙanci"!!

Daɗa fasa wata enlargement din yayi ya matso kusa da ni kamar zai shige ni yana huci

"Kar ki ƙara am warning you"da ɓacin rai ya karasa maganar ni abin wani iri ya ke min akan me zai dau zafi dan na faɗi waɗannan maganganun

"You are losing your mind you don't know Mr Abdulsalaam" a rikice ya ce min

"Yes yes am losing my mind am losing my mind i don't know all because of you am losing my mind i don't know because i love you"a tsawace ya karasa maganar yana zazzare min ido kamar zai min wani abin

Out of the blue maganar tasa ta iso min kunnuwa na har ya shiga cikin kwakwalwa na na dago a hankali na kalle shi sannan kuma kaɗan kaɗan na mayar da idanuna ƙasa ina jin wani iri wani iri a lokaci guda wani baƙon yanayi na shiga na daɗa leaning da bangon na yi

Ɗakin ya lalace da glasses ko ta ko ina ga dripping din jini nan daga hannun shi flowers a barbaje a ƙasa brushes ɗi na duk sun zube colours din wasu a bude suke dan haka suka zube a floor din wasu kuma a rufe suke ko da suka fado basu zube ba air conditioner da ke dakin bai iya dauke mana zafin da muke ji ba dan daga ni har shi gumi muke yi painting board din da ke dauke da zanen da nake kan yi na kalla na ga babu zanen a hankali na rinƙa duba ɗakin ko zan gani chan na hango painting din ya baci da jini koh da na ɗaga idanuna a hannun shi na tsinci painting din idon shi ya koma jazir saboda ɓacin rai kallon ido cikin ido muka yi kafin ya jefo min wata tambayar da girgiza ni

"If you wanna deny abubuwan da khadijah ta faɗa akan ki ɗazu ina so ki yi proving min cewa you don't have any feelings for me and tell me reason why you decided to painting me bayan ga mutani da yawa da ya kamata ki yi painting amma kika zaɓi painting di na"?

Cikin salama na miƙe zan fita dan ban da amsoshin tambayoyin shi wani irin fisga ya kai min ya dawo da ni
Cikin bacin rai ya ke magana

"You dare not walk out of me ko baki ji abin da na faɗa bane agreed kin yi amfani da tricks ɗin ki a kai na kuma you succeeded and i asked you ki bani amsa don't you have any feelings for me"? ya kura min ido a ranar da wani ne ya yi tempering min da dignity dina by touching me only God knows abin da zan mashi amma shi kuma yayin but na kasa yin komai ko me ya sa hakan

Kallon shi na yi na ce
"Ka yi kuskure da ka yi mafarkin cewa ina da wani abu wai feelings about you,you are wrong dan tun daga kan first love ɗi na bana kallon wani namiji a matsayin namiji sai mace dan har yau ban ga namiji mai qualities din namijin da zan saurara ba har ma in yi developing mai feelings so yanzu ka gamsu da bayani na?zaka iya bari na in tafi"?wani dariyar takaici yayi kafin ya haɗe fuskar shi

"Karya kike yi karya kike yi in har da gaske ne me yasa kika kasa kallon kwayar idanuna ki furta?me yasa kike kuka a yayin da kike maganar da ni?me yasa kika kasa furta min ba kya so na kuma ba ki da feeling a kai na? Eyye?""

Ni kaina ban san dalili ba

"Baki da amsar hakan koh?"daure ni yayi da jijiyoyin jiki na dan haka na juya da sauri na fita ina jin shi yana cewa

"I said i love you Aisha Murad i love you""!!!

Da hawaye na karasa fitowa balcony din cincirindon mutani na gani a wajen da masu jira na da masu jiran su ga kwaf kwaf me ke faruwa sakamakon jin karar farfaahewar abubuwa daga ɗakin wasu kuwa so suke suga fitowar mu ni da shi ganin akasin haka sai aka fara jeho min maganganu kamar

"Ms Murad ko me je faruwa ne a dakin zanen ki mun ji karar farfaahewar abubuwa ga shi kin fito kuna kuka"?
"Ko zaki iya sanar da mu abin da ya faru" da sauran su kallon su duka na yi na daga ƙafa zan wuce sai na ji ya ce

"Ai bata da amsar ba ku saboda ta yi amfani da tricks din ta ta yaudari wani"!! Kaiwa nan ya yi gaba abin shi nima sai na wuce na bar su a wurin

Rufe kofar na yi na zauna a ƙasa na buɗe babin kuka yi nake yi kamar me sosai na yi kukan nan har hawayen suka daina fitowa me na yi wa kaina ne shin da na dau matakin da na fara dauka a farko?nikuma irin tawa kaddarar kenan? Haka na rinka surutai marasa kan gado kamar zararriya ban bar building din nan ba sai kusan 7:25pm na dare

***************

Abbu da su aunty mama duk hankulan su ya tashi jin ban dawo gidan ba gashi an basu tabbacin cewa na bar office din duk inda suke saka ran sami na sun duba basu same ni ba sun kira wayoyi na amma switched off a daidai lokacin da Abbu ke cewa a baza hotunan a fara nema na na shigo falon katse wayar yayi cikin mamaki ya ce

"Mama na ina kika shiga kika saka hankulan mu tashi haka"ran shi a bace ya ke bai taɓa yi min irin wannan fushin ba so a ranar da ya min din sai na ji bacin rai na ya daɗu na saka kuka da sauri aunty mama ta karaso ita da ummi suka rungume ni ina kukan ummi na taya ni dan tun tasowar mu bata taba ganin ran Abbu ya baci a kai na ba sai ranar aunty mama ce ta ce mu tafi daki baby haka muka tafi ya rage daga Abbu sai yaya ib karshe yaya ib din ya koma ba wa Abbu hakuri dan shima bai jima da dawowa ba ya tarar da labarin

Wanka ta saka ni yi kafin ta kawo min abinci a kan in ci kallon abincin na yi na ce mata

"Na koshi"ko sauraro na bata yi ba ta diba a plate ta matso kusa da ni ta ce min
"Haa buɗe bakin"ba yadda zan yi haka na bude tana saka min spoon daya na bishi da kuka bata kula ni ba sai da ta bani kusan rabin plate din ummi ta miko mata fruit juice din ta bani na sha kadan sannan ta ce ma ummi ta kwashe kayan ta kai kitchen sannan in ta kai kar ta dawo dan magana zamu yi haka ta fita abin ta

Juyowa tayi sosai ta kure ni da ido tana son gano me ke dami na chan sai da tambaye ni

"Mama na me ya faru kuma bayan lafiya kalau kika fita yau ana wasa da dariya"?

Kamar jira nake na saka kuka sai ta dakatar da ni

"A'a fah yanzu zamu ɓata da ke tambayar ki na yi ba kuka na ce ki min ba"sai na tsagaita kukan na fuskance ta na fara magana

"Aunty mama mutuwa zan yi, mutuwa kawai zan yi dan ba zan iya daukar wannan kaddarar ta wa ba, aunty kin gani ko kin ga abin da shawarar ki ta janyo min aunty mama an min abin da har abada ba zan taɓa mantawa da shi ba an min kazafi an tozartani a gaban media a gaban jama'a a gaban duniya aunty mama kin ga ni ko"?da kuka na karasa maganar ita kanta bata san ta inda maganar tawa ta dosa ba dan haka sai ta tambaye ni

"Baby me ya faru ne wai ban gane inda maganganun ki suka dosa ba"share hawaye na na yi na fara warware mata abubuwan da suka faru a karshe na ce

"Aunty mama ba zan iya cin amanar khadijah ba kin san me ya ce min"? Cikin zumuɗi ta ce min
A'a sai kin faɗa baby"

Jan hanci na yi na share hawayen fuskata

"Ce min yayi i love you Aisha Murad har sau biyu yana nanata min wannan kalmar"da kuka na karasa maganar ga mamaki na shewa na ga aunty mama ta yi tana tafa hannu

"Kwaliya ta biya kudin sabulu baby ai shi kenan me ke kika ce mai"? Shekeke na kalle ta dan ta bani mamaki ita dariya maganar ke bata ma

"Me yasa ko da yaushe kike daukar magana da wasa aunty mama"?

"Saboda maganganun naki na wasa ne baby kin ga kamar wannan maganar ta ki ai ba abin kuja bane abin murna ce yanzu dai me kika ce mai"?

"Babu babu komai ban ce mai komai ba"!
Na share ta kawai sai ta janyo hannu na tana kokarin kallon idanuna ni kuma kaucewa na yi

"No tell me the truth baby me kika gaya mai"?

Na gaji da nauyin da ke zuciya ta dan haka na gaya mata komai na danne zuciya na dan kar in yi kuka

Mamaki ƙarara na hango a idon aunty mama salati ta saka kafin ta cire hannun ta daga na wa ta tashi tsaye a karon farko da ta kira sunana rai a bace

"Aisha ban taɓa sanin cewa ke din shashasha ba ce namiji ya dizga budurwar shi ya ƙi ta a gaban ki a gaban duniya ya tsaya maki ya kare ki karshe ya nuna maki son ki yake yi amma ki rasa da me zaki saka mai sai wannan hurtful words din? eyye?wace irin yarinya ce ke Aisha?yanzu da kika ƙi shi ɗin so kike ki ce min da gaske ba ki jin wani abu game da shi?so kike ki ce min ba kya son shi kema?kina so ya yarda da cewa babu digon son shi a zuciyar ki ko ƙanƙani? No Aisha kin tafka babbar kuskure dan mutum irin shi mai ilimi da dukiya ya tsaya zabar ki a cikun tarin matan da yake tarraya da su yau da kullum abin burgewa ne but what did you do kin yi rejecting din shi Allah ya kawo maki karshen wahalhalun da kike ta faman shiga amma kika yi shunting ma karshen wahalar ƙofa what more did you want me to do for you Aisha? na taka rawar da zan yi akan in ga kun bayyana sirrin ran ku shi ya fallasa amma ke kece mai taurin kan da baki fallasa ba sannan shi da ya faɗi maki kin yi rejecting din shi har da kara gwasale shi Aisha am fed up with all these childish attitude of yours so ki yi duk abin da kika ga ya dace da ke a rayuwar ki na cure hannu na a sabgar ki Boss Lady"!!!! Kaiwa nan ta tashi ta fita abin ta leaving me all alone cikin ruɗu da rashin madafa na rasa uwa a karo na biyu a rayuwa ta na rasa mai share min kuka na toh me na yi wa kai na kuma inalilahi wainnailaihir raji'un sosai na yi zurfi cikin tunani ina yi ina kuka har bacci ya dauke ni a wurin..

************"
_Next morning_

Cikin simple outfit na atamfa doguwar riga da dankwalin ta na fito zuwa falon inda na gan su suna having breakfast peacefully joining din su na yi na gaida su Abbu kadai da yaya ib suka amsa ummi ta gaida ni na amsa amma aunty mama bata amsa min ba abin ya dame ni matuka abincin ma kadan na ci dan damuwa sun min yawa karshe tashi na yi na wuce zuwa bayan gidan wato garden din gidan mu dan ban da niyyar zuwa office na gama planning for the next two weeks zan yi quitting zuwa office sai abubuwa sun ɗan min sauƙi

Zama na babu daɗewa sai ga yaya ib ya biyo ni kallon shi na yi na mai murmushin yaƙe zama kusa da ni yayi ya kira sunana amsa mai na yi na juya na kalle shi

"Ko me ya faru ki san maganin shi addu'a dan haka duk matsalar da kike ciki kar ki manta cewa Allah shine zai maki maganin komai amma ba damuwa koh regrets ba had i know won't lead you to anything but karayar zuciya dan haka ki cire tunanin baya ki yi focusing a future kin ji ƴar lukuta"? Da murmushi ya karasa maganar nima sai na mayar mai da murmushin kafin ya ce min

"anjima ki shirya zamu tafi cinema ni ke da ummi ok"!! da toh na amsa mai ina nuna jin daɗi na a fili haka na yi spending kusan rabin ranar a garden kafin daga baya in shige cikin gidan na shirya cikin kananan kaya na dora doguwar riga mai igiya biyu na fito da ƴar karamar side bag inda na tarar da su ummi da yaya ib na jira na fita muka yi tare da yi ma su aunty mama sallama bata amsa min ba sai ta ce ma su ummi a dawo lafiya couple of the month tana murmushi suma suna yi haka muka fita rai na na ɓaci saboda ganin irin fushin da aunty mama ke yi da ni dan bata taɓa fushi da ni ba tun da muke sai a wannan karon dan haka da tunane tunane muka iso cinema din a rai na i promised to make things right with her in mun koma gida...........

*_🍒 S,Ibraheem🍒_*
Follow@Siyama ibrahim
#vote
#comment

Seguir leyendo

También te gustarán

442K 24.4K 166
Featured at Wattpad's Editor Picks list. Luna, an overworked Engineer, had an unfortunate end. Her spirit, feeling wronged, fights Death for a second...
1.4K 423 36
A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishada...
26.9K 1.4K 29
LABARI NE WANDA YAKE DAUKE DA BOYAYYAR SOYYYAH, BOYYAN HALI MARA KYAU,DA TSANTSAR BIYAYYA.
158K 9.9K 45
Elizabeth has been ruling her kingdom for 3 years now. She's gone through countless advisors in those 3 years. When she's finally ready to give up on...