๐Ÿ’๐Ÿ’SOYAYYA MAI GARฦŠI๐Ÿ’๐Ÿ’

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 27-28
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 29-30

550 44 0
By SiyamaIbrahim

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

2⃣9⃣➖3⃣0⃣

  _BEGINNING OF THE LOVE STORY_

11:50Am
A daidai lokacin da aka taru a gidan su salma kenan an baza nema na wai na bace jin wannan labari sai da falmata ta sume sama da sau uku dan duk blame ɗin akan ta ta ɗora koh ta kanta yaya kabeer bai bi ba yana chan yana ta nemana dan har lokacin bai gama fita daga raɗaɗin abin da ya faru jiya ba yaya umar kuwa Allah ya wadaran halin ta yayi ya ja hankalin salma dan kar ma ta ɗaga hankalin ta akan maganar falmata ummi da tashin ta kenan daga bacci ta karanta papern da na ajiye mata ta share kwalla ganin rubutun ciki kamar haka

_"Baby sis na san zuwa yanzu kin farka daga baccin da kike yina san kina karanta saƙon nan well ba komai zan faɗa miki ba dama so nake ki kama kan ki a matsayin ki na ƴa mace naji wai jiya hasina ta tona abin da kike ta son yaya Ibrahim ya sani i don't know how you reacted a jiyan but ina gargaɗin ki da ki kama ajin ki ki koyawa yaya Ibrahim son ki kafin ki bari ya gane mutuwar son da kike mai ki riƙe girman ki kin san ke babbar yarinya ce yanzu falmata is far away from yaya Ibrahim zai kasance cikin damuwa da ɗimuwa a matsayi na na ƴar uwar ki shawara da taimakon da zan iya baki shine ki taya yaya Ibrahim jinyar rashin da yayi na masoyiyar sa a lokacin ne kuma zaki dasa mai kaunar ki amma kar ki kuskura ki bari ya gane son da kike mai yayi yawa saboda ki a nan gaba kar ya sami laggon rainaki ko wasa da feelings din ki a nan gaba ni na koma Egypt kuma ba zan dawo ba har sai na kammala karatu na ki ja jikin ki da gidan su hasina ba zan hana ki mu'amala da ita ba amma ki san me zaki na fada mata kin dai ji kuma kin gani da idanun ki irin yadda aka yi mana a wun kamun yaya Aqeeb da yadda aka tozarta mu saboda ki iya takun ki kar ki kuskura ki ƙara zuwa shagalin bikin nan har sai komai ya lafa ki tsaya tare da yaya Ibrahim and be with him i love you baby sis take care of your self darling"_

Ta karanta papern ya fi a ƙirga tana ƙara bada kanta assurance ɗin cewa she can do it

  Yaya umar da ke kokarin reaching family demr din su dr hakeem ya yi nasarar samin shi ya mai kirar gaggawa akan ya yi saurin zuwa dan ko yaya naka ya lalace ai naka naka ne da haka dr ya ce su tsimmaye shi nanda mintuna kaɗan komawa ciki ya yi ya tambaya koh ta farfado  aka ce mai eh amma ta kwanta tun ɗazu bata tashi ba shiru yayi ya tambayi inda salma ta shige dan bayan ya ja ta suna gaba da fita daga mu aka danna mai kira haka ya neme ta ya rasa ya koma gidan shi ɗaya sai daga baya ta dawo itama ta karanta saƙon da na bari mata akan ta kula da falmata tare da kwantarwa yayan ta hankali akan ya yarda da ƙaddara itama ta gafarce ni saboda ba zan sami damar attending bikin ta ba but in na dawo zan zo gidan ta

Daga baya ne yaya Ibrahim da salma suka sanar da mutani cewa ai na koma makaranta ne still yaya Aqeeb bai daddara ba jin na koma makaranta shi so yayi ranar auren shi ya yi committing scene da zai saka dan dole ma a haɗa auren shi da ni bayan an daura da aunty mufeedah sai dai ya makaro bai shiga taitayin shi ba har sai ranar da ya ga an ɗaura auren shi da aunty mufeedah kuma taron ya ƙare ranar kuka ya ci sosai har aka shigo da amaryar sashen iyayen sa amma bai sani ba an kai ta gidan ta da ke cikin Apo gida mai kyau da tsarin kallo tun ana jirar zuwar ango har ɗaya bayan ɗaya aka watse bai zo ba hakan ya daɗa tunzira amarya ta daɗa daura ɗamarar yaƙi da ni dan ta san ni ce silar hana shi zuwa gidan ta kira lambobin shi amma shiru bai je ba tana kuka tana tuge kwaliyar da aka mata tsanata na daɗa shigar ta sosai bai dawo gida ba sai biyu saura na dare a lokacin da ta gama ciki fam yana shogowa falon ta fara zazzage mai kwandon bala'i in ban da kallon ta ba abin da yake yi dan a ranar bai yi gigin shan giyar ba ganin ya rasa ni rasawa ta har abada tana kaiwa ƙarshen aya ya wuce ta ya haura sama wani ɗaki daban ya shige ya ƙulle kan shi maganar duniyar nan ta yi kukan ta yi masifa ta yi karshe rokon sa ta koma yi dan ba ta shirya rasa shi ba a nan ta yi bacci shikuma zaman kurma yayi dan kwakwalwar shi ya dai na aiki haka suka karasa daren cikin wani hali washegari da ya tashi ya shirya cikin suit din sa ya fito ya same ta kwance a bakin ƙofar ya kalle ta dan tausayi ta bashi sai dai ai shima abin a tausaya mai ne masoyiyar sa ya rasa fah daka haka ya tsalake ta ya wuce zuwa office abin shi ko da ta tashi ta ga baya nan kukan ta ɗora akan wanda tayi jiya karshe ta shige ta gyara mai ɗaki ta yi nata dakin haka rayuwar su ya cigaba babu walwala babu magana mai daɗi kuma ko daidai da rana ɗaya bai taba kuskuren shiga ɗakin ta ba koh ta shigo nashi ɗakin to barin mata ɗakin yake yi shi kuka ita kuka duk sun rame..

Bikin salma da yaya umar saura wata ɗaya yayin da na yaya kabeer da falmata saura watannin shida a wadannan lokutan abubuwa sun gudana kamar kula da falmata da ake yi gudun kar ta rasa rayuwarta dan bayan komai ya lafa aka sanar da iyayen yaya kabeer da su mama abin da ya faru har yasa na bar ƙasar na koma takaici da haushi kam sun ji shi musamman umma dan gani take an cutar da ni ban cancanci haka ba shikenan dan ban da uwa sai a rinƙa kuntata min yaya kabeer bai bin ta kanta yayan ta umar gaisuwar ma sama sama yake amsa mata gashi ya hana salma kula ta amma ita bazata iya ba duk abin da tayi bai sa ta ji ta tsaneta ba dan ta san ba yin kanta bane baba ya bata laifi sosai dan har horo ya mata na hana ta komawa makaranta wai bata da amfani sai da yaya umar ya mai magana akan ya barta kafin ya yarda suka koma tare da salma rashin kulata da ƴan gidan keyi ya daɗa haddasa mata ciwon zuciyar da take fama da shi daga nan ne dr hakeem ya sanar da su in son kashe ta suke yi toh bismilah tun daga lokacin ne aka ɗan sarara da halin ko ohon da ake mata yaya kabeer ma ya fara shiga dubata da jiki wataran har ɗan tsayawa yake yi da ita kafin ya tafi ita a hakan ma ya mata koh da zagin ta zai na yi a wani ɓangare kuma in ta tuno ni sai ta yi kuka dan tun da abin ya faru bamuyi communicating da juna ba but ta san kowa da kaddarar sa matar mutum kuma ƙabarin sa

Yaya Ibrahim tun yana sharewa da batsewa akan kular da ummi ke ba shi yana mata tsawa da korar ta wataran ma har hantarar ta yake yi akan tana ƴar ƙarama da ita amma ta san wani abu wai shi so har dai ya daina ganin ita ɗin itace nashi dan bata guje shi ba tun tana yarinya take son shi ba ta sanar da shi ba ta riƙe sirrin ta har ta iya controlling kanta a lokutan da yake kula falmata kenan she doesn't deserve all these hatred dan ga wacce yake mutuwar so ta ƙi shi ashe wani daban take muradi har ta ke son salwantar da kanta akan shi ga wacce take kaunar shi haka yake dama naka baya taɓa gudun ka duk lalacewar ka ya kuma duba irin hallarcin da mahaifin ta da yar ta suka mai bai kamata ya saka masu da haka ba tun daga nan ya fara saukowa yana sauraron ummi wata rana har fita outing yayi da ita inda ya yi confessing mata soyayyar da yake mata har da alƙawarin zama da ita har ƙatshen rayuwar shi ma'ana auren ta zai yi ranar ummi bata bar ni na huta ba dan murna da farinciki na taya ƴar uwa ta murna dan ita kadai ce gareni wacce zamu iya sharing damuwar mu da farincikin mu tare hasina kuwa ta kasa boye murnar ta har sai da ta je ta sanar da falmata cewa ai yaya Ibrahim auren ummi zai yi nan ba da dadewa ba a lokacin ta ke ƙara tuno da rashin adalcin da ta yiwa ahalin mu

Akan maganar motar da yaya kabeer ya bani kyauta kuwa wanda yaya Ibrahim ya tambaye ni yadda za'a yi da shi nace ya bar min shi kawai ni nasan me zan yi da shi

Bikin falmata ma a bakin salma nake ji dan ita nauyi na take ji duk yadda na so ta share maganar abin ya ci tura nikuma sai na bar ta ina jiran zuwar ranar da zata sake da ni a karo na biyu

During those moments Khadijah happens to be the only close friend of mine ita ce ke kwantar min da hankali tana iya kokarin ta dan ta ga na sake jiki na though akwai lokuta da dama da nakan zauna tunanin kamar na yi wawta barin masoyi na ya kufce min amma in na tuna da ƙaddarar bawa da kuma maganar "matar mutum ƙabarin sa" sai in ji sanyi killa ma yaya kabeer ba alkhairi bane a gare ni adduo'i na rike da kyar da dambe da zuciyata na samu na tunɓuƙe yaya kabeer a zuciya ta da kwakwalwata na yi ƙokarin dasa ƙaunar aminiyata falmata a zuciyata wacce kaunar har ta fi ta da bikun salma ya gabato a inda take sanar da ni wai anjima zata turo min pre wedding pictures din da suka yi ita da yaya umar abin dariya ya bani ustaz yaya umar da pre wedding pics sai ta ce min ai ita ba zata iya da ustazancin nan nashi ba sai da ta juye mai kafin ya amince haka kawai abin lokaci guda ya ce ba zai yi ba shi ustaz dariya sosai ta bani irin wacce na daɗe ban yi irin ta ba ai kuwa muna gama video call din ta turo min hotunan kala kala wani dariya yake bani ganin kamar salmar ce ke yin style din wani kuma kamar bai da niyar haɗa jikin shi da ita wasu sun yi kyau sosai tun ma wadanda suka saka kaya kusan iri ɗaya wato blue colours shi ya saka da babbar riga ita kuma bata saka gyale ba suna tsaye murmushin sa ya fi wadda ta yi da na tambaye ta dalili sai ta ce min wai ai raina mata wayo yayi yace ta kalli mai hoton tana juyawa ya mai signal da ya ɗauka shi yasa murmushin sa ya fi nata abin dariya..

Haka dai duk shagulgulan bikin salma take turo min da hotunan ina gani tare da videos din bikin it juat feel like ina wurin abin ke faruwa jefa jefa na kan hango falmata a wurin bikin duk yadda na so mu yi magana ƙin yi ta yi still ina bata chance akan in na dawo dole sai ta min magana mun shirya dan na gaji da wannan rugujajiyar ƙawancen tamu..

An yi biki lafiya ango da amarya sun tare a gidan su da baba ya gina wa yaya umar ɗin a cikin anguwar manya wato maitama cikin Abuja cikin rantsatsen gidan su mai hawan bene bayan an kai ta ne aka sake sabon shirin zuwa dinner sai 12 na dare suka koma gida an yi siyan baki akan naira dubu hamsin ƙawayen uku ne dama daga falmata sai safiya wacce muka yi makaranta tare tun muna yara sai wata hafsat da ke ajin su a Turkish sun tafi sun bar amarya da ango sai fatan zaman lafiya..

*******************

A yau ne muke murnar kammala karatun mu ni da Khadijah da sauran mazan ajin mu haɗa wata kwarya kwaryar party muka yi a wata garden da ke cikin eatery din babbar hotel din da ke birnin garin da mukai karatu duk mun yi kyau matan mun saka plain gowns masu tsantsi da daukar ido peach colour su kuma mazan sun haɗe cikin suit ɗin su maroon colour mun yi kyau sai ɗaukar ido muke yi chan muka baje muka nuna murnar mu muka ci abincin mu muka yi hotuna masu rawa na yi ni da Khadijah na zaune muka bar mazan na yi ita hira take yi da saurayin ta ni kuma ina kallon environment din hotel din kafin in sani sai na ji wata uban ƙara a firgice na juyo Khadijah ce wai saurayin ta yace shi zai kasance mutum na farko da zai mata welcome back surprise shine fah take wannan haukar  harara na danƙara mata na yi tsaki sai ta min dariya ta ce
"Mijin ki zai haukace wataran da irin wadannan kallo naki"

Halbin ta na yi da purse ɗi na muka saka dariya dan ni bana ma jin zan iya wata aba wai soyayya a halin yanzu maybe sai nan gaba kaɗan around 6 pm muka bar wurin ni kam washegarin ranar nake da nufin tafiya Khadijah kuma jibi ina shiga gida da nufin ƙara packaging kaya na na ji kirar Abbu wai gobe jirgin saudiya zan bi da mamaki na ce

"How Abbu"
Ya ce min eh aikin umra zan je yi na rasa ta ya zan fasalta murna ta shi kuma yayi hakan ne dan bikin falmata ya rage saura sati ɗaya kuma bai so da gama makaranta na in fara cin karo da abin da zai ɓata min rai..

Na sanar da Khadijah ta min murna tare da ce minan gama processing min komai na ce mata eh ai ta jirgin yawo ma zan tafi a daren muka sha hirar mu a nan ma ta kwana as soon as 6am na gama haɗa komai na tafi airport Khadijah ce ta min rakiya 7 muka tashi sai saudiya..

****************

Bikin falmata ya gabato ba wani shagulgula aka yi ba bayan kamu sai walima sai yinin biki dan kin yarda yayi akan a yi dinner salma ba daman yin shagali isashe dan ta fara nauyi kaɗan shi kuma mijin nata bai son ta yi wani dogon motsi da kyar ma ya amince da zuwan su bikin amma ta jirgi suka taho aikin da ta daɗe tana kwaɗayin yi ya hana wai ba yanzu ba sai ta haihu abu kamar wasa sai ga salma da ciki kuka ta saka mai da kyar ta amince akan zata haifi baby ɗaya sai ta fara aikin ta,gidan shi bai da nisa da family house din su a nan aka kaita komai da ke gidan tsari na ne tun lokacin muna tare hatta painting ɗin da na kawo mai lokacin da na dawo yana nan bai cire komai ba haƙuri ya zama dole wun falmata dan ta san ba zata taɓa samin attention din sa ba sai dai wata kaddarar bayan an watse a gidan amarya yaya kb ya shigo dakin ta ya gasa mata maganganu marasa daɗi

"Ni kike so ko? fine ga ni nan ki yi yadda kike so ki yi amma ki sani ni ba tsaran ki bane kuma  har abada bazan taɓa haɗa shimfiɗa da ke ba dan baki kai wannan matsayi ba ni da jiki na mallakin Aisha ne hankali na da tunani na duk akan aisha suke ba ke ba in kin shirya zama da ni bismilah"

Ranar ta yi kukan baƙin ciki har ta kasa hakura ta kira salma haƙuri kawai ta bata dan yaya umar na online lokacin so ba zata iya mata wata doguwar magana ba dan ƙin yarda yayi su kwana a gidan  su na Abuja suka yaɗa zango

  Haka suke zaman doya da manja babu daɗi ga yaya Aqeeb ma babu wani sassauci tsakanin shi da aunty mufeedah sai dai godiya babu wasu masu baje soyayya illah salma da yaya umar

Mun sauke farali lafiya kalau dan sai da na isa chan na haɗu da su Abbu ummi da yaya Ibrahim abin sai ya min daɗi mun gama mun dawo gida lafiya gabadayan mu bayan kamar kwanaki biyar da dawowar mu Abbu ke min albishir da  painting company da ya min akan duk lokacin da na shirya ina iya zuwa dubawa kafin in fara zuwa aiki rasa bakin godiya na yi sai kuka shabe shabe yaya Ibrahim ne ya fara teasing ɗi na wai raguwa mai saurin kuka suka saka min dariya shi da su ummi na turo baki ina cewa Abbu ya ja masu kunne

Washegarin ranar da muka dawo na shirya cikin riga da wando deep black ta canfanin H&M na daura doguwar riga buɗaɗiya mai botura na saka heels ɗina tare da rike bonia hand bag ɗina na ɗau car key dina wacce yaya kabeer ya bani kyauta dan tun jiya na sa aka wanke min na sauko na sami su abba a falon dama ni suke jira muka fito su mota ɗaya suka shiga nikuma da ummi motata muka shiga ni ke jan motar su a gaba mu a baya har muka iso apo hills inda companyn yake wata babbar company ce tun daga bakin gate ɗin ta zaka gane kamfanin zane zane ne dan yanayin tsarinta daga kai na nayi na ga sunan  mai tambarin " *M""MOTIVES PAINTING COMPANY LTD"*
  Sunan ya min ya burge ni daga haka muka shiga daga ciki ma'aikata gasu nan MashaAllah office ɗina muka wuce direct inda yake cike da hotuna na kala kala gefe kuma family enlargement ɗin mu ne na yi murna sosai ɗaya bayan ɗaya aka fara shigowa ana introduction sai next week zan yi resuming aiki sai 4pm muka koma gida na gama planning yadda zan yi visiting ɗin su falmata da salma zan fara ne da gidan falmata saboda ina so mu fahimci juna kafin in kai wa salma ziyara..

*********

Da sauri ta fito ta zo buɗe kofar dan tun ɗazu take jin ƙarar budewar gate ɗin gidan a tsammanin ta koh mai gidan ne bude ƙofar kenan ta hango motar da bata san ta ba sai ta karasa bude ƙofar gaba ɗaya gwalalo idanuwar ta ta yi tana kallo na ta kasa cewa komai ni dariya ma ta bani har na ɗan dara kafin in yi magana

"Mrs Kb can i come in kin bar ni a tsaye gashi na dauko rana"
Da sauri ta matsa min na shiga ciki sai ƙamshi palon ke yi dan dama chan falmata ba mai son jiki bane tana ƙokarin aiki zama na yi daga ɗaya daga cikin kujerun palon ta dau mimti uku a tsaye ta rasa ya zata juyo ganin hakan ya sa na tashi na matso na ce

"Koh dai ɓatar hanya na yi ne"
Shar sai ga hawaye tana girgiza kai

"Aisha am sorry am so sorry haƙƙin ki ya ƙi bari na har yanzu aure na sa babu duk ɗaya ne wallahi na san haƙƙin ki ne ke bibiyata ki yafe min" tana kuka sai nima ta bani tausayi dan ta dan rame sai haske fayau

Jan ta nayi muka zauna na fara share mata hawayen ta na ce

"Yanzu dai yunwa nake ji ina abinci"
Da mamaki ta ɗago ta kalle ni irin ni abin ma kamar bai dame ni ba daga mata kai na yi nace am hungry dear sauri ta yi ta tashi ta shige kicin minti kaɗan ta dawo da tray shake da abinci ta ajiye min zata tashi na ce

"Hey gun ki fa nazo ya kike ƙokarin tashi" da haka ta koma ta zauna tun tana ɗari ɗari da ni har ta sake jiki na mata alkawarin dawowa bayan kwana biyu har bakin mota ta raka ni na so in tafi gidan salma amma dare yayi ga hadari haka na kama hanya tun ina kan hanya ruwa ya ɓarke ni kuma na dage sai na isa gida kafin ruwan yayi tsanani tun daga nesa nale jin horn amma saboda irin speed ɗin da nake yi ban ma iya dakatawa ba har sai da na ji motata ta buga wata motar sannan na dakata tun kafin in fito dan duba me na aikata mai motar da na bugen ya fito ya fara bala'i

"WTF ya zaki rinka tuƙi idanun ki a rufe kuma kina jin yadda nake ta miki horn kin zo kina driving recklessly kamar titin gidan ku what nonsense in kun bugu sai ku hau yin rashin hankali a ko ina mtsww"

Tsaki yayi ya shige motar shi ya wuce ni kamar wata mutum mutumi dan ban sauke mai tawa masifar ba kuma ya tafi amma na cutu gaskiya nima tsakin na yi na shige motata na cigaba da tafiyata sai dai na rage speed ɗin................

*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

187K 9K 51
My name is Alex Cruz, I'm a omega, so I'm just a punching bag to my pack. But Emma, Queen of werewolves Sam, queen of dragons Winter, queen of vampi...
77.3K 4.4K 23
โ๐™ˆ๐™–๐™œ๐™ž๐™˜๐™–๐™ก ๐™ž๐™˜๐™š ๐™˜๐™ง๐™š๐™–๐™ข ๐™ฉ๐™๐™–๐™ฉ ๐™™๐™š๐™จ๐™˜๐™ง๐™ž๐™—๐™š๐™จ ๐™ฎ๐™ค๐™ช๐™ง ๐™จ๐™ค๐™ช๐™ก๐™ข๐™–๐™ฉ๐™š? ๐™ž๐™ข๐™ฅ๐™ค๐™จ๐™จ๐™ž๐™—๐™ก๐™š.โž โ๐™”๐™ค๐™ช'๐™ก๐™ก ๐™ฃ๐™š๐™ซ๐™š๐™ง ๐™ ๐™ฃ๐™ค๐™ฌ ๐™ž๐™›...
659K 23.7K 200
[FIXED/FAN TRANSLATION] A student who was preparing for the Civil Service examination for 4th year suddenly found himself in an unfamiliar body 3 yea...
443K 24.5K 166
Featured at Wattpad's Editor Picks list. Luna, an overworked Engineer, had an unfortunate end. Her spirit, feeling wronged, fights Death for a second...