🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 45-46

568 48 0
By SiyamaIbrahim

*🅱RILLIANT WRITERS ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers}_

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈 

_Kafatanin wannan shafi naku ne *Soyayya mai garɗi fans group* da *Brilliant Writers Association group* na san ya maku kaɗan amma ku yanyana shafin duk kalma ɗaya ku dauka na baku kyauta Allah ya bar zumunci yadda kuke nuna min so da ƙauna da adduo'in da kuke min ko na wa na jini ne sai haka_

4⃣5⃣➖4⃣6⃣

"Uban wa ya baki izinin zama a kujerar offishi na bayan kin rasa wannan damar kimanin mintuna arba'in da shida da suka wuce"a tsawace na karasa maganar not minding presence din Abdulrahman a wurin..

  Wani kallon ikon Allah ya min nima na mayar mai da martanin kallon da ya min tare da dage glass din sama na cunno baki gaba kaɗan

"Ya aka yi ne kake kallo na kamar ka ga sabuwar mutum huh"??

Bai ce min komai ba instead sai ya ce wa dija ta zauna zata zauna kenan na kuma tsawatar mata
"Malama in kika yi gigin zama a kujerar nan ki yi kuka da kanki dan kiran ki nayi ba wai kizo ki zauna min ba yawwa"?

Ban basu damar yin magana ba na yi proceeding

"Mr Abdulsalaam dalilin kiran Ms Alhassaan cikin meeting din mu shine ina so ne in yi clearing mata misconception din da take da shi a kai na da kai kanka dan gani take ko wata abin muke yi bayan mu'amalar aikin mu da kai toh so nake ta gyara tunanin ta ta san cewa ni Aisha Murad na fi karfin yi wa kawata kwacen saurayi sai dai sai dai ni a yi min again bana ɓata lokaci na a kan abin da na san ko zan mutu in dawo ba zai taba zama mallaki na ba na fi karfi kwace sai dai in mutum ya kawo kan shi gare ni da niyar agaza mai akan duhun da yake ciki na takurar wata" kaiwa nan na bar su da tunanin zuci

"Khadijah abin da yasa na yi kiran ki ba komai bane illah so nake ki ganewa idanun ki na fo karfin tijara dan na so magana da fiance din ki shiyasa na kira ki kar ki ga kamar wani abin zamu ƙulla sirri zamu yi a da na so in yi maganar a gaban ki but yadda kika yi reacting sai ya saka ni chanza ra'ayi na dan ba tsoron ki nake ba haka zalika ba ki isa yi min shamaki da abin da nake da ikon yi ba ni da building ɗi na so now that you have seen it with your naked transparent eyes kinaiya tafiya Ms Alhassaan"..

Fuuu kamar zata tashi saman ita in ba dan ya tilasta mata zuwa bada hakuri ba da ban isaa in daga mata murya ba dan a ganin ta ai ta min komai a lokacin da nake cikin tashin hankali ta manta cewa ita wahalar da kanta ta ke yi ba son ta nake yi ba amma ni ban taba wahal da kai na akan ɗa namiji ba hasalima su ke wahala akan soyayya ta ba tare da na sani ba

  Har ta kai kofa zata fita ta ji nuryar shi yana mai dakatar da ita cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba saka ta juyowar yayi haka ta juyo fuskar nan ya daɗa cika fam kamar zai fashe

"Kin yi abin da na aike ki yi"?

"Hero kana fa gani da idon ka yadda ta ke nuna min mulki a offishin ta kawai dan ina aiki a karkashin ta ta manta cewa a matsayin team ta roke ni mu yi aikin amma har ta ke da bakin gasa min magana still hero kana tsammanin ni Khadijah Alhassaan zan buɗe baki na in bawa Aisha Murad haƙuri toh wallahi Allah bata isa ba sai dai ta cinye kan ta dan bakin cikin abin da na mata amma ni ba zata tozarta ni ba dan babu abin da ban sani ba game da ita da rayuwar ta komai a hannu na yake yanzu ta ce har zata dakatar da ni a aiki saboda na nuna kishin ka a fili bayan maza kusan uku ta hana zaman lafiya biyu na nan na faman azabtar da matayen su saboda ita dan ta ki amsar soyayyar su wa ya sani halan kai ta hango take kokarin kwace min kai sai ta fake da cewa aiki aiki tunda ta zama injin aiki bata da hutu in ba wata manufa ce da ita ba ya zata dau zafi akan wannan ƴar ƙanƙanuwar maganar... ban bari ta gama maganar na dakatar da ita

"Khadijah ya isa haka ban kira ki nan dan ki cigaba da duldule min rashin mutunci da kika min a jiya ba nima dakatar da ni ɗin ta yi
"Oh excuse me Aisha da ban san ki bane da ban san ire iren tricks din da kike amfani da su bane wurin capturing attention din maza ba ina lure da ke tunda kika sauke idanun ki akan hero kike mai shigishigi har sai da kika samu yayi signing agreement da ke still bai maki ba kin cigaba da amfani da tricks din ki kina son jan ra'ayin shi zuwa gare ki in ba dan kina da wata manufa ba ya zaki rinka kiran shi every now and then wai aiki shi da ya yi signing da ke ai shi ya kamata ya na kiran ki time to time ba ke ba kina mace kina faman kiran namiji ina saukar Alqur'anin da kike takamar kina da shi?ina hadisai da kike iyayin kina da haddar su ina hadisin da kullum kike sanar da ni in ina nuna soyayya ta a fili a kan hero: _Alhaya'u minaal iman_ right ko ba shi bane kunya tana daga cikin imani ko ba haka bane? amma ke ina naki kunyar kin kama kina keɓewa da namijin da ba muharram din ki ba wai aiki ko?ashe dai kanki kike wa sharan hanya amma kike bi ta kasar gida yanzu kenan wa ya san ko anjima tallar kanki zaki yi tunda kin yi kokarin raba ni da shi kin kasa banz..... Ai tuni ban san lokacin da na daka tsale na fado gaban ta ba na yanke mata wata  irin rikidaɗiyar mari wanda sai da ya sanya yatsu na biyar bayyanuwa a kyakyawar fuskarta kafin in nuna ta da yatsa

"Kin yi kadan wallahi kin yi kadan ki taka ni yadda kike so kina iya yi min cin zarafi ta yadda kike so in kyale ki amma ba zan taɓa yarda da kazafi ba kazafin ma na tallar kai na a wulaƙance no not at all ba'a hallice ki ba for making this statement sai kin amsa dalili ki kuma bada shaidun kama ni da kika yi ina tallar kaina wa maza"kasa cigaba na yi da maganar dan wata irin hawayen baƙin cikin kazafin da ta min ga tozarci da wulakancin da ta min a gaban shi komawa na yi na zauna ina kokarin danne hawayen dan kar su zubo domin kuwa zubowar su daidai yake da lowering self esteem di na a gabn su dan daga ita har sho din laggo na zasu gani su cigaba da min abu son ransu dan as at then su biyun nake blaming for my misery a rayuwa na dan ita ta min rashin mutunci shi kuma ya bani laifi gashi kuma yanzu a gaban shi ta gama min tatass amma kanzil bai ce da ita ba hakan ya min suya a rai na sosai

  Ban akara ba na ji ya ce da ita

"In kin gama rashin kunyar ki da fitsarar sai ki bamu wuri coz in manya na magana yara bada wuri suke yi"!!  Komai bai sake cewa ba har dai ta gama yi mai kallon mamakon shi da ya kamata ta fita riƙe da kuncin ta tana kudirin sai ta fa karashen feleƙe na

   Juyowa yayi yana kallo na ganin hawayen da suka ci karfi na suka rinka tsere a tsakankanin ido na da kunci na sai yayi gyaran murya

"Amma kin san ke din shirmamiya ce tunda muke haduwa ban taba ganin kin yi abu da full confidence ba sai an sami mishkila why are you too weak?? Huhh??

Ban san me zan ce da shi ba dan haka kamar daɗa tunzira ni yake yi hawaye kuwa suka ce salamu alaikum da wa suka hadu sai ɓulɓulowa suke yi wasu na korar wasu

Kusan mintuna goma muna zaune a haka bai ce min yi shiru ba bai ce min yi hakuri ba ni kuma ban daina kukar ba kuma ban da niyar yin shirun dan duk zubar hawayen da nake yi daidai yake da fitar sa baƙin cikin da ke takura ni a rai na kenan dan ni Allah bai nufe ni da yin aure ba duk kawaye na sun yi ya zama aibu?ya zama abin da za'a na min gori da har ake kokarin min ƙazafin anjima ina iya yin tallar kaina wa abokin kasuwanci na wani irin tijara ne haka wai ni shikenan rayuwa ta gabas zafi kudu wuta yamma azaba arewa radadi? shin meye aibu na dan Allah ya kaddara min rashin aure da wuri har sai wani lolacin da ban yi tsammani ba? Dubawa na yi ta ko ina rayuwa na akwai taɓo a baya shekaru huɗu zuwa ɓiyar da suka wuce na nisan ci kaina da aminaina biyu dan in sami hutu in kuma gujewa gorin duniya kamar yadda aunty mufeedah ta min a ranar shagalin bikin su ina tunanin samin Khadijah shi ne alkhairi a gare ni dan ta nuna min so da kauna wanda hakan ya sa na buɗe mata sirri na, ashe akwai ranar duniya da za'a wayi gari Khadijah ta tona min sirri na a gaban wani bare?  akwai ranar duniya da zata goranta min rashin samin masoyi?akwai ranar da zata iya min kazafin zan tallata kaina? Toh wai ni ya zan yi da kaina i have been strong and enduring duk misfortunes da suke sami na a rayuwa amma still yau ɗaya an min kwancin zani a kasuwa saboda zato da zargin gaibu? 

A haka na share lokaci ina kuka ina maganar zuci har dai ya gaji ganin kukar ba mai tsayawa bane sai ya tashi tsaye yana gyara hannun rigar shi ya ce

"In ba zaki damu ba Ms Murad zan so ki zo mu fita daga nan dan daga dukkan alamu zaman ki a kan kujerar nan na daɗa boosting maki ego to the extent that ba kya iya yin shiru ki fidda damuwar ki dan dai ni ban san abin da aka maji har haka ba da kike zubar da hawaye har haka"!!

Wani irin kallon haushi na mai wato bai ma san abub da aka min ba bacin a gaban shi budurwar shi ta min ɗibar albarka akan shi zai wani ce bai san me aka min ba da nake kuka

Ga mamaki na sai naga ya nin murmushi ya dau min wayoyi na yayi gaba ya ce

"Freshen up and cone out ina jiran ki a mota na make sure you clear your face dan in kika fito a haka tsaf ma'aikatan ki zasu raina ki su fara gulmar boss lady na kuka har da jan hanci"maganar ta bani dariya amma sai na ƙi yi na harare shi a fakaice shi kuma yayi gaba abin shi

Bayan fitar shi babu dadewa na miƙe na shige toilet na wanke fuskata da ta baci da hawaye zama na yi na daɗa fente fuskata da kyau na fito tare da bada umarnin duk wanda ya zo nema na ya jira ni a ranar laifin Khadijah ya shafi kowa a office din fitowa na yi har harabar kamfanin inda motar shi take nan na nufa buɗe min motar yayi ta ciki na shiga ya gyara ya ja motar ban san inda ya dosa ba amma dai tafiya mai ɗan tsayi yayi kafin ya dakata a wani wuri mai kyau shi ba gida ba shi ba office din ma'aikata ba dan haka ya fito nima na fito ya min maraba yana gaba ina baya har muka shige ciki babu gini koh daya a cikin illah tekun da ke wurin sai ƴan shuke shuken itatuwa wasu sun girma wasu na hanyar girman kujerun zama ne a tsare a wurin karkashin wata rumfa kwata kwata rumfar ba zata wuce uku ba ko wacce dauke da kujeru hudu abin gwanin ban sha'awa dan haka na shagala da kallon wurin sai na ji ya ce

"Ms Murad ya dai kamar baki cikin existing living things m ya aka yi"?
Kunya sosai na ji ganin ya kama ni ina kallon kauyanci amma sai na masge na ce

"Babu kawai tunanin ruwan bala'ain da za ka je ka tarar ne in Khadijah ta san cewa ka fito ba tare da izinin ta ba"..

  Daga shi har ni din dariya maganar ta wa ta bamu wato Khadijah ce saurayin shi kuma budurwar wannan tunanin ya sa duka muka rinƙa rasgar dariya kafin daga bisani mu tsagaita cire madubin ido na nayi sai na ga annurin fuskar shi ta kau kusan seconds biyar ya ƙura min ido ban san me yake kallo ba amma kallon ya saka ni cikin tsarguwa har na kasa yin shiru na ce mai

"Mr Abdulsalaam ya dai da kallon ko baka san ni ba ce ka dauko hala ka zata da Khadijah ka fito"na ida maganar ina wata dariyar amma me shi bai yi instead ma sai na ga ya turɓune fuska ya chanza direction din da ya ke zaune a da facing juna muke yi amma sai ya juya fuskar shi zuwa dayan gefen ua bani baya sai na ji wani iri tsammani na ko sunan Khadijah da nake ta kira da making jest of ya sa ranshi ya bacci dan haka na kira shi

"Mr Abdulsalaam me ya faru? "Shiru bai amsa min ba sai na ƙara shiga wani halin

"Mr Abdulsalaam wani abu na faɗa da bai maka daɗi ba"? Nan ma shiru bai amsa ba

"Ina ta magana kana min shiru ko dai sunan Khadijah da nake ta maimaitawa ne da tsokanar ta da nake yi ya sa ka ji haushi ka yi fushi da ni"?

A nan ya juyo completely yana kallo na same look da ya ba ni the other time irin shi umya bani a yanzu ma dan haka sai na kara birkicewa na fara tuntuɓar kaina da shiga sabgar da babu ruwa na

  Dan kanshi ya kawar da fuskar shi daga kallon da yake min ya share fuskar shi ban san me ya share ba

"Ms Murad why are you too simple"?

Da mamaki na kalle shi me kuma yake nufi da why am i too simple sai dai ban gane inda maganar tashi ta dosa ba

"Ms Murad me yasa ba ki da saurin fushi da daukar zafi ne huh"?

Rasa abun cewa na yi dan haka sai na ji hawaye na ƙoƙarin cika min idanuna

"There gashi nan ai i thought you were a woman of pride and loyalty na dauka kina da dakakiyar zuciya da karfin zuciya irin ta maza kamar yadda kike physically but i was wrong dazu kika kira ni akan zaki zo kina da magana da ni mun yi sallama kika kuma kira na akam ni in zo na amimce na zo amma kuma you couldn't say your words sai kika ɓige da yin faɗa da wata a gaba na ba tare da kin faɗi abin da kike son sanar da ni ba and still you wasted my time with your cry kin zauna kina ta kuka akan abin da bai kai ya kawo ba ina ga sau uku ina sanar da ke akan ki daina daukar maganar mutani dan baki ga komai ba in ko kika ce duk abin da aka maki zaki zauna kina kuka toh kafin ki haifi ƴaƴan ki zaki karar da hawayen ki"...

Yanayin maganar shi kan bani dariya wasu lokuta a da ban taɓa tunanin zai iya zama da ni har muyi wata doguwar magana da shi akan rayuwar mu apart from aikin mu ba but he turns out to be gentile and kind though he can be annoying at times saboda halin ban sani ba da yake nuna min

Share hawaye na na yi dan in na cigaba da sauraran maganar shi ina iya raba abin kunya dan kuwa kuka zan yi mai sosai wannan kuma abin kunya ne a gare ni

  "Hmm Mr Abdulsalaam mu bar wannan maganar kawai let's talk about abin da ya sa na neme ka"

"No ba za mu bar maganar ba Ms Murad because yin shiru da damuwa a ran ki ba komai zai haifar maki ba illah cutarwa ko ke a jin ki ita Khadijar abin zai dame ta ne?no dan she have said her words kuma as far as she is concern ta wuce wurin ke ta bari da ɓacin rai and if you don't pour it out zaki cutu believe me Ms Murad"

  Akwai ƙamshin gaskiya a cikin maganar shi dan haka na yi ta riƙe damuwar shi a zuciya ta ban sami sa'ida ba har sai da na yu sharing da aunty mama dan haka na ga ya kamata in fidda damuwa ta ai ba ni na yi kaina ba balle a ce kaddara ta ni na rubuta shi

"Am i wrong dan na ƙi samin abin da kowace ƴa mace ke burin samu a rayuwa? Am i wrong dan na kasance shugabar kamfanin M Motives amma ban da aure? laifi ne dan ban da mai tsaya min in wani ya min ƙazafin abin da ban yi ba kuma ban sani ba?laifi na ne dan wasu basu da zaman lafiya a gidajen su da matan su? ""

  Kasa karasawa na yi sai kuka sharr sharr shima kuma bai hana ni kukan ba har sai da na tsagaita dan kaina

"I never knew that of all people Khadijah will do this to me ban sanar da ita sirri na dan ta tozarta ni ba ban san me yasa bata yarda da ni ba kamar yadda ni na yarda da ita ba na dauka zata iya barin amanarta a hannu na kamar yadda ni nake tsammanin barin mata amanata ashe i was wrong i was only deceiving my self all friends are the same ba ka da kwanciyar hankali a lokacin da kakr tunanin ka saba da wannan ka sake jiki da shi a lokacin yake disappointing din ka why?whyyy? "Da kuka mai cin rai na gama maganar

Yanayin fuskar shi ne ya fara chanzawa sai kawai ya miƙe tsaye ya ce

"Because they thought you are a fool,because they think you don't know what they are doing behind your back, because they think you are as simple and reckless as a dumb"

Tsayawa yayi yana furzar da iska kafin ya cigaba

"They are all the same trust them and they shatter you  ba su da tausayin wani sai kan su suna wasa da tunanin ka a ruɗin su ko baka sane da abin da suke yi suna ganin kamar in sun ce maka ga baƙi ko da fari ne ka amince ka ce baki ne shikenan baka da wayo  they don't know that so many things are being ignored saboda wasu dalilan they don't that at all kawai what they know shine baka da wayo kuma kai wawa ne wanda bai san ciwon kan sa ba"tsit yayi daga haka ya zauna idanun nan sun yi ja sosai ni da ban san yana da zafin zuciya har haka ba sai na yi sakaka ina kallon shi kamar wani mutum ne a gaba na ina ganin tawa rayuwar abin rubutu ne gun wasu ashe akwai wanda ke da story to tell about his life kwatankwacin nawa labarin rayuwar toh ko dai shima akwai wanda ya taɓa betraying mai trust ne kamar yadda aka min?ban da mai amsa min sai shi dan haka na dan matso da kujera na kusa da shi kaɗan

"Mr Abdulsalaam kaima ka taɓa experiencing betrayal of trust ne kamar yadda na yi experiencing ne yanzu"? Bai amsa min ba sai ya ce

"Please say what you wanna tell me am tired already"

Sai juya fuskar shi yake yi kamar mai gudun haɗuwa da mata sai da na yi nazarin eh in faɗa ko a'ah kar in faɗa amma in ban faɗa mai ba yanzu yaushe zamu ƙara samin lokaci irin wannan mu yi maganar tunda gashi Khadijah ta fara gasa min mummunar maganganu akan shi ina ga nan gaba me zai faru in aka kuma ganin mu tare maybe ma a ce ni mistress din sa ce yin wannan tunanin sai na yi istigfari na nemi tsarin ganin wannan rana a rayuwata

"Ba wani abu bane illah son sanar da kai wani abu mai muhimmanci a rayuwar ka da ya kamata ka sani saboda ba zan iya cigaba da kallon ka cikin duhu ba bayan na ga hasken da zai haskaka maka duhun da kake ciki"na tsagaita ina jiran ganin facial expression din shi amma ko gezau bai yi ba wannan alama ce ta ranshi ya bushe sakamakon tunowa da yayi da wannan mutumin da yayi betraying trust din shi ganin bai yi reacting negatively ba sai na cigaba

  "A labarin ka da na ji ban gani ba amma na san it wasn't a good past da kyar ka yarda da mutum ɗaya daga baya har ka bashi yarda da amana sai dai wani abu guda da baka sani ba shine same mutumin da ka bawa yarda da aminci is that same person da ke maka yankan baya yake maka baƙin hali ta karkashin ƙasa kuma ba jiyau bace ni ganau ce shi yasa na ga ya dace in sanar da kai wannan abim saboda ka farka daga tunanin da kake yi na ganin kana da amintaccen amini kuma abokin shawara"dakatawa na yi yayin da nake kokarin fiddo wayata na shiga gun music na duba record na fiddo da maganar da muka yi da shi ta farko na danna shi kuma gyara zaman shi yayi ya natsu yana sauraron voice record din har ya kai karshe kafin in kunna mai second conversation record din nan ma natsuwa yayi ya saurara har ƙarshe daga haka sai na mayar da wayar jaka na na rufe na miƙa mai hannu na na ce ya bani ɗayar wayar da ke hannun shi sai ya min banza dan muna motar ya miƙa min dayar na mai shiru ban tambayi ɗayar ba da baga bai bani ba sai na yi shiri ina zaton koh maganar da ya ji ne ya saka shi shiga wani hali sai ya bani tausayi har na ƙura mai ido ina kallon shi shima ni yake kallon chan ya ce min

"Faɗi abin da ke ran ki Ms Murad"

Kamar wanda ya min sai kawai na fara magana har da shesheka

"Am feeling very bad ina jin tausayinka yana da ciwo a ce wanda ka yarda da shi ya zama mai bin dubduniyar ka yana son ganin you are no more it hurts a lot and am sorry i know it may sound strange ka ji wanda ka fi yarda da shi shi ke neman ganin ƙarshen ka am sorry da na so in bari ka ganne ma idon ka but na ga abin na daɗa cigaba i had no any other choice but to let you know"kaiwa nan na mika mai takardar da mj ya aiko min na fita dinner tare da shi karba yayi ya karanta ya kuma karantawa sai ya miƙa min yana min murmushin takaici ya ce

"I know about this already is that tge reason you were looking for me"??

A mamake na kalle shi ko dai bai g sunan da ke jikin papern bane ko dai bai gane muryar bane

"Mr Abdulsalaam did you understand what i have been saying? ka gane muryar wanda yayi maganar kuwa?ka ga sunan da ke rubuce a jikin takardar bane"?

Murmushin ƴan boko ya min dan shi ya daɗe da sanin wannan abin ni ce dai ya kasance nlmin sabon abu dan haka ya zauna yana kallo na

"Ms Murad am not new in the making komai da kika nuna min ina sane da su dan na daɗe da sanib hakan ke ce dai baki sani ba amma ni na sani kuma kowa gani yake kamar na yarda da shi na bashi amana na but that's not true all those things were fake dan haka har yanzu ina jan baka na na ƙin amincewa da kowa ciki har da ke dan kema ba abin in yarda da ke bane i have been betrayed several times dan haka it will be hard for me to trust anyone dan koh dija ban yarda da ita ba kenan dan ban yarda da ke ba kar ki ji wani iri"yanayin maganar nashi zai nuna maka ɗacin da yake ji a zuciyar sa abin da zafi dan haka ban ga laifin shi ba dan ya ce bai yarda da ni ba amma yana sane bai yi magana ba menene dalilin sa?oho

"Toh amma kana sane baka dau mataki ba me yasa ko ka san ba iyakar abin da ke faruwa ba kenan na sanar da kai"?? Saurin rufe baki na nayi dan na ga ina son sake layi ya gano hakan sai ya ce min

"Me kuma kike boye min da baki son sanar da ni huh Ms Murad"?

Rufe idanuna nayi gam ina jin kunya kaɗan kaɗan na buɗe idon na sauke su tarr a fuskar sa na yi saurin juyar da kai na gefe

  "Ina jin ki Ms Murad"?

Ohh ya rasulilahi na faɗa a rai na wannan mutumin akwai kididige

"Babu kawai dai so nake ka kara kiyayewa da mutanin da kake mu'amala da kai you never can tell when your enemy will manifest it real colour"

Murmusawa yayi kawai ya ce min

"Ms Murad kin cika tsoro shi yasa Khadijah ke raina kiki bar tsoro saboda enemies ɗin ki yanzu suka fara bayyanuwa in dai a kan profession din ki ne so i want you to feel free and more courageous the journey has just began Ms Murad""!!

Tashi yayi ya ce min ib tashi ya mayar da ni office dan lokaci na tafiya abu musu na miƙe na bishi a baya fita muka yi daga wurin ina ta so in tambaye shi ina ne nan din amma ban son ya ga zalamata na son wurin sai na yi shiru kawai  har ya bude min kofar motar na shige ya ja muka bar wurin

_5:15pm_

A bakin gate din companyn ya mana ya bude kofar shi ya fito nima ya zagayo ya bude min kofar nawa gafen na fito ina kokarin rufe kofar amma bai bari na rufe ba sai ya ce min

"Don't worry i respect women a lot dan haka kar ki damu" yayi maganar yana min murmushi nima sai na mayar mai da murmushin na matsa ya rufe ƙofar motar madaɗin ya koma motar shi ya tafi sai naga yayi gaba na ce

"Mr Abdulsalaam ya dai i thought tafiya zaka yi"?

Sai ya tsaya ya ce min
"No am not going ms Murad i want to see you to your office kafin in tafi koh zunubi ne"??

Ikon Assamadu so yake ya saka ni a bakin duniya wai?ga matsalolin da suka kunno min kai ga shi shi kuma yana son kara min wani shi namiji ne ba za'a ga laifin sa ba ni kuma fah ai ni za'a zaga a duniya dan haka na yi kokarin hana shi rakiyar amma inaa shi bai san wannan ba haka ya dage har sai da ya raka ni cikin office ɗi na ya kuma zauna yana kallo na

"Aren't you going Mr Abdulsalaam"? Sai a sannan ya tuna ya tashi ya fita yana min goodbye har da ɗaga hannu abin banbarakwai ya min sai nima na ɗaga mai hannun thinking that's all amma sai me ya dawo da baya yana ce min

"Take care goodbye"uhum kawai na ce na saukar da kai na ƙasa ina duba wasu zanen da aka dawo da su daga wun gyara kusan mintuna biyar da tafiyar shi amma na kasa mayar da hankali na in duba abin da ke gaba na sai tunanin abubuwan da suka gudana ɗazu nake ta faman yi wasu in yi murmushi wasu su bani tausayi especially jin wai yana ankare da abubuwan da mj ke mai amma ya kyale yayi shiru wani irin mutum ne shi a wannan halin na ji bugawar agogon office din alamun 6pm dafe goshi na na yi ni da na yi alƙawarin presenting painting din washegari wa board amma ni ce koh kallon gyaran ban yi ba na ƙura mai ido ina wasu tunane tunanen chan i just have to go dan dare na yi haka na tattara kayana na haɗa da corrections din na kwashe na rufe kofar office din na fito a mota na na saka su a baya na shige gaba ina tuƙi ina shirme sau biyu ina kaucewa mota da kyar na koma gida ban ga kowa a falon ba dan haka bayi na wuce na yi wanka na na haɗa da alwala na fito na tada sallah yau sai gani cikin adduo'i na har da saka Abdulrahman ban san ta ina tunanin shi ya faɗo min ba amma ni dai na san kamar wajibi ne so ma dan uwan ka abin da kake son ma kanka dan haka sai na dage ina zuba mai adduo'i kamar wani mahaifi na bayan na shafa na fito sanye da pyjamas da flat slippers na sauko wun cin abinci dan na san dai sun daɗe da gama dinner din su sai na ce kar a kawon abincin a bari zan sauko in ci duk samma kal dan zaman tunanin shi na rinƙa yi ni dai dan tausayi yana bani tausayi ko da ya ce min bai yarda da ni ba abin bai min zafi ba haka dai na lalace ina tunanin Abdulrahman tare da tausaya wa rayuwar shi sai 10 na wuce daki na sai da na yi kokuewa da tunane tunane barkatai da suka ishe ni kafin in karasa aiki na in kwanta wuraren 12 midnight sai na ga kira na tsorata amma sai na dauka dan ban dade da kwanciya ba sai kiran ya shigo

Da farko shiru duk muka yi kafin daga baya yayi magana

"Hey Ms Murad baki yi bacci ba me kika tsaya yi ne har wannan lokacin"? Shiru na ɗan yi lafin in ce

"Aiki ne ya tsayar da ni Mr Abdulsalaam"

"Hmmm i see boss lady"
  Gabadayan mu dariya muka yi amma nawa dariyar ta fi nashi sauti dan kira na da yayi da boss lady abin sai ya min a baibai dan bai saba kira na da boss lady ba

"Mr Abdulsalaam why are you making fun of me huh"?

Bai amsa ba sai kawai ya ce min good night take care ɗif ya kashe wayar na sai na ajiye wayar kawai wondering me ke faruwa da mu ne yau babu amsa sai na kwanta abi na sound sleep na yi ranar har sai 5:15am n tashi kasancewar ina da presentation sai na yi saurin shiryawa na fita ko breakfast ban yi ba na tafi a chan na ga har an gara taruwa a conference room ɗin dan haka na yi saurin duba office ɗi na na ga wasu papers alamun ya iso kenan fitowa na yi na gan shi tsaye tare da wani board members din suna magana gani na sai ya bar mutumin ya fara takowa gare ni a daidai lokacin ne kuma na amshi takardar da aka bar min wai shory note budewa na yi kai tsaye nit minding what i will see in the paper na karanta sau biyu shi din da isowar shi kenan shima ya karɓa ya karanta koh kafin ya sani na fara hawaye ina ganin haka na fara kokarin barin wurin amma sai na ji a riƙe min hannu ban kuma sanin inda kai na yake ba........,,,,,,,,

_Hmmm readers me kuke hangowa zai faru a shafi na gaba base on abubuwan da suka faru a wannan chapter din na barku da brainstorming din amsar_

~Happy Monday in this beautiful new month may Allah Subhanahu wata'ala shower us with the blessings in this special month of muharram with much love from me siyama ibraheem to you all lovelies~

*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama Ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

88.6K 785 12
အသက်ရွယ်ကန့်သက်ချက်တွေ လွန်လွန်ကြူးကြူးပါဝင်လို့ ကိုယ့်ဟာကိုယ် ဆင်ခြင်ဖတ်ပါ။
431K 18.1K 123
SYPNOSIS Reading Purifying Love made Rachelle D'magiba feel very insulted. The ending that the author had written didn't go well with her expectation...
1.4M 96.8K 24
#Book-2 in Lost Royalty series ( CAN BE READ STANDALONE ) Ekaksh Singh Ranawat The callous heartless , sole heir of Ranawat empire, which is spread...
1.9M 97.2K 38
Presenting the story of ISHIKA MEHRA Whose innocence made the king bow down to her AND ABHIRAJ SINGH RATHORE Whose presence is enough to make the per...