🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

By SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining More

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 25-26
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 27-28

513 43 0
By SiyamaIbrahim

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
_(Pure Love, Revenge and bargaining)_

By
*Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

2⃣7⃣➖2⃣8⃣

"Barkan ku da zuwa taron aure na ni da masoyiyata sahibata wacce take tare da ni tun yarinta na wacce ta amince zata aure ni a mafarki na ohhh na manta aunty habiba(kanwar umma ce uwa ɗaya uba ɗaya a kasar jamis take aure shekaran ta 15 da aure amma Allah bai taɓa bata haihuwa ba) ban faɗa miki ba hmm kin san kuwa jiya na yi mafarkin mun yi aure ni da ita wai mun zo muku ziyara har kike ce mata ta zauna a hankali saboda cikin dake jikin ta har fah fushi na yi dan kin nuna son kai da yawa koh da na tashi sai naga ba ita bace wai mafarki naje yi yau kuma wai aka ce min za'a yi kamuuuuuuu" ya ɗan dakata daga nan ganin kowa kallon shi yake kamar wani sakarai sai ya daɗa hade fuska ya cigaba da maganar shi

"Kin cuce ni kin cuci amanar da na baki ta zuciya ta na so ki son da ban taɓa yiwa kaina ba duk wani mafarki da tunani na ke ce a cikin su rayuwar da na daɗe ina mafarkin shimfiɗa ta duk da kece koh daidai da rana ɗaya ban taɓa cire ki a zuciya ta ba duk saukar numfashi na kece amma kika rasa gane hakan kika kasa buɗe idanuwar ki ki gani har wai kika amince aka yaudare ni da sanin ki da saka hannun ki aka min yankan baya why why whyyyy""

Tsit hall ɗin ya dauka kowa da abin al'ajabin da ke yawo a zuciyar sa gefen amarya sun matukar firgita da jin waɗannan kalamai ace ango a ranar kwanakin bikin shi ya ƙi halara a wurin taro sannan ya shigo a bige yana maganganu marasa madafa da ma'ana kuma wai da wannan ake so a haɗa zuri'a na har abada inaa ba zai taɓa yiwuwa ba sai dai a fasa wannan aure dan suna ji suna gani ƴar su ta shiga irin wannan ahali kuma ta yu zaman din din din da mashayi dan haka ba zai saɓu ba..

Gefen iyayen ango da ƴan uwan shi kuwa abin kunya hakan ta kasance a gare su dan koh da a mafarki aka ce musu yaya Aqeeb zai kalli wani abu wai barasa za su musanta bare a ce har ya kai ga shan ta wannan abu ya zame musu abin kunya kunya babba kuwa dan duk kafafen yaɗa labarai na ɗaukar rahoto wannan abu da ban mamaki yake salma da ke digesting maganganun yayan nata ta kasa hakura ta yi saurin dumfaro shi da azama ta rike hannun shi

"Yaya me yasa me yasa a ranakun bikin ka ka nunawa duniya halin ka na ɓoye da bai kamata a gani ba why yaya i thought we were done with this issue why now baka tunanin ya aunty mufeedah zata ji a zuciyar ta ganin abin nan da ka ke displaying"??

Fisge hannun na shi yayi ya ce

"Allow me to pour out my mind she cheated she cheated kid sis" da karfi ya kai karshen maganar yana zub da hawaye zuwa lokacin amarya mufeedah ta fara fita a hayyacin ta dan tuntuni controlling kan ta take yi saboda son da take ma yaya Aqeeb ya ɗare wanda yake mata because ita ta nuna zakuwan ta akan ayi maganar auren su dan kar ya kufce mata ganin ta in aka yi auren komai zai lafa akan wannan ƙaddararen suna da yake kira mata kullum ranar Allah ta'ala ashe ruwan dafa kanta ta ɗebo wannan wace irin fitina ce gaskiya ba za ta iya ba in dai haka son da ya ke yiwa yarinyar nan ya kai toh ba zata iya zaman auren takura ba dan zai kasance kamar gangar jikin sa ta aura ba tare da ruhin shi ba saboda ruhin shi da nutsuwar sa na wun wancan yarinyar oh ya salam me yakamat ta yi kafin a sani kawai sai aka ji saukar wata ƙara tasss daga inda ya birkita ɗaukakin jama'an hall ɗin dan kuwa yaya Aqeeb ya amshi wannan zazzafar marin daga wun amaryar shi aunty mufeedah sai huci take tana zubar da hawaye ta daga yatsan ta tana nuna shi

"Aqeeb me ya rage in yi maka a duniyar nan da zai nuna maka cewa kaunar ka nake yi ba son ka ba me zan yi in janyo ra'ayin ka zuwa gare ni duk na wulaƙanta na hargitse na rasa hankali da tunani na duk saboda kai Aqeeb why are you torturing me why are you humiliating me da me ita waccan kucakar ta fini eyee? Kyau koh iya kwaliya,ilimi koh iya magana,dirin jiki koh akasin haka huh?? Answer me for crying out sake na gaji Aqeeb i can't i just can't saboda ko na aure ka mutuwata na aura dan kai ne *ajali* na a *ajalin so* da nake maka zai yi *ajalin ajali* *na* saboda haka na barka na barka ka ji daɗin duniyar ka kai da yarinyar da kake neman yin *ajalin* kanka a kai yarinyar da bata san kana yi wacce take kaunar ɗan uwan ka shima ya ke kaunar ta yarinyar da koh a yanzu aka ce ta zaɓe ka ba zata taɓa zaben naka ba wa zai auri matsala mashayi babu sai ni son da nake maka ya sa har laifin iyaye na na gani amma kai baka damu da ni ba it's ok na fahimce ka ni na nace maka shi yasa nake kwasar wulaƙanci amma na hakura da kai na yafe gomma in mutu da ƙaunar ka a zuciyata da in aure ka in yi rayuwar ƙunci da takaici dan har abada bazaka taɓa zare soyayyar yarinyar nan daga zuciyar ka ba"..

Yaya kabeer da shigowar shi hall ɗin kenan dan an kira shi a waya an sanar da shi ga ango nan ya shigo a buge ya tarar da abin da ke faruwa tun daga farkon kalaman ta har ƙarshe duk ya ji komai ni da ke ƙokarin zuwa wun salma in tambaye ta hala falmata yaya Aqeeb ke so ya yi shiru bai faɗa har ya janyowa kanshi wannan abin maganar da zuwa na wurin ta na saka hannu kenan da zumar jan ta gefe sai karaf a kunne na na ji muryar yaya Aqeeb yana kira na

"Aisha kar ki kuma kuɓce min for the second time mutuwa zan yi in kika tafi"?..

Abin da salma ke gudu kenan gashi ya faru wannan abu ya daɗa tunzira aunty mufeedah har ta kasa hakuri ta bangaje shi ta isa wun mc ta fisge mic ɗin ta fara sauke nauyin zuciyar ta

"She is the Aisha that stole my happiness ita ce yarinyar da Aqeeb ya ke son halaka kan shi saboda muguwar son da yake mata itace yarinyar da ta dasa min mummunar lamba a kundin rayuwata Aisha Murad koh toh Aqeeb nan na bariki shi halak malak ki je ki mai abin da ba zan iya yi mai ba ga ta nan ku shirya ta a cigaba da shagalin auren da ita"kaiwa nan ta cila mic ɗin ta yi hanyar waje da azama ya karasa wurin ta ya riko hannun ta ta fisge tare da kara sauke mai wani marin dan tana takaici da jin zafin abin da ya mata wato ta nuna ɓacin ran ta amma bai damu da bata hakuri ba instead ni ya juya yana tonawa sirrin zuciyar sa lallai ta tafka asara da ta kasa banbance mafarki da ainihin rayuwa

"Feedah feedah pls don't go ki min rai wallahi ba yin kai na bane kin gani kalle ni idanuwana son ki ne a ciki ba na wata ba believe me"..

Ya fara dawowa hayyacin sa already wuta ne ya dauke min na wucin gadi me zan ji me zan gani yaya Aqeeb kanin yaya kabeer di na ke so na dama yana so na ne koh dai wata Aishar ce ba ni ba noo that's not possible ba ni bace i was shock har kasa motsawa na yi yaya kabeer karasa shigowa yayi ya juyo yaya Aqeeb ya ƙura mai ido ya ce

"Aqeeb kalle ni kalli cikin idanuna ka ƙaryata min zancen da kunnuwa na suka ji pls"
Unfortunately yaya Aqeeb ba zai iya kallon cikin kwayar idanun yaya kabeer ba dan ba zai taba ƙaryata feelings ɗin shi akai na ba so sunkuyar da kai yayi ƙasa yana kuka

"Aqeeb talk to me ina jin ka"by then yaya kabeer ya fara losing patience din sa already da tensed voice ya kara tambayar shi karshe har daka mai tsawa yayi dagowa yayi shima ya daka mai tsawar

"Yes abin da kaji gaske ne Aisha Murad has been my dream my wife in my dream ita ce yarinyar da nake so tun ban san menene so ba a kanta na fara sanin garɗin so

Maruka yaya kabeer ya firgita nima haka da na dauka ɓatar hanya ce amma ashe da gaske ne ni ni Aisha yaya Aqeeb ke so anin mamaki da al'ajabi koh a wasa ban taɓa kawo hakan ba koh shi kanshi bai taɓa nuna min a zahiri ba toh how ta yaya wai ma duk ni ni daya nake da samari har uku ban san da zaman biyu ba sai ɗaya a xikin su abin da Abbu ya sanar da ni washegarin da na dawo daga Egypt ne ya fara min yawo

. "Aisha dama akan maganar yaron nan ne wato yahaya toh ban ɓoye mishi komai ba gameda neman auren ki kabeer ya yi da farko ya ji zafi har yake neman sanin dalili bayan ya san ya riga kabeer ɗin shigowa bai san cewa ina da masaniya akan sirrin shi da ya ɓoye min ba a matsayin shi na ɗan aiki na kuma ni uban gidan shi sirrin kuwa ba komai bane illah aure auren da yake yi kafin ya haɗu da ni duk auren da yayi matar bata wuce shekara ba a ga gawar ta ba koh ta mutu haka kawai koh ya mata duka sosai da zai yi ajalin ta daga wanda ya bani cikakiyar labarin shi ya sanar da ni cewa yara ƙanana yake aura duk wacce bata rasu kafin shekara ba toh sai ya mata dukan da zai yi ajalin ta tun ƴan garin ba sa ganewa suna bayar da auren ƴaƴan su har suka gane suka daina shi ɗin mutumin Nijer ne chan cikin wani yanki mai suna Tawa a cikin wata dajin kauye mai haɗari kuma ba komai yake yi da gawarwakin matan ba illah bayar da su ga abin bautar su saboda koh bai bayar ba lokaci na yi zasu amsa dan tarihin gidan su ya nuna an tsine musu tare da la'antar su duk abin da zasu yi ba zai taɓa yin ƙarko ba suna ji suna gani toh da aka kora shi a kauyen ganin yana nema ya zamo masu annoba shine ya bar garin ya dawo nan a kano ya fara sauka ya yi sa'ar samin mafaka har ya yi aure amma da yake abin na bin shi haka matar nan ta yi shekara ta rasu ganin haka sai ya bar garin kafin a gane shi toh shine muka haɗu da shi har ya zama ɗan aiki na wanda na fi aminta da shi dan yahaya na da hankali da sanin ya kamata amma da yake mutum tara ne bai cika goma ba shi irin nashi ƙaddarar kenan ko da ya min maganar ki babu jimawa na saka amin bincike akan shi na wahala kafin in san tarihin shi amma ko da na sani sai na mai shiru ban ce komai ba dan jira nake in ga ko zai bayyana da kanshi amma bai yi hakan ba ni kuma na yi ƙokarin rufe duk wata kafa da zai haɗa ku gudun kar ki sake jiki da shi yana ɗaya daga cilin dalilin da ya sa na amince da ki tafi karatu ƙasar Egypt da kabeer ya nuna yana son ki sai na amince dan in yi amfani da damar wurin sanar da yahaya cewa na aan sirrin shi bayan na gama bayyana mai komai akan shi da na sabi sai ya roki alfarmar in bar shi ya tafi wani wurin dan ko ya zauna a nan ɗin yana iya cutar da mu ba a san ran sa ba ban da zaɓi illah na barin sa ya tafi tare da bashi jari mai tsoƙa"...

Tuno da wannan doguwar bayani da Abbu ya min sai ya sa na rasa ta ina zan fara da wanne zan ji kenab duk wani mafarki da tsarin da na yiwa kaina akan rayuwa ta ya tafi kenan dan bana jin zan iya cigaba da zama inuwa ɗaya da yaya kabeer saboda kullum kallon wan yaya Aqeeb zan na mai mutumin da ya so ni ba tareda na sani ba ina kuka na saka kai na zan fita na ji muryar aunty mufeedah tana gaya min wata magana da ta girgiza ni

"Duk abin da ya same ki nan gaba kiyi kuka da kanki dan wallahi bilahilazim sai na ɗaiɗai ta ki dan matukar na auri Aqeeb bai daina maganar zuci akan ki ba na miki alƙawarin ganin ƙarshen ki kina bare ba ƴar gida ba korar maiduguri marar asali a dukiya na fi ki a kyau da komai na fi ki amma ƴar kankanuwa da ke kice har kin isa ki dasa kaunar ki akan abin da nake so toh kiji da kyau Aisha kika kuskura kika bari Aqeeb ya aure ni ba tare da bani zuciyar sa ba hmmm...

Bata kuma cewa komai ba dan dama duk baki ne bazata iya rabuwa da yaya Aqeeb ba ta fita waje ƙam na yi a wurin dan kuwa zuwa wannan lokacin na gama tsimme maganganun aunty mufeedah already na fara shiga tsakanin yaya kabeer da kanin shi yaya Aqeeb tun yanzu ga maganar aunty mufeedah idan har na cigaba da zama da shi me zan janyowa kaina ga gorin da ta gama yi min toh au gaskiya take faɗa nibɗin bare ce ba kowa ba amma jin daɗin zaman da nayi yasa nake son mantawa da hakan Alhamdulilah ta tunatar da ni bana jin zan iya cigaba da tsayawa a wurin kuka kawai nake jin yi dan ban da uwar da zata sanyaya min zuciya ta da kalamai masu daɗi anya ba zan hakura da yaya kabeer ba without second thought na ɗaga ƙafa na da niyar fita dan kai na ya fara juya min yaya kabeer ne ya yi kokarin tsayar da ni ganin yanayi na amma ina bana jin shi ina bada baya aka dasa hayaniya masu zagin amarya na yi masu goranta min na yi media kuwa sai nanata kalamr ganin baya na da aunty mufeedah ta yi suke ta yi sarai na ji su amma na fita yaya Ibrahim da bai daɗe da zuwa ba na ce mai ya kirawo ummi a waya ta fito mu tafi gida ya nemi sanin ba'asi amma ina kuka ya ci ƙarfi na ganin haka yayi saurin shiga ciki ya fara neman ummi a inda ya ga ana hayaniya da ita yayi ƙoƙarin jawo ta suka fito hasina da ke kuka tuntuni dan akwai magana a bakin ta amma ta rasa ya zata fara dan ita akwai hankali unlike ƙawarta ummi da bata tunanin abin da ya dace magana in ta zo mata faɗar ta take yi kai tsaye she is a straight foward person da hasina aka fito ina kuka na kalle ta nace

"pls hasina go back inside bana son jin wani magana"

Kukar take yi itama ta ce bazata koma ba magana take son yi da ni da mamki na ce wata magana ta ce min mu dai tadi gida ban kawo komai ba muka shige motar tare muka bar harabar hotel ɗin

Chan ciki kuwa taro ya wargaje falmata da salma barin wurin suka yi ganin iyayen amarya na neman ɓata rayukan mutani ga ango ya bi bayan amarya yaya kabeer aka bari kamae wani statue kwakwalwar shi ma ta kasa hasko mai mafita sai daga baya ya fito shima ya bi bayan motar mu ko da labari ya riski su umma kasa zama wu daya tayi tana ta kai kawo dama yaya Aqeeb na shaye shaye ne ko kuma yanzun ya fara ta yi kuja sosai jin irin cin zarafin da aka min kuma shi ya janyo min hankula duk sun tashi rai sun baci sai da aka dangana da yin family meeting da roko daga wun iyayen amarya akan abin da ta yi sa'anan aka amince za'a cigaba da shagulgulan bikin da sharaɗin zata yi withdrawing kalaman ta tare da ba ni hakuri..

********************

Zazzaune muke daga ni har su salma,falmata,ummi,hasin,yaya ibrahida uban gayyar dan hakan yin hasina ne bayan na ci kuja na na ƙoshi na ma gama yanke shawarar rabuwa da yaya kabeer koh ya shirya ko bai shirya ba ko Abbu zai yi fushi da ni ne kuwa sai dai a yi amma bazan iya zama da yaya kabeer ba dan matukar na amincewa auren shi lallai akwai yin yaƙi wataran ganin haka ya sa na yanke rabuwa da shi da toshe duk wata alaka ta da shi da ahalin shi ganin tun yanzu an fara goranta min sai dai soyayyar shi ta yi *ajali* na but na haƙura

""Na san dai ni yarinya ce ban gama yin hankalin da zan yi magana da ku har ku amince ba but ina so koh bai da amfani ku saurare ni ƙila ku tsinci wani abu a ciki"

Dukkan mu ita muke kallo da sauraro dan ni dai na fara shiga taitayi na wannan wata iriyar rana ce

"Am so sorry yaya falmata ba zan iya cigaba da cutar da ke ba dan ina ganin ki kina zaman kuka more than how i can count kullum ina ganin ki kina zama a dakin ki kina kuka kina maganganu ke kadai ina ganin ki da irin magungunan da kike sha every night kafin kiyi bacci jiya na ji wayar da kika yi da dr hakeem komai a kunne na yake na ji sau da yawa kina ciwo amma ba kyau faɗa sai dai kiyi shiru koh an tambaye ki sai koce babu komai alhalin akwai ni na san komai yaya falmata kuma yau kowa ma zai sani am tired""

Tsit aka yi yayin da falmata ta gama fita a hayyacin ta tana ma hasina magana da ido akan ta yi shuru kar ta faɗa mu da bamu gane kan maganar ta ba muka matsu mu ji inda ta nufa dama falmata na ciwo ne?

Ta cigaba kamar haka
"Yaya Aisha ki yafe min ba da wata manufa zan faɗi wannan maganar ba ba kuma abin da aunty mufeedah ta miki bane ya sa nake son faɗar maganar ba a'a saboda ku taimaki yaya falmata ne dan wallahi she is about losing her mind"ta kuma yin shiru toh me take nufi ni kuma? in yi hakuri? meye haɗi na da yin hakuri?ita ke da wannan amsar dan haka na dago na ce

"Hasina go straight to the point coz na fara gajiya da wannan abin da kike yi yana daɗa karya min zuciya"babu wanda ya ce ƙalla sai ido

"Yaya kabeer yaya falmata is dying for you tana ƙokarin kashe kanta a kan ka duk ranar da ta gan ku kai da yaya Aisha wuni take yi tana kuka ƙarshe sai ta sha magani kafin ta yi bacci a halin yanzu ma jiya nake jin conversation din su akan rashin bin dokar da take yi" tana kuka ta karasa da cewa "zuciyar ta ya buga for the first time kuma dr ya bata dokoki amma bata bi"

Salati aka dauka ban da ni da na yi sumar zaune wai ni Aisha yau kaddara ta ce take ta zuwar min min a haka koh dai menene hakan ƙawata babbar aminiyata ke son hallaka kanta akan masoyin da nake so kuma ta kasa sanar da ni inalilahi wainilaihir raji'un duniya me yasa kika min irin wannan juyi just few days da dawowa na ina murna ace yau ɗaya komai nawa ya juya haka kukan ma ƙin zuwa yayi dan zuciya na ya rigada ya bushe kawai sai jin hayaniya nake yi na ɗaga kai na ashe Khadijah ce ta shigo palon ni nama manta tare muka tafi falmata ce a sume ga salma da ke faman kuka kamar me yaya kabeer kuwa daskarewa yayi me zai ce yaya Ibrahim shiru yayi ya ƙurawa falmata idanu daga ƙarshe ma barin wurin yayi ya je ya ɗebo ruwa ya yayyafa mata dan shi har a lokacin yana jin kamar ƙarya hasina ta faɗa ko da ta farfaɗo kasa kallon kowa tayi sai ta yi sauri zata fita a 360 na sha gaban ta na ce

"Babu inda zaki tafi har sai kin sanar da ni gaskiyae lamarin nan falmata"

Itama bata san hakan zai faru ba sai kawai ta saka min kuka ta ce
"Aisha pls let go off me"

Kallon tsab na mata na ce
"Should i consider what hasina said as the truth"??

Zamewa ƙasa tayi tana kuka tana cemin in yafe mata ta cuce ni ta kasa haramtawa kanta abin da yake mallaki na ita yanzu mutuwa kawai zata yi da sauri ta tashi zata fita a ɗakin na rike ta tana turjewa akan ita in bar ta she wants to die sai da na sauke mata mari mai zafi sannan ta dawo hayyacin ta tana kuka na rungume ta ina kukan nima dan sai a yau nake sanin abin da ake kira da son maso wani wasu har biyu sun min ashe haka suka ji da ba su same ni ba ga falmata nan ta faɗa a wannan rariyar itama sai a ranar nake jin zafi da tuna kalmar sadaukarwa wani abin da yake so mudim ya fi ka buƙatar abin nan ashe haka falmata ke fama da raɗaɗin son da taje yiwa yaya kb ni da yau kadai ne na kasa controlling kaina sai ita da ta kai sama da shekaru huɗu tana jinyar zuciyarta har tana ƙolarin rasa ranta wa ya fi bukatar yaya kabeer a tsakanin mu in zan lura..

"Falmata me kike tunani da huh?na mata tambayar ina mai ɗago ta
"A jin ki har akwai wani abu da zaki nema ne in hana miki kokuma kina ganin har akwai abin da kike da ikon samin shi ne a wuri na amma in hana ki menene ma'anar so da yarda da juna da muka yi menene ma'anar amintakar mu in har ke zaki iya sadaukar min da rayuwar ki ta ɓoye son da kike yi ma yaya kabeer ni mai zai hana ni yi miki abin da kike so huh"??

A hanzarce ta ɗago tana kallo na tana girgiza min kai alamun a'a dan ita ta san rayuwar ta bai da wani sauran amfani koh da kuwa na yafe mata soyayyar da nake yiwa yaya kabeer ne toh rayuwar auren ta bazai yi maraba da ta aunty mufeedah ba toh me yasa hasina ta faɗi wannan boyayen sirrin nata

Nima girgiza mata kai na nayi ina kallon yaya kabeer kallon so da ƙauna haɗe da kallon ban kwana dan har abada bazan iya auren wacce aminiyata ke kauna ba shima ni yake kallo idanuwar shi duk sun yi ja sun rine kamar garwashi yana jiran ya ji me zan ce

Gaban shi na isa na ce

"Yaya kabeer ina so in nemi wata alfarma a wurin ka kuma kar kace min a'a"ido cikin ido yace min
"Ina jin ki sweetgirl muryar shi na rawa dan tsoro ya fara kama shi nikuma jin sunana da ya kira ni da shi sai na ji zuciya ta na neman karyewa amma na dake na share hawaye na na cigaba

"Ga amanar aminiyata mai kauna ta tsakani da Allah nan na baka na baka ita har abada ka aure ta ka yi rayuwar da ka daɗe kana mafarkin yi da ni da ita ka goge ni da sunana da kamannina a zuciyar ka da kwakwalwar ka ka manta ka taɓa son wata wai Aisha Murad ka auri falmata na bar mata kai halak malak in ka aure ta zan fi kowa murna da farin ciki kin auren ta da zaka yi kuwa shine zai tabbatar min da cewa ban da muhimmanci a rayuwar ka koh da chan ka amince zaka min wannan alfarmar"??

Sai ga hawaye a idanun yaya kabeer abin da ban taba gani ba koh da wasa yana son girgiza kan shi alamun a'a amma nima girgiza nawa kan nake yi alamun kar ya ƙi ni kuka shi kuka karshe dai bayan doguwar tunane tunanen da yayi da girmar kaunar da yake min ya ce

"In dai auren wannan yarinyar shi zai kwantar miki da hankali sweetgirl na amince amma ki sani duk halin da zan shiga nan gaba kece sanadi kuma har in daina numfashi bazan daina kaunar ki ba Aisha"kaiwa nan ya fita ya bar gida gabaɗaya

Nima barin falon na yi na wuce ɗaki na na saka key tuni na zauna a ƙasa na saka kuka mai sautin gaske yi nake yi kamar zan karar da hawayen gabadaya saboda the more ina kukan the more ina samin saukin nauyin zuciya ta buga ƙofar ake yi kamar za'a ɓalle ta amma na ƙi buɗewa haka na karasa ranar ina cikin ɗaki ina kuka yayin da salma ke rarrashin falmata dake blaming kan ta akan ita ce silar faruwar komai Khadijah dai tafiya gida tayi akan gobe zata dawo dan dare ya fara yi ana haka sai hasina ta kuma tono wani sirrin wato son da ummi ke tuwa yaya Ibrahim abin al'ajabi baya ƙarewa har dare yayi salma na gidan mu falmata dai ta tafi dan bazata iya cigaba da ganin halin da nake ciki ba yaya Ibrahim kuwa kwanar kuka zaune yayi shima dan shi bai dau maganar ummi a ka ba ta rasa masoyiyar shi yake..

**********************
8:30Am na fito cikin shiri na na doguwar riga da takalmin wage na maka shades a idanuna baka wuluk dan idanun sun kumbura na fito janye da trolley ɗi na tun jiya na yi video call da Abbu da ke ƙasar turkey dama a kwana ta biyu da shagalin bikin ya sami kirar gaggawa ya tafi turkey ɗin yin wata meeting na sanar da shi komai kuma ya bani kwarin gwiwar cigaba da kyautata abu mai kyau a zuciya ta na sanar da shi cewa zan koma washegari yace min zai zo min visiting in na koma da haka na hharhaɗa kayyayaki na tun hutun bai kai ko ina ba na fara shirin komawa

Koh da na fito ɗakin ummi na leƙa tana bacci na ajiye mata note na ƙara gaba salma dake bacci na ajiyewa note ɗin itama na shiga ɗakin yaya Ibrahim na same shi yana zaune gaya mai komai na yi nace ya kai ni airport ba bata lokaci ya kai ni muka rabu jirgin mu ya lula zuwa ƙasar Egypt ina ciki ina bawa kaina kwarin gwiwar manta komai kafin in gama school ɗin in dawo gida gabadaya na ji mamakin dauriya da dakewar da na yi na hana zuciyata yin abin da take raya min wai nice Aisha na sadaukar da masoyi na wa aminiyata saurin kawar da tunanin na yi dan na rigada na bayar bana so ladan da zan samu ya wuce ni da haka na jingina kai na da kujerar na lumshe idanuna ina adduo'i .................

*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow@siyama Ibrahim
#vote
#comment

Continue Reading

You'll Also Like

186K 9K 51
My name is Alex Cruz, I'm a omega, so I'm just a punching bag to my pack. But Emma, Queen of werewolves Sam, queen of dragons Winter, queen of vampi...
64.6K 5.1K 40
Dad! Mi... ji.. n... UMAIMAH.. ne! ****ta Yaya musaki yasan soyayyah? Wannan wani salon munafurcin ne!
83.2K 6K 67
a love story, this is a love triangle between 4 lover's.
434K 18.1K 123
SYPNOSIS Reading Purifying Love made Rachelle D'magiba feel very insulted. The ending that the author had written didn't go well with her expectation...