🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒

Autorstwa SiyamaIbrahim

39.1K 2.4K 94

It's all about love betrayal of trust and bargaining Więcej

Page 11
Page 1
Page 2
Page 3
Page 4
Page 5
Page 6
Page 7
Page 8
Page 9-10
Page 11
Page 12-14
Page 15-16
Page 17-18
Page 19-20
Page 21-22
Page 23-24
Page 27-28
Page 29-30
Page 31-32
Page 33-34
Page 35-36
Page 37-38
Page 39-40
Page 41-42
Page 43-44
Page 45-46
Page 47-48
Part 49-50
Page 51-52
Page 53-54
Page 55-56
Page 57-58
Page 59-60
Page 61-62
Page 63-64
Page 63-64
Page 61-62
Page 65-66
Page 67-68
Page 69-70
Page 71-72
Page 73-74
Page 75-76
Page 77-78
Page 79-80

Page 25-26

544 47 0
Autorstwa SiyamaIbrahim

🍒🍒SOYAYYA MAI GARƊI🍒🍒*
       _(Pure Love, Revenge and bargaining)_

  By
   *Siyama ibraheem🍒*
Wattpad@siyama Ibrahim

'''DEDICATED TO SURAYYAHMS'''🐈

2⃣5⃣➖2⃣6⃣

Kalau muka sauka a filin saukar jirgi ta ƙasar Egypt inda daga nan na wuce zuwa taxi da zai kai ni har masauki na wanda da taimakon yaya Kb aka shirya min ƴar ƙaramar safe apartment dina babu ruwa na da komai daga school sai gida har bakin ƙofar aka sauke ni na biya ƙudin na wuce ciki dan dama akwai wanda nake ta communicating da shi shi ya kwatantawa mai taxi din har muka iso a wun wata mata na ƙarbi makulin gidan na shige..

Wanka na yi na bi salolin da ake bi na daga bisani na fiddo da soyayiyar miya ta na juye na shige kitchen din na dafa noodles shaf shaf na juye saura a kula na bar shi a kitchen din na fito da na plate din na zauna a falon ina ci sai da na yi nisa har na kusa gamawa na dau wayata na saka sabuwar sim dina ta ƙasar da na siyo a hanyar zuwar mu gidan na duba nambobin su Abbu shi na fara kira muka dan taba hirar mu ya dora da nasiha da jan kunne dan ya amince da tarbiyata shi yasa ya bar ni in ba haka ba sai dai in hakura har yake cemin da ummi ce babu inda zai ma bari ta tafi haka muka rabu na kira kawaye na muka sha hirar mu bai musu ba suka ce min anjima kafin in kwanta in yi connecting mu yi video call dan suga environment din da nake da toh na amsa musu muka sauke wayar ajiyar zuciya na yi kamar mimtuna goma sai na kira yaya kabeer kashewa yayi ya kira ni mun dade muna magana kamar kar mu rabu haka shima muka rabu sa shi akan anjima zu yi video call da shi..

Fita na yi na ɗan zaga gida ba babba bane amma akwai tsari da kyawun kallo two bedroom flat ne da toilet sai kitchen yar daidai chan bayan gidan akwai swimming pool da ƴar karamar garden ni mamaki ma abin ya bani ganin ni da nazo karatu har wani gidan hutu aka samo min Allah ya sakawa yaya kb da alkhairi dan shi ya daɗa convincing Abbu akan zuwata kasar yin karatu...

Chan cikin dare bayan na idar da sallah ne na zauna shiru though na saba da kaɗaici amma ban taɓa yin nesa da gida irin haka ba ya zanyi ni na ji na gani ai ina cikin wannan tunanin na ji ƙarar waya ta dauka na yi sai na ji muryar yaya Ibrahim

"Angon falmata da ummi" sai yayi shiru kafin yace me kike nufi da angon falmata da ummi kuma?

Shiru nima nayi dan subul da baka na yi sai na yi saurin canza topic din na ce
"Yaya Ib ya makaranta duk kewar ku ya ishe ni wallahi" dariya kawai ya min ya ce haka zan saba mun ɗan taɓa hirar mu kafin mu ajiye wayar kamar jira na yake ina ajiye wa na ji kira dubawar da zan yi na ga yaya kabeer ne murmushi na yi na janyo hijabi na na saka dan banda towel din da nayi wanka da shi ban saka komai ba har ta kusa tsinkewa na yi saurin dauka na saita a kan teburin karatu na

"Haba sweetgirl tun dazu fah nake ta kiran ki amma baki daga ba koh duk a cikin jan ajin ne"

Dariya maganar tasa ta bani dan haka na dara kaɗan kafin in tsagaita na ce mai
"A'a wallahi yaya na yi hakuri ba zan kara ba forgive me"

Haɗe girar sama da ta ƙasa yayi wai akan me zan na ce mai yaya bayan na san ya hana ni kiran shi da yaya wata dariyar ya daɗa bani dan haka na kuma yi a karo na biyu
"Wai toh me kaje son ina kiran ka da shi ne yay..."sai kuma na yi saurin rufe baki na dan kalamar yaya da ta so fito min a bazata shima dariyar na bashi amma murmushi kawai yayi ya kyale ni dan ya san sunan da ya bani in rinka kiran shi ba zan taba amfani da shi har sai ƙila mun yi aure shiyasa shima bai damu ba sai muka cigaba da hirar mu a nan yake min bayanin in tabbatar da gobe na gama komai nawa a school saboda next day din in fara attending lectures di na yace min wannan mutumin zai taimaka min godiya na daɗa yi mai muka yi sallama na kara saita wayar na kira salma a lokacin hira suke yi a sashen su falmata dan haka tare suka yi receiving call din da murna muka taba hirar mu har tsokana ta suke yi wai matar babbar yaya ta taho ƙasar larabawa har wata hijabi ce da ni a cikin daren nan ni dariya kawai na musu dan in har zan biye musu toh ba zan yi bacci ba ga shi na gaji maruka ina son rintsawa sun lura da hakan sai suka min saida safe muka rabu saka wayar nayi a chargi na cire laptop di na na ajiye a bedside drower kashe light din na yi na jawo duvet na tofa adduo'i na kwanta da gefen dama daga nan sai bacci..

5:45 am na tashi na duba gefe na kunna light da sauri na tashi na watso ruwa na yi alwala na tada sallah ina idarwa na wuce na hada breakfast mai sauki a kitchen din nayi na wanke kayan da nayi amfano da su na fito zuwa falon na kira lambar mutumin d ban san sunan shi ba ringing uku ya daga muka gaisa na mai bayanin yanda muka yi da yaya kabeer ya ce mu hadu a makarantar by 9 godiya na mai na kara kimtsawa na haɗa komai a jaka ta na fito dan dama doguwar riga ce a jiki na peach colour sai na dora karamar hihabi peach na rufe kofar na tare taxi muka tafi school din..

Komai da ya kamata ya kammalu ya kammalu mun ajiye akan gobe zan fara attending classes di na godiya na mai sosai muka tafi straight gida na wuce it was already 2pm so yin komai nayi na kira yaya kabeer na mai bayani daga shi sai na kirawo Abbu na sanar da shi shima sai su salma daga haka na kwanta dan a gajiye nake sosai ban farka ba sai huɗu saura sallah na yi da na idar na yi wanka na shitya cikin simple gown grey colour na yi rolling mayafi shima grey na saka wage shoe na fito na ɗan zaga wuraren da muka wuce ɗazu kafin mu tafi makarantar sai shida da rabi na dawo duk inda na tafi na dau hotuna na turawa yaya kabeer da aminaina..

As early as 6am na shirya na dau karikitai na sai makaranta saboda ina so in san lokutan lectures di na in case zan yi scheduling activities di na bin direction din department din mu na yi na shige hall din ba daɗewa aka fara shigowa har dai aka taru duk fararen fata nake gani ni kadai ce bakar fata sai chan da aka fara introduction ne naji wata ta ce sunan ta Khadijah Alhassaan sai na waiga da sauri na ware idanuna ina duban inda zan hamgo ta chan na tsinkayo muryar ta tana cewa
"From Nigeria"

Ƴar kyakyawa doguwa fara da ita ga iya daukar wanka haka nima na fadi na wa sunan da ƙasar da na fito itama sai ta kai duban ta gare ni kafin mu haɗa idanu ta sakar min murmushi nima na mayar mata lectures mu ka yi a karshe aka ce mana next week zamu fara practicals murna kamar me daman na matsu in ji yaushe zamu fara practicals din nan..

Mun fito kenan sai ga Khadijah ta taho gare ni tana min murmushi nima ina mata sai ta ce min
"Yar kasar mu ya kike a wani gari kike"ni dariya ma tambayar tata ta bani duk a lokaci ɗaya sai na dan dara nace mata

"Daga Abuja nake a wuse zone 2"da sauri ta ce haba da gaske nima ai ƴar Abj ce saidai a zone 4 muke ya aka yi bamu san junan mu ba tun kafin mu zo

Dariya muka yi alokaci daya na ce maybe lokacin haɗuwar mu ce bata yi shi yasa ta gaya min inda take da zama nima na sanar da ita inda gida na ya ke muka yi exchanging contacts din juna akan zamu na jin motsin juna har gobe kafin mu haɗu tafiya muka yi kowacce ta tafi hanyar ta..

   ********************

_Turkish University ABJ_

Motar su salma ce ta shigo falmata ce ke jan motar yayin da salma ke gefen ta tana ta faman kyalkyale fuska dan bata gama ba lokaci ya fara hararar ta sai ta fito kawai da zuwan su parking suka yi suka fito ƴanmatan jami'a joude maroon jallabiya suka saka da rolling din su wage suka saka aka maka black speck mai design  fuskar nan ta sha makeup ana taku dai dai sai kallon su ake yi haka suka daure fuska ana cicin magani sai rigima ake zubawa har department din su falmata salam ta raka ta blowing kisses suka wa juna kafin su rabu ita kuma salma ta wuce tata department din lectures ya musu daɗi sai hudu saura suka fito duk a gajiye suke wannan karon salma ce ta tuka motar suka isa gida dakin su salma suka baje a nan aka kawo musu abinci suka ci suka yi sallah wanka suka yi kowacce da towel a kirji ga net cap suka saita wayar falmata aka danna kira zuwa Egypt ni dake kallon wani painting da aka ba mu a matsayin assignment na ji kira dubawa ta na ga ƴanmatan mu ne sai na dauka da sauri na yi positioning wayar na dauka ganin su babu riga na ce

"Yanmatan jami'a ya lectures din ne wai"

"Babu daɗi sweetheart very stressful mun gaji ya naku lectures din"

Nace musu alhamdulilah har ma na yi wata kawa itama a Abj take a zone 4

Sai naga sun ɓata fuska na nemi jin dalili buɗar bakin salma sai ce min ta yi
"Aishon yaya Kb kar dai in ce mantawa zaki yi da mu wai kin yi sabuwar ƙawa mu fah"

Dariya suka bani na dara har da hawaye na ce
"Haba sweethearts babu wacce ta isa ta shigo tsakanin mu ai kun sani ku din na daban ne a rayuwa ta soyayyar ku da kaunar ku mai girma ce a gare ni aure koh aiki na a rayuwa ba za su taba raba mu ba

Sauke numfashin gamsuwa suka yi kafin daga bisani muka yi sallama du juna muna masu jin kewar junan mu...

*****************

Time has been passing kamar kiftawar idanu mun share uku da rabi a kasar Egypt muna fama da karatu suma su salma na chan na ja yayin da yaya Aqeeb da yaya Ibrahim suka gama karatun su sun dawo gida yaya Ibrahim na serving a Ikeja yaya Aqeeb da guzurin matar aure ya dawo babu daɗewa aka yi fixing ranar auren su akan an debi watanni 4 masu zuwa yaya umar kuma sai bayan watanni 7 zai gama karatun shi koh da labari ya iso min murna na taya yayan namu da shi salma da ta rasa ya zata tambaye shi akan koh ya yafe soyayya ta bata sami damar yin hakan ba har sai lokacin da aka haɗu wun dinner ta ke ce ma yaya na akwai magana fah in mun gama dinner da murmushi ya ce ok

"Yaya dama so nake in tambaye ka akan maganar Aisha naga ka kawo aunty mufeedah a matsayin matar da zaka aura shin hakan na nufin ka cire soyayyar Aisha a zuciyar ka ne"??

Murmushi mai ciwo yayi kafin ya ce
"Nahh kid sis son Aisha a jini na yake ba zan taba iya rabuwa da son ta a zuciya ta ba sai dai yin auren shine mafita a rayuwata dan bazan iya cigaba da zaman kadaici ni kadai ba maybe marrying mufeedah might decline all those thoughts" kaiwa nan sai idanun shi ya ciciko da hawaye tausayi ya bata dan itama tana son yayan nata haka dai ta yi calming din shi ta bashi assurance din aunty mufeedah zata zamo mishi alkhairi a rayuwar shi ya ɗan ji sauki a zuciyar shi amma jin ta yake yi akan mufeedah zata yaye mai wani abin Aisha jigo ne kuma fitila ce mai haska birnin zuciyar shi kenan in fitila ta fashe hasken da yake fitarwa zai dauke duk wani abin haskawar da za'a kawo dan ya haska ba zai taɓa haskawa ba irin fitilar nan toh ta yaya ma zai haɗa soyayyar Aisha da wata noway sai dai kawai a yi sha'ani..

Su Abba sun yi zama har an saka ranar bikin su salma da yaya umar dan umma ta matsawa Abba ganin salma sai buɗewa take yi kamar ana hura ta itakuma tsoro ta ke ji kar jikin ta ya ruɗi maza marasa imani da tausayi su je su mata aika aika a bata mata tarbiyar da ta daɗe tana yi wa ƴar ta reasoning da maganar ta Abba yayi suka yi maganar da su Baba a ka tambaye su salma da gudu ta ce ma umma ita ta yarda koh kunya babu yaya umar ma amincewa yayi toh da haka aka yanke date akan watanni takwas masu zuwa that is bayan yaya umar ya gama karatun shi da wata ɗaya in ya so sai yayi seeving din shi da auren shi ita kuma at then zata shige ajin ta na karshe kenan ita da falmata yadda aka yi haka salma ta mayar min nace lallai muna da shagulgula a jere ga na yaya Aqeeb bayan watanni uku kuma ga na babbar kawalli murna kan murna

_Tuesday 4:35pm_

Zaune nake akan rest chair da ke cikin garden din gida na earpiece ne makale a kunne na gefr guda ga coffe cup da kayan zane da nake son karasawa wata magazine ce a hannu na ina ta karantawa abin da ya fi bani al'ajabi shine sample din painting din nandai da na daɗe ina cin karo da shi sama da shekaru masu yawa ban san sunan mammalakin wannan zane ba dan ban tsaya dubawa ba instead nayi saurin daukar laptop dina na yi searching company name ɗin full details ya fito min da shi akan company din da mai company din na daɗe da ganin magazine din a hannun Khadijah amma koh da wasa ban taba karba in karanta ba sai dai in yi glancing a cover din zuwar ta gida na a jiya da yamma bayan mun gama team work din da aka bamu sauran sun tafi ni da ita muka rage toh ta shiga yin wanka dan ta ce min she was exhausted mun saba sosai sabo irin na yarda dan har dare takan kai min muna hira da ita in mun gama ayyukan makaranta wataran ma if she is less busy takan kwana a gida na in bamu da lectures din safe.

Saving page din na yi na cigaba da jin abin da ake cemin a waya ummi ce take min ɓuruntun ta da ta saba na yau da kullum wato maganar yaya ib chan da ta she ni nace

"Ummi am very busy kuma am stressed out already ki bari gobe zamu karasa huhhn baby sis"kitt na kashe na yi leaning akan rest chair din ba komai nake hasasowa ba illah conjunction din da zan yi da mai wannan zanen in na yi setting nawa painting company din dan ina bala'in son in ga nice mace ta farko a arewa da ta fara kafa nata painting din ba tare da aiki a karkashin wani ba koh wani company so nake a san cew mata can do much more what the men are capable of doing ina so sunana ya fita ya zaga koina a fadin duniyar nan saukin haka na gani sabpda Khadijah told me that mammalakin wannan zanen family friend din su ne and that akwai soyayya mai karfi a tsakanin ta da ɗaya daga cikin family members din wanda son da ta ke mai ya sakata zuwa nan kasar karatu kuma karatun ma na painting saboda shi din painter ne as well ta bani mamaki dama mutum yi abu saboda wani ba dan kan shi ba ni ina da passion ma painting abin da ya rinjaue ni kenab har na fito zuwa wannan duniyar dan in koya kuma in kafa tarihi mai karfi...

Ba ni na bar wurin ba sai da aka kira sallar magrib na shige na yi wanka na sauya kaya na zuwa na bacci dan ina fashin sallah daga nan masoyi na na kira muka sha video call din mu kafin ya min sai da safe...

_Months later_

   Mun yi jarabawar mu ta karsgen zango wanda ya zo daidai da bikin yaya Aqeeb Khadijah da take shirin zuwa gida itama na yi inviting din ta ta min alkawarin zuwa zan rigata dawowa dan ita sai ta biya ta cyprus kafin ta dawo so tafiyar mu ta banbanta zuwa lokacin mun rigada mun fara zama abin kwatance saboda mu mata daga arewa iyakacin mu kenan ni da Khadijah sai dai maza biyar da ke institution din waɗanda muke mutumci da su sosai sai dai christians da suka fi mu yawa amma a musulmai mu bakwai ne kawai sauran ma a cikin mu ba daga nigeria din suke ba wasu daga wasu kasashen suka zo amma indigenes din nigeria ne kusancin mu da su bai taɓa saka ni kuskuren karbar soyayyar koh daya daga vikin su ba dan yaya kabeer di na ya wuce matsayin in haɗa shi da wani son shi daban yake a zuciya ta..

  *******************

12:30pm falmata, salma, yaya kabeer, hasinah da yaya umar

Su suka zo filin saukar jirgi dan dauka na zuwa gida da murna muka rungume junan mu sai tsiya suke min wai na zama balarabiya ni koh na ce musu sun zama ƴan turkiya muka yi dariya gyaran murya muka ji yaya kabeer ne juyawa nayi sai na ga yana cin magani wai na manta da shi dariya ya bani sai na koma kusa da shi ina gaishe shi sai da ya ja min aji kafin ya amsa abin kallo muka zamowa masu tafiya duk sai aka rinka kallon mu kawaye na sai suka saka mana wai miji na fushi da matar shi juyawa na yi na ce su kiyaye ni sai suka kara saka mana dariya shima a wannan lokacin dariyar ce ta kufce mai ganin irin fuskar kyanwar da na saka wun yin maganar a nan ne ya ce min
"Welcome home sweetgirl" dariya nayi ina sunkuyar da kai na ƙasa saboda na ji kunya ganin yaya Ibrahim a wun

Bayan na yi wanka na daɗa kimtsawa na fito zuwa wun cin abinci inda na tarar da dukkan abokan arziƙi a wurin wato family and close friends mun ci mun ƙoshi an min tambayoyi har na gaji daga ƙarshe dauke min hankali yaya kabeer yayi muka fita zuwa bayan gidan inda muka baza soyayyar mu san ran mu har sai da aka fara kiran sallar magrib shi ya tafi massalaci ni na shige ciki na yi sallaj na ƙara kwaliya dan so nake in farantawa yayana rai da kwaliyata shi yasa na dau lokaci ina pente fuska ta har tsokana ta suke yi na musu banza

Bayan sallar isha'i ya dawo da sauri na fita ina dariyar shirmen su salma dan itama ta kusa fita wun yaya umar kasancewar ta gaya mai a nan gidan mu zata kwana ita da  falmata dan babbar kawa ta dawo ya ya iya mata shima kuma kamar dole ba zai iya tsallake kwana ɗaya ba tare da ya ganta ba koh a gida haka ake musu tsiya akan ba sa jin kunyar yin soyayya Abba dai biye mata yake yi ya ce ai ƴar gwal din shi ce shi bai son saka ido da haka yake rufe bakin su

Snacks da drinks na ɗora akan karamar tray da cups biyu na nufi rumfar gidan mu inda yaya kb yake zama nayi a daya daga cikin kujerun rumfar na ajiye tray ɗin a saman teburin na daɗa gaida shi amsa min yayi ya kuma tsaya kallo na kamar bai taɓa ganina ba toh eh mana bai taɓa ganina da kwaliya haka ba sai yau tun bayan ranar liyafar mu da ta kasance ranar alkhairi a gare ni ban kara yin kwaliyar da ta burge shi kamar ta yau ba..

Hura mai ido na yi na ce
"Ya kallon koh wata Aishar ce ka gani saɓanin wacce ka sani"?
Sai ya min murmushi yace

"Sweetgirl kin girma sai ki daɗo wayo am happy"
Wato yau na zage a gaban shi ina mai irin wannan tambayar alhalin da bana yi.

Hira muka sha har nake sharing experience di na da shi he was amused ya ji ban taba samin matsala ba tun da na fara karatu na har kawo yanzu he couldn't help it but praise me nima sai na ji daɗin haka har nake rayawa a raina anya zan iya yin soyayya da wani ɗa namiji kuwa bayan yaya kb shi kaɗai ya san yadda nake ji shi ke riga ni furta damuwa ta da shi na fara sanin menene soyayya shi ya koya min yin *_soyayya mai garɗi_* kuma ina fatan cigaba da shimfiɗa rayuwa ta da shi har karshen numfashi na son da nake mai na daban ne ina girmama shi da ganin girman shi killa shi yasa nake mai so wadda bana yi wa kaina..

Bai tafi gida ba har sai da na roke shi da ya tafi saboda dan 9 yayi kuma ina tsoron hanya har fushi yayi da ni wai korar shi nake yi da kyar na shawo kanshi ya amince damuwa na yi da shi ba korar shi na ke ba bayan tafiyar shi na shiga cikin gida na ma Abbu sai da safe a nan yake ce min washegari in na karya in zo yana da magana da ni akan yahaya ne kuma maganar tsakani da Allah ni na ma manta da wani yahaya sai a lokacin da Abbu ya kirawo sunan

  hajiya ummi ana ta shan kamshi dan tun da aka dawo daga airport yayaibrahim ya like ma falmata har ɗazu da taj duba shi waya ta tarar da shi yana yi da falmata abin sai ya cika ta tayi fam ta shaƙa jira take in dawo ta kawo ƙara dan ni kadai ke sauraren ta Abbu har make ta yayi rannan da ta kurawa yaya ib ido o sai da ya ja mata kunne kafin ta sarara da irin ƙallon da take mai a cikin jama'a toh ni kaina gudun haɗuwa sa ita nake dan magabar ta a matsayin shirme nake daukar shi

Kowacce chatting take yi sai da na ɗaga murya kafin su dago falmata ce mai ce min lailar majnoon har an dasa aya a hirar yau kenan hararar wasa na mata nace ai in da laila majnoon toh kece ke da yaya Ibrahim dariya ta min kawai chanza kayana nayi zuwa na bacci na zauna a gaban mirror ina goge fuskata saboda kwaliyar da na ma fuskar ina yi muna hira har nake tambayar falmata yaushe za'a saka rana take ce mi ai ba yanzu ba sai nan gaba maybe ma tare za'a haɗa da nawa dariya kawai nayi dan tuno da maganar nu sa yaya kabeer ɗazu da ya zo wai shi fah shekaru sun fara ja kar ya tsufa bai mori auren shi ba ni kunya maganar ya bani sai na kyalkyal shi..

_Week of the wedding_

A rana ta uku da aka fara shagulgulan bikin yaya Aqeeb Khadijah ta zo gidan mu tare muka ranƙaya zuwa federal housing inda daga nan Sheraton muka nufa dan yin shagalin ranar koh da muka isa introducing din su salma na yi mata itama na masi introducing din ta tun da aka fara shagalin nan ban taɓa ganin yaya Aqeeb ba amma salma ta ce min na yau zai zo saboda kamu ne..

Mun sake jikin mu muna jirar shigowar ango dan amarya ta daɗe da isowa shiru har aka kai rabin Shagalin nan babu yaya Aqeeb abin ya fara ankarar da iyayen mu da jama'ar taron kiran duniyar nan an mishi amma ya ƙi dauka

Kusan shida na yamma duk an bazu neman shi sai ga motar shi ta shigo harabar hotel din a karkace ya yi parking ya fito ya dumfaro hall din duk juyawa aka yi ana kallon shi saboda a matuƙar buge yake yayi tatil har wari warin giyar yake yi waɗanda ke kusa da shi na iya agakar warin giyar a buge ya fara magana kamar haka.............

_Don't miss out the next update because d real story is about to begin amma yawan comments din ku shi  zai yi determining whether in warware labarin kokuma in bar shi_

Happy friday
*_🍒S,Ibraheem🍒_*
Follow @siyama ibrahim
#vote
#comment

Czytaj Dalej

To Też Polubisz

83.2K 6K 67
a love story, this is a love triangle between 4 lover's.
40.4K 901 9
I am Elizabeth Swann's older sister. I was the only one who ever fell for Norrington. This is the story of how we came to be. Our story is one of lov...
443K 24.5K 166
Featured at Wattpad's Editor Picks list. Luna, an overworked Engineer, had an unfortunate end. Her spirit, feeling wronged, fights Death for a second...
1.4K 423 36
A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishada...